Showing 15001 words to 18000 words out of 18821 words
Chapter 6 - Dakarun Musulunci Book 1 By Abdulaziz Sani M Gini.txt
zakk tamkar sarewa.
Uzaifat ya dubi Abul shaja'a yace, anya kuwa wannan mutumin da ya cecemu ba shibane mai bakaken kaya na birnin shumbul wanda aka bamu labari? Wata kila wata muguntar ya ke son ya shirya mana shine ya ke son ya yaudaremu.
Sa'adda Abul shaja'a yaji wannan batu sai yace, anya kuwa hakane? Ai inda shine ba zai cecemu ba. Ai kawai mubi umarnin sa mu ga abinda zai faru tunda dai bamu da wani zabi, babu yadda zamu iya fita daga nan face mun hau kan wannan tsauni.
Cikin gaggawa uzaifat da Abul shaja'a suka cire igiyoyin daga wuyansu sannan suka kama igiyoyin suna hawa izuwa saman tsaunin. Babu abinda ya basu mamaki face ganin irin tsabar karfin wannan mutum mai bakaken kaya, domin shine ya rike igiyoyin da hannayensa har suna lilo a kai ba tare da nauyinsu ya rinjayeshi ba.
Shi dai wannan tsauni ya kai zira'i dari da arba'in.
Amma mutumin nan mai bakaken kaya bai gajiya ba har su uzaifat suka gama hawa saman tsaunin suka riskeshi.
A sannane yayi haki guda daya yayi watsi da igiyoyin kawai sai ya kwaye rawanin da ya rufe fuskar sa.
Take uzaifat da Abul shaja'a suka dimauce, bisa yin arba da fuskar. Ba komai suka gani ba face wata tsaleliyar budurwa mai tsananin kyawun na gaban kwatance.
Gashin kanta ya zubo har kasan kwankwasonta. A bayanta tana goye da wata jibgegiyar takobi.
Budurwar ta dubesu tayi musu murmushi tace, lale marhabun da yarima uzaifat dan sarki uwaisul karni.
Kayi sani cewa akwai labari mai yawa a bakina, domin na san komai akanku. Hatta abokan tafiyar ku da suka bace na san da inda suke.
Koda jin wannan batu sai uzaifat da Abul shaja'a suka sake cika da tsananin mamaki.
Uzaifat ya dubeta cikin mamaki yace, ya akayi duk kika san wannan al'amari? Kuma wacece ke ? Sannan saboda me kika ceci rayuwar mu?
Koda jin wadannan tambayoyi sai budurwar ta sake yin murmushi tace, duk za kuji amsar tambayoyina, amma sai kun nutsu tukunna. Abin da nake so daku shine, ku kwantar da hankalinsu ku bani yarda, na rantse da girman uwata ba zan cutar daku ba, domin kuna da mutukar amfani a gareni.
Ku biyoni izuwa cikin gidana domin mu zauna mu tattauna a cikin nutsuwa.
Koda gama fadin hakan sai budurwar ta kama dokita ta hau tayi gaba tana mai tafiya a hankalin, su kuwa sai suka bita da sauri don kada tayi musu nisa ta bace.
Sannu a hankali suka gangara kasa tsaunin, sannan suka iso bakin wani katon mulmulallen dutse fari fat, irin wanda basu taba gani ba a rayuwarsu.
Koda isowar wannan budurwa gaban farin dutsen sai ta sauka daga kan dokinta ta shafi dutsen da hannunta na hagu, kawai sai suka ga wata kofa ta zinare ta baiyana akan dutsen, ta bude kanta suka hango kayataccen gida a cikin dutsen.
Budurwar ta waiga ta dubi uzaifat da Abul shaja'a cikin murmushi irin wanda ke ruda dukkanin da namiji tace, ku biyoni izuwa ciki.
Nan take ta kunna kai cikin gidan, shi kuwa wannan doki na ta sai ya raba jikinsa da wannan farin dutse, take ya shige cikin dutsen ya bace bat! Tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen.
Abul shaja'a da uzaifat suka dubi juna. Abul shaja'a yace, ya shugabana anya kuwa ma shiga cikin gidan nan? Na fuskanci cewa wannan budurwa ma'abociyar tsafi ce, bai kamata muyi Hulda da. ita ba.
Uzaifat yayi ajiyar zuciya yace, ai akwai hulda ta lalura, don haka ba laifi bane. Mu shiga cikin wannan gida, amma dole ne mu kiyaye ga barin duk abinda zayasa mu sabi Allah.
Koda gama fadin haka sai uzaifat ya bi bayan wannan budurwa, shima Abul shaja'a sai ya bi bayan sa yana tafiya a cikien dari dari.
Gaba daya kasan gidan an malaleshi da lu'ulu'u ne, kuma komai na amfanin gidan da zinare aka yi shi. Babu abinda ya baiwa su uzaifat mamaki face yadda gidan ke da girman gaske, sannan an tsarashi wuri wuri, kuna ko ina an zuba kayan alatu na gaban kwatance. A takaice dai wannan gida aljannar duniya ce a cikin sa.
Nan dai suka yi ta wuce barori da kuyangi suna ta hidima, har suka isa wata kasaitacciyar fada mai dauke da shimfidu da kujeru na alfarma iri iri.
Da Isar su wannan fada sai budurwar ta hau kan wata karagar mulki ta zamu, sannan ta yiwa su uzaifat nuni da wasu kujeru tace su zauna. Zamansu ke da wuya sai aka kawo musu abinci iri iri da ababan shaye shaye kala kala da kuma 'ya 'yan itatuwa.
Kyakkyawar budurwar ta dubi uzaifat da Abul shaja'a tayi musu tayi. Kawai sai uzaifat ya dauki tuffa guda daya ya soma ci.
Ganin hakan ne shima Abul shaja'a ya dauki tuffa ne sai uzaifat ya dauki tambulan na kayan shaye shaye yana shinshinasu har sai da yaji wanda ke kanshin ruwan inibi sannan ya dan dana kadan ya tabbatar da cewa babu giya a cikina, ya sha.
Shima Abul shaja'a sai yayi koyi dashi. Sai da suka sha ruwan inibin suka koshi sannan suka yi hamdala suka zubawa Wannna kyakkyawar budurwa idanu.
Budurwar ta bushe da dariya tace, hakika ku dai ma'abota addinin musulunci kuna da tsantseni akan alamuran duniya. To ku sani cewa na san duk irin dokokin cin abinicinku, don haka na zan taba cigar da ku abin da addininku ya haramta ba. Ina mai sanar daku cewa na zauna da ma'abota addinin addininku har tsawon shekaru shida, babu abinda ban iya ba na dangane da yadda ake bautar ubangijin ku.
Nayi ilimi dai dai gwargwado, kuma nayi nazarin addinin naku da kyau, na gano shine addinin gaskiya, amma na ki karbarsa saboda in na karbeshi ba zan taba cika burina ba na duniya. Wannan wank darasine Daban a cikin tarihin rayuwata.
Yanzu dai ina mai sanar daku cewa sunana Lafirat, kuma na kasance 'ya ga sarki sha'aran ibn Nukaib mai mulkin birnin shumbul, wato birnin abokan gabarku.
Ina son ku sani cewa ba nice kadai 'yar sarki shaaran ba, akwai 'yar uwata mai suna sazirat, wacce aka haifemu tare.
Ma'ana Hassana da Hussain's muke, wato uwa daya uba daya. Ni da ita kamarmu daya tamkar an tsaga kara, komai Kular mutum ba zai iya bambancemu ba , to amma akwai bambancin, kuma duk duniya babu mai iya tantancemu face mahaifinmu. Tun da aka haifemu muka taso da tsagwaron sadaukantaka, wato karfin damtse na tsiya tsiya, sannan kuma sai mahaifinmu ya rinka tsumamu da tsumin tsafi har izuwa sa'adda muka zama cikakkun mata.
A sannane na fara samun sabani da 'yar uwata sazirat, bisa burinta na son ta gaji mahaifinmu, watota zamo sarauniyar birnin shumbul kamar yadda a yanzu kaima ka sami sabani da dan uwanka ukashat.
Kafin wannan lokaci daga kuruciyarmu zuwa gairmanmu ni da sazirat bamu taba yin koda sa inda ba, amma sai gashi a ta kaimu ga zagin juna, harma da yin kazamkn fada. Idan muka fara kwamarzuwa sai mu kwana uku muna yaki bamu saurara ba har mu rushe wurare da dama a gidan sarautar mu, mutuwa junanmu mugayen raunika.
Babu wanda ya isa ya rabamu wannan fada face Mahaifinmu, amma kuma sai yaki rabamun sai dai ta kaimu ga sumar da juna.
Bisa wannan halaiya ne watarana sarki shaaran ya taramu a gabansa yace, a cikin ku duk wadda take son ta gajeni dolene tayi abu uku.
Abu na farko dole ne ta bani kanta na kwanta da ita.
Abu na biyu dolene ta yanka jariri a gabana ta shanye jikinsa. Abu na uku kuwa dole ne ta hakura dayin aure har abada.
Koda naji wannan batu sai na kwalla ihu mai firgitarwa na rushe da kuka, sannan na dubi mahaifinmu nace.
Tur da wannan bakar al'ada taka. In dai sai nayi wannan abubuwan uku sannan zan gajeka na hakura da mulkin kasar nan har abada. Ni kan da na aikata wadannan abubuwa uku gwara ma na rasa rayuwata.
Na dubi 'yar uwata sazirat nace, yake 'yar uwata kada kwadayin mulki ya rudeki ki bata rayuwar ki. Lallai kema ki hakura da wannan bukata.
Yayin da sazirat taji wannan shawara tawa, sai ta bushe da dariya, daga can kuma sai ta murtuke fuska tace,
Ni kan na sami hanyar da zan cika burin a cikin ruwan sanyi. Don haka dole na aikata wadannan abubuwa uku.
Koda jin wannan batu sai hankalina ya dugunzuma ainun, na sake fashewa da kuka na shiga rokon sazirat, ina maicewa da ita.
Kada ta yarda ta aikata wadannan mummunan aiki.
Koda na ga ta nufi inda mahaifinmu ke tsaye, sai na duga da gudu da nufin na riketa na hanata zuwa gareshi.
Kawai sai mahaifinmu ya nunani da hannunsa na hagu, taje wata irin murtukekiyar sarkar tsafi ta nannade jikina gaba daya tayi min mugun dauri ya zamana cewa na kasa koda motsa hannayena.
Nan fa ma shiga amfani da karfin sihirna don na kwance kaina, amma sai tsafina yaki yin tasiri.
Mahaifinmu ya sake dubana ya kyalkyale da dariya yace, yake 'yata ki hakura kawai, domin baki isa ki iya hanamu aikata wannan aiki ba. Yin wannan aiki ne kadai zai sa ki samu cikakken tsafin sihirin tsafi dai dai da nawa.
Nan take sarki shaaran ya farwa 'yar uwata sazirat ya santa 'ya mace a gaban idanuna, a lokacin da na ke ta faman rusa ihu da kuka saboda tsananin takaici.
Bayan sun gama aikata lalatarsu sai sarki yasa aka je aka nemo jariri sabon haihuwa aka kawo. Nan take sazirat ta yanka jaririn da wuka akan makogwaronsa, ta kafa bakina ta sha jinin jaririn.
DAKARUN MUSULUNCI
LITTAFI NA DAYA 1
MARUBUCI:- ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
TYPING:- UMAR FAROUQ ZANGO
LAFIRAT ta ci gaba da cewa.
Koda na gama ganin wannan mugun aiki na rashin imani da batanci, sai nan take naji na tsani mahaifina da 'yar uwata sazirat kamar yadda na tsani mutuwa ta.
A sannane sarki ya sake nuna ni da hannunsa na hagu, wannan sarka data daure ni ta bace bat. Kawai sai na dubi sarki da sazirat a lokacin da hawaye ke zuba a idanuna nace, Hakika daga yau bani baku! Wannan gidan ya haramta a gareni, zamana daku ya kare har abada, tsakanina da ku sai yaki! Kiyayya ta a gareku ba zata gushe ba face na ga na zare muku ruhin numfashi saboda mugun aikin da kuka aikata.
Ya kai Abbana hakika ka cika kazami wanda yayi amai ya lashe abinda. Wannna abu da ka aikata ya shafe matsayinka na uba a gareni. Kuma ka cusa mini bakin ciki wanda har abada ba zai kankaru ba a cikin zuciyata face ajali ya riskeni. Ina nadama da na zamo tsatsonka.... Gwara ace na kasance ba 'yar kowa ba sai 'yar talakan da babu kamarsa a talauci a fadin duniya.
Da wannan furuci nake yi muku bankwana na karshe... Duk ranar da kuka fa na dawo gidan nan, to ku tabbata cewa wannan rana itace ranar mutuwarku.
Koda gama wannan jawabi sai na juya na fice daga cikin fadar.
Sarki sha'arn da 'yar uwata sazirat kuwa, suka yi ta kyalkyala dariya kamar bazasu taba dainawa ba har abada."
Lokacin da Lafirat tazo dai dai nan a labarinta, sai ga hawaye na sartu akan kumatunta. Al'amarin da ya sa uzaifat da Abul shaja'a suka kamu da mutukar tausayinta kenan.
Uzaifat ya dubeta a nutse yace, " Hakika kina da babbar hujja wadda ta sa kika rabu da mahaifinki da kuma'yar uwarki.
Yake wannan kyakkyawar budurwa, yanzu una batun abokan tafiyar da kika ce kin san inda suke, amma haryanzu baki sanar da mu ba.
Haka kuma baki fada mana dalilin da yasa kika ceci rayuwar mu ba, kamar yadda na bukata a baya?".
Lafirat tayi gyaran murya tace, "A jiya da daddare, lokacin da kuka yada zango a cikin dajin nan, mai sarkakiya har kuka kafa tantuna kuka kwanta a ciki. Dukkanin ku kunyi barci face wadanda ke tsaitsaye a wajen tantin suna gadi.
Sa'adda dare ya raba ne, sarki sha'aran ya turo wadansu zakwakuran aljanu dai dai adadinku suka zo suka kwashe mutanen ku gaba daya face ku biyun nan kawai. Abin da ya hana kuma a dauke ku shine, kafin kuyi barci kai Uzaifat ka tofa addu'a a cikin tantin naku a gabas da yamma kudu da arewa da kuma sama da kasa. Karfin wannan addu'a da kayi ne tasa duk aljanin da ya doshi tantunku sai yaji kamar zai babbake. Bisa dole suka hakura suka tafi suka barku a cikin tantin.
Bayan aljanun sun kwashe jama'ar taku sun yi sama da su, basu zame ko ina ba sai fadar mahaifina sarki sha'aran ta birnin shumbul.
Tsananin ganin munin wadannan aljanu ne yasa jama'arku suka dimauce har suka kasa yin addu'ar daza su kubuta daga hannunsu. Suna ji suna gani aka kaisu har cikin fadar aka kuma daddauresu da sarkokin tsafi, kuma aka kukkulle bakunansu yadda bazasu iya motsa harsunansu ba bare suyi addu'a. Dayawa daga cikinsu ma sun haukace, wasu sun suma saboda yin arba da wadannan aljanu. Mutum dayane daga cikin jama'ar taku ba a daureshi ba da wannan sarkar tsafi. Wannan mutum ba kuwa ba kowa bane face mai jajayen tufafi, wato dan uwanka Ukashat.
Lokacin da Ukashat yaga shi kadaine ba daureshi ba sai ya cika da mamaki, kuma ya zama dan kauye ya kama kalle kalle a cikin fadar mahaifina saboda ganin irin aljannar duniyar da aka shirya a cikinta.
Ba zato ba tsammanin sai Ukashat yaga sarki sha'aran da sazirat sun baiyana a gabansa suna kyalkyala masa dariya.
Cikin tsoro ya kura musu idanu ya kasa yunkurin komai.
Sarki sha'aran ya dubeshi yace, "Ya kai Ukashat dan sarki uwaisul karni wanda ke burin zamowa sarkin Darul Husufa, ka kwantar da hankalinka ka sani cewa mu ba zamu cutar da kai ba shiyasa ma muka tura aka daukkoku tun gabannin ku iso filin daga inda zamu fafata yaki daku. Ina mai tabbatar maka sa cewa koda an fafata wannan yaki, dayanku ba zai tsira da rayuwarsa ba, domin munfi karfin ku nesa ba kusa ba. Sarkinkune kadai ya zame mana matsala.
Yanzu gashi mahifiyarka tayi mana maganin sarkinku, ta ciyar da shi guba wacce zata zamo sanadiyyar ajalinsa. Babban sirrin da baka sani ba shine, asalin mahaifiyar ka 'yar mu ce, run tana jaririya muka shayar da ita komai na al'adarmu, amma sai muka Kaita cikin birnin ku ta taso a hannun wani aminin sarkin ku a matsayin 'yarsa. Abinda bai sani ba shine, a ranar da matarsa ta haifi 'ya mace sai muka yi masa musanya da tamu ya ci gaba sa renonta a matsayin 'yar cikinsa. Tasa 'yar kuwa sai muka kawota nan muka ci gaba da renonta ta girma a matsayin mafita 'yar uwarmu.
Wannan amini na Mahaifinku ba wani bane face likita Abu sharaz, wato kakana".
Sa'adda sarki sha'aran ya zo nan a jawabinsa sai Ukashat ya cika da tsananin mamaki.
Koda ganin haja sai sarki sha'aran ya sake tuntsurewa da dariya yace, Ai na san za kayi matukar mamaki bisa jin wannan labari, amma duk abinda nake so ka fahimta shine, abokin gaba yana iya bata shekara da shekaru wajen neman hanyar da zaibi yaga ya samu nasara akan abokin gabarsa.
Ya kai wannan dan sarki kasani cewa na dade ina aika dakarun aljanu domin suje su baje birninku, amma ba dayansu da yake dawowa a raye. Lokacin da nayi bincike sai na gano cewa akwai wasu layu da aka binne a Kar kashin katangun da suka kewaye birnin ku guda hudu, tunda aka kafa ganuwar wannan birin wadannan layun suke, a cikin bincikena an tabbatar min da cewa indai ina so naci birninku da yaki har nasamu basarar shiga cikin birnin to dole ne sai an tone wadannan layu, sau shida ina tura dakarun aljanu domin su tone wadannan layu shima duk wa'yanda suka tafi basa dawowa.
Daga baya sai na sake shiga halarar tsafi ta kwana bakwai, a sannan na gano cewa ba wanda ya isa ya tone wadannan layu face tsatson gidan sarautar birnin, Ma'ana sai jinin sarautar birnin.
Tunda na fahimci haka na dukufa wajen ganin ya za'ayi na samu nasara samun tsatson jinin gidan sarautar, ina cikin bincike na ne aka nuna min fitowarku yaki zuwa filin daga inda aka saba gwabza yaki tsakanin mu.
Nayi amfani da wannan dama bayan kunya da zango a cikin wancan daji nasa zakwakuran dakarun aljanuna suka je suka deboku. Kasani ya kai yarima na dade ina jiran irin wannan dama amma bansameta ba sai yanzu.
Tabbas indai ka yadda muka hada hannu ka hada kai damu muka ci birninku da yaki kuma muka samu nasarar kashe Mahaifinku da dan uwanka to tabbas duk