Showing 21001 words to 24000 words out of 95753 words

Chapter 8 - BABBAN YARO Part 2 By Binta Umar Abbale .pdf

24 Jul 2025

2960

daya Dari
biya abun dubu goma dubi biyar. Mutanan gari sun kunzige kudinsu suna jiran ranar domin su je
su kwaso garab'asa.


***
Washe gari muka tashi da jiki a sanyaye Mimi ta rame lokaci guda, shi ko Ya Aminu dama tunda
Kawu Yunusa ya Sanar dashi cewar an fasa karb'ar kud'in Mimi ya watsake ko da ya tashi da
safe tamkar Wanda bai yi ciwo ba, yanzu Mimi CE abun tausayi so ya tasa ta a gaba.

Da kyar na rarrashe ta ta Karya kummalo
Umma ta tsaya bakin kofar mu tana fadin "Menene wai naji kuna takkadama."?
Zuciyata tace kawai ki fadawa Umma ko menene ko Allah zai sanya ta fahimta."
Kaina a kasa nace"Umma ina ganin wa....Shiru nayi na kasa magana.
Umma tace." Meye kika yi shiru."?
Bakina na rawa nace"Umma don Allah Ya Aminu ya janye kudirin sa a kan Mimi akwai cutar wa
a ciki, ya kamata Mimi a bata zabin zuciyarta Ya Aminu Namiji ne shi zai iya jure komai kinga
Mimi ko yarinya ce mai karanci shekaru gata kuma mace."
Shiru Umma tayi tana nazarin magana ta.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace"Kin yi gaskiya Asma'u ni ma zuciyata batayi na'am da
haka ba, saboda ina gudun zagin jama'ar gari tunda duk sun San komai Da Aminu da ke da
Mimi duk daya kuke a gurina babu Wanda zan ce nafi so, amma kina ji da bakin ki tace ta
amunce da Aminu kuma ko jiya Kawun Ku ya maimata min maganar babu gudu babu ja da
baya tunda sunyi magana da mahaifin ta a waya yace ya bashi wuka da nama, Babansu Munnu
ma har dashi cikin maganar kin ga bani da ta cewa."

Nace "Umma kina da ta cewa mana don Allah ki sanya Ya Aminu ya janye magana.....kafin in
karasa naji saukar Mari a kuncina Ya Aminu ne tsaye a kaina yana wani irin huci! Yace." Kina so
naci ubanki Asma'u, wato kina zu ga Umma kina zuga Mimi kan su bujirewa Bukatata ko me? Ni
kinsan halin da Zan shiga idan na rasa ta, ko kinsan irin son da nake mata, mutukar ina Raye a
duniyar nan bani da mata sai Mimi, dake da ita kuje kuyi abunda zakuyi akin gama ya Riga ya
gama."
Yana gama maganar shi ya fuce daga gidan a fusace!
Umma barin gurin tayi ni da Mimi mukayi shuru muna sak'e-sak'e

A hankali naji tace"Asma'u don Allah kar ki kara wata magana kan al'amarin nan, kinji tunda dai
kince zaki taya ni addu'a tom na gode miki.".
Murya na rawa take maganar
Nima naji zuciyata ta karye nace"Mimi sai dai idan gani nayi am d'aura muku aure da Aminu
shine zan daina magana domin nasan ki nayi a banza ne, bakin alkami ya bushe, amma
magana kan al'amarin yanzu na fara."
Shiru tayi tans kallona.
Mik'ewa nayi na futa daga dakin zuciya nayi min zafi!



*RANA BATA KARYA*

Manyan attajirai da manya manyan 'yan boko 'yan siyasa masu mak'ami daban-daban Sarkin
Kano sarkin Zazzau Sarki Katsina Jama'ar gari tsakunsu da kwarkatar su, sun hallara a wannan
guri.

Hayaniya ce ta tsananta tare Da jiniya wannan ya tabbatar min da cewa me girma governor ne
ya iso bani kadai ba, duk wani Wanda yasan da akwai dabi tsakanin *Amjadu* da me girma
*Governor* sai da yayi mamaki, tuni jama'ar gari suka fara ihu!! Suna fadin abunda ransu yake
so ga me girma governor.
Ko kunya babu me girma governor ya futo daga mota tare da jamarsa ya dinga ratsa jama'a
Yana daga musu hannu hade da washe musu baki wai shi lallai ga governor tsagerun matasa
masu goyon bayan Amjadu suka sanya ihu!! Da dariya suna fadin abun da yayi musu kan
governor din, wasu na fadin"Ba mayi!!!! Sai da 'yan sanda suka tsawa tar sannan hayaniyar ta
lafafa, can gurin da aka tanadar wa manyan baki governor ya nufa, police na biye dashi a baya
domin sun tsorata da irin ihun da jama'ar gari sukeyi,
Sai da suka ga ya zauna sannan suka koma gefe suka tsaya da bundigun su a hannu.
Can na hango Mai citta shida abokanan shi, sai zare ido suke.
Limamin babban massalacin jama'a na garin kano ne ya tashi ya bude taro da addu'a yayi
karatun alkur'ani me girma sannan daya baya daya manya baki suka fara jawabi kowa yana
yaba kwazo da jajircewa irin ta Amajdu
'Yan jarida a gurin baza su kirgu ba, domin wasu jamar gari na gida kowa na gaban TV Wanda
bashi dashi kuma kunne shi mak'ale da waya ko redio yana saurara.

Lokacin da Amjadu ya futo zai yi Jawabi Ihu!! Jama'ar gari suka sanya tare da fadin"Sai kayi fari
me farar aniya ka iya ka huta *AmjaduAbulAbas* muna biye da kai insha Allahu *2004* taka ce
sai ka zama shugabanmu." Ihu! Kawai suke, sun hana aji bayanin da yake, da kyar jami'an
tsaro suka shawo Kansu suka yi shiru. *Amjadu* yayi jawabi me gamsarwa jawabin da ya ratsa zukatan al'umma Su Kansu manyan
gurin sun jinjina masa kuma sunyi masa fatan alkairi.mai Martaba Sarki yaji dad'i sosai da
samun hazikin Yaro a garin shi yana mutukar alfahiri da shi.

K'arfe goma sha biyu da rabi taro ya watse saboda ranar juma'a ce za'a tafi massalaci, nan
Amjadu ya bada sanarwar cewa jamar gari suje massalaci su dawo bayan an idar da sallahr
za'a bude company daga nan har zuwa goma na dare.

Haka akayi kuwa bayan an sakko jama'a sukayi ta tururwa company suna kwasar garabasa.Sai
k'arfe daya na dare sannan aka samu saukin Jama'a.

*****

Duk abunda yake faruwa a gari muna da labarin shi munji a redio Kuma mun gani a TV dake
ranar sun bar mana wuta, abun mamaki Mimi yini tayi tana farin ciki.
Amjadu ya sha addu'a gurin Umma, aunty Hauwa ma ba abar ta a baya ba, kusan a dai-dai ta
sahu guda tayo da kayan da bata koma gidan ta ba sai bayan sallahr Isha'i.
Ni ko tunda nayi masa kallon farko a TV ban sake kallonsa ba daga k'arshe ma tashi nayi na
bar gurin naje na tsiri ninkin kaya ina tunin yanda Allah ya dauka kashi a duniya 'yan da yake da
kyauta da son talaka da yanda yake da farin jinin jama'a, yanda yake da ibada, amma yana
aikata sabon Allah domin zina mugun aikine Wanda Allah ya hana shi, kawai sai na tsinci kaina
da yi masa addu'ar shiriya naji wani irin tausayin shi, babu uwa babu uba ga makiya da d'umbun
masoya gaba da baya, Allah ne kadai yasan abunda zai zama nan gaba, a fili nace"Ubangiji
Allah ya kare ka daga sharrin ma su sharri Allah ya shirye ka shirin addinin musulunci yasa ka
daina aikata zina."



******
Yau sati guda kenan da faruwar al'amarin Wanda yayi dai-dai da kwanaki goma da afkuwar
al'amarin Auran mu komai ya dai-dai ta, tun ranar da ya kira wayar Mimi na kashe ban kara
kunnawa ba sai yau, sun kawo wuta na jona ta a chaji.
Mimi ta shigo dakin jikinta babu k'wari ta zube kan katifa.
Binta nayi da kallo. Nace"Mimi kinga yanda kika rame kuwa."?
Shuru tayi min
Nace"Wallahi Ki yiwa kanki fada ni yanzu kin daina bani tausayi haushi kike bani wallahi, wai
Amjadu shi kadai ne namiji a duniyar nan."
Shiru dai tayi min bata ce min komai ba.
Tsaki naja na futa daga dakin.

***
Tun lokacin da ya kira wayar yaji an kashe bai Kara kira ba yasan Mimi baza ta kashe masa
waya ba.
Tabbas Asma'u ce shiyasa bai kara kira ba.
Yana zaune gefan bed da wayar a hannunsa numbar ya kira sai yaji ta shiga har ta katse ba a

dauka ba, kira ya kara yi a karo na biyu nan ma ta katse ba a dauka ba, a je wayar yayi hade da
Jan tsaki a fili yace." Mata masu aji kenan." Mik'ewa yayi ya futa parlor.


Mimi na kwance a dakin lokacin da yake kiran wayar tarin da take ne ya hanata d'aukar wayar
har ta katse.
Cikin wani irin mugun tari da galabaita ta mike zaune hade da dafe k'irjinta tana cigaba da tarin
sosai wa
[11/8, 6:21 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*




*Mallakar_BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN
ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA
KUDIN TA.*



*45*


Ni da Umma muka shigo dakin da sauri!
Mimi na durkushe ta rike k'irjinta tana ta tari.
Da sauri Umma taje ta rike ta ni kuma ns dauko ruwa hade da fasawa na dago kanta ina bata,
k'arfin tarin ya hanata ta karb'i ruwan.
Umma tace"Maza kije ki dauko gishiri a kicin.
Cikin tashin hankali na nufi kicin din na dauko ledar gishiri
Umma ta dangwala a hannuta ta sanyawa Mimi a baki tana Dan bubbuga bayanta hade da yi
mata sannu.
Mimi idonta ya rufe sosai take tari! Da haki tare da hawaye.
Ni da Umma duk mun shiga tashin hankali.
Nace"Wallahi Umma jiya da daddare haka ta dinga yi da kyar tayi bacci."
Umma tace"Ikon Allah watak'ila busawar sanyin nan ne,.
Nace"Ina jin hakane " cikin ikon Allah tarin ya lafa sai dai haki da take yi.
Umma ta rungume ta a jikinta tana yi mata sannu
Ya Aminu ne ya shigo dakin ya tsaya bakin kofa fuskarsa s daure yake tambayar menene?
Umma tace"Mimi ce babu Lafiya in anjima ka siyo mata maganin tare saboda dare."
Wani irin kallo yake wa Mimi daga bisani kuma ya tab'e bakinsa Yace. " Umma ki rabu dasu duk

karya ne,nasan wannan'yar iskar ce take zugata."
Umma ta bata fuska tare da fadin"bana son wannan halin naka Aminu ina ruwan Asma'u anan.?
Futa yayi daga dakin ransa a bace.
Nace"Umma shifa bazai taba ganewa ba tunda ya samu ya kubuta Mimi CE abun tausayi.'
Shiru Umma tayi min, sai da taga Mimi tayi bacci sannan ta gyara mata kwanciya ta futa daga
dakin jikinta duk babu k'wari.
Kallon Mimi nake gwanin tausayi duk ta rame tayi Dan wuya k'irjinta sai sama yake yana kasa
alamun tana jin jiki.

Jikina babu k'wari na kwanta kusa da ita ina tunani
Ringing din wayar naji wacce take jone a chaji na mike da sauri hade da dauka
Babu sauk'i a murya ta nayi sallama

Ajiyar zuciyarsa naji a hankali yace." Ya kike mata masu aji."!! Sama nayi da murya ta nace."
Ina nan kallo kamar tsumma a randa, amma kasan da cewar zuciyar da ka yaudara da sunan
so kake azabtar da ita tana cikin gararin rayuwa tana cikin halin ha'ulai kullum bata da sukun
hawayen idonta ya kasa daina zuba....... Katse ni yayi kafin in karasa magana ta yace." Wannan
wace irin banzar magana kike min kina yi kina daga murya kamar kina yi da sa'an ki, kiyi min
magana yanda zan fahimci me kike nufi ."

Haushi maganar shi ta bani saboda haka nace "Da Hausa nake maka magana ba da harshe
nasara ba, nace" D'aya zuciyar daka yaudara tana cikin halin ha'ulai da damuwa saboda haka
in ta shiga mugun hali to kai ne sila."
Lokaci guda ya fahimci inda maganar ta ta dosa.
Babu ya bo babu fallasa yace." Bani Momyna mu gaisa. "
A hasale nace"Ya ina yi maka magana daban kana yi min wata maganar, Mimi dai na bacci
Wanda muka samu ya dauke ta da kyar don haka bazan tashe ta."
Na k'arashe maganar tawa a kufule!
Wannan karon akwai sassauci a muryarsa yace." Nace kiyi min bayani dallah-dallah yanda zan
fahimta ni har yanzu ban gane abunda kike nufi ba."

Nace"Mimi na kwance babu lafiya tana jin jiki saboda sonka shine Abunda nake nufi. Ina jinsa
yayi murmushi cikin nutsuwa yace." To waye mai laifi tsakanin ni da ita da iyayen Ku."?
Da sauri nace "Kar ka sake ka zage mu ko kafad'i bak'ar magana kan iyayen mu."
'Yar dariya naji Yayi yace." 'Yan matana kenan, dags magana zan zage iyayen Ku cewa nayi
waye mai laifi sai ki bani amsa ta."

A fusace! Nace "Kai kasani."
Yace."OK naji bani Momyna muyi magana. "
"Kasan Allah bazan tashe ta ba wai me ma zaka fada mata ne bayan ka yaudare ta."
'Yar dariya yayi tare da fadin"Ina ruwan ki? Ke dai nace ki bani ita." Shiru yayi sai kuma ya
cigaba da cewa"Kina maganar na yaudare ta, nifa ita nace s kawo wa kud'in aure akayi mistake
aka kawo miki, bayan nan Kuma maganar Aminu ta futo, ai ni ne ma zan ce an yaudare ni an

bani wacce bana ra'ayi."
Tsaki! Naja na kashe wayar ganin yana nema ya Mai da mutane mahaukata.

Ganin magariba ta kusa ne yasa na tashi Mimi domin baccin magariba babu kyau.
Lokacin Ya Aminu har ya kawo magunguna dasu Lemo da ayaba sai kai wa yake yana kawo
wa, in muka hada ido ya buga min harara.

Muna idar da sallah na sanya Mimi a gaba taci abunci sannan na bata magunguna sai ta
kwanta.
Nida Umma muna addu'ar Allah yasa kar tarin ya kara sark'e ta.

K'arfe Tara dai-dai naji ringing waya tsaki nayi Dan nasan wanene. Dauka nayi hade da sallama
ba tare da ya amsa min ba yace." Ki futo yanzu ina jiran ki."
Ya kashe wayarsa.
Umma na kalla naga tana kallona nasan wayar handsfree ne taji komai
Tace "Ki tashi kije su manya mutane basa son jira."
Nace"Umma wane irin zance ne wannan k'arfe Tara na dare."
Umma tace"Sai kinyi surutun dai ko ki tashi kije Kuma kar ki sake ki futa da wannan kayan na
jikin ki, masu kaurin hayak'i Dan dare yayi ma da sai kinyi wanka, ki gyara fuskar ki duk ki goge
wannan maikon na fuskar ki, don nasan bs hankaline dake ba sai ki futa haka.

Mik'ewa nayi na shiga dakinmu wallahi dai dai Umma tace in sanja kaya amma da bazan sanja
ba, material dinmu na anko na dauko na tusa a cikina ina nishi na fesa turare na me saukin kudi
goge fuska ta kawai nayi da abun goge hoda na yafa mayafi karami. Takalmi plate na sanya a
kafata na futo Umma ta bini da kallo cikin zuciyar ta tana tunanin kayan jikina domin sun futo da sassan jikina,
Shiru kawai tayi nace"Umma na tafi."
"To ki nutsu dai banda kaifin harshe nasan halin ki."
Raina babu dad'i na futa daga gidan ina mamakin kallon da Mimi take Min tunda taga na futo.


Dake dare ne kuma babu wuta a gari yasa bansha kallon gurin Samarin layinmu ba.
Na karasa har inda motar tasa take fake.
Sabuwar mota ce yazo da ita, fara tas! Daga yau ya fara shigar ta sai walwali take motar tayi
kyau kuma daga ni zata ja kudi sosai.
Cikin zuciyata nace"Kaji dadinka yanda ka samu duniya Allah ya baka lahira."
Dake motar bata da duhu yana hangota sosai yake kallonta har ta k'araso ya bude motar tare
da fadin"Bisimillah.." Kin shiga nayi na jinga jikin motar tare da fadin"Yau kam bazan shiga
motar ka ba, domin bansan inda zaka kaini ba, in ka damu ka futo waje sai ka fada min abunda
ya kawo ka."

*8/November/2019*
[11/9, 8:14 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*



*Mallakar_BINTA UMAR*



*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN
ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA
KUDIN TA.*




*46*



Nafi minti goma da magana banji motsin sa ba, nace"Zan tafi tunda dai baza ka futo ni kam na
daina shiga motar ka."
Daga ciki naji muryar shi a hankali yace." Ki shigo ciki shi yafi arziki ko kin manta da yanda nake
cikin jama'a ? Yanzu zaki zama abun kallo, bayan haka kuma ga sauro a gurin , bana kaunar
cizon sauro."
Nayi mamakin yanda yayi min magana Cikin kyakyawan lafazi nace" kayi alk'awarin baza ka
kaini ko ina ba."?
Kai tsaye yace." Eh nayi alk'awari."
Motar na shiga wani irin sanyi da k'amshin sa suka cika min hanci.
Ina kokarin rufe motar ne ya ziro hannunsa ya rufe jikinmu ya had'u gurin haka.
Nace"Ka gani ko."?
Kallona Yayi tare da fadin"Me kuma nayi."? Shiru nayi masa ina dauke kaina.
Yace." Duk kin sanya sauro ya cika min mota dole a kaita car wash gobe. "
Ni dai bance masa komai ba.
Gyaran murya yayi tare da fadin"Babu gaisuwa ne."?
A hankali nace "Ina wuni."?
" Lafiya Lou ya halin ki."?

Ya fada yana min wani irin kallo.
Kauda kaina nayi zuciya ta tana wani irin bugawa bana son in kalleshi ballanta in rasa kuzari na
shiyasa nake kiyayewa yana sanye da kananun kaya As'usuel ya kyau kamar ka sace ka gudu.

"Ya jikin Momyna."? Yafad'a idanunsa tsaye a kaina."
Nace"Da sauk'i dai."
"D'azu kina min magana ban fahimta ba, me yake damunta."?
Kai tsaye nace " Ciwon so."?
'Yar dariya yayi hade da Sosa kansa yace." Allah ya bata lafiya, 'yan mata da dama suna fama
da wannan lalurar a kaina."
Kallonsa hade da bata fuska nace "Naga dariya kake yi kamar babu abunda ya dame ka, kasan
kuwa Mimi tana jin jiki."
Girgiza kansa yayi yace." Ban sani ba, amma yanzu zan sani muje ki rakani in siyo mata kayan
dubiya sai kiyi min jagora gidan naku."
Nace." Indai Lemo da ayaba ne kayan dubiyar bakin layinmu ma ana siyarwa."
"Ba irinsu zan siyo mata ba."
Yafad'a yana wani lumshe min ido tsabar munafurci.
Nace"Ni kam babu inda zani in ka shiga ka duba ta haka babu Wanda zai ce maka don me."
Siririn sajansa ya shafa hade da yin kasa da murya yace." Momyna tafi k'arfin haka a gurina ke
dai kice baza ki rakani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login