Showing 51001 words to 51592 words out of 51592 words

Chapter 18 - SHAUKIN SO BOOK COMPLETE By MRS SADAUKI .pdf

23 May 2025

3395

waje sai Aliya ta ƙara mayar da mu can wurin nan mai datti.
“Yanzu ya za a yi kenan?” Lubna ta tambaya.

Aliya ta ce “mafita guda gare mu a yanzu shi ne mu je can gidansa”

Kamar wacce aka tsikara na ce “na san gidan” duk suka kalle ni da mamaki,amma tun da abin
da suke so ne kawai ba su tambaye ni ta yaya ba sai muka ɗau taxi ni ce na dinga nuna masa
hanya har muka isa gidan.


Bayan mun sallami mai taxi muka fito muka yi cirko-cirko,unguwar tsit take sosai ma na yi
mamakin ta yadda aka yi Meelat har ta iya ganin maƙwabtan Alhajin.

Aliya ce ta soma juya hannunta mai power ta ɓalle kwaɗon da aka rufe gidan da shi,su biyun
duk suka shige ciki yayin da ni kuma na tsaya ina kallon wata matashiyar budurwa wacce ke
zabaya tana leƙena ta wata can saman benen ɗaki.

‘Wace ce ita kuma waccan mai farar fata kamar fulawa?’ na tambayi kaina a zuci,ban kai ga
samo amsa ba na ji kururuwar su Lubna daga can cikin gidan.A guje na nufi ciki sai na tarar
suna gurmuzu su da wani gogon Biri duk yadda Aliya ke da power ta kasa tsayar da shi domin
shi ma an tsafe shi.Abun mamaki ina shigowa sai ya tsaya cak tare da zubewa ƙasa yana wani
irin abu kamar yana gaishe ni,ƴar kallon-kallon muka fara yi mu ukun .

“Haule ke ma irin wannan protector ɗin gare ki? Na ga duk jikinsa yayi sanyi” Aliya ta yi min
tambayar da sam ban ma gane mene take nufi ba hakan yasa na share ta na ce “ga ɗakin
akwatin gawar nan” na nuna musu shi da yatsa sai suka nufi ƙofar yanzu ma Aliya ce ta buɗe
ta. Sai bayan sun shiga na take musu baya ina mai waiwayen Birin da har zuwa yanzu yana a
yadda yake.

Kiciniyar buɗe akwatin suke amma sun kasa,don power Aliya ma ta ƙi yin aiki.Sai na zo na
kama musu amma ta ƙi buɗuwa,Lubna ta ce “ina ga akwatin nan jini ne makullin buɗe shi”

Duk sai muka kalle ta,kai ta jinjina ta ce “wannan tambarin Family ne” ta nuna wani logo da ke
jikin akwatin.

“To jinin wa za a tsaga?” na yi tambayar.

Aliya ta ce “in dai haka ne da na Lubna za a yi amfani duba da ta taɓa zama cikin ƙungiyar,na
san har zuwa yanzu zanen hannunta bai goge a rubutun da suka yi ba” sam ba mu yi tunanin
wannan babban kuskure ne za mu tabka ba,haka Lubna ta tsaga yatsanta ɗigon jininta ya ɗiga
sau uku a jikin tambarin nan take akwatin ya soma buɗe kansa a hankali wari da ɗoyi yasa suka
ja baya,yayin da ni kuma na toshe hancina tare da matsawa ina leƙen akwatin.Yana gama
buɗewa na ji an tunkuɗa ni ciki na faɗa yayin da kuma akwatin ya rufe ruf da ni a ciki.Cike da
tashin hankali na soma kiciniyar buɗe shi amma ya ƙi yi,ina jin muryar Aliya kuma na cewa
Lubna “don me kika yi haka? Yanz...” ban ji ƙarashin maganar ba sakamakon ƙanƙame ni da
gawar ta yi tana yi min maganar da ta birkita lissafina.Daidai nan free page ya ida in kina son ci
gaba sai ki tura 500 via2670215530
ZULFAU YAHAYA
ECOBABK sai ki turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822

Yanzu nake rubuta shi Ni ma banda complete in kin biya group ne zan saka ki
06.Apr.25

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login