Showing 15001 words to 18000 words out of 51592 words

Chapter 6 - SHAUKIN SO BOOK COMPLETE By MRS SADAUKI .pdf

23 May 2025

3394

sau da
ƙafa wannan yasa ta ciri tuta gun malam Nur har ya faɗa cikin kogon sonta ba tare da ya sani
ba.



Tun safiyar yau Nazifa ta tashi da wata irin kasala da zazzaɓi,tun tana daurewa har ta kasa
hakan yasa ta nufi part ɗin Sappa.Ƙwanƙwasa ƙofa ta yi amman ba'a amsa ba hakan yasa ta
cigaba da bugawa da ɗan ƙarfi,jin an buɗe ƙofar yasa tayi saurin ɗago kanta Sappa ce sanye
da rigar bacci iya cinya.Hamma ta yi ta kalli Nazifa ta yamutsa fuska tace "yaaa lafiya irin
wannan dukan ƙofa?"
"Banda lafiya ne"Nazifa ta bata amsa kamar za ta yi kuka "to sai aka yi yaya? Ni na ɗora maki
ciwon ne da za ki wani kwaso jiki ki zo gaya min?"da mugun mamaki Nazifa ke kallonta kafin
tace "ki kira min shi ya kai ni asibiti"kallon baki da hankali Sappa ta watsa mata tace "barci yake

kuma saboda wata banza ba zan tada mijina ba"gammm ta rufe ƙofa ta bar Nazifa sake da baki.


Ganin tsayuwar ba ta yi mata yasa ta koma ɗaki,kuɗi ta zuba a jaka ta kulle ɗaki ta nufi bakin
titi.Ba jimawa ta samu abun hawa asibiti Agaji ta tafi bayan ta ga likita yayi mata tambayoyi,nan
yayi ƴan rubuce-rubuce ya bata takarda ta sawo alluran da za'a yi mata ta dawo .
Allura ruwa ya saka mata dandanan barci ya ɗauke ta ,ko da ta farka ƙarin ruwan ya ci rabi.Text
ta yi ma Samira ba jimawa sai ga ta tazo, result ɗin likitan ya shigo ya bata tare da yi mata
congratulations.
Cike da murna Samira ke karanta farar takardar da sakamakon ya nuna Nazifa na ɗauke da ciki
na tsawon wata biyu.......




Please share
[21/05 11:57] MRS SADAUKI: *SHAUƘIN SO*


```LoVe story```


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}


*FCWA*☀️

________________________


Page 15-16


Cike da mamakin ganin ta kulle part ɗinta malam Nur ya ciro waya ya danna mata kira,bugu
biyu aka ɗaga tare da yin sallama amsawa yayi yace "ina kuma kika tafi na ga ƙofar gidanki a
rufe?"
"Ina asibiti"ta bashi amsa "asibiti? Shine ba ki kira ni na zo na kai ki ba ? Shine kika fita ba da
izinina ba saboda kin isa da kanki ko mi?"a yadda yake maganar za ka gane cikin zafin rai ne
ya ke yinta hakan yasa Nazifa ta sanyaya murya tace "babyn ka ne ya matsa min tun safe nake
jin kasala ga kuma zazzaɓi shine na zo asibiti sai kuma aka tabbatar min da zaman shi"wata
sanyayar ajiyar zuciya ya sauke a ɗan bayaninta ya gane so take tace masa ta na ɗauke da ciki

"to kuma Naziii shine ba zaki kira ni mu je tare ba?"murmushi ta yi jin ya sauko daga dokin
zuciya tace "dan kar na shiga haƙin ƴar uwata ne shi yasa,ya ne kun tashi lafiya ina
amarya?"bai amsa gaisuwar ba sai tambayar ta asibitin da ta je yayi,tana gaya masa ba'a fi
minti goma ba sai gashi ya zo baki buɗe yana fara'a kamar gonar auduga.

Gaisawa da Samira yayi nan ta shiga zolayar shi kai kace ba malaminta ba ne, fuskar Nazifa
ya shafa ya na jin wani farin ciki na luluɓe shi.
"Mu ga cikin?"ya faɗa can ƙasan maƙoshi ta yadda ita kaɗai za ta ji,kallon shi ta yi ta turo baki
tare da yi masa alama Samira fah na nan.Inda Samira ke zaune ya waiga sai ya ga hankalinta
sam ba ya gare su waya take dannawa hakan yasa ya ɗan ɗaga rigar Nazifa ya shafi mararta
yace "ya aka yi ban gan shi ba?"sake da baki Nazifa ta kalle shi tace "wai mi ba dai cikin
ba?"gira ya ɗaga mata yace "eh mana"dariya ta shiga yi kafin ta tsagaita tace "duka wata biyu
ne fah,kuma har kake tunanin ya fito?"
"To sai yaushe kenan?"kafin ta bashi amsa kira ya shigo wayarsa ɗagawa yayi bakinsa da
sallama sai dai bai kai ƙarshenta ba ya yanke sakamakon jin kukan Maman.



Fita yayi waje yana mai tambayar lafiya "Alhaji ne ba lafiya sai suratai yake dan Allah ko mi
kake ka tawo,ciwon na shi sai tsananta ya ke"Maman ta faɗa cikin kuka

"innalillahi wa'inna ileyhi raji'un"shine kawai abinda malam ya faɗa ya kashe wayar .Komawa
ciki yayi ya shaida ma Nazifa Baba ne bai jin daɗin jikinsa ,nan yayi mata sallama tare da ba ta
kuɗi in buƙatar hakan ta taso.



"Dan Allah Alhaji ka bar min maganar wasiya nan ai ciwo ba mutuwa ba ne,in ka mutu ka bar ni
ina zan sa raina?"Maman ke faɗar haka tana kuka gefenta Balkis ce ita ma tana rera
nata.Sallama yayi basu amsa ba,cikin halin kaɗuwa ya nufi mahaifin nasa wanda ke kwance
tsakiyar falo sai hawaye yake zubarwa. Kansa malam Nur ya tallabo ya ɗora saman cinyarsa yana goge hawayen da ke zuba kan
fuskarsa ,cikin rawar murya yace "Baba mine ne na kuka maimakon addu'a? Ka yi shiru ka bar
zubar hawaye in shaa Allah za ka samu sauƙi yanzu nan zan kai ka asibiti"kai Baba ya girgiza
yace "Nuradeen ciwona ba na asibiti ba ne,abu guda ke damun raina tun shekaru ashirin da
suka wuce shi nake ma kuka domin ban san mi zance ma ubangijina ba duk da dai ba yin kaina
ba ne "cikin sigar rarrashi malam Nur yace "No Baba zafin ciwo ne ni na san babu wani abu da
za ka aikata marar kyau da har Ubangij zai hukunta ka,ka bari kawai na kai ka
asibiti"murmushin takaici Baba yayi yace "miyasa ba zaku fahimce ni ba?zuciyata ciwo take min
saboda nauyin abinda nake ɓoyewa ku bar ni dan Allah na faɗa maku ko zan ji sanyi"
"Minene kake ɓoyewa Baba wanda har mu ba mu san shi?"
"Wata babba ƙaddara ce da ta taɓa abkuwa gare ni, Allah ya jarabce ni da son yin mata biyu

amman mahaifiyarku ta hana duk lokacin da na yi yunƙurin ƙara aure sai ta rogaza shi abun
takaici kuma ita ta kasa kula da ni kuma ta hana ni auro wadda za ta ɗebe min kewa.Da ƙarfi da
yaji ta sa na lizimci yin azumi dan kauce ma hanyar ɓata da farko na samu sassauci sai kuma
daga ƙarshe Rahanatu ta shigo rayuwata lokacin da na fara kasuwanci Kano-Kano ina saro
kaya.Tun farko da aure nake sonta amman ganin hakan ba zai samu ba sai sheɗan ya buga
min ganga na bi ruɗinsa ita ma da yake tana sona sai ta biye min wajen aikata kuskuren da har
ƙarshen rayuwata ba zan daina nadama ba.Ɓullowar cikin Rahinatu shi ya fargar damu cewa
saɓon Allah ne mu ke aikatawa mafi muni,kafin muyi tunanin zubar da cikin mahaifanta tuni sun
san da zaman cikin kawai sai suka kira ni da zancen doli sai na auri Rahinatu ko kuma su maka
ni kotu banda wani zaɓi na amince ta na haihuwa aka ɗaura mamu aure..."wata irin shaƙa
Maman ta yi ma Baba tana cewa "au mi?aure fa kace?ai gwara na kashe ka da na ida jin
wannan mummunan labarin"



Dakyar malam Nur ya ƙwaci Baba nan ya shiga tari ya kuma ɗora da faɗin "ai duk laifinki ne ko
ma minene ke kika jawo Allah ya shaida ban aure ki ba sai dan ina son ki kuma ki haifa min
ƴaƴa amma kika biye ma ra'ayinki na yara uku kawai za ki haifa duk gudun kar ki tsufa,saɓanin
Rahinatu da ta haifa min yara ɗaiɗaya har bakwai kuma duk maza"wani irin ihu Maman ta yi jin
abinda Baba ke faɗa,ririƙeta Balkis ta yi yayinda malam Nur ya ciciɓi Baba ya nufi waje
sakamakon jini da ya fara amayarwa .


CLINIC HAMDALLAH tafi kusa da gidansu hakan yasa ya nufi can,taimakon gaggawa suka
shiga baiwa Baba cikin ikon Allah jinin ya bar zubowa.Oxygen aka maƙala masa sannan suka
fito da shi ɗakin hutu,cike da tausayin mahaifin nasa ya zauna gefen gado tare da kamo
hannunsa ya jimƙe.Zantukan Baba ne suka shiga yi masa kai komo cikin kwanya, tabbas dattin
Zina ba zai taɓa gogewa ba ko da kuwa ka tuba akwai wannan tabon amman wani sa'in babu
yadda mutum zai yi da zanen ƙaddara doli sai haƙuri da roƙon Allah yafiya da kuma tsari.


Wasa-wasa sai da aka yi ma Baba ƙarin ruwa wajen sau bakwai a ranar,tun malam Nur na
tsimayen farkawara har ya fidda rai.
Ya na dawowa daga sallah magrib ya tisa Baba gaba yana kallo,wata ƙwalla ce ta zubo masa
wadda ya kasa tantance ta mi cece,ta tausayin Baba?ko kuwa ta farin ciki ce jin ya nada wasu
ƙannai bayan Balkis?.Motsi Baba ya fara yi da hannu gabanin ya buɗe ido,kusa da shi Nur ya
matsa suna kallon juna. Cikin murya ta maras lafiya Baba yace "ka yafe min Nuradeen mahaifinku bai so ya kasance
mazinaci ba,na bar maku mummunan tabon da zai rinƙa bibiyar zuri'arku har ƙarshen duniya sai
dai ka sani ba yin kaina ba ne wlh rabon a yi ne , Allah na gani tun ina ɗan saurayina ban yi ta
ba sai bayan na mallaki hankalin kaina..."ƙyalewa Baba yayi tare da rumtse ido jin saukar
hawayen malam Nur kan fuskarsa.

"Na sani Baba ni shaida ne a kan halayenka,kullum ka kasance mai min gargaɗi daga sharrin
Zina tun kafin na san mi kalmar take nufi har ya kai na santa.A kullum a ko da yaushe ina
alfahari da kai a matsayin mahaifi ka bani tarbiyya ta gari duk da tarin dukiyar da kake da a
kullum kana nusar da ni dogaro da Kai yafi zaman jira,ka nuna min dukiya ba komi ba ce fa ce
dauɗar duniya..."da sauri Baba ya lalubo hannun malam Nur yace "tabbas dukiya ba komi ba ce
dan ba komi take saya ba,akwai kuma ranar da ba tada amfani ga mai ita ka ɗauki darasi a
kaina milliards nawa ke a kwai cikin asusun bankina amman gani a kwance rai hannun Allah
kuma na san ba za ta tsinana min komi ba nan da ɗan lokaci zan barta na koma ga
mahallacina"kai malam Nur ya girgiza yace "no Baba ba za ka mutu ka bar ni ba ka fi kowa
sanin ina sonka fiye da komi, Please ka bar maganar mutuwa na gaya maka zafin ciwo ne
kuma in shaa Allah za ka samu lafiya"


Wani murmushi Baba yayi yace "Allah bai barin wani dan wani ya ji daɗi Nuradeen,ka riƙe ƴan
uwanka ka zamo masu BANGO(MRS SADAUKI )sannan kafin ku raba gado ina so ku baiwa
Suleyman gida guda da wani kaso na kuɗi duk da ya na shege jinina,ka ce ma Mamarka ina
sonta har kullum ta kula min da Balkis kar ka aurar da ita da mutumen banza,ina sonk...."tari ne
yaci ƙarfin Baba yayinda na'urar da ke manne da bango ta fara ƙara tiii-tiii jan layi na fitowa,cikin
azama malam Nur ya tallabo kan Baba yana mai maimata masa kalmar shahada shi kuma ya
na biyawa daidai nan likitoci suka shigo suka tsaya wuri guda suna kallon danjar da ta nuna jan
layi alamu rai yayi halinsa.


Ido malam Nur ya shafe ma Baba yana mai jan zane zai luluɓe shi likitocin suka ƙaraso,gefe ya
zauna yana kallon sarautar Allah shikenan Baba ya rasu "innalillahi wa'inna ileyhi raji'un"shine
kawai abinda ya ke maimaitawa.
Wayar ɗaya daga cikin likitocin ya ara dan tasa ta faɗi lokacin da ya ciciɓi Baba,malam Jabeer
ya kira yana ɗagawa yace "ka zo ka same ni CLINIC HAMDALLAH Allah yayi ma Baba
rasuwa"bai jira ta cewar shi ya kashe kiran.Ba'a ɗauki lokaci ba Malam Jabeer ya
ƙaraso,ambulance aka saka gawa Baba aka kai shi babba asibiti ta Maradi,GIDAN GAWA(MRS
SADAUKI) na sanyi aka shiga da shi aka laya shi kusa da gadajen matattu waɗanda wanda
suka riga mu gidan gaskiya.


Malam Jabeer ke tuƙi yayinda malam Nur ke zaune kusa da shi ,ko gama parking bai yi ba
mutane suka nufo motar dan duk illahirin unguwar ta ɗauka Alhaji Ali Ɗan Masani wanda kuma
shi ne Liman bai da lafiya.Jiki ba ƙwari malam Nur ya fito nan aka fara tambayar shi ya mai jiki
"ciwo ya warke"shine kawai abinda ya faɗa nan wuri ya ɗauki kabbara.

Ya na shiga cikin gida ya ci karo da Maman wacce kabbara mutane ce yasa ta saurin fitowa,ba

ta samu damar tambayar malam Nur ba ya wuce ta ko kallonta bai yi ba Malam Jabeer ne ya
sanar da ita rasuwar Baba.


Tun cikin dare malam Nur ya shiga shaida ma ƴan uwa na nesa da na kusa rasuwar Baba,wasu
tun lokacin suka ƙaraso ba'a ɗauki lokaci ba gidan ya cika da ƴan gaisuwa.
Miss call ɗin mutane ya shiga dubawa rabin su duk na Nazifa ne, text yayi ma Sappa ta zo gida
ba jimawa kuwa ta zo nan ta tarar da tashin hankali,bai cikin nutsuwarsa hakan yasa malam
Jabeer kai shi gida.
Kwance ya tarar da Nazifa tana kwana ledar magani kusa da ita,ɗaukar ta yayi ya maida ta
bedroom sannan ya shiga wanka.Sallah isha'i ya gabatar sannan ya dawo falo ya fara karatun
alƙur'ani,ya jima sosai yana karatun sannan ya koma jan casbi.Ranar nan yadda ya ga rana
haka ya ga dare ko kaɗan kwana bai gigin zuwa wurin shi balle har ya sace shi,ya na nan har
aka yi assalatu yayi alwala ya nufi masjid.Sai bayan ya dawo ya tada Nazifa tayi sallah,wanka
yayi yace ta shirya za su fita.
A ƙofar gidansu ya sauke ta wanda aka share tass kamar ranar sallah, zuciyarta ce ta tsinke ta
waigo ta kalle shi ido ya rumtse yace "fita ki shiga ciki"ba muso ta fita.



Malam Nur tare da wani ɗan uwan Baba su suka yi wankan gawa suka suturtata sannan suka
yo gida da ita aka sallaceta sannan aka kai Baba gidansa na gaskiya.Motoci na dawowa malam
Nur ya fito ya dubi ɗumbin jama'ar da suka zana'izanci gawar Baba,sai a lokacin ya ji wasu
hawaye masu ɗumi kan kumcinsa. Da sauri malam Jabeer ya riƙe shi ganin kamar zai faɗi,suna shirin shiga gida sai ga yaran
Baba na Kano sun nufo malam Nur ashe tun da safe suka zo sam shi bai ma san da zuwan su
ba,jiya dai ya shaida masu rasuwa mahaifinsu.
A tare suka shiga cikin gidan tun daga nesa Maman ta tsinkaye su, tabbas waɗannan sune
ƴaƴan Rahinatu dan kamar su ɗaya da Nuradeen.Yunƙurawa ta yi za ta miƙe Ummu Sappa ta
mayar da ita tana girgiza mata kai,kuka ne ya kubcewa Maman tana jin zuciyarta na suya.



Nuradeen kuwa shi da ƴan uwansa suka shige ɗaki suna rarrashin juna,malam Jabeer na basu
haƙuri tare da yi masu wa'azin mamaci addu'a ya ke buƙata.
Sun daɗe haka kafin su ba kansu haƙuri da juriya su koma waje suna karɓar gaisuwa.



Ranar sadakar uku Inna ta samu ta yi wa Maman gaisuwa da sauran jama'a kafin take komawa
gida, Nazifa wuri guda ta samu ta takure dan bata san kowa ba saɓanin Sappa da ya ke
gidansu.Duk lokacin da suka haɗa ido wani banzan kallo Sappa da ƴan uwanta ke jifarta da
shi,ganin haka yasa Nazifa tafiyarta gida wanda hakan da ta yi ya tunzura Maman tana ta

zaginta a ƙarshe ma bayan mutane sun watse ta yi mata gami malam Nur,cikin son kare
matarsa yace "Maman kin san ba ta jin daɗin jikinta sakamakon juna biyun da take da"cikin
masifa tace "gareta farau yin juna biyu?kawai ta raina mutane ne inda ubanta ne ya mutu ai da
yanzu ka na can kana baƙar wahala da su"malam Nur dai bai ce komi ba ya ficewar shi.



40days Ago


Wani sabon gini aka ɗora cikin gidan malam Nur wanda bai wani ɗauki lokaci ba aka gama aka
yi masa penti,cikin rana guda aka kwaso kayan Maman aka maido su ciki.
Cike da murna dawowar Maman gidansu Sappa ta shiga ta gaishe da Maman nan suka fara
taɓa hira ita da Balkis wacce rabinta duk ɓata Nazifa ne take gun su.Duk hirar da su ke Maman
na jin su da sauri ta ɗago tace "miiii?gori fah?"cike da jin daɗi Sappa tace "wlh Maman gori ta yi
min tace wai ni juya ce ban iya komi ba sai dai na ci na kai masai"ƙyaci Maman ta yi tace "eh
lalle ki ce yarinya ta girma ta isa yanka,yanzu har ta kalli tsabar idonki ta yi maki gori?"kai
Sappa ta ɗaga tace "wlh Maman ba ki san ta raina mutane ba sai kin ga yadda take sa Ustaz
aiki kamar Ɗan da ta haifa,jiya fah wankin kaya yayi mata"


Ƙirji Maman ta dafe tace "ke mi wanki?" jin sallamar malam Nur yasa Sappa ƙyalewa amsawa
suka yi,ya shigo Nazifa na biye da shi a baya.Durƙusawa ta yi tace "ina wuni Maman da fatan
kun zo lafiya?"sheƙeƙe Maman ta kalleta tace "mun zo lafiya?balaguro na yi?Ni da gidan Ɗana
kike min wani sanu da zuwa?oh!nufinki na zo zan takura maki ko baki so zuwa na ba"cikin
girgiza kai Nazifa tace "a'a Maman ba haka nake nufi ba,dama gaishe ki ne na zo na yi"
"To na gode madallah a tashi a tafi"miƙewa Nazifa ta yi tana kallon malam Nur wanda yayi
sumen tsaye.........




Please share
[21/05 12:33] MRS SADAUKI: *SHAUƘIN SO*


```LoVe story```


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}

*FCWA*☀️

________________________



Page 17-18



Cikin rashin jin daɗin abinda Maman ta yi ma Nazifa malam ya juya zai bin bayanta Maman ta
shiga taɓa hannuwa tana salati,tsayawa yayi ba tare da ya ƙara ko taku guda ba ne."A'a je
ka,tafi bi bayanta sai ka tabbatar min kai mijin tace ne"cewar Maman dawowa yayi ya
zauna,kallo guda yayi ma su Balkis

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login