Showing 30001 words to 33000 words out of 56183 words
Chapter 11 - WATA SHARI'AH 1 TO END COMPLETE Book By Amrah Auwal Mashi.pdf
cisu sosai, barin shiga
ciki ko Allah zaisa in dace" ya fara nad'e kafar hannunshi data wando yana k'ok'arin shiga ciki,
Da sauri wani mutumi ya kamoshi yace
"Kar kayi wannan sayar da ran bawan Allah, kana tunanin akwai mai rai anan ciki ne?",
Duk mutane suka hanashi shiga saboda sun tabbatar da kowa dake gidan ya mutu saboda
katangun da kansu suke fad'uwa tsabar wuta da sukasha.
°•°AKA°•°Princess Amrahí ½í¸˜
NWA
[12:22am, 28/01/2017] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: *WATA SHARI'AH* í ½í¸ª
í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“
í ½í¸ª
Na Amrah A Mshí ½í²“
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)
*_In dedication to Aunty Sdy Jegalí ½í¸˜_*
{~70~}
_Gaisuwa ga masoyiya ko ince abar k'aunata *Aunty sisí ½í²ž* muna jin dad'in yanda kike kula
damu a koda yaushe, bamu san ta wace hanya zamubi don ganin mun gode miki ba, saidai
muyi fatan Allah yabar mana ke yaja da rai, Allah kuma ya raya zuri'ah bisa tafarkin manzon
Allah (SAW), wannan shafin sadaukarwa ce gareki, Allah yabar zumumci ameen. #onelove#_
******
Saida wutar ta gama cinye gidan k'urmus sannan mutane suka fara shiga ciki dukda gumin
dake tasowa daga cikinshi,
Alamar gawama babu a ciki, hakan yasa wasu suka fara tunanin ko wuta ta cinye gawarsune?
Cike da tausayi suka ringa fita daga cikin gidan wasu har yanzu basu daina hawayen tausayi
ba.
****
Sultana ce ke jan mota a sukwane sai faman k'ara wuta take,
Can daga bayan motar na jiyo murya ana fad'in
"Wallahi bansan garinya na manta kayan sakawar mama ba, kuma abun haushi wai duka
nawane kawai na had'a a jikar bakon, babu nata ko d'aya"
"Ai saisa kikaga ina gudu dan kar dare ya nitsa sosai bamu koma gida ba, amma da yake
kayan ne kawai zaki d'auka ai da sauk'i ma" Sultana ta fad'a bayan ta rage gudu da motar.
Murza idona nayi dan tabbatar da muryar wadda naji, ko tantama babu wannan muryar
Ummimah ce, to amma garinya hakan ta kasance? Kenan basu cikin gidansu lokacin da wutar
ta kama?,
Ku biyoni yanzu zaku samu amsoshin wannan tambayoyin.
Lokacin da Sultana ta nufi gidan su Ummimah dan ta tambayeta address d'in Zarah da
Rabiatu,
Ta samesu itada Mama yanzu sun d'an saki ransu akan baya,
Bayan sun gaisa ne ta fad'a masu abunda ya kawota,
Ko amsa Ummimah bata kaiga bama Sultana ba taji wayarta ta d'auki ruri alamar k'arar
shigiwar text message,
D'auka tayi ta fara karantowa
_ina shawartarki daku d'aukesu daga wannan gidan da suke ciki, saboda muguntar waccan
nasan komai zata iya aika masu savoda tasan gidansu, amma idan kika d'aukesu daga ciki
kinga shikenan hankalinku kwance kuna tare dasu, sannan kuma ku kanku zakufi samun
sauk'in yi masu tambayoyi ba sai kun tado mota kunzo har gidansu ba. #shawarace#_
Cike da mamaki take karanta sak'on,
Kanta ta jinjina alamar ta gasgata maganar,
"Ina zuwa mama" ta fad'a bayan ta mik'e tsaye ta nufi waje,
Umar ta kira ta shaida masa sak'onda aka tura mata,
Suna cikin wayar shima nashi ya shigo a k'aramar wayarsa,
"Ki d'aukosu kawai idan zasu yarda" ya fad'a cike da mamakin wanda yake turo masu
wannan sak'unan wanda su kansu su Ummimah d'in basu sani ba, nima kuma Amrah ban sani
ba kawai dai ina baza idona don ganin ko wanene wannan amma kuma shiru har yanzu.
Tsinke wayar tayi ta shiga cikin gidan har yanzu bata daina mamaki ba,
Bayan ta sauna tace
"Dama wata tambayace ta kawoni inyi miki Ummimah, to amma kuma sai mai gidana ya kirani
yace idan babu damuwa ko zaku bini mu koma gidanmi da zama na wani lokaci? Saboda
zamanku anan zai iya zama matsala koba yanzu ba".
Ajiyar zuciya mama ta sauke sannan tace
"Tabbas maganarki gaskiyace Sultana, ni kaina tunda aka fara maganar kai k'arar nan
hankalina ga baki d'aya bai kwanta da zaman gidan nan ba, dan haka mun amince mu tafi d'in
babu damuwa mungode sosai Allah yayi maku albarka, Allah kuma ya mana jagora".
Dad'i sosai Sultana taji da Mama bata musa mata ba,
"Ameen mama, sai ku had'a kayan da zaku tafi dasu yanzu mu tafi yamma nayi".
Tashi Ummimah tayi ta nemi 'yar Gana most go ta fara ziba kayanta, saida ta gama kuma
kwata kwata ta manta bata had'a na mama ba, sai hijabi d'aya wadda ke rataye a k'ofa ta saka
wadda saboda itane tayi tunanin ta saka kayan mama d'in, ga kuma sauri da takeyi kasantuwar
Sultana tace suyi sauri tana so ta d'auko Hafsa daga islamiya.
Tafiya kuwa sukayi suka d'auki Hafsa sannan suka wuce gida,
Saida dare Mama taje canja kaya suka tuna ashe Ummimah bata saka kayan mama ba,
Shine Sultana tace tayi sauri suje can gidan su d'auko kayan mama d'in dan bazai yiwu ta
zauna batada kayan da zata saka ba. Wannan kenan.
***
Koda suka isa k'ofar gidan basu kula da komai ba har Sultana tayi parking suka fito,
Hafsa dake gaban mota ma ta fito itama Ummimah d'in ta fito,
Mamaki k'arara a fuskokinsu lokacin da sukaga yanda gidansu ya k'one sosai har wasu
katangu sun zuba,
"Ya salam" Ummimah ta fad'a hannu bisa kai hawaye sun fara mata sintiri,
Kamar a mafarki ta d'auki abun,
Cikin hanzari suka shiga ciki har a lokacin mutane basu gama watsewa ba kowa na al'ajabin
wannan mummunan al'amarin.
Baki d'aya kallo ya koma ga Ummimah dake kuka sosai tana k'ok'arin shiga cikin d'akin,
Hamdala mutane sukayi saboda sunji dad'i da bata ciki, amma kuma basu tabbatar da
mamanta tana ciki ko bata ciki ba,
"Kiyi hak'uri ki daina kuka, kinsan ita k'addara babu ruwanta, idan har abu saiya faru bawa
tofa babu makawa sai ya sameshi, ita kuma maman taki data rasu Allah yayi nata rahama" wani
dattijo ya fad'a saboda yayi zaton ko mama tana ciki gobarar ta tashi.
Share hawayenta tayi tace
"Mamana bata rasu ba, bata nan gidan, kamar sun sani sukace mu koma gidansu mu zauna,
lallai wannan ikone daga Allah, Allah ya k'ara karemu",
"Ameen" kowa ya fad'a tare da yin hamdala ga Allah da yasa wutar bataci kowa ba.
Sultana dai nata kallo ne kawai, tana kuma k'ara mamaku sosai,
Kamar mutumin yasan haka zata faru ya turo mata sak'o akan su d'aukesu daga gidan,
'To kodai aljani ne wai?' Ta tambayi kanta.
"Ki daina kukan nan ki tashi mu tafi Ummimah, dama haka allah ya tsara gobara zata tashi
kuma komai naki zai k'one, abunma yazo da sauk'i tunda bataci rai ko d'aya ba ai, dan kayan
sakawa ko kayan amfani duk mai sauk'i ne za'a iya hin wasu, rai kuwa k'waya d'aya ne tak ba'a
aro ko canjin wani, ki tashi mu tafi kawai" Sultana ta fad'a tare da mik'ar da Ummimah tsaye duk
jininta ya b'aci da bak'i inda ta zauna.
Babu musu kuwa tabi bayan Sultana, ranta cike da mamakin wannan abu,
'Allah dai yasa wannan d'inma ba aikenta bane' Ummimah ta ayyana a ranta wanda tuni
Sultana ta gano hakan, kawai dai tayi shiru ne saboda yanda taga Ummimah ta rikice bata so
tayi maganar a cikin mutane.
Shiga mota sukayi har yanzu Ummimah bata daina kuka ba,
Hakan yasa Hafsa uwar surutu ta koma baya inda Ummimah take,
Dafa k'afad'arta tayi tace
"Ki daina kuka Aunty, ai mamanku bata mutu ba ko?",
Cikin mamaki Ummimah ta d'aga mata kai alamar ehh
"Ok tunda tanada rai ai shieknan sai ki daina kuka, idan kayanku kike mawa zan cema
Abbana ya siya maku wasu, idan kuma na momy zasu maku sai ku d'auka ku saka, kinga idan
baki daina kukan nam ba har muka koma gida zaki saka mamanki ma ta ringa yin kukan, kinga
dai ni bana kuka kuma ga momyna ma bata kuka".
Har Sultanan ma saida tayi mamakin wannan maganganu na Hafsa,
"Hafsa dan Allah ki rage surutu maras ma'ana mana, ki barta taji da abunda yake damunta
kar ki saka mata ciwon kai".
Bakinta ta kama bayan ta dawo wurin zamanta tace
"Nayi shiru momy, na manta kin hanani yawan magana".
Ita kanta Ummimah saida abun ya bata dariya, saboda surutun Hafsa idan tana yinshi kamar
wata babba haka take.
Bayan sunje gida suka labartawa Umar da Mama abunda ya faru,
Umar bayyi mamaki ba saboda shi lawyer ne yasan irin wannan abubuwan suna faruwa a
case, saidai yaji dad'i da Allah yasa saida suka baro gidan sannan abun ya faru.
Mama kuwa hamdala tayi ga Allah tace
"Allah mungode maka da saida muka fito gidan sannan wutar ta kama, Allah ya k'ara karemu
baki d'aya",
"Ameen" Ummimah ta fad'a bayan ta cire takalmin k'afarta duk k'afar tayi bak'i k'irin.
"To yanzu mama ya za'ayi da kayan sakawarki? Gashi naki duk sun k'one" Sultana ta
tambayi mama.
"Haba Sultana ai dan kayan sakawa abune mai sauk'i, ni wallahi basu dameni ba, ke koda
kayan jikina zan iya rayuwa duk dare in ringa cirewa ina wankewa, kunga kafin asubah sun
bushe sai in miyar a jikina".
Dariya suka d'auka su duka kafin Sultana tace
"Barin duba ko a kayana inada rigarda zata miki sai in kawo miki masu zani ki saka, kinga
gobe akwaa zaman kotu bamuda lokacin siyo miki wasu, sai idan mun samu natsuwa sosai".
"Masha Allahu Allah miki albarka, hak'ik'a kun taimakemu keda mijinki ko ince kuna kan
taimakarmu, Allah kad'ai ne zai iya biyanku, mungode sosai Allah yashi albarka",
"Ameen mama ki daina yi mana godiya, wannan al'kawari ne muka d'aukarwa gwamnati
cewa zamu taimaki al'ummah baki d'aya, mu taimaki mai gaskiya tare da karen hak'k'inshi".
Da wannan maganar Sultana ta tashi domin ta samowa Mama kayan da zasu mata daidai a
cikin nata.
Shigarta kuma ta samu Umar mijinta yana waya da Dr. Rafiq.
_ina cigiyar k'awata Zarah bb, koda shike bakida lafiya ashe kwana biyu na jiki shiru, Allah
ya baki lafiya yasa kaffara ce ameen. #onelove#_
°•°AKA°•°Princess Amrahí ½í¸˜
NWA
[1:00am, 29/01/2017] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: *WATA SHARI'AH* í ½í¸ª
í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“
í ½í¸ª
Na Amrah A Mshí ½í²“
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)
*_In dedication to Aunty Sdy Jegalí ½í¸˜_*
{~71~}
Zama tayi a kusa dashi jin wayar da yakeyi, hakan yasa ya kalleta ya mata murmushi kafin
yaci gaba da wayarsa,
Ganin wayar bata k'arewa bace yasa Sultana ta mik'e ta bud'e wardrobe d'inta,
Ta samu kaya wanda zasuma Mama daidai harda supopinta da lasuka masu tsada.
Har ta fita ta kaima Mama kayan ta dawo Umar bai gama wayar ba,
Kwanciya tayi akan k'irjinsa tana wasa da 'yan yatsun hannunta tana k'ara tuno da gobe ne fa
zasu shiga kotu.
Tashi daga jikin Umar tayi jin ya gama wayar,
"Ya kukayi dashi honey?" Ta tambayeshi.
Tashi zaune shina d'in yayi yace
"Munyi magana dashi yanada kirki sosai,
Ya shaida min cewa sai nextweek Friday zai dawo,
Ya min bayani cewa wallahi shi kanshi baki d'aya kanshi ya d'aure da wannan maganar,
Saboda yasan ya ajiye takardar asibitin Ummimah wadda ta nunar da cewa fyad'e aka mata
sannan kuma tana d'auke da cutar hawan jini,
Amma kuma wai daga baya ya nemi takardar ya rasa,
Saidai wai yaji magana ta fito cewa ciki aka zubar mata,
Baki d'aya ya rasa yanda akayi hakan ta faru kuma yaso ya mata bayani tun a lokacin tak'i
saurarshi, ya rantse ya kuma rantsewa da Allah akan baisan yanda akaui hakan ta faru ba,
Yadai san daga shi sai abokin aikinshi ne suka san da maganar, kuma abokin aikin nashi shi
yasan yanda komai ta kasance,
Kuma da zarar ya nufi abokin aikin nashi da maganar sai ya nok'e akan baya son maganar,
Shidai wai yana zargin Dr. Khalid d'in akan yasan komai ko kuma da had'in hannunshi a
wannan maganar,
Amma yamin alk'awarin cewa idan ya dawo zai sake tuhumar abokin nashi da maganar ko
za'a dace,
ya nunar min da farin cikinshi sosai akan tsaya masun da mukayi domin k'watar masu
hak'k'insu, kuma shima ya tabbatar min da zai bada gudummawa d'ari bisa d'ari dan ganin mun
samu nasarah".
Cikin farin ciki Sultana tace
"Allah sarki ashe mutumin kirki ne, saisa akeso idan mutum yace ka saurareshi to ka
saurareshi d'in, gashi kuwa gaskiya ta fito,
Ni kaina ina zargin wancan likitan, to idan bashi ba waye zayyi haka? Su biyu ne kawai suka
san halinda ake ciki",
"Hakane wifey, dare nayi mu kwanta kinga gobe sammakon fita zamuyi",
"Ok dear" ta fad'a tare da mik'ewa ta kashe wutar d'akin.
*KOTU*
Kotu ta cika mak'il wasu na k'ara shigowa wasu kuwa fita sukeyi savoda rashin halartar
alk'ali,
Tsabar cika da kotun tayi yasa har wasu basu samu wurin zama ba saidai a tsaye suke.
Shigowar alk'ali ne yasa kowa ya natsu akayi shiru har lokacin daya isa mazauninsa ya
zauna.
Daga can gefe na hangi Mama da Ummimah sunyi zuru zuru hankalinsu ya k'ara tashi dan
suna matuk'ar jin tsoron ganin idon mutane ace wai duk yawansu sai sun tashi sunyi magana
cikinsu.
Mai gabatar da k'ara ne ya tashi yace
"A yau d'aya ga watan d'aya shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai ne kotu zata fara
sauraron k'arar da Aishatu Abubakar ta kawo Salmah Abubakar akan wai tasa an mata fyad'e
wanda hakan yayi silar korarta daga makaranta" ya mik'a file d'in ga alk'ali tare da rusunawa
sannan ya dawo mazauninsa.
Alk'ali ya gyara zaman gilashinsa tare da yin gyaran murya yace
"Idan akwai lauyoyi ko zasu gabatar da kansu?".
Tashi Umar yayi bayan ya gyara rigarsa yace
"Sunana Barrister Umar Mohd Bashir, a tare dani akwai",
Sultana tayi saurin mik'ewa tsaye tace
"Barrister Sultana Saddam Bakori"
"Mune masu kare wadda take k'ara" Umar ya fad'a sannan suka koma suka zauna.
D'ayan Barrister'n yace
"Sunana Barrister Sa'eed Bebeji, lauya mai kare wadda ake k'ara" yama Umar shu'umin
murmushi sannan ya koma ya zauna.
Alk'ali yace