Showing 9001 words to 12000 words out of 18821 words

Chapter 4 - Dakarun Musulunci Book 1 By Abdulaziz Sani M Gini.txt

bushe da dariyar farin ciki har kwalla ta zubo mata, sannan ta hade fuska tace, ya kai dana kayi sani cewa tabbas yanzu sarki ya gane cewa nice na zuba masa guba taci, kuma a shirye nake na fuskanci kowanne irin hukunci daga gareshi, koda kuwa na kusane, domin bukatata ta biya tun da babu maka wa sai ya mutu domin gubar da na bashi taci ta gama ratsa jinin jikinsa, babu yadda za'ayi ya rayu.
Koda jin wannan batu sai ukashat ya zazzaro idanu cikin firgici sannan yace, ya ke ummina yanzu kina da tabbacin cewa sarki mutuwa zai yi?
Yayin da muzaira taji wannan tambaya sai ta bushe da dariya sannan tace, ai ina tabbatar maka da cewa sarki ba zai wuce nan da kwana bakwai ba, kaga kenan kafin ku dawo daga yaki anbinne sarki a kabarinsa.
Abu na biyu sa zan sanar da kai shine, idan kuka tafi wannan yaki duk gumun da da zaku shiga kai zaka dawo a Raye, shi kuwa dan uwanka uzaifat sai dai a dauko gawarsa, amma dole ne ka kiyaye abinda zan gaya maka a yanzu.
Abu na farko, ka tabbatar dagewa baka rufe fuskarka ba a cikin hular yaki.
Abu na biyu, kayi shigar jajayen tufafi maimakon farare.
Indai kayi haka zaka tsira da rayuwar ka,kuma zaka dawo gida cikin koshin lafiya. Kayi sani cewa daga cikin mayakan birnin shumbul akwai wani sadauki mai bakaken kaya kada ka kuskura kace sai kaga bayansa, domin yafi karfin ku duk ku biyun kai da dan uwanka don haka kada ka matsa yayin da kuna hadu dashi a filin daga.
Sa'adda muzaira tazo nan a zancenta sai ukashat ya cika da tsananin mamaki, don haka sai ya dubeta cikin rashin gamsuwa yace, ya ke ummina wai shin menene dogaronki bisa samun tabbacin nasara akan abinda muka sa gaba?
Muzaira ta bushe da dariya a karo na biyu tace, ya kai dana ka zuba ido kawai kasha mamaki, amma ina tabbatar maka da cewa komai zai tafi dai dai kuma sai bayan mun sami nasara sannan zan yi maka bayanin komai yadda akayi duk na tsara shirina.
Koda jin wannan batun sai ukashat yayi murmushi yace, na yarda dake ya ummina tabbas na san cewa zaki iya domin duk abinda kika sa gabanki sai kin cimma gaci.
Koda jin haka sai farin ciki ya lullube muzaira ta rugume ukashat tana mai cewa, in mai alfahari da kai ya dana.

* * * * * *

A can bangaren yarima uzaifat da mahaifiyarsa kuwa, lokacin da ya labartama halin da sarki ya shiga sai ta rude ta dimauce ta mike tsaye zumbur d nufin ta ruga izuwa turakar sarki, amma sai ya rikota da sauri yace, yake ummina kiyi sani cewa koda kinje kofar turakar sarki baza a barki ki shiga ciki ba, domin sarki ya kafa doka cewar bai yarda kowa ya shiga wajen sa ba hatta mu din kuwa sai ya bukacemu da kansa.
Koda jin wannan batu sai shulaifa ta cika da tsananin mamaki, na take idanunta suka ciko da kwalla, hawaye ya fara zuba. Al'amarin da ya kefa uzaifat cikin mamaki kenan, ya dubeta yace yake ummina ina dalilin zubar wannan hawaye naki alhalin sarki na nan a Raye bai mutuba?.
Shulaifa ta dubi uzaifat cikin alamun karayar zuciya tace yakai dana kayi sani cewa tun daga ranar da na auri mahaifinka kawo i yanzu ban tana ganin yayi rashin tafiyar da ta kaishi kwanciya ba sai wannan karon. Koda naji sarki ya bada wannan doka sai jikina ya bani cewa lallai ba karamin ciwo ne ya sameshi ba. Lallai bayason ma ganshi a cikin wannan hali shi yasa ya kafa dokar shiga wajen sa. Bugu da kari a cikin wadannan 'yan kwanaki nayi mafarki mai ban tsoro wanda aka dinga nuna mini sarki uwaisul karni a cikin mawuyacin halo wanda ban taba ganinsa a ciki ba. Duk sa'adda na tuno wadannan mafarkai sai tsoro ya baibayeni zuciya ta ta kama daka da karfi. Ga yadda kayi min bayani cewa a lokaci guda sarki ya kama kumallon jini na gasgata mafarkina. A cikin mafarkina nawa an nuna min cewa guba aka baiwa sarki a cikon abinci. Hannun da ya baiwa sarki wannan guba makusancinsa ne, in ba don zargi haramun ne ba ni kain na san wannan hannu. Shin baka zargin cewa tabbas guba ce sarki yasha?
Uzaifat ya sunkui da kansa kasa yace, ko shakka babu akwai alamun haka, domin acikin aman jinin da sarki yayi akwai wani bakin abu mara kyan gani.
Kafin uzaifat ya gama rufe ba kinsa sai ya ga shulaifa ta yanke jiki ta fadi sumammiya. A tude ya nemo ruwa ya yyafa mata sannan ta farfado, ya dubta yace yaje ummina ki sani ta da mutuwa duk a hannun Allah suke saboda haka guba bata isa ta kashe sarki ba face idan kwanansa ya kare. Abin da nake so dake kawai shine, kici gaba da yi masa addu'a akan Allah ya bashi lafiya, ni kuma Allah ya bani sa'a a wannan yaki da zamu fita gobe. Sannan ya karemu daga sharrin dukkan sharrin abokan gaba da makiyanmu.
Koda jin haka sai shulaifa tayi ajiyar zuciya sannan tace, madallah da wannan da nawa na gari mai tunasar da ni kadaitar Allah.

Alhamdulillahi, anan zamu dakata sai kuma gobe Insha Allahu zamu dora daga inda muka tsaya.
Ina muku Fatan alkhairi b
[29/01, 3:20 pm] Umar Farouq: DAKARUN MUSULUNCI
LITTAFI NA DAYA 1.
MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO

Kashe gari kuwa tun da duku dukun safiya bayan any isar da sallah asuba, rundunar biyu ta DAKARUN MUSULUNCI suka yi sahu sahu a kofar fada bisa dawakai kuma cikin shigar yaki mai kwarjini da ban tsoro. Al'amarin da ya janyo hankalin jamaa kenan aka firfito daga cikin gidaje aka tari ana yi musu kabbara, don kara musu kwarin gwiwa saboda sanin cewa JIHADI za su fita.
Sai da dakarun biyu suka shafe kusan rabin sa'a a tsaitsaye sannan masu jagorantarsu suka fito daga gidan sarauta. Ba wasu bane face yarima uzaifat da yarima ukashat.
Koda ganin iri shigar da jaruman biyu sukayi sai gaba daya jama'ar gari suka cika da tsananin mamaki. Suka zuba musu idanu kawai a lokacin da fadar tayi tsit tamakar babu mai rai a wajen. Ba komai ne ya janyo hakan ba face ganin irin shigar da yarima ukashat yayi wadda ta saba da al'adar dakarun yakin kasar. A ka'idar wannan dakarun musulunci na wannan birni duk sa'adda za'a fita yaki kowa na sanya fararen tufafi ne ba'a taba ganin wanda sanya wani kamar ba daban, amma yau sai aka ga yarima ukashat shi kadai ya sanya jajayen tufafi. Nan fa fadar ta rude da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinsa.
Uzaifat ya tafi izuwa gaban dakarunsa ya tsaya, sannan Shima ukashat ya tafi izuwa gaban tasa rundunar. Faruwar hakan ke da quya sai ga wazirin sarki uwaisul karni ya fito daga cikin fada, sauran 'yan majalisa na boye da shi.
Koda juma'a suka hangosu sai filin fadar yayi tsit aka zuba musu idanu har suka zo gaban juma'a suka tsaya.
Bayan waziri ya wuce gaba sai ya tsaya cak ya fuskanci alumma a cikin nutsuwa sannan yayi sallama iri ta addinin musulunci.

Cikin hadin baki gaba daya gaba daya jama'ar gari suka amsa sallamar sannan yayi gyaran murya yace, yaku 'yan uwana musulmi kuyi sani cewa ni wakili ne na sarkinmu mai girma sarki uwaisul karni, kuma na tsaya ne a gaban ku domin na isar da sakonsa a gareku bisa kasan cewar ba zai iya fitowa ba a yau ya fuskanceku sakamakon 'yar lalurar rashin lafiya data riskeshi a jiya.
Koda jin wannan batu sai fadar ta sake rudewa da hayaniya, masu salati nayi masu yin addu'o'i nayi.
Wasu kuwa sai hankalisu ya dugunzuma. Bakomaine ya haddasa hakan ba face mamaki da kima fargaba, domin a tarihin rayuwar sarki tun da ya hau kan mulki bai taba yin tashi lafiyar da ta hanashi fitowa ba sai yau. Koda waziri yaga fadar ta rude sai ya daga hannunsa sama, take kuwa juma'a suka yi shiru kamar mutuwa ta gifta waziri taci gaba da bayani yana maicewa.
Yaku 'yan uwana musulmi, kuyi sani cewa babu wani abu dauwamamme face Allah da kansa, kuma ciwo ba shine ajali ba.

Kada ku tayar da hankalin ku bisa lalurar data samu sarkinmu mai adalci, domin babu mai yaye masa face ubangijin daya dora masa.
Abinda ya kamacemu shine muci gaba da yi masa addu'a akan Allah ya yaye masa wannan lalura.
Koda gama fadin haka sai fadar ta rude da amin!!
Nan take waziri yace a karantawa sarki falaki da nasi da ayatul kuriyyu.
Aka rufe da sirril fatiha.
Cikin hadin baki kuwa aka kammala wannan addu'a.
In da mutum na kusa sa'adda ake wannan addu'a sai gaba daya tsigar jikin sa ta tashi saboda jin dadin sautin addu'ar a bakin jama'a wacce ta cika dodon kunne, kuma ta sanyaya zukata. Koda mutum kafirine in dai ya jiyo wannan sauti sai zuciyarsa ta karaya.
Bayan am idar da wannan addu'a sai waziri yavi gaba da jawabi yana mai cewa.
Yaku jama'ar wannan birni, kuyi sani cewa sarki yace a sanar daku ana bukatar gudunmawar ku ta addu'a bisa wannan yaki wanda 'ya'yansa zasu jagoranta izuwa birnin shumbul.
Kamar yadda kuka sani shekara da shekaru muna fafata yaki da wadannan mutanen kasar shumbul amma bamu taba samun nasara akansu ba, suma haka.
To fa a wannan karon anyi shiri na musamman wanda ake sa ran cewa lallai za a sami nasara akan abokan gaba, don haka ana bukatar jajircewar gudunmawarku ta addu'a daga yanzu har zuwa lokacin da za a dawo daga wannan yaki.
Wannan shine iyakar sakon da sarki ya bayar a shaida muku. Idan akwai wani mai korafi yayi bayani. Idan kuma babu yanzu mu yi bankwana da mayakanmu domin su kama hanya izuwa filin daga.
Koda waziri yazo nan a zancensa sai yayi shiri ya kurawa jama'ar gari idanu ko zai ji wanda zai zo da korafi.
Tsawon 'yan dakiku fadar ta sake yin tsit. Daga can sai wani Dattijo mai yawan shekaru ya dogara sandarsa a hankali yana mai rantsowa ta tsakiyar jama'a ya ido gaban waziri ya tsaya sannan yayi sallama irin ta addinin musulunci ya ce, ya kai wazirin sarkinmu, kayi sami cewa mi dai a garin nan Allah yayi baiwar kwana domin a halin yanzu bana tsammanin cewa akwai mai yawn shekaru na, domin da wayona aka haigi kakan sarki na ukj. A iya taso wata a wannan birni namu mai albarka ban taba ganin bakon al'amari ba irin na yau.
Wannan bakon al'amari kuwa ba komai bane face irin shigar tufafin da yarima ukashat yayi a yau. A iya sanina tun daga kafa wannan birni kawo I yau duk sa'adda za'a fita yaki kowa fararen tufafi yake saw a jikinsa, ba'a taba ganin wani ya sanya sabanin haka ba, shin ko yarima zai iya yi mana bayanin da yasa yazo da wannan sabone tsari a yau?
Yayin da waziri yaji wannan tambaya daga bakin Dattijo sai ya gyara murya yace, to masu iya magana sunce waka a bakin mai ita tafi dadi, saboda haka yanzu zan bukaci yarima ukashat da ya fito gaban jama'a ya kare kansa in da hali domin ni kaina ban san hujjar sa ta sanya jajayen tufafi ba a yau.
Kafin waziri ya gama rufe bakinsa tuni ukashat ya sauko daga kan dokinsa yazo gaban jama'ar ya tsaya yana mai murmushi ba da fargabar komai ba.
Nan take ukashat yayi sallama jama'a suka amsa masa, sannan yace.
Yaku 'yan uwana musulmai, da farko dai ina son kusani cewa a har kullum ana son musulmi yayi aiki da kyakkyawar niyya. Al'ada bata gaban farilla ko sunana.
Sanya fararen tufafi yayin fita yaki a wannan birnin namu al'ada ce ta iyaye da kakanninmu ba wai farilla bace a cikin addinin Allah, don haka sabanin haka baya nufin an kauce hanya ko an sabi Allah.
Ina son kowa ya fahimat cewa na bambanta suttura ta da ta sauran abokan tafi yane domin kawai na darsa shakku a cikin zuciyar abokan gaba kuma na firgitasu suyi tunanin wani abun Daban wanda zai iya kawo musu nakasu a cikin wannan yaki. Wata kila yin hakan yazamo sanadin samun nasara akansu.
Abu na biyu da nake son jama'a su fahimta shine, mahaifinmu ya tura mu wanann yaki ne akan babban hujja guda daya.

Wanna hujja itace, ya raba mayakanmu izuwa kaso biyu, naso na farko na Karkashin jagorancin dan uwana uzaifat, daya kason kuwa a Kar kashin nawa jagorancin yake.
Za'a fara wannan yaki ne da tawa rundunar sannan daga baya rundunar dan uwana su kafsa da abokan gaba. Duk wanda rndunarsa ta samu nasara shine zaigaji karagar sarki.
Shin ba kwa tunanin cewa wannan gasa wadda sarki ya shirya mana bata dace ba? Shin ba kwa ganin cewa akwai son zuciya a cikinta?
Koda jin wannan batu sai fadar ta rude da hayaniya, al'amarin da ya dugunzuma hankalin 'yan majalisar sarki kenan ga dayansu suka ware gefe guda suka tattauna.
Daga bisani sai waziri yace shi kenan an yarda yarima ukashat ya tafi wannan yaki a cikin shigarsa ta jajayen tufafi.
Ba tare da bata lokaci ba aka buga tambarin yaki dukkanin dakaru suka yi bankwana da iyalinsu wasu na kwalla, wasu kuma na yiwa dakarun murna akan zasu tafi neman shahada.

Daga nan sai dukkanin dakarun suka hau dawakansu. A lokacin ne shulaifa ta zo gaban yarima uzaifat domin suyi sallamar karshe.
Ta dubeshi cikin yanayin damuwa tace, ya kai dana kada ka mance da nasihata a gareka bisa abubuwa uku nan da nace ka kiyaye su. Abu na farko shine, gaskiya, sai amana, sai cika alkawari.
Uzaifat yayi murmushi yace, ya ke ummina ki kwantar da hankalin ki da izinin Allah zan kiyaye bisa wadannan abubuwa uku, ni dai bukatata a wajenki kawai itace ki tayani da addu'a.
Koda jin haka sai idanun shulaifa suka ciko da kwalla tafara zubar da hawaye, al'amarin daya dugunzuma hankalin uzaifat kenan ya dubeta cikin matsanaiciyar damuwa yace ina dalilin zubar wannan hawaye naki ya ummina
Shulaifa ta share hawayenta sannna tace, ya kai dana kayi sani cewa dolene nayi kuka domin ina cikin tsaka mai wuya.
Katuna halin da mahaifinka ke ciki yana kwance cikin jinya babu tabbacin zai tashi, kai kuma gashi yanzu zaka tafi jihadi ba lallai bane ka dawo ba, kaga kenan zan iya zama bazawara kuma mara da, idan na rasaku duk ku biyun. Sa'adda shulaifa tazo nan a zancenta sai tausayinta ya kama yarima uzaifat har shima ya kama hawaye, kawai sai ya sauka daga kan dokinsa suka rungume juna.
Tsawon 'yan dakiku suna Jade sannan ya janye jikinsa daga cikin nata suka fuskanci juna yace.
Yake ummina ina son ki kasance mai yin tawakkali bisa kaddara, ki tuna cewa RAI DA MUTUWA duk na Allah ne, kuma Allah baya barin wani domin wani. Idan sarki na da sauran shnaruwa a duniya dole ne ya tashi daga wannan cuta.
Ni kan takaicina daya ne da ya hanamj ganawa da shi. Yanzu gashi zan tafi wannan yaki ba tare da nayi masa bankwana ba wata kila kuma shikenan har abada ba zamu sake ganin fuskar juna ba.
Yayin da uzaifat yazo nan a zancensa sai itama shulaifa ta kamu da tsananin tausayinsa ta rungumeshi tana kuka shima yana kuka kamar ba zai daina ba.

* * * * * *

A can bangaren yarima ukashat da mahaifiyar sa muzaira kuwa, lokacin da suka zo yin bankwana ko kadan babu alamar wata damuwa a tare da fuskokinsu face Farin ciki.
Kalma daya muzaira ta dubi ukashat tace dashi.
Nasara na garemu ya dana. Ukashat yayi murmushi yace, Tabbas maganar ki dutse ce.
Gama fadin hakan ke da wuya sai sukaji an sake buga tambarin tafiya. Nan take uzaifat ya sako mahaifiyar sa ya kama dokinsa ya hate.
Dam ukashat da dakarunsa ne akan gaba don haka sai suka wuce izuwa kofar fita daga cikin birnin, sannan uzaifat da nasa dakarun suka take musu baya a lokacin da jama'ar gari da 'yan majalisar sarki suka busu da kallo har aka daina hangosu, sannan waziri ya sallama kowa fada ta watse ya zamana cewa babu kowa a wajen face mutum biyu rak.
Ba wasu bane face muzaira da shulaifa.

Koda suka dubi juna sai muzaira tayi murmushin mugunta a gareta sannna ta taho daf da ita ta tsaya suka kurawa juna idanu.
Muzaira tace, to babban abokiyar gabata kiyi sani cewa lokaci yayi da zan dauki fansa akanki da mijinmu. Ina tabbatar miki da cewa nan da kwana bakwai rak sarki zai mutu, domin ba zai tsufa daga sharrin gubar dana bashi ya ci ba.
Wannan yaki da 'ya'yan mu suka tafi ina tabbatar miki da cewa sanki ba zai dawo a raye ba, dana ne zai dawo cikin koshin lafiya, kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login