Showing 3001 words to 6000 words out of 56183 words
Chapter 2 - WATA SHARI'AH 1 TO END COMPLETE Book By Amrah Auwal Mashi.pdf
A cikin wannan maganar? Bana tunani kam, koma waye idan da gaske
yake ai sai yazo ya tinkaremu da maganar tunda dai yasan gidanmu yazo ya kawo takarda jiya,
dan haka wannan shirmene kawai kuma kibar maganar nan kamar yanda na fad'a miki jiya,
kuma yau yau d'in nan insha Allahu zanje MTN Office suyi min bincike akan layin nan" yayi
gaba bayan ya miyar da wayarsa a cikin aljihu,
"Ku fito mu tafi lokaci na tafiya" yayi waje.
"Safiyya!" Ta k'walawa Nany d'in Haydar kira,
"Na'am momy" ta fad'a tare da saukowa daga kan bene da sauri.
"Gani momy" ta fad'a tana kallon Sultana,
"Ki d'auki Haydar ki goyashi nasan yanzu zayyi bacci tunda na mashi wanka ya karya kuma".
D'aukarshi tayi kuwa ta goyashi, harda ba-bye yayima Momy'n shi, Hafsa ma ta d'aga mashi
hannu sannan suka fita suka samu Umar har ya fitar da mota waje yana jiransu.
"Afuwan honey, kanata jiranmu",
"Hmm! Bakya laifi wifey, ku shigo mu tafi".
Saida suka fara dropping d'in Hafsa sannan suka nufi Federal High Court Katsina,
Kai tsaye kowa ya nufi Office d'inshi,
Zaman Sultana keda wuya kuwa sak'o ya shigo mata,
Exactly irin wanda akama Umar ne,
Aikuwa bata jira komai ba ta miyar da amsa,
_"A shirye muke da taimakonta indai har da gaskene wannan sak'onnin da ake turo mana,
kullum burinmu shine muga mun taimaki wanda aka zalunta ko kuma wanda ake k'ok'arin
zalunta, dan haka ina jiran address d'inta yanzu"._
Tayi sending tare da ajiye wayar akan desk d'inta.
Bada jimawa ba kuwa sak'o ya kuma shigowa, d'auka tayi ta karanta
_"Tudun Wada layin farko gida na biyu yana kallon masallaci"._
"Good" ta fad'a a bayyane,
"Insha Allahu zan taimaketa, zanyi shiru bazan fad'awa Umar ba har sai na tabbatar da
gaskiyar al'amarin sannan in sanar dashi, shima kuma nasan bakin k'ok'arinshi zai taimaketa
idan ya tabbatar da maganar".
K'arfe hud'u daidai suka tashi aiki,
A cikin mota Umar yace "nikam na rasa menene tsakanina da Barrister Sa'eed, kwata_kwata
baya k'aunata, ko a hanya na had'u dashi na bashi hannu mu gaisa baya amsa, na rasa dalilin
hakan".
"Hmm! Ka rasa dalili fa kace honey, ga dalili k'arara a bayyane,
Ko ka manta shari'arka ta farko dashi kayi winning? Kuma tun daga nan na kula yake neman
shari'ar da zakuyi dashi amma ba'a sameta ba, a tunanina dalilin jin haushinka kenan da yake,
Kumafa na samu labarin tunda yake a rayuwarshi kaine mutum na farko daya fara kadashi a
shari'ah, kuma har yanzu ba'a samu wani ba",
"Ehh hakane kam, amma ni sai naga kamar duk wannan bai isa yasashi jin haushina ba, ki
duba kiga tun lokacin da akayi shari'ar, kusan shekaru goma kenan fa k'ilama anfi, me zai sashi
ya rik'e wannan abun? Kuma in banda abunshi ma yanda yake babban barrister wanda duk
fad'in k'asar nan an sanshi yayi suna me zaisa ya ringa jin haushina ni d'an k'aramin barrister?". "Hmm! Kai kaga haka honey, ai kuwa yanzu idan baka take mashi baya ba to k'iris ya rage
ka take bayanshi, yanda yayi suna kaima d'in haka kayi, duk inda ka shiga Barrister Umar Mohd
ake fad'i, kaga kuwa ka godewa Allah",
"Kema kinyi magana Wifey, Allah dai ya k'ara bamu ikon cin halaliyarmu, Allah ya karemu
daga cin kud'in cin hanci da rashawa, burinmu a kullum muga mun taimaki mai buk'atar
taimako, bama fatan mu tauye gaskiya akan k'arya kawai saboda kud'i ko wata k'awa ta
duniya".
Da wannan firar suka isa gida, da sauri kuwa Haladu ya wage masu gate suka shige da
motarsu, cike da soyayya suka fito hannunsu mak'ale da juna,
Jin k'arar motarsu yasa da gudu Hafsa ta fito tana fad'in "oyoyo oyoyo" ta rungumesu su
biyun,
"Oyoyo Hafsa" Umar ya fad'a bayan ya saki Sultana ya d'auki Hafsa.
Shigarsu ciki suka samu Haydar da Safiyya sunata wasa abunsu cike da so da k'auna,
Ganinsu da Haydar yayi yasa ya daina wasan yazo yama iyayenshi oyoyo,
"Momy yau Safiyya bataje ta d'aukoni School da wuri ba duk saida aka watse aka barni
sannan tazo" Hafsa ta fad'a tare da tunzuro baki ita a dole mai fushi.
"Hafsa me naji kin fad'a?" Sultana ta tambayeta,
Saurin dafe bakinta tayi tare da fad'in "Aunty Safiyya bataje ta d'aukoni da wuri ba har aka
watse aka barni ni kad'ai a School".
"Au! Kin gyara kenan? Kuma ma ban hanaki kawo min k'arar Safiyya ba? Na hanaki ko ban
hanaki ba?" Ta had'a hannayenta biyu ta zare mata ido,
"Kin hanani momy" Hafsa ta fad'a hawaye na shirin fito mata.
"To mesa zaki kawo min k'ararta? Sa'arkice ita? Waya fad'a miki ana kawo babba k'ara?",
"Babu" ta fad'a bayan hawaye sun fito mata,
"Ki bata hak'uri",
Juyawa tayi ga Safiyya bayan tayi kneel down ta had'e hannayenta biyu tace "sorry Aunty
Safiyya",
Cike da so da k'auna Safiyya ta jawota ta d'ora kan cinyarta ta rungumeta,
"Babu komai Hafsa nima ki yafe min kinji? Keke napep ce tamin wahalar samu saida nayi
trekking har bakin roundabout sannan na samu".
"Kema duk laifinki ne ai, dan me zaki tsaya kinama yarinya k'arama kamar Hafsa wai bayanin
abunda yasa bakije d'aukarata da wuri ba? Saisa take rainaki wallahi" Sultana ta fad'a dan ta
tsani taga k'arami ya raina babba.
"Babu komai Momy, Hafsa nada biyayya sosai wallahi, yanzu ma nasan fushi tayi ne saboda
babu dad'i a watse abar yaro shi kad'ai a School",
"Kudai kuka sani, akwai abinci ne?",
"Ehh akwai Momy" Safiyya ta fad'a tare da nufar Kitchen.
Dama ta riga da ta zuba a food flasks, d'aukowa kawai tayi takai dining,
D'aki Sultana ta shiga ta kira Umar akan yazo suci abinci,
"Wanka nake sonyi ne saboda yau na gaji sosai, idan nayi wankan sai in samu d'an
k'arfi_k'arfi a jikina",
"Ehh hakan yayi, nima kaga sai muyi tare dan bakai kad'ai keson samun k'arfin ba" tayi
murmushi bayan ta gama maganar.
"Wifey na ta kaina, ina sonki sosai" ya fad'a k'wayar idonshi akan idonta cike da soyayya,
"Hmm! Honey ni ba sonka nake ba k'aunarka nake, saboda kasan shi so yana raguwa watan
wata rana, amma k'auna bata tab'a raguwa duk tsanani duk wahala",
"Hakane wfey, ki kud'ura a ranki *ina tare dake* komai rintsi komai wuya",
"Nima *ina tare dakai* honey na" ta fad'a bayan sun kama hanyar shiga toilet,
Nidai Amrah gudowa nayi saboda abun yana shirin fin k'arfi na, amma fa ina bakin toilet ina
jiran fitowarsu saboda ina son yanayin soyayyar wannan ma'auratan dan ina son in koya nima.
Sun jima a cikin toilet d'in kafin su fito, Hafsa zaryarta biyu tana nemansu amma bata gansu
ba,
Dan haka ta koma ta fad'awa Safiyya cewa Abba da Momy'nta sun b'ata,
Dariya kawai Safiyya tayi dan tasan dalilin rashin fitowar tasu.
Da fitowarsu kuwa mai ta shafa mashi shima kuma ya shafa mata, k'anana kaya ta fiddo
mashi blue jeans sai white T-shirt a jikinta an rubuta *"YOU ARE MINE"* da kalar royal blue,
Itama k'ananan kayan ta fiddo, three qurter ne blue itama sai 'yar polo shirt white da logo na
polo royal blue bayanta itama an rubuta *"YOU ARE MINE TOO".*
Sosai sukayi masifar kyau, nidai "perfect couple" kawai bakina ke furtawa.
Mak'ale da juna suka fita kamar ba sune suka aje kamar Hafsa ba.
Kai tsaye dining suka nufa inda suka fara feeding junansu duk da idon Safiyya da Hafsa
baisa sunji ko kad'an d'in kunya sun daina ba,
Koda yake ai a soyayya babu kunya, idan kuwa aka saka kunya to bazaku tab'a jin dad'in
rayuwarku ba, wannan haka yake.
Princess Amrahí ½í¸˜
NWA
[1:27pm, 12/01/2017] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: *WATA SHARI'AH* í ½í¸ª
í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“í ¼í¾“
í ½í¸ª
Na Amrah A Mshí ½í²“
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(Jan. 2017)
{~11-20~}
Yau ta kasance Friday ne, dan haka tun k'arfe sha biyu Umar da Sultana suka tashi daga aiki,
Kai tsaye suka wuce Gobarau Academy suka d'auko Hafsa sannan suka wuce gida.
A cikin motar Hafsa tace "Abbah yau ina cikin Class Teacher Nasir ya kirani, bayan naje yace
min wai wani mutumi ne yazo nemana amma bazai barni in tafi wurin mutumin ni kad'ai ba dan
kar aje wani abu ya sameni kuma laifinsu ne, shine na bishi mukaje wurin mutumin a bakin
Head Master's Office, Na gaisheshi ya dafa kaina yace min "kece Hafsa ko?",
"Ehh nice Hafsat Umar Muhammad" na bashi amsa,
Shine yace min wai dama sak'one zai bani wurinku,
"Hafsa ki jaddadawa iyayenki cewa taimako yanada matuk'ar muhimmanci, idan Allah ya
baka damar taimako to kayi k'ok'arin aikatashi tun kafin damar ta kufce maka" ya kuma ce min
"karki manta ki fad'a masu wannan sak'on".
Yana gama fad'in haka English Teacher d'inmu yazo harda bulala a hannunshi
"Hafsa you are speaking vanacular ba? Hmm!" Naji tsoro sosai Abbah dan nasan sai ya bani
kashi idan na koma class,
Abbah abun mamaki ashe wannan mutumin wanda ya bani sak'o wurinku ya iya turanci sosai,
Aikuwa ya taimakeni ya fad'awa Teacher'nmu cewa ba Hausa nakeyi ba turancine, harda
cewa yayi wai yaji dad'in yanda ya jini ina speaking kamar ba 'yar Nigeria ba, kuma sak'o yake
bani wurin parents d'ina, daga nan kuma sai ya tafi" ta gama basu labarin hankalinta kwance
tana bud'e dash board dake side d'inta.
Juyowa Umar yayi ya kalleta taci gaba da wasanta,
Bai tanka mata ba, haka Sultana ma batace mata komai ba,
"Abbah da Momy kunyi shiru, nidai babu ruwana idan ya tambayeni nasan na fad'a maku
sak'onshi".
Shiru sukayi har suka isa gida,
Bayan Umar ya shiga d'aki ne Sultana ta juyo ga Hafsa tace "mutumin da yayi miki maganar
ya yake?",
"Momy nifa ban sanshi ba, kawai dai nasan ya iya turanci kuma yanada fara'ah" ta bata
amsa.
*****
Washe gari.
Da sassafe Sultana ta tashi, ita dama haka tsarinta yake kullum ita ke rigar Umar tashi, sai ta
gama ayyukanta kaf ta bad'e gidan da k'amshi sannan ta tasheshi yayi wanja, idan yayi wanka
sai su karya tare lokacin itama ta shirya kuma ta gyara Hafsa da Haydar.
Bayan sun zauna kalaci ne Sultana tace "Abbah yau kuwa ina son fita ko zuwa da yamma ne
insha Allahu".
Gyaran murya yayi yace "dama kinga nima inason fita, ina zakuje ne sai mu fita tare?".
Ido ta ringa zarowa dan batasan kalar k'aryar da zata masa ba,
"Gudan Hauwa nake son zuwa, kwana biyu bamu gaisa ba",
"Ehh kuma dama jiya ta kirani ni nama manta, tace ince miki Zarah batada lafiya saima yanzu
na tuna wallahi, afuwan".
"Amma dai honey ka cika mantuwa da yawa, yanzu inda ace bance zanje ba kenan da
bazaka fad'a min ba, saidai ta ringa kallona da abun ko? Ai babu dad'i ace yarinya batada lafiya
banje na ganota ba",
"Nidai kiyi min hak'uri tunda gashi na fad'a miki, anjima d'in kinga sai mu tafi tare nima in
dubata da jikin".
Damm! Gaban Sultana ya fad'i sai raba idanuwa take saboda bata son ya bita,
"A'a kafa san dama ba tare dakai nake zuwa gidan Hauwa ba, bana son inje ka azalzaleni sai
na tashi mun tafi gida, ni kuma ina son in zauna muyi fira sosai barin yanzu mun dad'e bamu
had'u ba".
"To naji uwar son fira, kije yau ni kuma gobe sai inje, kuma inji kince zaki bini yawon gobe in
kurta miki rashin mutunci" cike da soyayya yakeyin maganar.
"Ehh naji dai babu komai, nima kuma daga can sai mu wuce yawonmu ko Hafsa?"
"Ehh Momy, har ki kaini Royal Bakeries ki siya min shawarma da ice cream" Hafsa ta fad'a
tana murmushi.
"Karki damu ai yawo zamusha sosai cikin garin nan, harda inda wani bai tab'a zuwa bama sai
munje ko?"
"Ehh momy zanje, shi kuma Abbah sai mu barshi da Haydar ko?"
Kwakkwab'e baki Haydar yayi alamar zayyi kuka,
"Ni ba jakuje daniba ko? Appa kaji wai bajacu tafi dani loyal ba nima insha ayish kilim",
"Woiii Haydar bai iya magana ba, wai ayish kilim, yaro kazo in koya maka magana" Hafsa ta
fad'a tana mishi gwalo.
Kukane ya fito da k'arfi ya fasashi, yanayi yana kallon Umar dan yaji abunda zai fad'a,
"A'a fa Hafsa, wallahi idan kikaci gaba da samin yaro kuka duka ma sai in hanaku fitar, ni
kuma gobe muyi tafiyarmu nida d'ana Haydar" Umar ya fad'a yana rarrashin Haydar d'in.
"A'a fa wasa take masa, nidai ka barmu mu fita ai hardashi zamu tafi amma fa sai idan yayi
shiru da kukan nan",
Saurin goge hawayen yayi yace "nayi shilu momy, jaki tafi dani?",
"Ehh zan tafi dakai yarona" sukayi murmushi su duka ukun.
Ranar tunda wuri Sultana ta d'aura abincin rana, dambun cous cous da sauce d'in hanta ce
tayi, cikin lokaci kad'an kuwa ta gama komai ta saka a food flask,
Dining suka zauna suka shari abincinsu, Umar harda santi ya ringayi.
Ta sake yima Hafsa da Haydar wanka ta shiryasu sannan ta umurci Safiyya ma da ta shirya
su tafi tare.
K'arfe uku daidai suka fita, motarta k'irar vibe ja suka shiga, Hafsa ce gaba sai Safiyya da
Haydar a baya,
Basu wani d'auki lokaci a hanya ba suka isa gidan Hauwa kasantuwar babu nisa sosai
unguwar.
Sosai Hauwa tayi farin cikin ganinsu,
Sunsha fira sosai kafin Sultana tace "zanje in dawo yanzu insha Allahu",
"Daga zuwa kuma? Ina zakije ne?" Hauwa ta tambayeta,
"Ehh zan dawo ai anan zan bar su Hafsa, Tudun wada zanje yanzu bazan dad'e ba ai".
"Momy kince fa zaki tafi damu musha ice cream, ya kuma zaki tafi ki barmu?",
"Ai yanzu zan dawo Hafsa, ga Zarah nan kuyi wasa kafin in dawo sai mu tafi royal d'in ku
zab'i duk abunda kuke so",
"Yauwa momy na sai kin dawo",
"Ok sai na dawo, Safiyya ki kula da Haydar kin sanshi da b'arna da kuma yawo"
Tana gama fad'ar haka ta d'auki hand bag d'inta ta nufi hanyar fita.
Kai taaye Tudun wada ta wuce,
Wayarta ta fiddo daga cikin jaka ta sake duba text message na address d'inda aka turo mata,
A hankali ta ringa driving tana k'ara duba message d'in,
Daidai gaban gidan da yake kallon masallacin kuwa tayi parking kamar yanda aka rubuta
mata,
Bayan ta rurrufe motar ta fito tana rik'e da jakarta.
"Assalamu alaikum" Sultana ta fad'a bayan ta zare medical glasses d'inta daga ido.
Shiru taji ba'a amsa sallamar ba, hakan yasa ta sakeyin wata