Showing 102001 words to 105000 words out of 129443 words
Chapter 35 - ALKIBLA Complete Book by Safiya Abdullahi Huguma .pdf
qashin kansa sannan ya saurara.
Wankansa yayi har a sannan bata iya kallonshi ba,sai daya gama ya daura babban towel a
qugunsa,saiya bude rariyar ruwan ya fita ya tara mata wani
"Zaki iya wanka" daga haka ya taka ya fice.
Tana qananun qwalla tana wankan,a haka harta kammala,sai kuma ta rasa me zata sanya
ta fito?,idan ma ta fito din wanne kayan zata sanya tunda wanda tazo dasu sun jiqe?,towel ta
hanga don haka dole shi ta daura,Allah yasa ya cire mata hijabin bai jiqe ba,saita saka shi ta fito
daga toilet din a hankali kamar wadda ta yiwa sarki qarya kanta a qasa.
Waje daya ta samu ta zauna sanda ta fito din,yayin da yake gaban mudubi yana shafa
mai,wani wasai yakejin ranshi da gangar jikinsa,wani shauqi da baisan daga ina ya taso ba
yana ratsashi,itadai batasan me ake ciki ba sai taji sautin muryarsa yana cewa
"Hello hajja.....a samu yaro ya kawo mata kayan sawarta" shuru ya danyi da alama silleshi
hajjan take,don murmusawa yayi kadan sannan yace
"Gani nan....zanzo na dauka da kaina" da haka ya kife wayar,ya qarasa shiryawa a gurguje ya
fice,saita bishi da kallo tana dora hannu saman ka,shikenan ya janyo mata,ta shiga uku wajen
hajja,tasan wallahi watan yi mata tijara ne ya kama,yanzu duk wanda yaga yaje dauka mata
kaya saiya dauka wani abunne ya faru,kawai sai taji hawaye yana sauko mata.
Ya kusa minti goma sannan ya dawo,ya zube mata kayan wajen kala uku,abun kunyar ma
data daga harda undies dinta da bra,ji tayi kaman qasa ta tsage mata ta shige,sauqinta daya
ma daya dan fita ya bata waje ta shirya,bayan ya dawo yana daga zaune yasa tayi serving
nasa,saita samu waje ta zauna bayan ta gama,lokaci lokaci yana satar kallonta,murmushi na
subuce masa,can qasan ransa ya furta
"Silly girl,zanyi maganin wannan tsiwar taki" yana kallonta tayi kwanciyarta saman kujera,baice
da ita komai ba,saida baccinta yayi nisa kawai ta tsinci kanta saman gadonshi,ta motsa yace da
ita
"Kina tashi akwai punishment,just sleep" saita maida kanta ta kwantar tana irga qarfin hali da
iya qarfa qarfa na ya haidar din,ita gaba daya kwance mata kai yakeyi,dukka halayen da take
gani yanzu tattare dashi mugun baqin halaye ne da babu wanda ya zaceshi dasu
(Ni kuwa nace matar mutum ai ba wasa ba,duk wanda ke cika baki akan mace ba'a biyo ta
kansa bane),ta qasan ido take hango duk motsinsa,saboda bayan yaci abincin aikinsa yaci
gaba dayi,saidai wannan karon rubuce rubuce ne yaketa yi wanda batasan na meye ba.
A hankali qamshinsa daya kama zanin gadon da abun rufarsa ke ratsa qafofin
hancinta,wani tattausan qamshi data kasa banbance na meye da meye,tun da can kusan
lambarsa kenan,dashi ake gane yana waje,har zuwa yanzu kuwa duk wanda ya sanshi ya
sanshi da qamshi,sannu sannu take shaqar iska zuwa hunhunta har wani bacci mai cike da
nutsuwa yayi awon gaba da ita.
*_WASHEGARI_*
Tun bayan sallar asuba bacci ya sake daukarta me nauyi,ita da tayi niyyar zata gudu tunda
duku duku,don ba zata iya hada idanu da jama'ar gidan ba,sai gashi bacci ya kwafsa mata,ba
ita ta farka ba sai goma saura.
A rude ta sauka daga gadon,saita hau juye juye,babu kowa cikin dakin sai ita,don haka ta
nufi qofa da hanzarinta tana addu'ar kar ya shigo har sai ta fice,don babu abinda taqi jini irin su
hadu a yanzun,idan ta tuna abinda ya faru jiya ji take kamar qasa ta tsage mata ta shige.
Saidai ta makara,addu'arta bata ci ba,tana murda handle din shima yana murdawa,sai
sukayi kacibus bakin qofa,yadda ya sako kai gaba daya yana tsareta da idanu ya sanyata ja
baya ta bashi hanya ya shigo.
"Ina kwana" ta gaidashi tana kauda idanu,ya amsa mata da
"Kin tashi lafiya?" Saita kasa maida masa amsa,bai damu ba yace
"Muje....ciki nima zan shiga" da sauri tayi gaba,kamar wadda ake tsunkuli
"Easy mana" ya fada yana taddota,suka jera kafada shi da ita
"Ko sau daya mana,yau kawai hajja ta yaba mana" da xata iya juyawa zatayi ta maka masa
harara,wanne yabon hajja ita takeso,bayan ta kaita ta barota,babu wani abu a jikinta a yanzu da
baisan wajen zamansa da size dinsa ba,itakam ai sun gama da ita shida hajjan,bai sake cewa
komai ba itama haka,haka suka ci gaba da takawa har zuwa cikin gidan.
Duk wanda suka gamu dashi sai taji kunya ta kamata kamar ta shige qarqashin
qasa,musamman da sukaci karo da abba babba,cikin farinciki yake dubansu sanda suke
gaidashi,harda yi musu addu'a sannan suka wuce.
"Muje ki fara gaida ummi" yace da ita yana tareta daga yin sassan hajja,saita bishi suka
wuce sassan ummin tata.
Tana cikin yin breakfast suka shiga,saita ture kwanon,fuskarta itama cikeda jin dadin daya
kasa boyuwa take amsa gaisuwarsu,haka taci gaba da binsu da kallo har suka fito daga sassan
"Kinsan girman ladan sanya farinciki a zuciyar iyaye?,muje ki gaida mama itama" ya fadi yana
nuna mata hanya,bata ce masa uffan ba ta bishi suka isa sassan maman,ita dinma kamar
sauran,farincikinta bai boyu ba,hatta da momy da suka gaisar,sai jikinta yayi sanyi,dukka
wannan farincikin na meye?,na ganinsu ne tare da Aliyyun kawai?,da wannan tunanin suka
wuce sassan mai gayya mai aiki hajja.
Dukkansu suna falo harda me jego,suwaiba da badi'a,saisu anty aliya da suka zo suyar
nama,idanun da sukayo kansu gaba daya sai taji kamar zata zube a qasa,kunya kamar ta
kasheta,saita dinga mammazewa,ta qarasa cikinsu ta gaidasu,hajja ce dai sai data tura mata
qeya sannan ta amsa.
Bayan sun gaisa haidar din yadan zauna a cikinsu anty aliyan,abinda yakan jima baiyi ba
kenan,ba kasafai suke samun damar zamansa cikinsu ayi hira sosai ba,sai lokaci lokaci,hakan
ya sanya zahra barin falon ta shige dakin hajja,don nata dakin su suwaiba su shige ciki.
Tana nan kwance hajja ta shigo dakin yakai sau uku,a fakaice take mata habaici a waqe
anaso ana kaiwa kasuwa,irin salon waqoqin mutan da din nan,dadai ta gaji da habaicin hajja
saita miqe ta fice tabar mata dakin.
Har yanzu yana falon shida anty aliya da anty nusaiba,zata wuce kitchen ta samu abinda
zataci taji suna masa godiya,da alama ya musu irin alkhairin daya saba ne.
Inna gaje ce kawai a kitchen din,sai tayi zamanta kawai a ciki,ta hada mata abincin ta soma
ci suna hira,ita dinma zancan haidar din take mata
"Ai gaskiya uwar masu gida kin dace,kinyi dace da mijin qwarai mai hannun alkhairi,inda ace
shidin wani hamshaqin attajiri ne Allah ne yasan mutum nawa me zasuyi kudi ta sanadinsa,ko a
yanzun ma ya zama inuwa ga mutane da yawa,saidai addu'ar Allah ya qara arziqi" murmushi ta
yiwa inna gajen kawai,ta can qasan ranta sai taji zuciyarta na amsawa da amin............ 10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 38
Wani mugun shewa taji sanda ta shiga dakin kwanansu,dama tun cikin aji ta fuskanci suna
gulmarta da ido,don dai da malami a ajin,babu damar suyi mata magana ne.
Da ido ta bisu ganin yadda suketa mata dariya
"Dalla malamai,banason iskanci,meye abun dariya a jikina?,koni mahaukaciya ce?" Sai sannan
hindatu tace
"Mahaukaciya tuburan kuwa......ah,ya haidar din da bashi da mutunci,ya zakin da babu ruwanki
dashi,aka hanani neman soyayyar dan bawan Allahn nan,ash kinsan cewa qarshe ne shi a
soyayya,ya gama haduwa tako ina,sai gashi ya kasheki da soyayya agun ajiyar motoci,har
jama'a suka wuceku ma baki sani ba...nidai gaskiya qawa kinmin yankan baya ba kadan ba" ta
fada tana hade fuska,janna tace
"Nifa banga laifinta ba,tsakani da Allah fa,waje zaiga guy irin wannan yana da dama ya bari ya
wuceshi,wallahi ko nice sai inda maina ya qaremin,idan kuwa ina zaune yazo ya taya,ai babu
wani kwane kwane zanyi wuff da abina".
Babi babi na tsiya suka bude suka dinga yi mata,ita dai ci kanku bata ce musu ba,hakanan
ta samu kanta da kasa tanka musu,sai data tafi bandaki sannan suka saurara mata,data dawo
kuma aka shiga hirar yaushe gamo,nan ma sai da suka tsokaneta
"Daga yanzu zanje na dawo qawa kuma sai mukaji dif" tsaki taja tana nade abun sallarta
"Wallahi hajja ce,ashe ta timer min" dariya duka suka saka,janna tace
"Allah dai ya biya hajja,wallahi ta kyauta min" harara ta jefa mata,hindatu ta cafke
"Ta taimakeki kuwa,don bakiga kyan da kika qara ba,Allah yasa anyi me gaba daya" ta fada
suna tafawa,dadai ta fuskanci iskanci da tsiya suka tanadar mata buhu buhu,saita miqe tabar
musu dakin,saidai zancan hindatu ya tuna mata da abinda ya faru a wancan ranar,ranar da
yaso yayi mai gaba daya din,sai wani qaramin murmushi ya sube mata,ita kadai taja hijabinta
zuwa qasan hancinta tana jin kunyar kanta da kanta.
Dawowarta ba jimawa aka soma jarrabawa,wanda daga ita din watanni kadan suka rage
musu suyi jarabawar kammala makarantar,kamar kowanne lokaci dai bata daga qafa ba,ta bada
himma wajen karatunta sosai,duk da cewa lokaci zuwa lokaci tunaninsa yakan fado mata a
rai,har yakan tsaidata na wasu mintuna kafin ta dora,tun tana yaqin ture zuwan tunanin
kwanyarta harta haqura ta bashi dama,saiya zame mata jiki,don kusan duk sanda tazo
kwanciya bacci shine abu na qarshe da zatayi kafin baccin ya dauketa,kaf xamansu na abuja
sai tayi bitarsa,ranar da zasuyi sallama na qarshe da sauran moments nasu.
Batasan me yasa a kwanakin take yawan duba wayarta ba,koda yaushe tana kan
cheaking sms da watsapp massages fiye da yadda ta saba,batasan dalili ba,sai randa zuciyarta
tayi mata wata tambaya,wanda a take ta girgiza kai alamar a'ah
"Kina tsammanin samun kira da gareshi ne?" Wannan itace tambayar data yiwa kanta,wanda ko
sau daya bata taba yarda da hakan ba.
Jarabawar wannan karon suna samun intervals sosai,don haka duk sanda taga akwai
interval mai yawa saita tafi gida,tafiya gidan yakan sa mata nutsuwa,kuma yakan sanya taji
kamar tadan rage nisan dake tsakaninta da wani abu wanda ada yake nesa da ita.
Sannu a hankali ta tabbatarwa da kanta damuwa ce,damuwa ce ta rashin ganinsa ko
rashin jin muryarsa na tsahon tagwayen sati,har ana neman shiga sati na uku,hatta a gida hajja
ta fara qorafin shuru haidar,bai kira ba,koda an kira ba'a samunsa,to Allah yasa dai
lafiya,addu'ar data sanya gaban zahran mugun faduwa,saboda tuna maganar daya gaya mata
_"zanyi tafiya me nisa.....waje me hadari,zan iya dawowa....zan iya salwanta a can.....ki yafemin
idan na saba miki a tarayyarmu"_,kawai sai taji kuka ya subuce mata,ta danneshi har sai data
kai daki sannan ta sakeshi.
Kuka tayi sosai wanda ta kasa yarda da dalilin kukan nata da zuciyarta keta bata,saidai ko
ba komai ta danji nauyin dake qirjinta ya ragu,ranar sama sama tayi karatun jarrabawar da zata
zana a jibi,washegari ta hada kayanta ta koma makaranta,wanda jarabawar kawaidai tasan
saidai Allah ya tsallakar da ita,amma ita kanta bata gama tantance abinda take rubutawar haka
yake ba,ko akwai kusakurai da gyararraki ba.
Hajja kuwa bin zahra tayi da kallo tun sanda taga tayi daki da sauri sanda take jajjabin
kwanakin da haidar din ya shafe babu shi babu labarinsa,murmushi ta saki,duk da tana cikin
fargaba,saita daga hannunta sama tana cewa
"Allah na gode maka,Allah na gode maka,ko yau na mutu ubangiji ka cikamin dukka
burina,Allah ka qara hada kan zuria'ata da iyalina,Allah ka qarawa annabi muhammad S A W
wasila da fadila" daga haka ta sauke hannun nata,zuciyarta na mata dadi,ba shakka komai yayi
dai dai yadda takeso,tasan cewa da zarar ya dawo komai zai kammala dai daita.
Ranar da suka kammala jarrabawarsu suka samu hutu na wasu kwanaki ba masu yawa
ba,saboda zasu dawo ne suyi maza su dora sabuwar semester ta qarshe,tana kwance a
dakinsu kamar ba wadda ke shirin tahowa gida ba,tana kallon su hindatu sunata shiri.
Tun sanda ta dawo daga abuja ta lura da wani abu,dabi'un su hindatun su canza gaba
daya,abubuwa da yawa sun daina yinsu yanayin shigarsu ya canza sosai,wanda hakan ya bata
mamaki,saidai bata taba tambayarsu ba.
Hindatun ce ta qaraso ta taba zahran dake kwance rub da ciki,saita daga kai tana duban
hindatu,hijabi ne dan madaidaici a jikinta wanda ta dorashi saman abayarta,wadda ta rufe jikinta
ruf
"Tunanin me kike mrs haidar?" Murmushi ta saki,ta tashi ta zauna tana duban hindatun,fuskarta
qunshe da murmushi
"Ina mamakin me ya canza qawayena haka tashi guda" murmushin itama hindatun tayi,ta zauna
gefan zahra
"Tasirantuwa mukayi da qawar qwarai,hakan shiya canza mu,sannan kuma mukayi aiki da
hankali da tunanin da Allah ya bamu,muka ga cewa
10/17/21, 10:25 PM - Jummi Hanya: 37
*KIJI TSORON ALLAH,������KADA KI TABA KAYAN DABA NAKI
BANE,BA KUMA MALLAKINKI BANE*
Washegari kuwa qaryar ciwo ta yiwa hajja bayan ta gama hada kayan da xata koma
makaranta dasu a washegari,tayi kwanciyarta da wuri,duk da baccin bai dauketa ba amma
tasha chart dinta,har daga bisani baccin gaske yayi gaba da ita.
Tunda ilham ta kawo masa abincin yace ta ajiye a nan,tsahon wani lokaci yana zaune,shi
baici abincin ba,bai kuma ce a fita dashi ba,haka kawai duk yaji baya cikin sukuni,abincin ma
baya sha'awa ci,xuwa wani lokaci sai gashi ya miqe,ya saka hannu ya bude dakin,ya leqa
farfajiyar waje kamar me neman wani abu,daga baya kuma ya rufe qofan ya dawo ciki yana jan
tsaki.
Gaban kwanukan abincin ya dawo ya soma saving kanshi,abinda ya jima rabon da
yayi,tsakula kawai yayi yaji cikinsa ya cushe,saiya tura abincin gefe ya miqe ya nufi bakin fridge
don dauko abin sha.
******** ***** ********
Tsaye take dakin hajjan rataye da qaramar jakarta,tana tsayen amma sai faman duba agogo
take,tana so ta isa akan lokaci ne,akwai lecturer din dake nemansu,kuma tasan halinsa
sarai,mtuqar ta wuce lokacin tofa ba shakka ko dawa take yawo ba zai bari ta shiga ba.
"Don Allah hajja ki sauri....zan makara fa" ta fada a shagwabe,saita rufe akwatin data bude
din,ta miqa mata baqar leda
"Gashinan,ki tabbtar komai dake ciki kin shanyeshi kafin dawowarki gidan nan,Allah ya
tsare....ina shi haidar din?"
"Munyi sallama fa,bacci yake,mustapha zai kaini" idanu hajjan ta tsareta dashi,bata yarda da
zancanta ba,don tun jiya taga tana aiken yara suna siyo mata abubuwan da bata dashi a kantin
layinsu da É—ai da É—ai,ta mata shuru ne kawai tayi kamar bata gani ba
"Motarsa kam dama ai wajen mustapha ta kwana,don ya aikeshi gidan innarku da safe zaije
yakai mata saqo" qafa ta bubbuga
"Wai hajja yarda ne bakiyi dani ba"
"Na yarda dake,Allah ya kiyaye hanya" ta fada tana tattare kayanta data fito dasu,sanadin
daukowa zahran abinda ta batan,ta san sarai indai baisan da tafiyarta ba bazai qyale ba,don
baya daukan irin wadan nan abubuwan.
Sai data shiga ta yiwa duk mutanen gidan sallama,bata tarda mama ba ta fita tun sassafe
dubiya,umminta dubu biyu ta bata,sai taqi karba,duk da ta yiwa account dinta tas saboda
siyayyar data yiwa kanta da kanta,don kada ta tambayi haidar din,wanda tunda take bata taba
yiwa kan nata siyayya ba sai wannan karon.
Gaban motar ta shige sanda mustapha ke kunna motar,ya tasheta suka fice daga gidan.
Tun basuyi nisa ba suka soma hirarsu yadda suka saba,cikin raha da zolaya,gab da zasu
shiga farawa wayar mustaphan tayi tsuwwa,sai zahran ta xolayeshi
"Tun daxu ake faman kiranka,hala wata mai rabon wahalarce" ta fada tana sheqe masa da
dariya
"Allah kinga makwancina da yawa.....ki zuba ido,sai nafi mijinki kudi,kibar ganin aikinmu har
yanzu baizo hannu ba,hausawa suka ce gayawa wanda ya tara ya kiyayi me nema.....kai shine
ma ke kira" ya fada yana zaro ido,sai zahran ta qyalqyale da dariya
"Qaryar kawai,ashema cika bakin naka bai kai ba,tunda gashi daga ganin sunansa kawai ya
saka fargaba" hannunsa daya ya daga
"Na yarda wallahi....ke....kinsan soja kuwa....hmmmm" daga haka ya daga wayar,ya sanyata a
handsfree.
Husky voice dinsa ce ta cika wayar,kamar bai jima da tashi a barci ba
"Kai kana ina?" Ya tambayeshi a dake,cikin girmamawa yace
"Gamu a hanya zan maida inna wuro makaranta"
"Waye ya baka izini?" Ya jefa masa tambayar data saka mustapha ware idanu yana duban
zahra,wadda itama shi take kallo,dukkansu gabansu na faduwa,bai iya amsa mishi ba ya
tsintoshi yana cewa
"Duk inda kuke ku dawo yanzu yanzun nan" daga haka É—if ya katse wayar,saiya soma neman
wajen tsayawa,ya gangara gefan titi zaiyi reverse.
Kallonsa zahran tayi
"Wai komawa zakayi?" Girarsa ya dage duka yana kallonta sannan yace
"Eh mana....au so kike nace masa a'ah,tab....wallahi bazan iya ba,ke