Showing 36001 words to 39000 words out of 56183 words

Chapter 13 - WATA SHARI'AH 1 TO END COMPLETE Book By Amrah Auwal Mashi.pdf


{~73~}



Bayan sun koma gida sukaci gaba da tattaunawa inda Rabiatu da Zarah suka ringa tsinewa
Gentle bayan Ummimah ta basu kaf labarin abubuwan daya samesu har mutuwar Baba, da
kuma ta Afrah, ga Amrah maras lafiya bama asan inda take ba.

Sunji haushi sosai kuma suma sukayi fatan samun nasara a wannan shari'ar da ake, saidai
kuma a yanda sukaji labarin dukiyar mahaifin Gentle, da kuma babban Barrister d'in daya
d'aukar mata, sun shiga kokonton samun nasararsu, saidai kuma sunyi fatan Allah yasa
dukiyarsu kar ta amfanesu.
Da wannan firar har yamma tayi Sultana da Umar suka dawo gida cike da gajiya,
Su kansu a mota firar shari'ar kawai yakeyi, amma shi yana ji a jikinshi next zaman da za'ayi
insha Allahu zasuyi nasara bama sai ansha wahala ba.

Koda suka shigo gida Hafsa ta taresu, murna fal a ranta ta gaishe da iyayen nata sannan
suka k'arisa daga ciki inda suka samu har yanzu su Zarah basu daina firar abunda ya samu su
Gentle ba.

Bayan sun natsu sosai Umar ya kira Dr. Rafiq, ya k'ara tabbatar masa da cewa fa ranar
Monday next week anada buk'atarshi a kotu, ya amsa da 'insha Allahu zayyi k'ok'ari ko zuwa
ranar Sunday ya shigo Katsina, saboda ranar Friday zai koma Jalingo',
Sallama sukayi Umar ya kashe kiran,
Sultana tace
"To ya maganar wancan ma'aikatan na makarantarsu?",
"wannan kuma ai bamuda case dasu, kotu zata aika da sammacinta" Umar ya bata amsa
yana k'ok'arin cire suite daga jikinshi.

Taimaka masa tayi ya k'arisa cirewar, itama ta cire nata sannan suka shiga wanka.

Fitowarsu suka samu abinci jere a dining, murmushi Sultana tayi saboda tasan babu tantama
wannan aikin Ummimah ne, tunda suka dawo gidan da zama ta hana Safiyya yin aiki sosai,

komai ita takeyi bata gajiyawa.


*Ranar lahadi 10:45pm*
A daidai wannan lokacin ne Umar ya latsa kiran Dr. Rafiq domin yaji ko ya iso Katsinar amma
shiru bata shiga ba,
Sake latsa kiran yayi still dai 'not reachable',
Hakan yasa ya fuskanci Sultana da itama shi take kallo yace
"Ban san mesa ba number'n Dr. Bata shiga, kinga tun yamma naketa fama kiranshi amma
duk maganar guda ce",
"Ina tunanin ko yana hanya ne, wata k'ila kuma hanyar babu network mai kyau" Sultana ta
bashi amsa tana kallonshi cikin soyayya.

Basu kawo komai a ransu ba a haka suka bar maganar su a tunaninsu ko yana hanya, dan
haka cikin kwanciyar hankali bacci ya d'aukesu mai cike da walwala da nishad'i saboda yanda
suke jin dad'in zasu shiga kotu da hujjarsu babba, wadda suke ganin da ita wannan shari'ar
zata kawo k'arshe.
*KOTU*

Yau ta kama ranar Monday bakwai ga watan d'aya, shekara ta dubu biyu da goma sha
bakwai,
Kotu ta cika kamar zaman farko, harma zan iya cewa a wannan lokacin ma tafi cika sosai,
Kowa burinsa yaga yanda k'arshen shari'ar zata kaya.

Bayan mai gabatar da k'ara ya tashi yace
"Yau 7-1-2017 kotu zataci gaba da sauraron shari'ar data fara a makon daya wuce, wadda
Aishatu Abubakar ta kawo Salmah Abubakar k'ara akan zargin da take na sakawa an mata
fyad'e wanda yayi silar dakatar da ita daga karatunta".

Alk'ali yace
"Barr. Umar da Barr. Sultana ku muke saurare, kotu na fatan kun kawo mata shaidun data
buk'ata a zaman farko",
Shiru ya biyo baya kasantuwar daga Umar d'in har Sultana basu tattare da natsuwarsu,
Tun shigowarsu kotu suke baza ido dan ganin Dr. Rafiq amma shiru har yanzu baizo ba,
Kuma gashi idan sun kira lambarsa bata shiga,
Baki d'aya hankalinsu a tashe yake,
Ita kanta Ummumah nata hankalin a tashe yake, barin k'awayenta Rabiatu da Zarah da suma
basu tattare da tasu natsuwar.

"Barr. Umar!" Alk'ali ya fad'a a hasale savoda yayi tunanin ko yajishi.

Firgigit suka dawo hayyacinsu,

A daburce Umar ya mik'e tsaye duk jikinshi yayi sanyi,
Sunan Allah kawai yake ambata a ranshi, saboda yasan matuk'ar Dr. Rafiq baizo ba to
shikenan basu ba winning d'in eannan shari'ar.

Bayan ya tashi tsaye yace
"Kotu tana buk'atar ganin Sister Maryam, Sister Fatima, Sister Rooth da kuma Sister Ifeoma".

Wasu mata ne suka taso, biyu daga ciki manyan mata ne ak'alla zasu kai talatin da biyar
zuwa da shida,
Biyun kuma da ganinsu yaran matane, idan sunyi aurema to sabon aure ne, dan babu alamar
sun tab'a haihuwa koda d'aya ce.

Bayan sun fito sun jera wuri d'aya rankas Umar yace
"Wannan sune nurses na Talented University, wanda sune suka karb'i Aishatu a lokacin da
aka kaita".

Qur'ani aka bama musulman sukayi rantsuwa da zasu fad'i gaskiya,
Christians d'in kuma aka basu bible sukayi ranstuwa da zasu fad'i gaskiya tsakaninsu da
Allah,
Hakan yasa Ummimah tad'an samu sassauci a zuciyarta.

"Rabiatu da Zarah k'awayen Aishatu su fito idan suna kusa" alk'ali ya fad'a yana kallon ta
inda zasu fito d'in.

A hankali suka taso suka iso inda sisters d'in suke tsaye,
Alk'ali ya miyar da kallonshi ga sisters d'in yace
"Ko kun shaida wannan 'yan matan kuwa?".

Da hanzari Sister Maryam tace
"K'warai kuwa na shaidasu, su suka kawo wannan marar lafiyar mai suna Aisha da wata
safiya bazam manta ba".

Ifeoma ma tayi caraf tace
"Yes I can recognise their faces".

"Da kyau, Zarah da Rabiatu zaku iya komawa ku zauna" alk'alin ya fad'a bayan ya duk'ar da
kanshi yayi rubutu.

Umar yace
"Zan fara dake Sister Fatima, a lokacin da suka kawo maku Aisha batada lafiya, zaki iya tuna
a yanayin da take kuwa?",
"Ehh zan iya, sun kawota ita ba matacciya ba ba kuma rayayya ba, amma kuma jikinta duk
ya b'aci da jini" ta bashi amsa.

"Saura ke Ifeoma, bayan kun karb'eta wane irin treating ne kuka fara bata?" Umar ya
tambaya yana yi yana lek'en k'ofa ko zaiga shigowar Dr. Rafiq amma babu ko alamarshi.

Cikin dakewa Ifeoma tace
"Mun fara k'ok'arin vata first aid domin tsayar da jinin dake fita daga k'asanta amma kuma
abun ya gagara, na kira sauran abokan aiki nawa su tayani amma suma sunce abu yafi
k'arfinsu, gashi kuma babu Dr. Ko guda a asibitin suna huta" ta fad'a cikin hausarta da bata
k'ware ba.
"Sister Maryam daga nan kuma sai kukayi me? Sannan kuma ai naga jini ne, taya za'ace
kuda kuka karanci nursing kuma kun kasa tsayar da jini, ko kunga wani ciwo ko rauni a wurin
ne?".

Saida tad'an rarraba ido sannan tace
"Gaskiya babu rauni ko d'aya, kawai dai jinin ne mukaga fitarshi tayi yawa,
Ga dunk'ulr dunk'ulenshi yana fita,
Muna shirin fita da itane mukaga wani k'aton jini ya fad'o, koda muka duba da kyau ashe
halittar jariri cr har ta fara fita, hankalinmu ya tashi sosai munyi tunanin ko shikenan yanzu jinin
zai tsaya, amma kuma bai tsaya ba saboda da alama ba jariri d'aya bane a cikin cikinta,
Da sauri muka shiga mota mu duka harda k'awayen nata muka tafi Kadraq clinic,
Mun samu Dr. Khalid eanda yake gaeny Dr. Ne sai waai abokinshi shi kuma ba gaeny bane,
Sun duddubata sosai Dr. Khalid ya tabbatar mana da k'wayar zubar da ciki ce tasha kuma
mai muguwar illah, ta sata ta zubar da jini sosai kuma inhar ba'ayi saurin k'ara mata ba zata iya
rasa rayuwarta, kuma...." bata k'arisa maganar da take ba Zarah ta mik'e a fusace tama manta
inda take tace "Wallahi ku munafukai ne k'arya kuke, kuji tsoron Allah mana, ku duba darajar rantsuwar da
kukayi ku fad'i gaskiya, haba bayin Allah! Ya da girmanku zaku zubar dashi saboda an baku
kud'i? Kud'i masu saurin k'arewa, ko kun manta da akwai babbar shari'ah ne? Wadda ranar baki
da ido zasuyi magana, hannu da k'afa zasuyi magana, dukkan gab'ob'in jikin mutum zasuyi
magana, wallahi..."
Da k'arfi alk'ali ya buga guduma yace
"Ki rufewa mutane baki, nan kotu kikr ba wurin shirme ba, ki bari har saa idan kin nemi izini
kotu ta baki damar yin magana sannan kiyi".

Cike da b'acin rai da kuka Zarah ta koma mazauninta ta zauna, tana tunanin k'araurayin da
nurses d'in nan suke sharawa, gashi kuma Dr. Rafiq d'in da zai fad'i gaskiya baizo ba, ta yiwu
shima an siyeshi da kud'i shine yak'i zuwa kuma ya kashe wayarshi, Dr. Khalid kuma yazo tun
d'azu suka ganshi.
A sab'ule Barr. Umar ya koma ya zauna,
Yama rasa abunda zai fad'a, he has no idea yanzu kam, yasan dole za'ayi winning nasu.
Ita kanta Sultana kuka takr tsabar tashin hankali.

Alk'ali yace
"Ko lauya mai kare wadda ake k'ara yanada tambayar da zai masu?".

Cike da gadara Barr. Sa'eed ya mik'e, saida ya kalli Umar yaga tsantsar tashin hankali a
bayyane dashi, yaga kuma Sultana ta dage sai uban kuka take marar sautu,
Shu'umin murmushi yayi sannan ya isa inda sisters d'in suke.









_Alhamdulillah, masha Allah, dukkan yabo ya tabbata ga Allah mai kowa mai komai, Allah
mungode maka daka bawa k'awata ko ince aminiyata (Zarah bb) lafiya, Allah ya k'ara mata
lafiya da dukkan sauran marasa lafiya, masu ita kuma Allah ka k'ara masu. #onelove#_





°•°AKA°•°Princess Amrah😘
NWA
[11:08pm, 1/02/2017] Amrah💓Pinky💓durling😘: *WATA SHARI'AH* 😪
🎓🎓🎓🎓🎓🎓
😪

Na Amrah A Msh💓
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)


*_In dedication to Aunty Sdy Jegal😘_*


{~74~}



"Bayan likitan ya tabbatar maku da ciki ne ta zubar sai kuma me ya faru?" Barr. Sa'eed ya

jefo masu tambaya yana kallon Sister Fatima da nufin ita zata amsa masa.

"Gaskiya munyi mamaki sosai, bamuyi tunanin d'alibar wannan jami'ar zatayi wannan ta'asar
ba, ganin munyi mamaki yasa Dr. Khalid ya tabbatar mana da wannan ba shine zubar da
cikinta na farko ba, saboda yaga alamomin haka da dama a tattare da ita".

Kallonshi ya miyar ga alk'ali yace
"Ina so kotu ta bani dama domin gabatar da Dr. Khalid idan yana kusa".

"Kotu ta baka dama" alk'alin ya fad'a yana kallon ta inda likitan zai fito.

Dr. Khalid ne ya taso a hankali ya tsaya kusa da sisters d'in,
Qur'ani aka bashi yayi rantsuwa da zai fad'i gaskiya sannan Barr. Sa'eed yace
"Ko zaka fad'a mana cikakkrn sunanka da kuma abunda kayi karatunka a kanshi?".

"Ehh zan fad'a" Dr. Khalid ya bashi amsa.

"To myna saurarenka",
"Sunana Khalid Muhammad Khalid, ni d'an asalin garin Katsina ne amma iyayena suna
zama a Jalingo nima d'in acan nake zama,
Ni cikakken likita ne ta fannin abunda ya shafi mata, yanzu haka inada asibiti tawa ta kaina
wadda duk fannin mata ne kawai a cikinta",
"Good" Barr. Sa'eed ya fad'a,
"Ko akwai gyara akan bayanan da sisters d'in nan sukayi? Ko kuma wani abu wanda ba
gaskiya ba?".

Shiru yayi kafin yace
"Tabbas babu k'ari ko d'aya a bayanansu,
Bayan sun kato Aishatu na dubata sosai na kuma gane irin k'wayar data sha wadda ta nemi
illaya rayuwarta,
Data farfad'o ne nake mata fad'a akan dalilinta nayin haka,
Shine ta cemin wai tana kunyar a ganta da cikin ne, savoda ita duk iskancinta da bin mazan
da takeyi a gidansu ba'a san tana yinshi ba,
Kuma ta tabbatar min da wannan cikin shine na biyu kuma wancan d'inma zubar dashi tayi,
Na mata nasiha akan ta daina bin maza amma tace sam bata san wannan ba, ta rigada ta
saba da maza dan haka dole sai ta bi...." bai k'arisa maganar da yakeyi ba Barr. Sultana ta
mik'e cikin hawaye tace
"Objection my lord! Bai kamata suna fad'in magana irin haka ba, saboda wannan tamkar cin
fuska ne".

Kallonta alk'ali yayi yace
"k'orafi bai karb'u ba Barr. Sultana,
Dr. Khalid ci gaba".

Wani wawan murmushi Barr. Sa'eed yama Sultana sannan yace
"Muna jinka Dr."

Ci gaba da zuba k'arairayi Dr. Khalid yayi, ita dai Ummimah mutuwar zaune ma tayi, ta rasa
avunda zata fad'a sai tsabar mamakin hali irin na mutanen yanzu take, lallai kam yanzu kowa
ba abun a yarda dashi bane.

Bayan ya gama duka suka koma suka zauna,
Alk'ali ya gyara zaman gilashinshi yace
"Ko akwai mai sauran hujjar da zai gabatar kafin a yanke hukunci?".

Kai kawai Umar da Sultana suka kad'a cike da takaici, sun san dole ba zasuci wannan shari'ar
ba, saboda duk wasu hujjoji nasu anbi an b'atasu, wanda suke da hope akanshi shiru baizo ba,
idon Sultana har ya kumbura tsabar kukan da tasha a kotun, Umar kuwa tagumi kawai yayi
yama rasa avunda ke masa dad'i.
Kallonsu suka miyar ga Sultana da Mama da suma hankalin nasu a tashe yake, jin alk'ali ya
fara magana yasa suka miyar da hankalinsu a gareshi.

"A bisa hujjoji da suka gabata na wanda lauyoyi masu kare wadda take k'ara, da kuma na
wanda yake kare wadda ake k'ara suka kawo,
Kotu tayi zurfin tunaninta tare da yanke hukunci.
Munji yanda kowa ya kawo nasa hujjar, dan haka kotu ta gamsu da kaf bayanan Barr.
Sa'eed,
Ta kuma wanke Salmah Abubakar a bisa k'ararta da Aishatu Abubajar data kawo akan ta
saka an mata fyad'e,
Ita kuma Aishar kotu zata d'aureta har na tsawon watanni bakwai a gidan mata (prison) a
bisa b'atawa Salmah suna da tayi, sannan kuma zasu bata tarar naira dubu goma na wahalar
zirga zirga data sha, ta baro karatunta ta dawo gida akan wannan shari'ar,
Amma kuma Aisha da lauyoyinta sunada damar da zasu d'aukaka k'ara idan hukuncin bai
masu ba.
Kooootu!". Alk'ali ya mik'e.

K'ara ta saki da k'arfi had'e da zubewa k'asa,
Mama dake kusa da ita tayi saarin duk'awa tana kuka sosai mai tsuma zuciyar mai sauraro,
Zarah da Rabiatu ma tuni suka fashe da kuka, suna bala'in tausayin k'awarsu,
Lallai wannan rayuwar ta yanzu avun tsoro ce, dukda cutar Ummimah da akayi amma sai
gashi wai ita aka bama rashin gaskiya,
Koda yake bataga laifin alk'ali ba, saboda shikam yayi amfani da hujjojin da aka kawo masa
ne sannan ya yanke hukunci.

Sultana ma tuni ta fasa kukan mai k'ara fiye da wanda takeyi d'azu,

Umar nata k'ok'arin rarrashinta dukda shima d'in k'arfin hali ne,
Tunda yake a rayuwarsa tun fara aikinsa bai tab'a yin shari'ar maras dad'in wannan ba,
Tsabar rashin gaskiya yayi yawa a cikinta,
Duk wata hanya da zasubi an dod'e ta.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login