Showing 12001 words to 15000 words out of 95753 words

Chapter 5 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf

24 Jul 2025

2961

a tsaye a parlor sai kace wani soja, bedroom dinshi ya nufa wayar shi
ya dauko ya dawo parlor ya zauna numbar Mimi ya kira yaji wayar a kashe, ranshi a bace ya aje
wayar yana tunanin ta yarda zaiyi ya gansu. Minti ashirin a tsakani ya k'ara kiran wayar kamar
da wasa aka dauki wayar, Muryar Namiji yaji yana sallama.Amsawa yayi Tare da gyara zaman
sa, Ya Aminu a nashi b'angaran ya gane muryar Amjadu da sauri ya gaishe shi, ya amsa babu
yabo babu fallasa, yace." Yallab'ai Ashe dai yaran nan da gaske suke yi." Amjadu yace."
Menene ? Aminu yayi masa bayanin yadda suka tada hankalinsu ganin wayar a hannunsu.
Murmushi yayi yace." Nine na bata domin mu dunga gaisawa, Ya Aminu yace." Allah ya saka da
alkairi gaskiya akwai alamun tambaya anan Yallab'ai idan banyi rashin kunya ina so in San
cikinsu wacece tayi dace da samun gwarzo miji irin ka."
Kai tsaye yace." Dukaninsu nake so zan aura lokaci guda idan zaku bani." Aminu yaji gabansa
ya fad'i yace." Yallab'ai a yi haka kuma."?
Murmushi yayi yace." Anyi an gama ni dai a gurina saboda haka ina so ka sanar da manya kafin
in turo magaba tana a tsai da magana domin baza a ja lokaci me tsayi ba."

Yaya Aminu yace." Insha Allahu Yanda kace haka za'ayi mungode sosai da wannan karamcin."
Sallama sukayi hade da kashe wayar.

********

Yaya Aminu ya dad'e zaune a gurin da yake kafin ya mike ya shiga gida jikinsa a mutukar
sanyaye, ya samu Umma na d'aurin sikari a rumfa zama yayi kusa da ita tare da fadin "Umma
kinji gagarimun abunda mutumin nan ya dauko mana kuwa." Umma tace"Wane mutumin ?
"Amjadu" Aminu ya fada jikinsa babu k'wari, tace "A ina kangan shi kai."

"Yanzu muka gama waya dashi, Wai yana son ya auri Asma'u da Mimi lokaci guda." Umma ta
saki ledar da take hannunta tana kallon Aminu cike da mamaki tace"Wannan wace irin magana
CE."? Yace." Wallahi haka yace" Shiru tayi tana nazarin maganar daga bisani tace"Mimi da
Asma'u Anya hadin yayi kuwa gaskiya Indai Yana so sai da ya zab'i d'aya a cikinsu." Aminu
yace"Umma mutum me girma kamar wannan ko mata hudu yace." Zai aura a lokaci guda za'iya
ya tsallake gidaje sama da miliyan yazo nan bamu aje ba bamu bawa wani ajiya ba, gaskiya ni
bazan iya fada masa haka ba."
Umma tace "Zaman kishi tsakanin Asma'u da Mimi akwai kwara Mimi sanyi hali Asma'u wayo
da rashin kunya gata itace k'arama bana son abunda zai tab'a zumumcin su." Aminu yace." Sai
dai idan sune suka so haka amma in sun hade Kansu babu wata matsala. Umma tace"
Shikkenan zanyi magana dasu." Ya Aminu ya mike ya futa jikinsa babu kuzari.
Mimi na daki a kwance ni kuma ina bakin rijiya ina wanki Umma ta kwala mana kira, aje sabulan
hannuna nayi na amsa hade da cewa "Gani nan zuwa Umma.

Ina zama Mimi ta shigo salo-salo Umma tace." Kun San abunda yake faruwa kuwa."? Girgiza
kaina nayi, tace" A cikin Ku Wa ya tab'a furtawa Kalmar so." Nace"Umma waye." ? Hararata tayi
tace"Wanda kuka sani mana." Kaina sai ya daure kawai domin ban fuskanci abunda take nufi
ba."
Tace"Ke ya baki KUDI hade da yi miki shopping ke kuma ya baki waya, shine nake tambayar
wacece a cikin Ku ya taba cewa wance ina son ki,saboda yau ya bujoro mana da bukatar son
ya aure Ku duk Ku biyun."

Das!das! Haka gababa ya dinga fad'uwa, baki na rawa nace"Umma ban...ban fahimce ki ba."
Mimi ta kalla tare da fadin"Ke dai nasan kin fahimce ni ko."? Mimi ta gyad'a kanta tare da
fadin"Na fahimce ki Umma a gaskiya ni dai Kalmar so bata tab'a hadani dashi ba sai da ko ita
Asma'u. " harara na banka mata nace"Ki fad'i gaskiya dai ko kinyi maganar aure dashi amma ni
meye shafe ni da har zai ce zai aure mu ni dake, babu wata kyakyawar alaka mybe ma duk
abunda yayi min saboda kene, Umma ni kam babu abunda ya shiga tsakanina dashi Mimi yake
so." Na fada raina a bace. "
Umma tace"Yanzu dai ya turo Aminu da sako saboda haka sai kuje Ku sasanta kanku."
[11/5, 7:40 AM] .: Tab'e bakina nayi na mike hade da barin gurin. Wankina na cigaba da yi ina
tunanin al'amarin lallai ma, wai yana so ya aure mu ni da Mimi kiji sai kace Wanda aka ce masa
mun rasa majin aure aiko sama da kasa zata hade bazan aure shi ba, Mimi taje ta aure shi, ni
gani nake ma kamar da wata manufa ya shirya hakan
Ina kallon Mimi ta futo salo-salo ta shiga dakinmu kallo na bita dashi ina tab'e bakina nace"Kin
had'u da aiki babba a rayuwar ki, Ya Aminu ne naga ya shigo cikin gidan da sauri hannunshi
rike da wayar Mimi ya nufi dakinmu, babu wayar ya futo, da alama shi yake kiranta. Zuciyata
naji babu dad'i naji ina son inji wace hira suke dashi, daurewa kawai nayi na cigaba da wankina,
ina jiyo muryar Mimi k'asa-kasa tana magana...... Kwafa! Kawai nayi cikin zuciyata
nace"wannan guy shigowar shi cikin al'amari mu ba k'aramin hatsari bane domin zai iya

wargatsa mana zumuncin mu." Sai da na gama tsaf! Sannan na shiga dakinmu ina k'okarin cire
kayan jikina Mimi ta kalleni baki na rawa tace." Asma'u kin San meye."? Kai tsaye nace"sai kin
fada."
A hankali tace"Wai Amjadu ne zai zo bayan sallahr Isha'i zai kawo mana tsarabar mu." Ba tare
da na kalleta ba nace"zai kawo miki tsaraba dai." Har da ke ai." Girgiza kai nayi nace" ni kam
bana son komai nashi, ban sani ba ko sai kunyi aure sannan zan daina jin haushin sa."
Tace"Waye ya fada miki zan aure shi." Cike da mamaki nake kallonta na kasa cewa komai ma,
na cigaba da saka kayansma tace" bazan Iya hada miji dake ba Asma'u, gwara in hak'ura in bar
miki shi." Muryar ta na rawa ta k'arashe maganar.
Sai ta bani tausayi mutuka nace"Mimi zaki iya hakuri da ruhin ki Ashe? Zuciyar ki tana mutukar
kaunar mutumin nan, idan kikayi haka to zaki jefa kanki a halaka, wallahi in har don ni zakiyi
haka, to bari kiji wallahi zan iya sadauakar miki da komai na rayuwata domin ki samu farin ciki,
ballanta d'a namiji ki kwantar da hankalin ki, ni ba bakuwar zafi bace, Sam Amjadu baya
gabana, a yanzu na bar miki shi zan cigaba da yi miki fatan alkairi har karshen rayuwar ki."

Kuka tq fashe dashi hade da rungume ni sosai take kuka nima sai na tsinci kaina da share
hawaye tace"Asma'u kin San Allah sai dai in mutu da sonshi mutukar kika ce baza ki aure shi
nima na hak'ura gwara soyayyar shi ta zama ajalina."

Yanda take fad'ar maganar tana shashshekar kuka hade da wani irin Abu yasa hankalina yayi
mugun tashi Mimi kuka take wiwi tana dukan k'irjinta hade da fadin"Me yasa zuciyata zakiyi min
haka.? Meyasa kullum kike azabtar dani akan son mutumin nan, Asmau da nasan inda zanje in
jefar da zuciya ta da najefar na huta da masifa" tana wani irin kuka ta k'arashe maganar. Hankali a tashe nace"Mimi meye haka? Mai yayi zafi? Kina so ki kashe kanki ne? Kike dukan
kirjinki." Cikin kuka tace" Asma'u gwara in mutu akan i n rayu a duniyar nan, kwata-kwata
zuciyata ba tayi min adalci ba, Asma'u na san ke Amjadu yake so amma saboda sharrin zuciya
kullum sai take fada min karya ne, ni yake so, kinga kuwa wannan zuciyar bata da amfani a
gare ni, Tunda tana kokarin sanya min abunda bazan samu ba." Cike da tausayin ta nace" Mimi
yaya zaki ce baza ki samu ba, kinga na farko dai mutumin nan ya fad'i kirkin ki da kyawun halin
ki kyawun zuciyar ki, ko wannan ma amsa ce ta ki gane cewar yana sonki, ki saka a ranki baki
da Miji sai Amjadu insha Allahu zan iya bakin kokarina gurin ganin tabbatuwar auran Ku."
Hawaye ne kawai yake zubo mata na sanya gefan zanina INA share mata, da kyar na samu tayi
shiru dadin da naji ma Umma ba taji ba yara sun cika gidan suna siyyaya.


*********
K'arfe shida dai-dai ya futo cikin kyakyawan shiri yau, shigar manyan kaya yayi wata lafiyayyir
galila ce a jikinshi skyblue dinkin babbar Riga da 'yar ciki taji lafiyayyan sirfani na masu hannu
da shuni yau mutumin Ku ya sanya hula inda ta kara futo masa da ainihin kyawun sa hade da
kwarjinsa, hannunsa daure da agogo shi mai tsada sai zabbuna na azirfa guda uku a ya tsunsa
masu wani irin ado hade da stons kana ganinsu kasan zasu ja kudi, takalmi me gidan ya tsa ne
a k'afafun shi kamfanin Gucci Dan Asali yayi kyau har ya gaji inda kasan wani ango, *Ni ko nace
ba dole ba za'a tafi neman aure* fuskarsa babu yabo babu fallasa ya futa, bodyguard d'insa

suka mike da sauri, hannu kawai ya daga musu ya karb'i key hannun Doh-doh da kanshi ya futo
da motar daga inda take mai gadi ya bude masa gate ya futa daga gidan suna daga masa
hannu Kai tsaye gidan granny ya nufa, bai shiga gidan ba sai da ya gabatar da sallahr magariba
a massalacin dake manne da gidan sannan ya shiga. Kamilar Dattijuwa na zaune kan dadduma da carbi a hannunta tana lazimi da alama ta idar da
sallahr ne, zama yayi a kujera Yana jiran ta kammala, minti goma a tsakani ta shafa addu'ar ta,
ta kalle shi bayan ta aje carbi tace"Babban mutum." Kallonta yayi cike da mamaki! Tace"Yau
dole in kira ka da wannan suna Wannan kwalliyar ta burge ni sosai don har na fara kishin ka tun kafin kaje inda zaka je." Dariya
ya sanya tare da fad'in"Ai kuwa sai da kiyi domin babu abunda zai hanani tafiya Neman aure,
auran ma na mata biyu kece ta ukun. Kafin in cika so ta hudun.
Hararsa tayi tare da fadin"Mace biyu ai bata kama ce ka ba kaji da guda daya, ta Isa." Yace." Ba
kin ce zaki shiga kauyika ki samo min maganin k'arfi ba."? Zama ta gyara tana kallonsa
tace"K'warai kuwa yau a can muka yini nida Iyami ga wani sassak'e can na karb'o maka Wanda
za'a dafa shi da jar kanwa ya zama shine ruwan shanka, insha Allahu mai maganin yace zaka
koma kamar zaki gurin k'arfi."
Dariya ya kyalkyale da ita Sam! Ya manta da b'acin ran da yake ciki yace." Toum kinga sai in
fara Neman aurena da hujja." Mik'ewa tayi tsakanin ta da Allah take fad'in"Ai mutukar zaka
diman ci shan maganin matar ka baza tayi takaici ba." Cikin dariya yace." To kawo min na fara
sha yanzu ya bi jikina nasan dai already kin had'a min." Tace"Yanzu kuwa a i mikewar da nayi
zan dauko maka ne, NASA Iyami ta k'ukkula maka shi a farar Leda kullum ka dinga shan d'aya."
Yace" maza ki kawo min uwargina." Bedroom dinta ta nufa, tana tafiya tana kara tisa maganar.

Shi kuwa bayan shigewar ta dariya ya kama yana mamaki wai shi Granny zata bawa maganin
k'arfi hummm! Yana zaune ta futo dashi cikin Leda viva sabuwa dal, dauru kusan ashirin ya
karb'a yana dubawa, dauri daya ya dauko yana sansanawa, cikin haushi da takaici tace"Meye
haka kuma zaka haramtashi fa." Cikin dariya yace." In na haramanta ma ai ni nawa ne kuma ni
zan sha." Tace" To fasa dauri daya kasha a gabana." Aikuwa ya fasa hade da zukewa yace."
Idan cikina yayi ciwo kece kin yadda." Tace"Na yarda wannan maganin bazai saka ciwon ciki ba
sai dai ma ya gyara ka." Yace." Naji to zauna muyi magana dake."
Granny ta zauna kusa dashi.
Yace." Neman aure zanje fa."
Granny tace." Alhamdullahi yau Allah ya kawo ni wannan lokacin. "
Gyad'a kansa yayi yace." Mata biyu zan aura ya kika gani. "
Shiru tayi tana nazari daga bisani tace"Ai Matsalar Ka ce abun ji." Murmushi yayi yace." Kar kiji
komai duk zan iya dasu.
B'ata fuska tayi tace"to naji amma dai ta biyun Hafsa ce ko."?
Yace."Wacece Hafsa kuma."? Tsaki taja tace"Kamanta kenan kana so ka hadani da Innar ka
kenan? Dama suna cewa sai abunda nace dakai kake yi baka zumunci dasu dukiyarka baka
Mora musu sai dai su ji a gari."
Shiru yayi kawai domin shi kanshi ya San baya kyautawa Sam baya ziyartar dangin mahaifiyar
sa, sun gani da korafin sun hak'ura dole yanzu ya gyara ko don kada duniya ta zage shi,
Granny ya kalla yace." Yanzu yaya kike so ayi. "? Zama ta gyara tare da fadin" Kaje ka nemi

auran Hafsa yarinyar na da kirki kuma tana sonka." Ya mutsa fuskar sa yayi wannan bukatar ta
granny baza ta yi wu ba, yace." Kiyi hakuri Granny bana so ayi Abu daga baya azo ana da an
sani kin fi kowa sanin halina bana rufa-rufa yarinyar bata yi min ba, zan dai yi kokari gurin ganin
naje mun gaisa dasu kuma zanyi musu alkairi sosai." Ajiyar zuciya ta sauke tare da fadin "Shikkenan to Ubangiji Allah yayi maka zab'i na alkairi "
"Ameen yace yana kallon agogon dake daure a hannunsa.
Mik'ewa yayi yace." Insha Allahu komai ya dai-dai ta zamu je ki ga kawayen naki ko kuma in ce
kishiyoyin naki." Tace",Allah ya kaimu yanzu ma ace dasu ina gaishe su."

Har ya futa ta bishi a bays hannuta rike da ledar magani tace." Ka manta kuma." Shiru yayi
yana nazari,hannu ya mik'a ya karb'a sukayi sallama ta koma gida

Mota ya bude ya zura ledar maganin kusa dashi ya zauna sosai hade da kunna motar mai gadi
ne ya mik'e da sauri ya bude masa Gate ya futa daga gidan.

Kai tsaye,....... Gidansu Asma'u ya nufa.








*5/November/2019*
[11/6, 5:13 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*




*Mallakar_BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN
ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA
KUDIN TA.*




*42*

Yana tafe cikin mota yana sauraron wak'ar Joy mutumin shi, gyada kansa yake da alamun
Yana jin dadin wak'ar, sai da ya kusa shiga unguwar tasu ne ya kira Mimi a waya, lokacin muna
zaune a tsakar gida bayan mun gama cin abunci muna ta fama da wasu shegun cinna ku da
suka addabe mu, dama duk lokacin damuna haka suke futowa a gidan ta cikin ramuka suyi ta
cizon mu. Wani ne ya cije ni a hannuna ina ta faman sosawa hade da haska gurin da toch din
wayar Mimi neman sa nake in kashe, kira naga ya shigo wayar *Heartbeat* abunda na gani
kenan, siririn tsaki naja hade da mik'a mata wayar ta karba hade da tashi daga gurin, Umma ta
bita da kallo tana girgiza kanta. Minti uku sai ga ta ta futo da wayar a hannu tana sink'e kai
Umma tace "Waye ya kira ki harda barin gurin."?
A hankali tace" Amajad ne, yazo Umma." Sakin fuska tayi tace" To masha Allahu, alamu sun
nuna ke yake so, tunda gashi ya kira ki a waya yazo zance maza je ki shirya Ubangiji Allah ya
sanya alkairi." Umma ta k'arashe maganar cike da murna da farin ciki.

Mimi ko kunya ta shiga dakinmu da sauri, sai abun ya bani mamaki ganin d'azu take kuka tana
cewa ta hak'ura dashi ta barmin amma dubi yanda take rawar kafa saboda zuwan sa. Ni dai
shiru nayi kawai, har ta futo Cikin shiri sai zabga kamshi take. Tace"Umma sai na dawo." Umma
tace." Ki gaishe shi da kyau kuma ki iya ladabi da biyyaya." Tace"To tana k'okarin futa sai farin
ciki take.
Hira muke da Umma sama-sama nake jin ta domin a lokacin bana cikin hayyacina wani irin lami
bakina yayi sai kace mace mai yaron ciki haka nake jin wata irin kasala da sagewar gwiwa jiki
babu k'wari na shige dakinmu hade da fadawa kan katifa ruf da ciki rumtse idona nayi sam
zuciya ta babu dad'i ni kadai nasan abunda yake damuna.
Parking yayi bakin hanya hade da kunna Fitilar wayar sa, unguwar duhu dumd'um!! Sai hasken
masu ababen siyarwa dake kan hanya, masu charge masu wanki da guga, masu provision da
sauran su, yaji dadin haka domin baya son ya futo har jama'a suka gane shi, wayar Mimi ya
kira hade da fada mata gashinan ya iso. Lokacin tana kan hanya. Inda ya Saba parking ta nufa
cikin yanayin tafiyar ta tsallaka titi tayi ta isa kusa da motar hade da d'an kwankwasa wa, a
hankali ya bude motar tare da haske fuskar ta da wayar hannunshi, sakin Fuska yayi yace."
Momy na tafi ta kowa." Mimi tayi wani fari da ido. Yace." Shigo ciki mana." Cike da kunya ta
shiga motar ya mai da murfin ya rufe. Kashe ta yake da kallonsa na goggun 'yan duniya,
sunkuyar da kanta take tana fadin"Sonka zai iya kashe ni." Cikin zuciyar ta tayi maganar
Yace." Bamu gaisa ba Momyna kunyar ki na bani mamaki tana d'aya daga cikin abunda yasa
naji kin kwanta min a raina"
Mimi tayi murmushi yace." Ok ni ne yafi kamata na gaishe ki tunda nine danki. Kinga kuwa dole
in nemi albarka." 'Yar dariya tayi sai kace sokuwa, tace"Ina wuni"?

Cikin sangarta yace." Umum!! Nine zan fara gaishe ki." Mimi taji kamar tana yawo kan gaji mare
don shauki gaskiya guy nan ya iya love.

Yace." Ya jin dadin ki Monyna hope komai lafiya Lou."
"Alhmdullahi wallahi."
Tafad'a fuskarta dauke da murmushi
"Ina *Asma'u?*
ya tambaye ta kai tsaye!!! Wata irin fad'uwar gaba taji jin ya baci sunan Asma'u.
Bakinta na rawa tace" Tana gida."
"Owk d'azu mun Dade da yayan Ku a waya ina fatan duk kunji sak'ona ni Amajadu zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Connection failed: SQLSTATE[HY000] [2002] Operation not permitted