Showing 27001 words to 30000 words out of 80273 words

Chapter 10 - KI YARDA DA NI COMPLET BY CUBADO.pdf

12 Jul 2025

2397


🎀🐾🎀

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSɷ📚âœ*

*💫DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*


_Page:18_

___________📖Basu wani dad'e suna jira ba se gata ta fito, sanye take cikin wata doguwar
rigar shadda, anyi mata d'inkin sinigalis, da fara'a ta k'araso parlourn tana fad'in lale maraba da
d'ana Maheer, ta fad'a tareda fad'ad'a fara'ar dake kan fuskarta,

Sunkuyarda kai Maheer yayi cikeda jin kunyar Ammin sannan ya gaisheta tareda tambayarta ya
samesu lafy? Da kulawa Ammi ta amsa tareda "fad'in ya mutanan gidan naku, fatan duk suna
lfy? Murmushi yayi wanda iyakarsa lips d'insa sannan yace" duk suna lfy Ammi,

Murmushin jindad'i ta saki sannan tace " masha Allah, wannan karon bakazo da sarkin tsokana
ba kenan? Dariya mujaheed yayi sannan yace" Ammi wai Abdul kike magana? Ai yanzu da
zakiga Abdul wllh Ammi bazaki ganeshi ba shakiyi, ya fad'a yana murmushi, zaro ido Ammi tayi
sannan tace "Abdul din girma ya k'ara sosai ne mujaheed? Kallon Ammi mujaheed yayi sannan
yace wllh Ammi bakiga yanda ya zama babban mutum ba, saura kad'an ya kamo Momys boy,
ya fad'a yana kallon Maheer yana k'unshe dariyarsa,

Wani d'an iskan kallo Maheer ya jefa masa sannan yace "heey dude wllh ka iya bakinka, wa
kake kirada Momys boy d'in? Batareda Mujaheed d'in ya kalleshi ba yace "duk wanda ya tsargu
to dashi nake, wata uwar harara Ammi ta wurgawa Mujaheed tace "ai gara Maheer akan irin
iskancin daka dinga tatawa kana k'arami, dariya shahida ta fito tanayi, sabida duk taji abinda

Ammi ta fad'a akan mujaheed d'in, a jikin Ammi ta jingina sannan tace" oh gaskiya na godewa
Allah daya tonawa wani asirin k'uruciyarsa har kunnuwana sukaji. Ta fad'a tana k'ara
k'yalkyalewa da dariya. Mik'ewa mujaheed yayi tareda binta da wani irin gudu da niyar ya
kamata, ihu ta dingayi tana zagaya perlourn tareda kiran sunan Ammi.
Da sauri Maheer ya mik'e yabar perlourn, lokaci guda kuma wani b'angare na zuciyarsa ya cika
da kewar mahaifiyasu, wadd baze tab'a mantawa da itaba a rayuwarsa, nanda nan abubuwan
da suka faru a rayuwarsa ta baya suka dinga dawo masa tsaf a k'wak'walwarsa tamkar a
lokacin abin yake faruwa, wasu irin zafafan hawayene suka dinga bin fiskarsa tamkar wani
k'aramin yaro, a haka ya fito daga gidansu mujaheed d'in ko sallama baiyiwa kowa ba illa
motarsa kawai daya bude ya fad'a ciki tareda murza mata keyy yabar k'ofar gidan, tabbas a
rayuwarsa daza'ace ya fad'i wanda yafi tsana a duniya da rayuwarsa gabad'aya wllh zece
Hajiya murja, a yanda yakejin zuciyarsa a yanzu wllh daze ganta seya kasheta har lahira sabida
tsanar dayayi mata,

Kallo d'aya zakayiwa Maheer a wannan lokacin ka fahimci tsantsar wutar fansar dake ci a cikin
idanunsa, gabad'aya idanunsa sun rufe, babu abinda yake gani a idanunsa se abubuwan da
suka faru shekaru Ashirin da suka wuce, wata irin k'arace ta gauraye a kan tintin da Maheer
yaketa sharara uban gudu, tun kafin yayi wani yunk'uri tsaida motar tini aikin gama ya gama, ji
kake gammmmm motocin sun had'u da juna.........

Tun daga wannan lokacin Maheer be sake jin komai ba se iface ifacen mutane sama-sama,
daganan kuma idanunsa suka rufe rub yadena jin komai......!





_Comment_
Nd
_Share_

_*🎀KIYARDA DANI...!🎀*_
🎀🐾🎀

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSɷ📚âœ*

*💫DEDICATED: to Sis naja'art*


_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*

_Page:19_

___________📖 iya muni kam wannan hatsarin yayi shi, cikin mintuna kad'an sega ambulance
ta hallara a gurin tareda motocin 'yan sanda, abinka da birnin tarayya, kallo d'aya zakayiwa
motocin da sukai hatsarin ka d'auke idanunka sabida yanda gaban motocin ya kwankwatse
tamkar an saka gudumar k'arfe an dandak'a su, banda salatin mutane babu abinda kakeji,
nanda nan jami'an tsaro suka fara gudanar da aikinsu tareda malaman Asibitin, da k'yar da
sid'in goshi suka iya b'anb'are murfin mitar da khabeer yake ciki suka fito dashi, kasancewar
akwai motar tanada isashshen matakan tsaro na Baloons ne yasa khabeer d'in beji wani ciwo
sosai ba, cikeda tsantsar tashin hankali gamida d'auriya Khabeer ya mik'e da k'yar, dukda
cewar shima ya bugu sosai a kansa da kuma k'afarsa hakan be hanashi k'arasawa jikin motar
maheer ba, sabida tsabar yanda ya tsorata da ganin yanda murfin motar ya wani lauye tamkar
an lank'wasashida gudumar k'arfe, babu abinda ke fita daga jikin k'asan murfin motar se jini,
dan haka hankalin khabeer ya k'ara tashi sosai,

Dak'yar ya iya had'a kalaman bakinsa ya k'wallawa malaman Asibitin kira, da wani mugun
sauri ya fara k'ok'arin b'alle murfin motar amma kuma ya kusa, hakanne ya jawo hankalin
Matakan tsaron da suke gurin, da gaggawa suka qaraso tareda taimaka masa wajen b'alle
murfin motar, seda sukai da gaske sannan suka samu nasarar zaro maheer daga cikin motar,
gaban khabeer ne ya buga. Dummmmm!! Sabida ganin yanda k'arfan dake saman sityarin
motar ya huda k'ahon zuciyar Maheer d'in, cikeda tashin hankali yayi baya tamkar ze fad'i, da
sauri *Asp Bala muhammad* ya taroshi cikeda zafin Nama, zaunar dashi yayi akan dandiryar
titin donya samu nutsuwa, sosai khabeer ya firgita da yanayin Condition d'in Maheer d'in,
sabida duk abinda ya faru laifin Maheer d'in ne, da ace yabi doka ya tsaya ya wuce wllh da duk
hakan bata faru ba, dukda cewar khabeer babban likitan tiyata ne (surgeon) hakan be hanashi
shiga tashin hankali ba, sabida a iya Rayuwarsa gaba d'ayanta be tab'a zama silar zubar jinin
dabba ba ballantana kuma mutum me rai!! Mik'ewa yayi da sauri sabida ganin yanda jini yaketa
zuba daga k'ahon zuciyar Maheer, tabbas idan aka tsaya b'ata lokaci tofa tabbas ze iya Rasa
Rayuwarsa ma gaba d'aya.

Matsawa yayi dak'ar zuwa gurin tareda bada umarnin abashi zaren k'arin ruwa, ada sunso suyi
masa gaddama, har seda ya daka musu tsawa sannan suka bashi abinda yake buk'ata, kallon
norse d'in yayi sannan yace "ki bani ma sarrafin yanka, babu musu ta mik'a masa, yana karba
ya saita askar ya yanka saitin gurin da k'arfen yake jiki sannan ya zura igiyar k'arin ruwan ta ciki,
wannan dalilin ne yasa zubar jinin ta tsaya, da sauri ya mik'e dukda irin juya masan da kansa
keyi, nan da nan ya bata Umarnin a kai Maheer *SUSHMAR INTERNATIONAL HOSPITAL
ABUJA, wanda yake a Centaral aria* ma'ana inda yake aiki, ada sunso suyi masa gaddama
amma kuma suka fasa sabida sun lura khabeer d'in ba k'aramin likita bane, nan da nan kuwa
suka sakashi a motar tareda khabeer d'in, suka d'au hanyar sushmer Hospital, Inda akabar Asp
Bala muhammad tareda sergen bashir suna gudanar da bikice a gurin domin gano cikakken
adreshin ma jinyacin, ko kad'an basu samu wata alama wadda zata iya nuna musu waye

majinyacin ba, abu d'aya kawai suka gani a cikin motar, Driving license d'in sa wanda sukaga
sunansa k'uruk'uri A jiki wato *MAHEER NASEER LAMIDO*, se kuma wayoyinsa da suka samu
suma, a haka suka tattara tareda kiran wayar sashin kula da titina ya sanar da su sannan suka
d'inguma zuwa Asbitin suma, 10minute ce ta d'aukesu zuwa Asibitin daga inda abin ya Faru, tun
kan su iso tuni har an shiga da Maheer tiyata, kasancewar khabeer yace mara lafiyan d'an
uwansa ne, seda ya tabbatar an shiga da shi sannan Khabeer ya yarda Dr. Abdullah ya fara
dubashi.

A b'angaren Maheer kuma Dr. Biru Sahastara Budde, shine wanda yake gudanar da tiyatar
tasa, ba indiye ne shi, aiki ne ya kawoshi Asbitin nasu Khabeer d'in, kaf Asbitin shine chf of
surgieon na Asbitin gabad'aya, indai K'warewa ce tofa Dr. Biru yanada ita, dagashi se Khabeer
wanda shine matemakinsa.
Masha Allah an kammala tiyata lfy, inda aka tura Maheer d'in zuwa d'akina musamman, gado
ne maidaidaicin a tsakiyar d'akin, gefensa kuma wata na'ura ce take nuna yanayin fitar
Numfashinsa, komai na d'akin a cikin tsari yake sekace a k'asar waje,

Bayan Dr.Abdullah ya gama duba lafyar Khabeer d'in ne Asp Bala muhammad ya samu zarafin
tambayar Khabeer d'in meye alak'arsa da Maheer har yace a kawoshi wannan tsadadden
Asibitin? Shiru Khabeer yayi sabida sam bayaso Asp wani abu a gamedashi, tabbas idan
yasan basuda wata alak'a da Maheer d'in tofa ya dinga bibiyarsa kenan har seyasa 'yan
gidansu sunsan Abinda ke faruwa, to amma idan yayi masa k'aryan ma still shine ze kwana a
ciki, bashida wani zab'i dan haka ya sanar da Asp gaskiyar abinda ya faru, shuru Asp yayi
sannan ya kalli Khabeer yace " Amma Dr. Ya kamata mu sanar da 'yan jarida sabida su sanar
koza'a samu iyayensa su gani wata qilah hankalinsu zefi kwanciya, da sauri Khabeer yace "a'a
Asp don Allah! Nidai banaso " yan jarida susan komai, da zarar sun sani tofa nima dolene
iyayena suji labarin Hatsarinnan, kuma wllh hankalinsu tashi zeyi wanda nikuma bazanso hakan
ba, don haka kabari nizan kula dashi har zuwa Ranar daze farka ya kuma dawo cikin haiyacinsa
sannan mu nemi iyayensa da kuma gidansu, da k'yar Khabeer ya shawo kan Asp ya amince,
wayar Maheer d'in Asp ya mik'awa Khabeer tareda lasisinsa na tuk'i, karb'a yayi tareda qurawa
katin idanu, a nan yaga cikakken sunan majinyaci. *MAHEER NASEER LAMID'O.*

Comment
Nd
Share

ZM chubado�
_*🎀KIYARDA DANI...!🎀*_
🎀🐾🎀

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾ'Ù‰ ASSɷ📚âœ*

*💫DEDICATED: to Sis naja'art*

_*WRITING BY: Zm (CHuBaDo)*_

*✨Special Gift for Hafsat Hafnan (my jika),.*

*_A Yau saukarwar takice my tunkuzar quliqulin zuciyata MOMYN FADYL, haka kuma my
abokiyar fad'a kokuma ince my abokiyar........����, don haka wannan shafin nakine kiyi
yadda kikaga dama dashi na mallaka miki shi halak malak, sannan abu na Qarshe kuma shine
Chubad'o tana sonki fisabilillahâ¤_*

_Page:20_

___________📖 shiru khabeer yayi tamkar wanda yake son tuna wani abu, a haka ya mik'e
dak'yar ya fito farfajiyar Asbitin, Dr. Abdullah ya hanga a prking space yana k'ok'arin shiga
motarsa, da sauri khabeer ya nufeshi tareda d'aga masa hannu, yana zuwa gurin murfin motar
ya bud'e tareda shigewa cikin motar ya zauna, tunda ya shiga motar Dr. Abdullah ya zuba masa
ido yana kallonsa cikeda rashin fahimta manufar Abokin nasa,

tab'e baki khabeer yayi sannan yace " why are you loking at me like that uhmm? Ya k'are
maganar tareda gimtse fuska,

Ajiyar zuciya Dr. Abdullah ya sauke sannan yace "bansani ba, me zan kalla a wannan
kuburarriyar fuskar taka da kake tuhumata haka? Murmushi khabeer yayi sannan yace " waya
san maka, kaga malam muje ka saukeni a gida nagaji jikina duk ciwo yakemin wllh, all i need
now is to reast. Ya fad'a yana wani yatsina fuska kamar wanda akayiwa dole seyayi maganar.
Harararsa Dr. Abdullah yayi sannan yace "ok ammadai kasan i'm not your driver ko? Dan haka
seka fad'a cikeda girmamawa tareda lank'wasa hashenka sannan ni kuma na taimaka maka na
kaika har gidan iyayenka yaro. Ya fad'a tareda gimtse dariyar data taso masa,


Shiru Khabeer yayi bece komai ba, shikuma Abdullah beja motar ba, sabida yace " yau kam
seyayi maganin Abokin nasa tunda be iya rok'ar abu cikin kwanciyar hankali da sanyi rai ba, sun
kusa 30mnt a haka ba tareda ko wanne yaceda d'an uwansa k'alaba, a k'arshe ma Dr.
Abdullah wak'a ya fara rerawa tareda k'ok'arin kunna redion dake manne a jikin motar, haushi
ne ya kama Khabeer dan haka ya shiga gallawa Dr. Abdullah wata uwar harara,

dariya kawai Abdullah yayi batareda ya kalleshi ba, ya cigaba da abinda yakeyi, illa kawai
k'udurtawa kansa da yayi cewar muddin Khabeer be rok'eshiba wllh baze kaishi gidan ba.
Kamar khabeer yasan abinda Abdullah d'in yake k'udurtawa a zuciyarsa yace "pls don Allah ka
kaini gida mana, wllh kaina ciwo yakemin sosai, a matsayinka na likita ya kamata ka fahimci
matsalata, i cnt tolerate any iskancin ka pls.

Wata uwar dariya Abdullah ya saki harda tafa hannu sannan yace "ohhhh ashe dai ka iya karya
harshe haka zuwa salon rok'o? Wllh nayi zaton kawai iy Rainin hankalin kafi iyawa. Ya k'are
maganar yana " yar dariya, wadda ta k'ara hasala khabeer d'in, seda ya gama yi masa iskanci
sannan yaja motar sukabar harabar Asbitin, a hanya ma be k'yaleshi ba har suka k'araso kofar
gidan, khabeer yana sauka ya kalli Dr. Abdullah tareda gyara tsaiwarsa yace "ohhhhh thank
you, but kasan wani abu? Wllh dama drivern taxi ka koma ba likitan ma jinyata ba, sabida na
lura babu laifi kasan aikinka na tuka mutane a mota, ya fad'a tareda sakin murmushi sannan ya
shige gida yabarshi nan tsaye,

dariya Dr. Abdullah yayi tarda barin k'ofar gidan, a ransa yana jinjina irin iskancin Abokin nasa,


Khabeer yana shiga cikin gidan be samu kowa a perlourn ba, sosai hakan yayi masa dad'i
sabida be shirya amsa tarin tambayoyin k'annan nasa ba, musamman Farouq da Usman,
muddin suka ganshi da wannan bandejin wllh ya shiga uku da tarin tambayoyin su, a hakan ma
dan iyayensu mata basa nan, a hankali ya fara takawa zuwa hanyar da zata sadashi da
d'akinsa, tsayawa yayi cak tareda zuba mata manyan Golden Eyes d'insa, sabida har ga Allah
beyi tsammanin ganinta a gurin ba,

Washe baki tayi tareda cewa yaya khabeer kag....... Kasa k'arasa maganar tayi sabida Bandejin
datayi arba dashi a nannad'e bisa kan khabeer d'in, nanda nan hankalinta yay masifar tashi,
da gudu ta nufoshi idanunta a cike taf da k'wallah,

tun kafin ta fara magana hawayen sun wanke mata fuska, kasa magana tayi illa fad'awa datayi
jikinsa tareda sakin wani irin kuka, kasa motsin kirki khabeer yayi sabida jin yanda k'anwar tasa
take kuka sosai,

Kokad'an beso Umaisa ta ganshi ba dama Rumana ce to dayasan ta yanda zeyi ya fahimtar da
ita ta yanda zata gane, amma se gashi wannan danger dince ta ganshi, yanzu koyaya zeyi da
itama oho!

hanunsa ya sanya ya zarota daga jikinsa tareda fara k'ok'arin share mata hawayen daketa
faman zubo mata babu k'ak'k'autawa.

Hannunta ya kama har suka isa perloursa sannan ya zaunar da ita a kan d'aya daga cikin
kujerun parlourn sannan ya kama fuskarta da tafukan hannunsa yace" its ok dear kukan ya isa
haka kinji? Kinga fa ba wani babban ciwo naji ba, kawai 'yar k'aramar kujewa ce so ki dena
d'aga hankalinki kinji k'anwata?
Kukan ta kuma saki tareda fad'awa jikinsa a karo na biyu sannan tace " ya khabeer wannan ne
k'aramin ciwo? Kallifa yanda fuskanka ya kumbura kamar ba kaiba, sannan a hakan kake
kiransa da k'aramin ciwo? "wllh nikam zan kira Abba na fad'a masa haliinda kake ciki yanzun

nan basai anjima ba. ta k'are maganar tana kuka sosai,

shiru yayi batareda ya iya cewa da ita k'ala ba, shirun daya ratsa d'akin ne yasa bakajin komai
se sautin kukan Umaisan.

Cikin sigar rarrashi da kuma dabara khabeer ya raba jikinsa da nata sannan ya kalleta yace"
kinga malama har sonawa zan fad'a miki ki dena rungumata? Bakisan kin girma bane yanzu
Umaisa, dafa ba yanzu bane k'anwata,

D'aga masa kai tayi dukda haka tana kukan bata dena ba, murmushi ya sakar mata wanda ya
baiyana ainihin kyawunsa, sannan yace " kinsan me nakeso dake?

D'aga masa kai tayi alamun a'a, fuskarta ya shafa sannan yace" kinaso na baki labarin yanda
akai naji ciwon nan?

Da sauri ta d'aga masa kai, shiru yayi yana kallonta sannan yace " zan fad'a miki amma da
sharad'in bazaki fad'awa kowa na gidannan ba, da sauri tace " wllh ya khabeer bazan fad'ama
kowa na i promise,

Shiru yayi yana kallonta sannan ya kwashe koma ya gaya mata, kuka sosai ta saka masa, seda
ya koma mata asalin yaya khabeer dinsa sannan ta shiga hankalinta tayi shiru,

Kallonta ya sakeyi sannan yace "zan dinga kaiki kullum gurin mara lafiyan ki dinga zama dashi
batareda kowa na hidannan ya sani ba, sabida banaso hankalin kowa ya tashi, sonake kidinga
kula dashi har mu samu ya warke sannan mu sallameshi shima ya koma cikin familynsa ko?

d'aga kai tayi alamun gamsuwa sannan ya mik'e ya shiga bedroom dinsa ita kuma ta koma
room dinta tareda fad'awa saman gadonta ta saki wani sabon kukan cikeda tausayin yayan
nata, dukda cewar Ya khabeer baya sakar mata fuska sosai amma dukda hakan tana sonshi
sosai sabida ya nuna mata k'auna tun tana k'arama, shiyasa bata k'aunar dukkan abinda ze
tab'a mata yayan nata, bama shi kad'aiba gaba d'aya ahalinta bata son wani abu ya samesu.


*GANO*

Tunda su Ummi suka iso garin aketa nan-nan dasu musamman ma Baba Binta, sosai tayi farin
cikin zuwan surukan nata, mutanan gari kuwa kusan kowa yasan da zuwansu, sabida gida-gida
Baba Binta ta dunga aikawa ana kai musu tsarabar da su Ummien suka kawo mata,

Idan dare yayi kuwa kwanukan turowon da ake aiko musu dashi ko Momyn fadyl bazata iya
k'igawaba sabida yawansu�, kunsan mutanan k'auye a kwai kara,

Seda sukai sati guda sannan suka fara haramar komawa Abuja, sosai Baba ta tada ballin cewar

itama seta bisu sun tafi tare sabida taje ta matsawa Usman da Farouq sesun fito da matan Aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login