Showing 9001 words to 10415 words out of 10415 words
Chapter 4 - Rijiya Gaba Dubu Book 3 Complete chapter C by Abdulaziz Sani Madakin Gini -1.pdf
tsakanin na
mugunta ko na alhini. Shi kuwa sarki taryan sai ya dubi Shumaira yace, Hakika yanzu na fara yarda da zargin da nake
yi akan sarki gurzalu, domin ban ga dalilin da yasa suka tsananta kiyayya ba akan jarumi
Imhal,bisa binciken da nayi ma tun farkon haduwar Imhal da sarki gurzalu laifin da yayi masa
bai kamata ayi masa hukuncin dauri a kurkukun Darul Maut ba balle har a sanyashi a cikin
RIJIYA GABA DUBU a azabtar dashi na tsawon kwanaki ba,tabbas an zalunceshi, ni kuwa a
rayuwata bana son zaluntar mutumin da yake kasa dani,musamman wanda ya kasance talaka
na".
Koda Gimbiya Shumaira taji wannan batu daga bakin mahaifinta sai farin ciki ya lullube ta
domin ta fuskanci cewa hakanta zai cimma ruwa a kokarin da take yi na raba alakar da ke
tsananin sa da sarki gurzalu, tunda gashi shi da kansa ma ya fara gano irin zaluncin sarki
gurzalu. Zan cigaba
RIJIYA GABA DUBU3 CIGABA 11
A daren wannan rana aka cigaba da shela a cikin birane da kauyukan kasar misra ana sanar da
cewa, "Lallai gobe da safe za a cigaba da gasar kambun JARUMTA.
Ai kuwa tun a cikin daren 'Yan kallo suka dinga tururuwa a cikin filin gasar don kada su rasa
inda za su zauna suyi kallo.
yayin da gari ya waye kuwa sai ya zamana cewa duk inda mutum ya duba a filin gasar babu
masakar tsinke, ko ina kawunan bil'adama ne rututu.
Kai! har kan katangar filin gasar mutane ne a zazzaune maza da mata,a tsakiyar filin ne kawai
aka bar hanyar da za a wuce don shigowar sarakai gami da jaruman gasa da alkalai.
Sai da aka shafe kusan rabin sa'a ana jira sannan aka ji tambura na tashi gami da bushin
Algaita alamar cewa sarakai za su shigo filin gasa,Nan fa filin gasar ya rude da shewar jama'a
suka kamu da tsananin murna don sanin cewa yanzun nan za a fara gasar.
Ai kuwa sai ga sarki taryan, sarki gurzalu, da 'ya'yayensu mata tare da sauran manyan
sarakuna na nahiyar sun shigo cikin filin gasar dakaru na biye da su a gaba da baya, gefe da
gefe, ana cigaba da buga tambura, har sai da suka isa inda mazauninsu yake suka zauna.
Zaman su ke da wuya sai mai gabatar da gasar ya mike ya fara jawabi yana mai yiwa manyan
baki barka da zuwa, sannan ya sanar da cewar jarumin da ya fara wannan gasa,wato jarumi
Imhal ya warke daga raunin da ya samu a cikin kwanaki uku kacal,kuma da shi za ayi wannan
gasa ta Yau kamar yadda dokar gasar ta tanadar cewa,duk jarumin da ya samu nasarar lashe
gasar ba zai yi fashin wasa ba face baya numfashi a doron kasa,kuma komai yawan raunikan
da ke jikinsa indai zai iya warkewa sai an jira shi ya warke har izuwa tsawon mako biyu, idan ya
wuce mako biyu ne bai warke ba an cire shi daga cikin jaruman gasar,
Lokacin da jama'a suka ji cewar jarumi Imhal ya warke daga ciwon sa a cikin kwanaki uku kacal
sai kowa ya kamu da tsananin mamaki aka shiga yi masa jinjina da kirari tun kafin ma ya fito filin
gasar,nan fa filin ya rude da shewa gami da hayaniyar mutane har sai da aka buga gangar fara
gasa sannan aka yi tsit! tamkar mutuwa ta fado filin gasar. A sannan ne mai gabatarwa ya kirawo sunan bakon jarumin da yazo daga birnin Askandariyya
wai shi ZAMBARU IBINI KULSAS.
Kawai sai aka ga wani bajimin katon mutum mai tsawon kamu ashirin da bakwai ya fito daga
cikin dakin jaruman gasa wanda ya kasance mai kauri da fadin kirji, inda za a yanke kafarsa
guda a dorawa mutum dakon ta a kansa,ji zai yi kamar an Dora masa cinyar katuwar giwa.
Koda jama'a suka yi arba da wannan narkeken kato mai kirar mutanen farko, sai suka firgice
suka dimauce ainun, domin gani suka yi kamar zai baje filin gasar gaba daya ya mutsittsike
kowa da komai da ke filin.
Nan fa jama'a suka kama mikewa tsaye domin su ruga da gudu izuwa wajen filin gasar,sai da
dakaru suka hau daka musu tsawa sannan kowa ya nutsu ya koma mazauninsa.
Duk sanda Zambaru yayi tafiya taku daya sai a ji birnin gaba daya yayi girgiza kamar kasa za ta
tsage komai da ke samanta ya rufta cikin ta, Kai hatta sarki Gurzalu da ya kasance jarumin da
ke rike da KAMBUN JARUMTAKA sai da ya firgita bisa ganin Zambaru, Ya Sha jinin jikin sa,ya
ayyana cewar lallai babu tabbacin shi kansa zai iya hallaka wannan basamuden kato Koda
kuwa da karfin sihirin tsafi ne.
Bayan Zambaru ya iso tsakiyar filin gasar sai ya tsaya ya daga kansa sama yayi wata irin
kururuwa mai tsananin kara da firgitarwa wacce ta cika cikin birnin misra da duk kauyukan da ke
kewayensa da amsa kuwwa, kuma ta firgita mutane da dabbobi har ma da aljanun dake
kawayen wajen. Al'amarin da ya janyo hargitsewar birnin kenan, mutane suka dinga guje-guje da iface-iface,
matan dake dauke da tsohon juna biyu kuwa ba shiri suka kama yin nakuda ta ba zato suka
dinga haife abinda ke cikin duba tare da lokacin haihuwar yayi ba,Har sai da Zambaru ya tsuke
bakinsa sannan komai ya lafa, mutane suka dawo cikin hayyacinsu. A wannan lokaci ne mai gabatarwa ya kirawo jarumi Imhal, kawai sai aka ga jarumi Imhal ya fito
da gudu daga cikin dakin jaruman gasa rike da takobi da garkuwa cikin shigar yaki ba tare da
shakkar komai ba.
Koda ganinsa sai filin gasar ya rude da shewa aka kama yi masa jinjina da kirari, mawaka na yi
masa lakabi da SABON JARUMI MAI ABIN AL'AJABI,
Koda Zambaru ya hango jarumi Imhal ya nufo cikin filin gasar a guje rike da wata takobi sai ya
zura hannun sa izuwa bayan sa ya fiddo wata lafceciyar takobi wadda inda za a ajiye ta a kasa
karti ashirin majiya karfi basa su iya dagata sama ba.
Maimakon jarumi Imhal ya tsaya a sake buga tambarin fara gumurzu, kawai sai ya cigaba da
gudu ya tunkaro inda jarumi Zambaru yake tsaye.
Shi kuwa Zambaru sai ya fara wulwula takobinsa a sama yana jiran isowar Imhal.
Yayin da ya rage saura bai fi taku shida ba kacal Imhal ya iso inda Zambaru yake sai ya daka
wawan tsalle sama kamar an cilloshi daga baka sai gashi ya iso dai-dai wuyan Zambaru.
Ai kuwa sai ya dankara masa Sara a wuya, take takobin ta makale a jikin wuyan Zambaru
tamkar a jikin bishiya mai kauri ta nutse.
Imhal ya finciko takobinsa da hannayensa biyu da dukkan karfinsa amma sai ya kasa Ciro
takobin.
Kafin ya sake yin wani yunkuri tuni Zambaru ya mako shi da hannun sa na hagu wanda baya
rike da makami, take Imhal ya fado kasa ba shiri ya duro akan kafarsa ta hagu,ai kuwa sai kafar
tasa ta karye ya kurma uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da ya ji ya sulale kasa a
matukar galabaice ya kasa mikewa tsaye. Koda ganin abinda ya faru sai Zambaru ya bushe da mahaukaciyar dariya ta mugunta, sannan
yasa hannun sa na hagun ya zare takobin Imhal wacce ta makale a wuyan sa, jini yayi tsartuwa
daga jikin wuyan nasa,amma ko a jikinsa.
Kawai sai yayi jifa da takobin ya nufi jarumi Imhal wanda ke zaune a kasa, yana mai daga
lafceciyar takobinsa.
Gaba daya 'Yan kallon da ke cikin filin gasar sai suka dafe kai suka fara ihu da kururuwa domin
sun San cewa lallai Imhal ya zama gawa tasa ta kare.
Su kuwa attajiran da suka zabi Zambaru a matsayin jarumin gasar su suka sa kudin su na caca
a kansa sai suka fara yin tsalle da murna suna kida da rawa don sun San cewar kakarsu ta
yanke saka, sun gama zamowa manyan attajirai.
Wadan da suka zabi jarumi Imhal kuwa a matsayin jarumin gasar su sai suka fara kuka suka
kamu da tsananin bakin ciki sabo da sun San cewa lallai karayar arziki ta zo musu!!!
YAYA KARSHEN WANNAN GASA ZA TA KASANCE TSAKANIN JARUMI ZAMBARU DA
JARUMI IMHAL? TA YAYA JARUMI IMHAL ZAI TILASTAWA GIMBIYA LAMIRAT TA KAMU DA
SONSA? SHIN IMHAL ZAI RASA RAYUWARSA NE A CIKIN WANNAN GASA TA KAMBUN
JARUMTA KO KUWA ZAI LASHE GASAR NE HAR TA CIKA BURIKAN DA KE GABANSA?INA
LABARIN TSOHO IMZANU KUMA A CIKIN WANE HALI YAKE YANZU A CAN BIRNIN KISRA?
Mu hadu a RIJIYA GABA DUBU 4 don jin cigaban wannan kasaitaccen labarin.