Showing 1 words to 3000 words out of 56183 words
Chapter 1 - WATA SHARI'AH 1 TO END COMPLETE Book By Amrah Auwal Mashi.pdf
[6:55pm, 8/01/2017] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: *WATA SHARI'AH* í ½í¸ª
í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“
í ½í¸ª
Na Amrah A Mshí ½í²“
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
Ina farawa da sunan Allah mai rahama mai jink'ai, dukkan yabo da godiya sun tabbata ga
Allah mad'aukakin sarki, tsira da aminci su k'ara tabbata ga shugabanmu annabi Muhammadu
(SAW) tare da Alayensa, na godewa Allah mai kowa mai komai daya bani damar sake kawo
maku wannan labarin nawa.
Wannan labarin mai taken *Wata shari'ah* k'irkirarren labarine, banyishi dan cin zarafin wani
ko wata ba, nayine domin fad'akar da masu hali irin na jarumar cikin littafin, ina fatan za'a
amfana da abunda za'a karanta a cikinsa, ina kuma fatan zakuji dad'inshi.
Jinjina, godiya, bangirma ga uwa mabada mama, k'ungiya mai albarka *Nagarta Writers
Association,* fatana a kullum Allah ya k'ara d'aukaka manaku, Allah ya k'ara baseerah, hikima,
ilimi, hazak'a da kuma zak'in hannu.
Godiya gareki *Aunty Maijidda Musa* dole na yaba miki saboda yanda kike k'ok'arin yad'a
littattafanmu, muna alfahari dake a matsayinki na masoyiyarmu baki d'aya.
*RAZ* daku nake tak'ama da tink'aho akoda yaushe, da bazarku nake taka rawa, banida
kamarku aduk *online writers,* Allah yabar zumunci yabarmu tare.
Sauran masoyana na duk fad'in duniyarnan ina k'aunarku kuma ina alfahari daku, inama ace
baki zai iya lissafoku baki d'aya? Aikuwa dana zage damtse wurin jera suyenku tare da sanar
daku kaf sak'unanku suna isowa gareni, saidai kuma kash! Ba abune mai sauk'i ba saboda
yawanku, saidai ince nima ina k'aunarku kuma ina alfahari daku.
*RAZ NOVELLA one and two* ina godiya gareku, Allah yabar minku da soyayya da k'auna.
********************************
{~1~}
Yammaci ne mai cike da ni'ima,
iska na kad'awa ta ko'ina, ganyaye sunyi tsanwa shar abun gwanin ban sha'awa, sama tayi
luf da hadari kwance a cikinta, ko'ina yayi tsit babu ko kukan tsuntsaye, kowa ya ladaftu a
gidansa dan gudun saukowar ruwan sama.
Tuk'i yake da k'arfin gaske kamar mai shirin tashi sama,
Daga gefenshi (kujerar zaman banza) wata mace ce ta hakimce fuskarta sanye da dark
glasses, kyakkyawace ajin k'arshe, tanata taunar chewing gum cikin natsuwa take kallon yanda
namijin yake sharara gudu abunshi.
"Dan Allah Honey ka rage gudun nan da kake, ka bimu a hankali mana" ta fad'a bayan ta
zare glasses d'in dake idonta.
"Ai dolece tasa kikaga ina gudun nan Sultana, bakiga yanda saman take bane? Ina gudun
kar ruwan sama ya saukone, kinsan watan August ruwan sama baya alerting kafin yazo saidai
kawai aganshi yazo, kuma da k'arfi yake zuwa yanda dole sai munyi parking har sai lokacin
daya tsaya sannan mu tafi" ya bata amsa still yana shararar gudunsa.
Shiru tayi bata kuma fad'in komai ba, ganin ya k'ara yawan gudun da yake yasa ta sake
maimaitwa,
"Abban Hafsa dan Allah ka rage gudun da kake, kasan fa bana son gudu da mota saisa
kakeyi".
Bai ko kalleta ba yaci gaba da tuk'inshi.
"Nikam wai kodai duk cikin fushin nayi winning d'inka a shari'ar yaune yasakaka wannan
gudun tsiyar? Nikam karka zubar damu garin fushinka".
A fusace ya rage gudun motar ya koma tuk'ata slowly,
"Sultana an fad'a miki wai naji haushine dan kinyi winning d'ina shari'ar yau? Kika sani ma ko
da gangan na barki kikayi winning d'in nawa dan na ganki sabuwar lawyer ne?"
"Kaidai fad'i gaskiya Honey" ta fad'a cikin zaulaya tana masa dariya.
"Kaga ai gashi yanzu nasa ka rage gudun ko? Inda ace ban maka hakaba da yanzu kana nan
kana sharara gudu damu".
"Au! Haka kika fad'a? Zakija inci gaba daga inda na tsaya kuwa" ya fad'a yana k'ok'arin
cigaba da gudunshi.
"A'a nidai dan Allah kayi hak'uri tunda ai mun kusa isa gidan ma".
Tana gama fad'in haka kuwa ruwan sama ya sauko da k'arfin gaske mai had'e da iska sosai,
"Kinga abunda nake fad'a miki ko? Inda kin bari baci gaba da gudun aida tuni mun isa",
"Ehh nidai na yarda kabi a hankali d'in koma dai yaushe ne zamu isa babu matsala".
Saida ruwan sama ya yawaita sosai sannan suka iso gida,
Saida yayi horn sau uku kafin maigadi ya fito hannunshi rik'e da lema ya wage gate d'in gidan,
D'aga ma maigadin hannu yayi alamar gaisuwa tareda tsaida motarshi a daidai inda aka
tanada domin ajiye motoci.
A hankali ta bud'e motar ta fito, irin rigar nan ta barristers ce sanye a jikinta da hular kayan,
shima namijin irinsu ne a jikinshi, a bayanshi ta bo'ye bayan ya rufe motar dan bata son ruwan
sama ya tab'ata ko kad'an sannan suka shiga cikin gidan.
Da shigarsu kuwa saiga wata yarinya 'yar kimanin shekara bakwai, sanye take da doguwar
riga armless baby pink in colour, da sauri kuwa ta taso
"Oyoyo Momy" ta fad'a bayan ta rungumi mamarta,
"Oyoyo my Hafsa" itama ta fad'a tana mata murmushi,
"Au! Momy'nki kawai kika sani ko? Nima barinje wurin nawa baby'n yanzu" namijin ya fad'a
bayan ya d'auke kanshi daga garesu.
"Am sorry Abbana, yanzu zanzo wurinka kaima" Hafsa ta fad'a bayan ta saki momy'nta ta
koma ta rungumi Abbanta.
"Ina Haydar ne?" Ya tambayeta bayan ya cire hular kanshi.
"Haydar yana wurin Nany, suna upstairs" ta bashi amsa,
"Ok kije kice ta kawo minshi, nayi missing nashi tun safe rabona dashi"
Da sauri kuwa ta haye sama don ta kira Nany d'in da Haydar k'aninta.
"Ammafa Abbah nayi mamakin yanda nayi winning shari'ar nan ta yau, ni kaina nasan ka
sakar min itane kawai",
"Thank God da kika fahimci hakan da kanki, yunwa nakeji wallahi",
"Ok am sorrie, barin shiga yanzu in dafa maka favorite naka" ta cire rigar jikinta da hular ta
shiga d'akinta ta ajiyesu sannan ta fito domin nufar kitchen.
K'arar shigowar text message taji a wayarta, da saurinta ta ciro wayar daga cikin jakarta ta
bud'e sak'on.
Ido bud'e take karantashi cikin mamaki, bayan ta gama karantawa ta kalli mijinta tace
"Abbah! Kalli sak:onda aka aikomin yanzu".
Karb'ar wayar yayi ya fara karantowa a bayyane.
Princess Amrahí ½í¸˜
NWA
[1:11pm, 9/01/2017] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: *WATA SHARI'AH* í ½í¸ª
í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“
í ½í¸ª
Na Amrah A Mshí ½í²“
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)
{~2~}
"Kamar yanda Allah yayiku masu taimako keda mijinki, nake amfani da wannan damar domin
rok'onku wata alfarma,
An cuceta kuma an hanata kuka, ku taimaka ku taimaketa, ku fiddata daga mawuyancin
halinda take ciki".
"Subhanallah! To waye yayi wannan rubutun? Kuma da alama koma waye ya sanmu, kuma
gashi babu wani cikakken bayani" Barrister Umar ya fad'a yana kallon matarshi Barrsiter
Sultana.
"Kaima kenan Honey, nikam banma fahimci komai dake ciki ba, bansan inda maganar ta
dosa ba".
"Barin kira number'n inji, dan wannan ba abune wanda za'ace wrong number ba, dama da
niyyar mu d'in aka turomawa" kafin ya gama rufe bakinshi shima wayarshi tahau ruri alamar
shigowar text message, exactly irin wanda aka turoma Sultana shima shi aka turo mashi,
Bayan ya gama karantawa yace "akwai matsala kam, kinga" ya mik'a mata wayar, "nima
irinshi aka turo min yanzu babu ko banbanci, barin kira dai".
Kiran lambar ya latsa amma da mamaki sai yaji ana fad'in "the number you are tyring to call
does not exist, please check the number and try again",
"A'ah" ya fad'a bayan ya sake gwada lambar, still dai abunda aka fad'a ne aka maimaita.
"Ya akayi? baka samu bane?" Sultana ta tambayeshi tana kallonshi.
"Wallahi kuwa babu itama wai sukace kiji tsiyar MTN, k'iri k'iri yanzu aka turo min text da
number amma wai ace babu ita, wannan k'aryane" ya sake kiran layin.
Saida ya kira sau goma amma babu ita, hakan yasa kawai ya hak'ura ya ajiye wayar idonshi
lumshe yana tunanin wanda ya masu wannan text d'in.
"Barinje in dafa maka abincin yanzu honey" ta fad'a bayan ta tashi ta nufi kitchen.
Hafsa da Nany ne suka sauko daga upstairs Haydar na goye bayan Nany,
Har k'asa ta duk'a tace "sannu da dawowa Alhaji" shiru yayi kasantuwar zurfi da yayi da
tunanin wanda ya turo masu wannan text d'in,
"Ina yini Alhaji" ta sake maimaitawa dan tasan baijita ba daya amsata.
"Lafiya Safiyya ina gajiya?",
"Ba gajiya, Momy fa?",
"Gata can a kitchen, kawo Haydar d'in"
Mik'oshi tayi, bayan ya karb'eshi tace "Alhaji an kawo wata takarda d'azu da bakunan, Haladu
ya mik'o yace wani yaro ya kawo wai a aje maku kaida momy".
"Ikon Allah! Ina takardar take?" Ya tambayeta bayan ya tashi zaune daga kishingid'awar da
yayi.
"Gata" ta mik'a mashi tare da nufar kitchen domin ta taya Sultana aiki.
Bud'e takardar yayi yaga ab rubuta "nine dai wanda ya rubuto maku sak'on waya, yarinyar
tana cikin matsanancin hali, an cuceta kuma an hanata kuka dan anga halinda suke ciki itada
mahaifiyarta
Kada ku wahar da kanku wurin kiran lambar tawa saboda ba zaku sameni ba, nasan kunada
halin taimakon nata, kuyi bakin k'ok'arinku na rok'eku karku bari wanaan damar ta taimakon
musulmai ta kufce maku, Allah kad'ai yasan ladar da zaku samu".
"Sultana!" Ya fad'a bayan ya gama karantawa.
"Na'am honey" ta fito da sauri saboda yanda ya kirata ta tabbatar da akwai matsala.
Gabanshi ta gurfana tace "lafiya dai honey?",
"Karanta kiga wannan",
Goge ruwan hannunta tayi a zanin jikinta sannan ta karb'i takardar a hankali ta fara
karantawa.
"Towai waye yake aikoda wannan sak'on? Waya kawo takardar?" Ta tambayeshi tana
kallonshi,
"Safiyya ta bani ita, wai Haladu ya kawo yace ta ajiye mana idan mun dawo ta bamu",
"Safiyya!" Ta kira sunan mai aikin tata.
Bayan tazota tace "jeki kiramin Haladu kice yazoshi da sauri yabar duk abunda yakey, kar
kuma ki biye masa kuita shirmen fad'an nan naku, dan nasan ku bakwa had'uwa wuri bakuyi
fad'a ba",
"To momy" Safiyya ta fad'a tare da fita da sauri harda gudu gudu takeyi.
A waje ta sameshi yana ban ruwan flowers,
Murmushi yayi daya ganta yace "ahh! 'Yan matana kece da kanki?",
B'ata fuska tayi tace "nifa bana son shashanci waye 'yan matan taka?",
"Kece mana Safiyya, ai banida wata budurwa wadda tafiki",
"Kai ni ba shirme ya kawoni ba, kajeka momy na kiranka, kuma tace kayi sauri yanzu take
son ganinka",
"To kije gani nan zuwa" ya fad'a yana mata wani murmushin,
"Tace mujemu tare, dan haka kazo mu tafi kana b'atamin lokaci",
"Ahh lallai 'yan matana ta fara sona tunda har takeson mujera tare, mu tafi to".
Bata kuma ce masa komai ba har suka isa, bayan sun zauna Sultana tace "Haladu waye ya
baka takarda d'azu yace ka kawo mana?",
Shiru yayi yana tunanin wace takardace take nufi? Sai daga baya ya tuna yace "wani yarone
ya kawota nima dai bansan yaron ba, yace min wai an bashine ance ya tabbatarda ya kawota
gidan nan".
"Oh my God! To waye wannan wai? Ai ya kamata koma waye ya bayyana mana kanshi mu
taimaki baiwar Allah'n tare dashi, b'oyon ai bashuda amfani" Sultana ta fad'a.
"Wama yasan ko k'aryar banza yake? Irin mutanen nan ne dai masu son su shiga
sha'aninmu, dan haka ki fita batun wannan maganar nima na fita, ku tashi ku tafi Haladu" ya
sallamesu.
Tashi kuwa sukayi, Haladu ya kalli Safiyya yayi mata murmshin soyayya sannan ya tafi, ita
kuwa hararshi tayi sannan ta koma kitchen Sultana ma tabi bayanta har yanzu batace komai ba
sai tunane tunane da take,
Ta tabbatarda akwai magana, bazai yiwu ace koma waye ya k'irk'iri maganar nan ba kawai
dan yaji dad'i, zataci gaba da bincike har sanda Allah zai bayyana wannan b'oyayyen al'amarin.
Princess Amrahí ½í¸˜
NWA
[4:46pm, 11/01/2017] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: *WATA SHARI'AH* í ½í¸ª
í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“
í ½í¸ª
Na Amrah A Mshí ½í²“
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)
{~2-10~}
Washe gari da sassafe Sultana ta tashi Umar suka fara shirin zuwa aiki,
Bayan sun gama shiri ta yima Hafsa da Haydar wanka sannan ta shirya Hafsa cikin Uniform
d'in School d'insu,
Sauran pepper soup d'in jiya tayi warming nashi sannan ta soya mata Irish da k'wai ta saka a
launch box d'inta.
"Wow! Kinyi kyau baby na, barin snapping naki"
Hafsa uwar iyayi kuwa aka wani yi style na d'aukar hoto,
Saida Sultana ta d'auketa hoto kala biyar sannan tace "to ya isa haka, barinyi Feeding haydar
shima tunda dai kinga anan zan tafi in barshi",
"Ok Momy ki d'iba a nawa ki bashi" Hafsa ta fad'a cike da soyayyar k'aninta,
"Ahh Hafsa ai na d'ibar masa nashi daban, gashi kin gani" Sultana ta fad'a tare da nunawa
Hafsa sauran Irish da k'wan data ragewa Haydar.
Saida suka gama tas Umar ya fito cikin suite d'inshi black and white,
Yayi matuk'ar yin kyau kamar in saceshi in gudu,
"Yadai Madam? Hope kun gama saboda inada aiki da yawa a Office yau, kuma kema d'in
nasan ba zaki rasa ba".
"I think bani da aiki nikam, bandai san ko sai naje zan sameshi ba, mun gama dama kai
muke jira",
"Ok muje kawai" ya fad'a bayan ya soka wayarshi cikin aljihu.
Bai gama sakawa ba yaji k'arar text message ya shigo masa,
Zarowa yayi ba tare da tunanin komai ba ya fara karantawa,
_"Nasan zakuyi tunanin kawai inason inyi wasa da hankalinku ne, to sam ba haka bane,
kamar yanda na fad'a maku an cuceta kuma bata da halin karb'ar fansa saboda anfita kud'i,
mulki da komai ma, na rok'eku dan Allah da soyayyarshi ga mafificin halitta ku taimketa,_
_Idan har kuna bisa ga ra'ayin taimakonta zaku iya maido min da reply ni kuma sai in baku
address nata"_
"Again?" Umar ya fad'a a bayyane.
"Menene ya faru honey?" Sultana ta tambayeshi bayan ta gama sakawa Hafsa socks and
sandals nata.
"Karb'a ki gani" ya mik'a mata wayar,
"Ana so ayi wasa da hankalinmu ne kawai, zanje wurin MTN su duba min wannan layin,
inhar na gano kowaye yake mana yawo da hankali wallahi sai ya raina kansa, ni bana son raini
ko kad'an".
Bayan Sultana ta gama karantawa ta mik'a masa wayarsa,
"Ni ina ganin honey kafin kayi haka ka tura da reply d'in, tunda har yanzu akace za'a turo
mana da address kaga kamar akwai alamar gaskiya a ciki".
"Alamar gaskiya?