Showing 18001 words to 18821 words out of 18821 words
Chapter 7 - Dakarun Musulunci Book 1 By Abdulaziz Sani M Gini.txt
abinda ke cikin fadar nan ya hallata a gareka.
Abu na biyu da ban fada maka shine duk wannan abinda ke faruwa da sanin mahaifiyar ka domin muna tura wasu aljanu suna sanar da ita ilimin tsafi a sirrance ba tare ya kowa ya sani ba, haka kuma mu muka tsara mata yadda zata kawo mana karshen sarkinku, kuma muka umarceta da lallai idan lokacin fita yaki yayi ta sa ka kasa jajayen tufafi.
Kuma mun mata alkawari indai burinmu ya cika to kaine zaka zama sarkin darul husuf.
Koda ji wannan batu sai Ukashat ya dubi sarki sha'aran yace, "Yanzu ina labarin 'yar likita abu sharaz koda jin wannan tambaya sai sarki ya dubi Ukashat yace, " Yar likita abu sharaz tana gidan gonata a cikin tsaro babu wanda ya isa yaje inda take face ni.
Abinda nake so da kai shine ka kwantar da hankalinka ka kall daular nan duk takace duk abinda kake so kayi amfani dashi, ga kyawawan kuyangi da 'yan mata duk wanda kakeso ka kwanta da ita zata baka hadinkai ko da kuwa 'yata ce Sazirat.
Koda jin wannan batu sai Ukashat ya daga kai ya dubi irin daular dake cikin fadar da irin kayan alatun dake cikinta, sannan ya daga kai ya dubi sazirat kawai sai ya duma wawa akan kayan abinci da abinsha da aka ajiye a gefen fadar a kan tebur, daga bisani kuma ya farwa sazirat suka aikata lalata. Wannan shine abinda ya faru ga dan uwanka sa abokan tafiyarku.
Koda Lafirat tazo nan a zancenta sai hawayen takaici ya zubowa Uzaifat yace, yanzu kina nufin dan uwana ya gujemu ya hada kai da kafirai makiya Allah akan kawai ya gaji karagar mulki, kuma ya yadda ya aikata zina kuma yasha giya a matsayin sa na dan sarkin musulmi me mulkin babbar kasa.
Tabbas sharrin zuciya yafi fa haka, to yanzu munji bayanin inda abokan tafiyarmu suke, amma kuma haryanzu baki fada mana dalilin da yasa kika ceci rayuwar mu ba.
Koda Lafirat taji wannan tambaya sai tace, ai nafada muku bukatata da kuma dalilin da yasa na ceci rayuwrku tun a cikin labarin da na baku ni da 'yar uwata.
Bukatar kuwa itace ina so ku taimaka min na samu damar da zan iya hallaka mahaifina wato sarki sha'aran da kuma yar uwata sazirat, domin a binciken da nayi dole sai na hada kai da ku domin samun wannan nasara na cika burina.
Sa'adda Uzaifat ya ji wannan batu sai yayi ajiyar zuciya yace damu dake duk bukatar mu irin daya ce bambancin dake tsakani kawai shine, ke kina sone ki kashe sarki da Sazirat don sun aikata wancan aikin, mukuma muna so ne muyi jihadi mu kafa turar musulunci a kasar.
Abinda nake so dake shine zamu taimaka miki amma bisa sharadi guda daya, sharadin shine zaki mana rakiya izuwa kurkukun birninku inda aka kai abokan tafiyamu domin na ceto rayuwarsu, kuma na dauko 'yar likita Abu sharaz a cikin wannan gidan gona inda aka tsareta, inyaso sai mu koma can kasarmu domin muyi sabon shirin yaki.
Kuma naje na ga halin mahaifina ke ciki, yana rayene ko ya mutu?.
Koda jin wannan batu sai Lafirat ta kwalla ihu mai razanarwa, sannan tace, ai kazo min da abinda yafi karfina. Idan har na bika izuwa cikin birnin mu tabbas hallaka zanyi, burina bazai cika ba, domin ban gama shirye shiryena ba na tunkarar ubana da 'yar uwata, A kalla ina bukatar wata uku nan gaba kafin na kammala shirina.
Shawarata agareku itace, ku koma da baya zuwa birninku kuje ku sanar da jama'ar ku abin da ya faru, domin kuyi gagarumin shiri kafin su sarki Sha'aran su iso birninku don yakar ku. Nima zan kawo gudunmawata idan yakin ya taso.
Koda jin haka sai Uzaifat ya dubi Lafirat a cikin fushi yace, yake wannan basadaukiya kiyi sani cewa ni bazan koma da bayaba, ba tare da na kaiwa 'yan uwana dauki ba! Da dai na koma na tare da cikakken labarin su ba gwara na sara rayuwata.
Idan har ba zaki iya yi mana jagora ba izuwa birnin shumbul to ki samu a hanya, in kuma ba haka ba sai dai mu ma mu warware alkawarinmu na baki had in kai.
Yayin da Lafirat taji haka, sai hankalinta ya dugunzuma, tarasa abinda ke mata dadi a duniya, don haka sai ta kasa zaune ko tsaye. Tayi ta kai kawo a cikin fadar tana tunani.
Alhamdulillahi nan zamu dakata sai kuma Allah ya kaimu gobe zamu ci gaba fatan kuna jin farin ciki bisa sharhin wannan littafi, na barku lafiya.
UMAR FAROUQ ZANGO