Showing 6001 words to 9000 words out of 10415 words
Chapter 3 - Rijiya Gaba Dubu Book 3 Complete chapter C by Abdulaziz Sani Madakin Gini -1.pdf
makahon kare
yawa gareta, ina da wata dabarar, cikin mamaki da zumudi sarki gurzalu ya dubi lamirat yace,
Ya ke'Yata wace irin dabara kike tunani? lamirat ta numfasa tace,Ni ina ganin cewa ka saka
sarki taryan ya kirawo maka gaba daya bokayen kasar nan su dukufa akan binciken gano
barawon ka,indai bokayen kasar nan suka hada karfi da karfe, lallai zasu iya gano barawon ka a
cikin kwanaki kadan kafin Imhal ya sami lafiyar da zai iya cigaba da wannan gasa har
haduwarka dashi tazo, Koda jin wannan shawara sai farin ciki ya lullube sarki gurzalu yace, ina
alfahari dake 'yata tabbas kinyi dogon tunani mai kyau, to amma fa dole ne muyi la'akari da irin
raunin dake jikin Imhal mu kiyasce iya tsawon lokacin da muke ganin zai warke, idan kuma yazo
dai-dai da sanda Bokayen za su samu nasarar gano barawon shikenan bamu da sauran
damuwa,amma idan har Imhal ya samu lafiya kafin su gano barawon akwai matsala
babban,Lamirat tace, kada ka damu ya Abbana, duk zan kula da hakan, kuma a Yau dinnan za
a gama komai, Koda gama fadin haka sai Gimbiya lamirat ta mike tsaye ta fice daga cikin
dakin,bata zame ko ina ba sai turakar sarki taryan, bayan anyi mata iso ta shiga inda yake sai ta
risina ta gaishe shi sannan tace, ya shugabana, Abbana ne yace nazo na nemi alfarmar zuwa
ganin jarumi Imhal, Koda jin haka sai sarki taryan ya girgiza kai yace,Ai bazan iya baki wannan
dama ba domin yana daga cikin dokar wannan gasa ba a barin abokin gasa yaje ya gana da
dan'uwansa,idan har kika je kika gana da Imhal kamar sarki gurzalu ne yaje tunda kin kasance
'yarsa,Lamirat tace,na yarda ka hadani da amintattun Hadimanka su rakani gareshi, idan ana
zargin ko zanje na cutar dashi ne,,Koda jin haka sai sarki taryan yayi shiru yana tunani, daga
can kuma sai yayi aniyar zuciya yace,shikenan na amince, Take lamirat tayi godiya, ba tare da
bata lokaci ba aka hadata da wadansu amintattun Hadimai su hudu gami da dakaru dari suka
tafi izuwa dakin da aka kulle jarumi Imhal.
Da isarsu suka iske jarumi Imhal a kishingide a jikin bango yana con abinci dakyar kamar zai yi
amai ko Riga babu a jikinsa sakamakon katon raunin da ke kirjin sa.
Tun daga nesa jarumi Imhal ya hango Gimbiya lamirat tare da dakaru sai ya kura mata idanu
yana mai yi mata murmushi.
Zan cigaba
RIJIYA GABA DUBU3 CIGABA 8
Ita kuwa Koda taga yana yi mata murmushi sai ta murtuke fuskarta tamkar taga bakin
kumurci(Bakin maciji mai masifa da mugunta) kuma sai ta dinga satar kallon raunin da ke kan
kirjinsa, tana nazari da tunanin adadin kwanakin da take ganin cewar ciwon zai iya warkewa har
ya iya cigaba da yin wannan gasa. Lokacin da Gimbiya lamirat suka iso daf da kofar dakin sai suka tsaya cak! Akayi tsit! ana
kallon-kallo tsakaninta da jarumi Imhal, kawai sai Imhal ya dubeta fuskarsa cike da annuri
yace,"Mene ne ya kawoki wajena,ko kuwa kinzo ne ki karasani saboda kina tsaron karona da
mahaifinki? " Koda jin wannan tambaya sai murmushi ya subucewa Gimbiya lamirat bata sani ba,ta dubeshi
cikin gadara tace, "Ai matsoraci baya kusantar abokin gaba,nazo ne domin naga lafiyar abokin
gaba, domin idan ka mutu yanzu sai nafi kowa bakin ciki, saboda bani da burin da yafi na sare
kanka da hannun nan nawa". Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama jarumi Imhal yace," Wai shin menene dalilin da yasa
keda mahaifinki kuka tsananta kiyayya a kaina,alhalin babu wani mugun sabani da ya taba
shiga tsakanina da Ku? shin ta yaya Zaki samu damar sare kaina da hannunki alhalin bakya
cikin wannan gasa ta KAMBUN JARUMTA? Koda ma kina cikin wannan gasa ni bazan iya
kashe ki da hannu na ba,domin a cikin fadin duniya kaf a yanzu babu abinda nake kauna sama
dake".
Koda jin wannan batu sai lamirat da gaba daya dakaru da hadiman dake bayan ta suka cika da
tsananin mamaki, lamirat ta fusata ainun, ta dakawa Imhal tsawa tace,"Kai talaka, makaskanci!
ka sani cewa wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa,kuma RUWA da WUTA basa haduwa, batun
soyayya a tsakani na dakai babu har abada sai kiyayya! Nayi maka alkawarin cewar wannan
karon baka isa ka kubuce ba daga sharrin mu face munga karshenka!!"
Koda jin wannan batu sai jarumi Imhal ya bushe da dariya, lokaci guda kuma ya hade fuska
yace,"Ni kuwa nayi miki alkawari sai kin nemi gafarata da murya mai taushi, kuma kin rokeni na
So kind......!!!"
Kafin jarumi Imhal ya rufe bakinsa tuni lamirat ta tofa masa yawu a fuska tace,"Da dai na SO ka
har na furta maka kalmar SO gwara na rasa rayuwata, kuma ka saurari ranar da za kayi gasa ta
uku, nice abokiyar gwaminka ".
Tana gama fadin haka sai tayi sauri ta juya cikin fushi zuciyar ta na tafasa tamkar zata kone,
cikin hanzari hadimai da Dakaru suka bita a baya.
Shi kuwa jarumi Imhal sai yasa hannun sa ya lakuto yawun da lamirat ta tofa masa a fuska ya
shanye shi yana murmushi yace, " Ba a soyayya da karya... kuma ba a kiyayya da karya, na
kamu da tsananin sonki Gimbiya lamirat, kuma bazan daina sonki ba Koda Zaki zamo sanadin
ajalina! Yana gama fadin haka sai ya koma ya kwanta a kasa, kansa yana kallon Rufin dakin yana
murmushi gami da mamakin yadda akayi radadin SO ya sa shi ya bayyana soyayyarsa a fili a
Yau ba wadda ta tsane shi kamar yadda ta tsani ajalinta, kuma ya cigaba da wasu-wasi a cikin
zuciyarsa akan cewar; "Wai shin da gaske ne Lamirat ce abokiyar gwaminsa ta uku a cikin
wannan Gasar Jarumtaka?"
Abinda baiwa sani ba shine, shi kansa sarki gurzalun baiwa San cewa Gimbiya lamirat ta shiga
cikin wannan gasa ba,don tun kafin su iso birnin ta aiko da wasika mai dauke da hatiminta da sa
hannunta ba sarki taryan tace lallai a sata a matsayin jarumar da zata fafata a karo na uku da
bakon jarumin da za su zo dashi ". Koda sarki taryan yaga wannan wasika sai ya cika da dimbin mamaki, amma da yaga hatimi da
sa hannun ta sai yasa aka rubuta sunanta a cikin jaruman gasar.
Wani iko na Allh kuma sai ya manta ya tambayi sarki gurzalu dalilin da yasa ya bar Gimbiya
lamirat ta shiga cikin wannan gasa.
Bayan lamirat ta baro wajen Imhal sai ta koma izuwa turakar sarki gurzalu ta gaya masa cewa,"
Dole ne Bokayen da za su kira suyi musu wannan bincike su kammala a cikin kwanakin da
basu wuce bakwai ba,saboda na tabbatar da cewar kafin Imhal ya warke har yaji karfin da zai
iya fitowa filin gasa sai ankai kwana bakwai ". Sanda sarki gurzalu yaji wannan batu sai fuskar sa ta fadada da murmushi, yace," Ai faduwa
tazo dai-dai da zama, domin tuni na gana da shugaban bokayen kasar nan a Yau bayan na
rabu da ke, kuma har ya tabbatar mini da cewar nan da cikar kwanaki bakwai dai-dai za su
gano mini Barawon,tabbas aikin ki yayi kyau. zan cigaba
RIJIYA GABA DUBU3 CIGABA 9
Da jin haka sai farin ciki ya lullube Gimbiya lamirat tayi godiya kuma sai fuskarta ta sauya
yanayi izuwa matukar damuwa ta sunkui da Kanta kasa tana mai yin shiru,Al'amarin da ya tayar
da hankalin sarki gurzalu kenan ya dubeta shima cikin damuwa yace, "Ya ke 'yata me ya
faru,kuma naga fuskarki ta sauya yanayi daga farin ciki zuwa kishiyarsa?" Sanda ta ji wannan
tambaya sai ta dago kai a lokacin da idanun ta suka kada suka yi jawur kamar hawaye zai zubo
mata tace,"Ya kai Abbana a iya sanina a cikin tarayya ta dakai ban taba yi maka karya ba kuma
ban taba yi maka laifi ba,ko ba haka bane?"
Cikin mamaki sarki gurzalu ya gyada kai yace,"Tabbas tun daga kuruciyarki kawo izuwa
girmanki baki taba yi min wadannan abubuwan biyu ba".
Lamirat tace,wannan karon nayi maka wani laifi tun kafin mu baro gida, kayi hakuri bazan iya
gaya maka wannan laifi ba sai bayan an kammala wannan gasa ta khango JARUMTA, amma
ina rokonka da ka yafe min wannan laifi tun kafin ka San shi"
Koda Gimbiya lamirat tazo nan a zancen ta sai sarki gurzalu ya sake kamuwa da tsananin
mamaki, yayi shiru yana tunani da nazari har izuwa tsawon dakiku, daga can sai ya dubeta cikin
murmushi yace, "Na yafe miki wannan laifi'Yar Lele,kuma ko bayan na San laifin na rantse da
girman abin bautarmu bazan yi fushi da ke ba" Koda jin haka sai farin ciki ya kama lamirat ta rungume sarki tana mai yi masa godiya, nan dai
lamirat tayiwa sarki gurzalu sallama ta tafi izuwa masaukin ta,wato dakin Gimbiya Shumaira.
Tana shiga dakin sai ta hango Shumaira zaune tana sarrafa hannayen ta alamar cewar tana yin
magana ne da wani.
Amma da lamirat ta karaso cikin falon sai taga Ashe babu kowa a cikin falon, Shumaira ce kadai
a zaune.
Al'amarin da yayi matukar bata mamaki kenan, ta dubi Shumaira tace,Shin akwai wani aljani da
yake zuwa wajen ki kuyi hira?
Cikin mamaki Shumaira ta dubi lamirat tace,Ai babu wani aljani da ya isa ya shigo cikin gidan
sarautar nan domin iyaye da kakanni sun gama shirya gidan da tsari na musamman.
LAMIRAT tace,"Wannan gaskiya ne,domin mahaifina ya tabbatar min da haka, amma yanzu da
na tunkaro wannan falon naki naga kina sarrafa hannayenki alamar cewa kina yin magana ne
da wani "
Koda jin haka sai Shumaira tayi murmushi tace,A'a babu wanda nake hira da shi ,kawai dai ina
tunani ne gami da zancen zuci ,
Cikin sanyin jiki Lamirat ta zauna a gefen Shumaira suka yi shiru tsawon'yan dakiku kadan.
Duk wannan abu dake faruwa MUZAIRA na zaune a gefe daya tana hararar lamirat, kuma
jikinta na tsuma, ji take kamar ta mike zumbur! ta je ta shake Gimbiya lamirat har sai ta kasheta
saboda kiyayya.
Ita kuwa lamirat gashi dai tana fuskantar kujerar da MUZAIRA take zaune a kai amma ba ta iya
ganinka,Shumaira kadai take iya gani a cikin falon.
Daga can sai lamirat ta katse shirun da suke ciki ta dubi Shumaira tace,Ya ke kawata ina son
zan baki wata shawara guda daya, shawarar kuwa ita ce,Kada ki so saurayin da ba shine ya
fara nuna soyayyarsa ba a gareki, domin watakila kiyi SON MASO WANI.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Gimbiya Shumaira tace, Ke kuwa mene ne dalilin da
yasa kika fada mini wannan magana alhalin ban taba gaya miki cewar ina son wani saurayi ba?
Koda jin haka sai lamirat tayi murmushi tace, Tun da dai nayi miki hannun ji mai sanda baki
gane ba bari na fito fili nayi miki baro-baro watakila za ki fi fuskantar inda nasa gaba.
Idan za ki iya tunawa, a ranar da aka fara gasar kambun JARUMTA tsakanin jarumi Imhal da
sadauki Darwaz sai da kowa ya gane cewar kin kamu dason jarumi Imhal sakamakon nuna
matukar tashin hankali bisa ganin zai hallaka da kuma yadda kika nuna farin ciki lokacin da ya
samu nasara, to ina mai tabbatar miki da cewa jarumi Imhal yana da tsananin so da bege a
cikin zuciyar sa,kuma har ya fito fili ya bayyana mata sirrin zuciyar sa,sai dai kashe! Anyi rashin
sa'a,domin wacce yake so din ta tsane shi kamar yadda ta tsani mutuwarta, bisa wannan dalili
ne na gaya miki cewa ki taka a hankali, kada kiyi SON MASO WANI wanda hausawa suke cewa
KOSHIN WAHALA. Na baki wannan shawara ne a matsayinki na tsohuwar kawata da muke tare tun
kuruciya,sannan idan kunne ya ji jiki ya tsira,shawara kuma ta rage ga mai shiga RIJIYA.
Koda gama fadin hakan sai Gimbiya lamirat ta mike tsaye ta shige cikin dakin bacci ta kwanta
domin ta huce gajiyar da tasha a ranar SAKAMAKON yawon da suka Sha na farautar barawon
mahaifin ta.
Ita kuwa Gimbiya Shumaira sai taji zuciyarta ta buga da karfi, tunani da wasu-wasi suka cika
mata ranta bisa kokarin gano ko Wacece budurwar da jarumi Imhal ya kamu da tsananin sonta
haka?
Koda MUZAIRA taga hankalin Shumaira ya dugunzuma ainun sai ta mike tsam! Daga kan
kujerar da take zaune ta koma wajen ta ta dafa kafadunta ta dubeta tace,"Kwantar da hankalin
ki ranki ya dade,a matsayina na uwa a gun jarumi Imhal in dai ina numfashi a doron kasa sai na
siyo miki soyayyars Imhal,domin kece kika dace dashi fiye da kowace budurwa a wannan
duniya, domin soyayyarki a gareshi, soyayya ce ta gaskiya, wacce babu algus! a cikin ta".
Koda jin wannan batu sai hankalin Shumaira ya kwanta ta rungume MUZAIRA tana mai yi mata
godiya gami da fatan samun nasara akan makiyansu.
Zan cigaba,
RIJIYA GABA DUBU3 CIGABA 10
Kwana Uku cur!da Faruwar wannan al'amari ne sarki gurzalu na tsalle-tsalle gami da yin wasa
da takobi a wani babban fili dake cikin harabar gidan sarki taryan don baiwa kansa horon yaki,
sai ga 'yarsa Gimbiya LAMIRAT ta durfafoshi sanye cikin shigar yaki kuma rike da takobi,
Al'amarin da ya bashi mamaki kenan, ya tsaya cak! ga barin baiwa kansa horon yaki har ta iso
daf dashi sannan ya dubeta yace,"Yake 'yata,ina dalilin fitowarki a wannan lokaci, kuma a cikin
shigar yaki? "
Koda jin wannan tambaya sai lamirat tayi murmushi tace,"Ya kai Abbana kayi sani cewa Yau
kusan shekaru uku kenan rabon da mu wasa jini ni da kai,don haka ina son mu dan fafata
domin na gani ko na samu cigaba a koyon yaki na fiye da abinda ka koya mini a baya tunda a
kullum a cikin neman Karin ilimi nake." Koda jin haka sai sarki gurzalu yayi murmushi yace, "Wannan ba laifi".
Nan take ya gyara tsayuwarsa, ita ma sai ta tsaya a nesa kadan dashi ta gyara tsayuwarta suka
fuskanci juna,Daga can kuma sai suka fara zagaya juna,
Kamar hadin baki sai suka ka da baya a lokaci guda sukayi taku uku kacal, sannan suka rugo
da gudu izuwa kan juna suka kacame da masifaffen yaki, ya zamana cewa suna kaiwa juna
SARA DA SUKA cikin azababben zafin nama,juriya da bajinta, suna neman hallaka juna da
dukkan karfinsu tamkar sun kasance tsofaffin abokan gaba, Tunda suka fara wannan gumurzu sarki gurzalu ya cika da tsananin mamaki, domin a saninsa
Sam gimbiya lamirat bata da zafin nama irin na yanzu, kuma kwarewarta a yaki ba ta kai hakan
ba.
Abu dai kamar a mafarki sai gashi karfinsu ma yazo daya,an rasa wanda zai iya cutar da dayan.
Sai da suka shafe rabin sa'a suna fafatawa a cikin wannan hali, Al'amarin da ya fusata sarki
gurzalu kenan, ya sauya salon yakin ya hada da kai mata bugu da naushi hannu da kafa.
Kawai sai yaga ita ma ta koma irin salon da ya koma kuma ya kasa cutar da ita,da kyar da sidin
goshi ya shammaceta ya daka wawan tsalle sama ya doketa da kafa a fuska,
Tana faduwa kasa a lokacin da lebenta ya tsage, jini ya dan zubo, sai ita ma ta kwarfi kafafunsa
yai sama ya rikito kasa,amma sai ya duro bisa kan tafin hannunsa guda cikin bajinta ya doki
kasa da tafin hannun nasa yai sama ya dawo kasa bisa kafafunsa.
A dai-dai wannan lokaci ne suka ji ana yi musu tafi, suna waigowa baya suka ga Ashe sarki
taryan ne tare da 'yarsa Gimbiya Shumaira suka durfafo inda suke, cikin hanzari lamirat ta mike
tsaye tana mai goge dan jinin da ke kan lebenta da tafin hannunta.
Sarki taryan ya dubi Gimbiya lamirat yace,"Hakika wannan 'ya ta gaji ubanta a jarumtaka, lallai
yanzu ne nasan cewa kin cancanci ki shiga.,...."
Kafin ya karasa fadin abinda ke bakinsa sai Gimbiya lamirat ta tari numfashinsa don kada ya
tona ma ta asiri tace,"Ai barewa ba ta gudu danta yayi rarrafe.
Ya shugabana me yasa kazo ka katse mana wannan horon yaki da muke yi?"
Koda jin wannan tambaya sai sarki taryan yayi ajiyar zuciya yace, "Ai wani gagarumin abin
mamaki ne ya faru yanzu shine nace lallai sai nazo na sanar da Ku, yanzun nan na kaiwa
jarumi Imhal ziyara a dakin da aka tsareshi, ina zuwa sai na iske likitana yana cire zaren da aka
dinke wannan rauni na kirjin sa,ina mai tabbatar muku da cewa raunin ya hade ya warke sumul
tamkar ma bai taba yin sa ba".
Koda jin wannan labari sai sarki gurzalu da Gimbiya LAMIRAT suka kallo junansu cikin fargaba
da tsananin mamaki.
Sarki taryan yaci gaba da cewa," A halin yanzu dai jarumi Imhal yace a shirye yake ya cigaba
da wannan gasa gobe, don haka na sanar da duk Alkalan gasar tuni ma an cigaba da
shirye-shirye."
Koda sarki taryan yazo nan a zancen sa sai sarki gurzalu yayi ajiyar dogon numfashi
yace,"Wace irin magana kake yi haka kamar Almara? Ya za ayi ace mutum ya samu irin
wannan babban rauni, kuma ace ya warke a cikin kwanaki uku kacal? "
Sarki taryan yace ai kada kayi mamaki da hakan, domin akwai mutane masu baiwar saurin
warkewa daga ciwo, idan baka manta ba ai har a cikin RIJIYA GABA DUBU ta kurkukun DARUL
MAUT aka sa jarumi Imhal ana yi masa azaba har tsawon kwanaki, amma aka fito dashi a cikin
kwanaki kadan duk raunin dake jikinsa suka warke, kuma ya samu lafiyar jikinsa. Koda jin wannan batu sai sarki gurzalu da gimbiya lamirat suka kalli juna cikin alamun damuwa
da takaici, sannan lamirat ta dubi sarki taryan tace,"Wanene wannan jarumin da zai fafata da
Imhal gobe? "
Sarki taryan ya jinjina kai yace "Wani bakin jarumi ne shima daga birnin Askandariyya,nima ban
taba ganinsa ba,sai gobe a filin gasar za muga ko wane ne".
Koda gama fadin haka sai sarki taryan ya kama hannun gimbiya Shumaira suka juya suka nufi
inda suka fito.
Suna cikin tafiya ne Gimbiya Shumaira ta juyo ta kalli sarki gurzalu da Gimbiya lamirat ta ga ko
kadan babu annuri akan fuskokinsu, tamkar an aiko musu da sakon mutuwa, kawai sai tayi
musu wani irin guntun murmushi wanda suka kasa fahimtar ko na mene ne