Showing 21001 words to 24000 words out of 27791 words

Chapter 8 - ZARINAT (زرينة) book 1 free page's by zainab dodo.pdf

04 Jun 2025

1870

nayi su dawo saboda baya son taje ta kwana idan taje ta kwana wazai masa
girki? a ina zai ci? Idan ya dawo gida dawa zai zauna suyi fira, husna koda yaushe cikin latsar
waya take idan ma aka mata magana, ga amsar da zata bayar amman sai kaji ta fad'i wani
abun daban hankalin ta nakan waya shida samun kulawar ta sai dare idan sunzo kwanciya
Wannan ne dalilin da yasa bai barta taje ba har yanzu,


Kamar kullum ta kawo masa abinci tare da jan table d'in dake gefensa ta d'aura akai tare da
lemo ta juya zata wuce, dasauri ya rik'o hannunta ta tsaya cak ba tare da ta juyo ba

"Yaushe ne sunan?" yah ansar ya tambaya, mai makon ta basa amsa sai kawai tasaka masa
kuka, janyota yayi tare da zaunar da ita saman k'afafunsa yana bubbuga bayanta alamar
rarrashi, ya kafe d'an k'aramin pink lips d'in ta da ido runtse ido sa yayi tare da furzar da

iska, yasan dalilin kukan nata don bazai wuce tambayar da yayi mata bane ya 'bata mata rai

Zuwa can yace " Shiiiiiiiiiiiiiiii ya isa mana me aka miki? tambayar ki fa nayi ko nace wani abun
ne? Girgiza masa kai tayi, k'ara gyara mata zama yayi saman k'afafunsa tare dasa hannu ya
zagaye k'ugunta

"Rinah" ya kirata ta d'ago ta kallesa " Yaushe ne sunan? " Jibi " ta fad'a cikin muryarda da kaji
kasan kuka take " Ki shirya idan allah ya kaimu gobe sai na kai ki" wani farin ciki taji tace"
dagaske?" Kai ya d'ago mata
Wata kyakkyawar rumguma takai masa tana fad'in " Nagode sosai yaya nagode " Murmushi
kawai yayi tare da k'ara rumgumeta

sun jima a haka sannan ya saketa ta fara k'ok'arin tashi daga jikinsa, rik'e ta yayi tare da fad'in "
Ina zakije?" Zanje ne na zauna " yanzu a tsaye kike ne?" K'asa kawai tayi da kanta ba tare da ta
basa amsa ba, hannu yasa ya d'ago ha'barta batai aune ba kawai taji lips d'in sa akan nata
yana tsotsa, zarinat ko k'auk'auran motsi ta kasa, sai da ya tsotsesu yarda ransa ke so sannan
ya cire, taso tashi amman ya hanata dan ya rik'e ta ne sosai " Muci abinci" ya fad'a " yaya
banajin yunwa.....................................................













Comment and share fisabilillah ♥️


ZARINAT ( ةنيرز )







Mallakar

Zainab dodo✍️












Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number
09046495943
Chart only




_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
T. W. F

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 1️⃣7️⃣

" Kin tabbata?" Kai ta d'aga masa alamar eh, yace" alright to ni bani yunwa nakeji" To " ta fad'a
a sanyaye, ta d'auko filet d'in abincin ta d'ora saman k'afafunta ta d'auki spoon, yayi saurin
fad'in "No! No! No! da hannun ki zaki bani" ba yarda ta iya dole tayi hakan, fried rice ce taji
kayan ciki sosai ga k'amshin dad'in da takeyi ko daga kallo ka kalleta ba tare da kaci ba zaka
gane tayi dad'i

'Debowa tayi ta d'ago hannunta amman ta kasa kai bakin sa ganin haka yasa ya rik'e hannun ta
tare da turawa cikin bakin sa ta zuba masa, yana taunawa yana wani irin juyi dakai idanunsa a
rufe irin na alamun idan dad'i yakai maka dariya ce ta kubce ma zarinat ba shiri ganin abunda
yake yi" Wai kin ci abincin nan kuwa? Kin ji dad'in da yayi? " Hhhhhhh naci " anya kuwa? Ya
fad'a tare da sa hannun sa cikin filet d'in ya d'ebo loma tare da kai bakin ta yace" Ci wannan kiji
" ta bud'e baki ya saka mata

" Kin ji? gaskiya nikam nayi sa a matata ta iya girki sosai allah ya miki albarka " cikin jin dad'i da
yaba mata da yayi tace"Amin yayanah "

Tana basa yana ta yabon girki har ya cinye tasss ta basa lemo da ruwa yasha ta tashi taje takai
kayan kitchen ta wanke hannunta ta dawo falon ta zauna tare da d'aukar remote ta canza musu
channel

" An daina fushin?" yah ansar ya fad'a, murmushi kawai tayi


Yau tara da rabi nayi yayi mata sai da safe ya wuce saboda baccin da yakeji kuma yana son
kafin ya kwana yad'an yi wani aiki cikin system d'in sa


Yana fita itama ta wuce bedroom ta had'a kayan da zataje dasu, tana gamawa ta fad'a toilet tayi
wanka ta shige cikin kayan bacci tayi kwanciyarta ganin baccin yak'i zuwa mata yasa ta janyo
wayarta ta kunna data ta shiga wajen chatting



Yah ansar kuwa yana fitowa 'bangaren zarinat d'akin sa ya wuce yayi wanka, ya d'auko system
d'in sa yayi d'akin husna, yau dai kam anci sa a bata dannar waya tana kwance sanye da wasu
arnayen sleeping dress, kallo d'aya yayi mata ya d'auke idanunsa akanta aiki yake son yi idan
ya ce zai biye mata bazai yi aikin nan ba, ya zauna saman kujera tare da jan table ya aza
system d'in sa

Husna ta saki wani shu'umin murmushi tare da saukowa saman gado ta nufosa tana tafiya mai
jan hankali, tana zuwa kawai ta fad'a jikinsa tare da fad'in " Dear tun d'azu fa nake jiran ka" ya
bud'e baki da niyar yi mata magana kawai ta had'e bakin su waje d'aya, wasu abubu take masa
wanda ya k'asa jurewa kawai ya d'auke ta suka nufi bed, sai da ya samar ma kansa natsu
sannan, bacci ya kaushe su ba tare da yayi aikin ba



Da asuba da yaje masallaci bai dawo ba sai da gari yayi haske,

ya wuce d'akin husna zama yayi tare da kunna system d'in sa ya fara aikin da zaiyi, aikin nada
yawa sai kusan sha d'aya ya gama, yana gamawa kuma ya haye gado ya kwanta bayan husna
da take baccinta tun d'azu shima baccin yayi gaba dashi




'Bangaren zarinat kuwa tana gama sallar asuba ta d'ora musu breakfast d'in da zasu ci daman
already jiya ta had'a kayan ta, tana gamawa ta gyara d'akin ta turare sa ta fad'a toilet ta tsala
wanka ta shirya cikin wani boil lace yellow riga da siket sun mata kyau sosai d'inkin ya amshi
jikinta ya sark'a da abun hannu, ta kashe d'auri mai kyau hannunta manne da tsadadden
agogonta sai zobuna biyu dake sanye a yatsunta ta yafa mayafi ta feshe jikin ta da turaruka tayi
kyau sosai ta fito falo tayi breakfast ta zauna jiran yah ansar,


tun tana dubin agogo har ta daina, kasa hak'ura tayi sai da ta Fito waje ta duba taga motarsa na
nan, Wanda ya tabbatar mata bai fita ba yana cikin gidan, wani 'bangaren na zuciyar take fad'a
mata " yana can tare da matarsa ya manta dake, ciki ta koma tana jin wani abu ya tokare mata
zuciya



Cikin bacci kamar wanda aka tuna ma ya tashi da k'arfi tare da salati ya dubi agogo" innalillahi
wa inna'ilaihi'raji'un wane irin bacci nayi ne haka " ya fad'a yana saukowa saman gado ya tada
husna ya kaushi kayansa yayi d'akin sa a gaggauce yayi wanka ya shirya ya fito ya nufi d'akin
zarinat


Kwance ya sameta idanunta a rufe amman ba bacci take yi ba, kallanta yake tun daga
k'afafuwan ta har sama tayi masa kyau sosai

K'amshin turaren sa da ya addabi hancinta yasa ta bud'e ido ta zubesu a kansa tashi tayi daga
kwance da take yazo ya zauna kusa da ita tare da fad'in " Sorry kinganni sai yanzu bacci ne ya
d'auke ni" Uhmm, kawai ta fad'a tare da Mik'e wa ta kawo masa breakfast d'in sa sannan ta
masa ina kwana ta koma ta zauna nesa dashi
Yana cin abincin yana lura da yarda take wani cic_cin magani har ya gama ta d'auke kayan taje
kitchen sai da ta wanke kayan da yayi amfani dasu sannan ta fito, yace suje ta d'auko akwauti,
ya amsa tare da fad'in " wad'an nan kayan da kika deba fa? Kin san fa da anyi sunah zaki
dawo" ita dai bata ce komai ba har suka fita taja 'bangaren ta ta rufe

Ya aje akwautin da niyar zuwa 'bangaren husna ya sanar mata sun tafi sai gata ta fito tana
sanye cikin wata atamfa doguwar riga ta mata kyau ta k'ara so wajen su " Dear ina zuwa haka?
" Tafiya zamuyi zan kaita ne na dawo " Okay har kasa na fara jin kad'ai ci amman da naji ka ce
dawowa zakayi naji sanyi a raina kasan bazan iya bacci ba tare dakai a gefena ba " ta fad'a tare
da sak'ala hannayenta a wuyansa

Zarinat taja akwautin ta tayi gaba, juyowa tayi daniyar ta kar'bi mukullin mota ta saka kayanta
kafin yazo, taga bakinsu a had'e, da sauri ta juya ta fizgi akwautin ta fita

Yakai kusan 10 mint kafin ya fito, zarinat na tsaye bakin mota haushi duk ya cika ta ga wani
abun da takejin yana taso mata a zuciya, a haka ya fito ya sameta ta cika

Mazaunin baya ya bud'e ya saka akwautin suka shiga yaja motar

Tafiya suke yana mata magana daga eh sai aah kawai take cewa, sun kusa fita gari ya tsaya
wata kanti, ya shiga ya siyo kayan baby's kala goma, ya shiga wata supermarket dake wajen ya
siyo ice cream guda hud'u ya dawo ya tada motar suka ci gaba da tafiya

Ice cream d'in ya Mik'a mata, ta girgiza kai yace " Miyasa? " Haka nan " what is wrong with
you?" Nothing " ya zaki ce ba komai bayan kuma ga damuwa nan a face d'in ki kuma ba haka
na saba ganin ki ba? " Ba komai, ta sake fad'a tasa hannu ta d'an kwantar da sit d'in ta juyar da
fuskarta gefen glass tana kallan ti_ti
Dukan su sukayi shuru bamai cewa komai,

sun yi tafiya mai nisa ya juyo tare da kallanta ya kira sunan ta ba tare da ta juyo ba ta amsa
yace " Shikenan yanzu nida sake cin abinci sai kin dawo sai dai nayita shan lepton " juyowa tayi
tare da fad'in" Yaya kamar ya? Ba matar ka na nan ba? " Hannun ta ya rik'o cikin nashi ya furzar
da iska tare da fad'in" tana nan bata iya girki ba masu aiki ke dafa mata nikuma bazan iya cin
abincin yan aiki ba " Ayyah, ta fad'a cikin jin tausayin sa tace" To yaya kaje wajen ammi kaci
mana " girgiza mata kai yayi alamar aah

" To zan fad'a ma mom a rik'a kai ma " juyowa yayi ya kalleta tare da sakin murmushi ya k'ara
damk'e hannun ta dake cikin nashi yace" Miye amfanin auren nawa idan har zan koma gida na
rik'a cin abinci " Yaya to yanzu sai ka zauna da yunwa" waya gaya miki zan rik'a shan tea" Tea
ai ba abinci ba ne" Zan daure har ki dawo gobe ne sunah ko? " Eh" okay allah ya kaimu " Amin
ta fad'a tare da d'aukar robar ice cream d'aya ta bud'e tasa k'aramin spoon d'in da aka had'a wa
dashi ta fara sha


Kallan ta yayi yace" Nima a bani nasha " To, ta fad'a tare da k'ok'arin bud'e masa d'aya yace"
No wanda kike sha zaki bani ai kinga driving nakeyi bazan iya bama kaina ba " d'iba tayi tare da
kai bakin sa ya bud'e ta zuba masa, idan tasha ta basa haka suka rik'a yi har suka shanye roba

biyu


Sunyi yi tafiya k'arfe uku suka isa gidan, mai gadi ya Bud'e musu gate suka shigo, d'aya daga
cikin ma ai katan gidan yazo ya kar'bi kayan su ya shiga dasu ciki

Afrah na ganin su da gudu tazo ta rungume zarinat tana murnar ganinta, su aunty Maryam na
nan zaune a falo ana mata k'unshi harda yaya bilal na wajen zaune suma sunyi farin cikin ganin
su sosai

Nan suka zauna aka gaggaisa a ka shiga fira kiran sallah la'asar ne ya tada su maza sukayi
masallaci sukuma sukayi d'aki

Bayan sun dawo masallaci zarinat ta kawo ma yah ansar abinci wanda k'anwar aunty maryam
ta girka, bai wani ci da yawa ba ya aje tare da Mik'e wa yayi musu sallama ya fito zarinat ta
rakasa har mota ya shiga itama yace ta shigo ta kar'bi sak'o ta shiga


Kud'i ya Mik'a mata masu yawa yace ta bama aunty maryam, ya d'auko ledar kayan baby's d'in
da ya siyo ya mika mata tare da fad'in "Wannan a bama baby" To sun gode sosai " ya sake bata
kud'i yace wannan nata ne koda zata siya wani abu, godiya tayi masa sosai, ya matso face d'in
sa dai_dai tata yana k'ok'arin d'aura lips d'in sa akan nata, tunowa tayi da yarda ta gansu d'azu
shida husna tayi saurin janye fuskarta tana turo baki,

Kallanta yake" Why?" Kalmar da ta fito masa kenan "Why rinat?" uhm uhm to ai matarka ta
maka kafin ka fito " ta fad'a cikin shagwa'ba, yah ansar da mamaki yake kallanta, ita kanta sai
da ta furta maganar ne sannan taji nauyin ta, hannu tasa ta bud'e murfin motar ta fito tayi masa
allah ya kai lafiya ta wuce, sai da ta shige sannan ya tada motar ya fice

Kayan ta bama aunty maryam da kud'i, tayi gadiya sosai, aunty maryam ta zaunar da zarinat
aka sa mata lalle


Ranar suna yaro yaci sunan aminu, sunan Mahaifin aunty maryam wanda aka masa lak'ani da
abba.....................................................

Comment and share fisabilillah ♥️
ZARINAT ( ةنيرز )










Mallakar
Zainab dodo✍️












Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number
09046495943
Chart only




_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
T. W. F

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 1️⃣8️⃣

Kwana biyu da sunah amman bata koma ba duk da yah ansar ya kira ta yace zai zo d'aukar ta
tace, yayi zamansa basai yazo ba yaya bilal zai wuce da ita dan shima garin zai je, amman har
yanzu shuru ka keji


Yau yah ansar koda ya dawo daga wajen aiki a gajiye gashi yunwar da yake ji allah ya gani ya
gaji da shan tea ya kwanta dan haka yana dawowa ya tasa husna a gaba akan dole sai ta girka
masa wani abu yaci, tashi tayi ta shiga kitchen shi kuma ya wuce d'akin sa yayi wanka

Tsaye tayi cikin kitchen tana kallan komai gadai kayan abinci nan kala_kala amman bata san
yarda ake dafawa ba wata dabara ce ta fad'o mata dan haka ta d'auko wayarta ta kunna data ta
shiga wajen Downloading tayi searching na video ake had'a delicious food


Wani video taci karo dashi na fried rice shi ta d'auka tayi downloading, ta d'ora tukunya ta
zuba ruwa, ruwan na fara zafi ta zuba shinkafa a ciki, ga video taga ansa boiling in ten minutes,
ta k'ara wuta sosai cikin 5mint ta saukar da shinkafar ta juye a gwau_gwau( mazubi) ta mayarda
tukunyar kan wuta ta zuba mai yayi zafi ta zuba markad'ad'd'un kayan miyan ta


Cikin k'ank'anin lokaci ta kammala ta zubo masa takai cikin falo ta aje tayi zaune tana huci,

Tun da ya shigo d'akin yake jin k'aurin girki ya iso ya zauna " ka dawo? " Eh ya na ganki haka
ne?" Dan bakaga wahalar da nayi bane wajen girkin nan duk na gaji" Yawwa sannu ko kefa da
haka kike min girki ai ba wanda zaiji kanmu " Nidai gashi nan ka d'auka wallahi na gaji bazan
iya kawo ma ba " Ba matsala" ya fad'a tare da Mik'e wa ya d'auko abincin yana bud'e wa k'aurin
girkin ya bugi hancin sa " Baby wuta kika saka da yawa ne naji sai k'auri yakeyi" Eh wai saboda
nayi saurin gamawa " okay, ya fad'a tare da Mik'e wa ya nufi kitchen yaje ya d'auko filet da
spoon yazo ya zuba ya zauna


Sai da ya cika spoon ya tura baki, cikin mugun sauri ya fito dashi, husna dake kallansa tace

"Dear lafiya?" Sai da ya d'an d'auki lokaci kafin ya samu daman magana dan ji yayi bakinsa ma
ya d'auke " Wannan wane irin girki ne haka,ya fad'a a fusace" Me yayi?" D'auka kici kiji" d'auka
tayi itama tana saka wa ta fito dashi ta tayi kitchen da sauri ta wanke bakin ta ta fito

Abincin gashi bai dahuba ga gishiri da magi da yayi yawa kamar me


Kallanta yayi yaja tsaki tare da fad'in " Aikin banza" ya fice daga d'akin


" To mena zuba da yawa haka wanda yasa abincin ya kasa ciyuwa? Husna ta tambayi kanta,
masu aiki ta kira suka d'auke abincin






'Bangaren su zarinat, suna zaune a d'aki ita da aunty maryam tana k'ara koya mata wasu
dabaru na yarda zata kula da mijinta da yarda zata saye zuciyar sa da kyawawan dabi'u

Wayar tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login