Showing 30001 words to 33000 words out of 63472 words

Chapter 11 - Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel By Hanne Ado Abdullahi.txt

09 Nov 2025

2192

Usman ne dai ba su basu kudi ba, amma sun bawa yaran gidan kyautar dubu dari da sunan su sha ice cream.
[8/7, 21:39] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 22
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Hajiya Rumaisa kuwa da ta debi yara da sunan mai da su makaranta sai da ta yi yawon shakatawa da su san nan ta mai da su. Ni kaina ban sani ba dama hutun nasu bai kare ba ko kuwa tsabar gata ne ban san abin da ya faru ba.
Da farko sun shiga Sudan suka dau tsawon kwana hudu. Nan suka ce tun da karatu bai yi zafi ba,za su bi Momi da Daddy yawo. Inda zaka san da plan dinsu duk visa su iri daya ce. Bayan sun bar Sudan, China suka wuce direct, anan ne Momi ta karbi makudan kudade a wajen Daddy da sunan zata yiwa yara sayayyar kayan aure. Komai na mutum uku ta saya. Daddy yaji dadi matuka ganin yadda ta hada Zainab da yaranta ta sai musu komai iri daya.
Bilkisu taji dadin wan nan ziyara ta su. Ga Momi ga Daddy ga Farida ga Farisa ga kuma ‘yar uwarta Sakina. Sosai tayi murna da ganinsu. Anan ne kuma aka ragargaji sayayya.
Daga nan suka yi tunanin shiga makka domin Ummara, amma ita ma tun da sukaje harami sau daya, basu sake komawa ba. Sai yawan mall mall da suka dinga yi. Malam Usman ma, ya debi nasa iyalan sun je ummara saboda alkawarin da ya yayi wa Hafsa na cewar idan jarrabawarta tayi kyau zai kaita ummara. Ya kuma cika mata alkawari har kannenta ma suka samu albarkancinta.
Ya san kwana biyu kafin tahowarsu Al bashir ya kai musu ziyara. Kuma tabbas bayan nan ko ranar da zasu taho sun yi waya da Hafsa kuma ba wanda yaji labarin za su zo kasa mai tsarki. Saboda tun da Albashir yaje zuwan farko zumunci na waya kullu tsakanin ta da mutan gidan da mahaifiyarta ta ke aure.
Gaskiya daga Dr Abdalla har hajiya Rumaisa ba su ji dadin yanayin da suka ga Khadija da mijinita a ciki ba.
Ga kyawawan ‘ya’yansu masu dimbin ladabi da biyayya. A wulakance su Rumaisa da nasu 'ya'yan suka gaishe su kamar yadda suka saba gai da dangin mahaifinsu.
Shi kuwa Mallam Usman bA wan nan ne a gabansa ba. Rashin ganin Zainab tare da su shi ya daga masa hankali.
Ya san kawaicin matarsa. Ko meye zai faru ba za ta taba nunawa ko a fuska rashin ganin su da Zainab ya sosa ranta ba.
Saboda haka suna shiga masauki, da hanzari yace “Hafsa nemo min wayar yayarku”.
Da sauri ta buga. Ringing daya na biyu ana uku ta dauka. Cike da murna tace “’yar kanwata kina lafiya”?
“lafiya kalua Zainabu. Ba ita ba ce Abban kune”.
Cikin dariya mai nuna ladabi tace “Lah Abba ban san kai bane. Abba barka da war haka”. Ta gaishe shi tare da dan rusunuwa kamar tana gabansa. Wan nan kuma al’adar ta ce. Domin ko shi Al Bashir idan zata gaishe shi a waya sai ta dan rusuna kamar yana kallonta.
Shi ya ci gaba da Magana, yace “zainab ina mutan gidan ku”.
“Abba sun yi tafiya. Sun je kai su Farida makaranta”.
“Tun yaushe ke nan sukayi tafiyar”?
Ta dan daga kanta alamar lissafa wani abu. San nan tace “Abba yau satinsu shida da kwana hudu”.
Kamar zai ce wani abu sai kuma yayi controlling kanshi. Yace “shike nan ba damuwa. Abin da nake so dake ki kiyaye mutuncin kanki ki kuma tuna komai ki ka yi Allah na kallonki. Kar ki yi san ranki don ganin ba idon dan Adam a kanki”.
“In sha Allahu Abba zan kiyaye. A dai ci gaba da samu a addu’a”.
“ba komai Zainab. Me kike so na sayo miki in zamu dawo”.
“Nan take ta tuna ankon bakar after dress da zasu yi naa sauka. Saboda haka da hanzari tace “Abba in so samu ne ina son bakar after dress”.
“Bayan nan fa”?
Ta sake cewa” Abba ita kadai nake so”.
Ba yadda bai yi da ita ba ta fadi wani abun, amma sam taki. Daga bisani ya mika mata ummanta da sauran kannen suka gaisa. Hafasat ce ta fita da wayar domin su dan sha hira da yayarta. Gashi dai dan kwanaki ne da fara mu’amalar ta su amma kai kace sun dade da juna yadda suka shaku. Sukan iya kashe sama da awa daya suna hira a waya.
Sai da ta shiga daki. San nan tace “Yaya Zee ina ya Bala”? nan dai suka dinke da hira. Sai da za suyi sallama ita ma ta bata sakon turare mai dadi saboda lura da tayi Balan ta mai son kamshi ne.
Tsaftar sa da kuma iya gayunsa yasa ya ke dada birgeta. Ba wanda zai kalle shi yace talaka ne a tunaninta. Sai da ma Fatu ta gaya mata ai masu san’ar gwanjo haka suke da gayu saboda suna samun kaya masu kyau kuma da sauki.
Da suka dawo kuwa driver ya dauko su a airport sai da suka fara zuwa wajen Zainab, saboda sanin da suka yi na cewa ita kadai ce a gidan. Tayi murna matuka da ganin mahaifiyarta da kuma sauran ‘yan uwanta da kuma Abbansu Hafsa. Rabonta dasu tun ran da taje Garko wajenta babanta yayi mata dukan kawo wuka. Ba yadda bata yi da su ba su shiga sam suka ki. Anan cikin mota suka gaisa. Akwati guda Abban ya mika mata a matsayin tsaraba. Ita ma Hafsa ta bata wata ledar mai dauke da turarrruka har shida duk kuma designer. Na mata uku na maza uku.
Anan ne kuma ta san ashe Mallam ya san Abbanta. Ya kawo kudi ya bashi,san nan sukayi sallama suka tafi.
Da AlBashir kuwa ya kawo mata ziyara da la’asar ta debo kayan da Abbanta ya sayo mata, wanda ya kasance after dress masu kyau da tsada guda goma da kuma wasu rin dogayen riguna na Morocco masu dan veil a kansu suma kala kala guda goma. Ta dai dauki after dress guda biyu da kuma doguwar riga daya. After din da doguwar rigar ta bawa Fatu. Ta bawa mama Hajjo turare guda daya. Daya kuwa ta bawa Baba laure.
Sauran kayan nan haka ta hada su sai ga AlBashir ya kawo mata ziyara. Nan dai inda suka saba tsayawa da shi bakin verender Mallam nan suka tsaya. Bayan sun gaisa. Ta debo tsarabar nan baki daya ta bashi. Tace “ka sayar da kayan na dauki daya na kuma bawa Fatu daya. Ga kuma turare Hafsa ta kawo maka”.
Ya dauki turaren Giogio for men ya bude shi sai da ya shaki kamshinsa san nan ya bude kwalbar yana fesawa. Wani dadin kamshi ya baibaiye su. Sai da ya lumshe idonsa domin dadin turaren, san nan yace turare dai na dauka, amma banda kayanki. Idan na dauka inyi me dasu. Ki ajiye mana ki dinga yi min kwalliya ina ganinki ina jin dadi. Da ace ina da hali ai da kin ga kayan kwalli…….”
Ita kanta bata san sanda ta kai hannunta ta rufe bakinsa ba alamun bata son maganar da yake yi. “Please na roke ka kar ka kuma yi min makamanciyar maganar nan. In ba haka ba zamu bata. Haka na ganka kuma haka nake son…..”
Sai a lokacin kuma taji kunya ta kamata na abin da tayi da wanda ta fada.
Shi kuwa he kind of froze saboda dadin kalamanta. Ya san tana son sa amma bata taba fitowa ta fada kuru kuru ba sai yau. Akwai dai alamun kauna da kyautatawa da ta ke nuna masa.
Ba shiri ya yi wani dana tsalle tare da juyin 360. Ya bude kwalbar turaren ya ci gaba da fesa musu shi da ita yana fadin “bari kawai yau ayi kamun amarya da ango, tun da yau amarya da kanta ta furta asirin zuciyarta”.
Kunya ce ta kamata ba shiri ta tashi da saurin tana kokarin guduwa. Take ya gano wayon da take son yi. Ba shiri shi ma kuwa ya cafki gefen hijabinta ya rike yana fadin “please kar ki kashe min tsananin farin cikin da nake ji a a yau din nan. Na san ki na kaunata, amma nayi ta mafarki ki furta sai yau kuma na samu amma ki na neman ki guje min. haba Putri salju na”.
Da kyar ya rarrashe ta ta tsaya, amma fa still yana rike da hijabinta. Tace to ka sakar min hijab mana ai na fasa guduwa”.
“tab di jan naki wayon. In saki kigudu ki barni” ya fada da maganar yara, wacce ta sa ta dariya. Haka ta saki jiki suka ci gaba da hirarasu.
Su Momi ba su dawo ba sai bayan kwana hudu da dawowar su Mallam Usman. Saboda daga Saudiyya sai suka nemi long transit VISA suka kwana uku a a Dubai. Na ma dai wasu kudin aka sake murkushewa. Wan da daga nan ne suka yi sallama su yaran suka hau jirgin komawa Sudan har da Khalil da yayi joining dinsu wan nan shekarar. Su kuma suka dawo da Halim da Hanif da kuma Sakina da yaranta guda biyu.
Ba zata suka yi mata saboda Momi ta so kamata da laifi, amma batayi sa’ar yin haka ba. Saboda ita dai yadda ta saba haka taci gaba da kula da gidan. Bai dameta ba da aka zo ana rabon tsaraba ita ba a bata komai ba, saboda ta saba da haka ranta bai baci ba. Ita kuwa yanzu ba abin da ke damunta in dai zata samu damar ganin rabin ranta to kuwa ba abin da zai bata ranta.
Kusan duk abin da Momi ta nunawa Dadi da sunan zainab ta sayawa, ashe karya take ‘yan gidansu ta rabarwa. Ba abin da ta bata. Da suka zauna da Dadi tace masa “waini Zaunab tazo tayi maka godiyar tsarabar da aka kawo mata”?
“Ni bata zo tace min komai”.
“kai ni na rasa bakin halin irin na wan nan yarinya. Yanzu duk abin da aka saya mata amma bata yi appreciating ba saboda kawai ba ayi tafiya da ita ba”. A dan hasale Daddy ya amsa wa Momi da cewar "tafiya ba ita jawo wa kanta ba. Itama da ta yi karatu ai da da ita za a dinga zuwa ko ina. Amma tunda haka ta zaba, sai ta zauna tayi ta sakarcinta. Ai tun da ma ta samu mai sonta, gwara kawai a aurar da ita”.
Yana fadar haka Momi taji faduwar gaba, saboda kuwa ba ta tsammaci jin haka daga gun daddy ba. Idan ta tafi wa zai ci gaba da yi mata bautar da Zainab ke mata. Ai kuwa zata san yadda zata lalata zancen auren nan.
[8/7, 21:39] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👪👪
IN FIKI A MIJI💏💏
PAGE 23
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Tun da mutan gidan nan suka dawo, Zainab bata huta ba. Allah ya taimake ta ko ina na gidan a share yake kal kal da shi. Da farko suna shigowa aka bawa driver kudi yaje ya sayo kayan abinci. Ba ita kuwa ta samu ta gama sorting din su out ba sai bayan isha. Ta sa food stuff a store a cikin robobin da suke arranging kayan abinci.
San nan ta dawo kan perishables ta wanke condiments ta barsu suka tsane san nan ta bi ta duddura su a cikin zip lock, yanda zasuyi saukin dauka idan za ayi amafani da su. Ta saka su a freezer su wacce take daban data nama.
Sannan ta dawo kan nama da su kaza da kifi da dai sauran su irin su kayan ciki da su ganda. Suma haka kowanne ta wanke shi ta barshi ya tsane, san nan shima ta duddura tasa a zip lock din. Suma ta zuba a tasu freezer.
Hatta fruits da vegetables sai da ta gyara. Su kuma kowanne da fridge dinsa. Ta debo ruwa da drinks masu yawa ta zuba a fridge din wajen dinning inda nan ne ya kasance nasu wurin zaman. Sauran kuma tayi arranging din su a kantar store din gidan. Hatta su tuna da su salad cream sai da ta zuba su a pantry cupboard dake kitchen san nan ta dawo dora abincin dare.
Ana tamabayar me za adora Anti Sakina da bata wuce gidan ta ba tukunna tace sakwara. Su Halim sukace wake da shinkafa. Ita Momi tace ferfesun kayan ciki da soyayyen dankalin hausa take sha’awa. Haka ta zage ta bata lokaci wajen sallamar kowa.
Ba dai ita ta samu kwanciya ba sai bayan sha biyu na dare saboda sai da ta jira suka gama san nan ta gyara ko’ina. Ga shi kuma an bata dokar da safe tayi doya da kwai da ferfesun naman kai. Daddy kuma ayi masa kosai. A kuma dama kunun gyada.
Saboda haka tanayin sallar asuba ta dora daga inda ta tsaya jiya.
Misalin tara na safe taji wayar Balanta yana kira, alamar yazo ke nan. Baba Laure ta bawa sako ta kai masa. Doyar data soya ta zuba a foil paper ta kuma hada masa da dahuwar da tayi ta zuba a ‘dan wani karamin flask da ta sayo musamman domin haka, tace ta mika masa zata kirashi a waya.
Tayi hakane gudun abu biyu. Ta san da taje zai shagaltar da ita har su Momi su tashi ba ta kammala abin da ta sa ta ba. Ko kuma a fito a same shi a gidan da safe bata san yadda zasu dauki al’amarin ba.
Mallam mijinta ta bawa ya mika masa sakon. Yana jin abin da ta fada ya kalle shi yace “hala mutan gidan sun dawo”. Shirun Mallam din shi ya dada tabbatar masa da cewa sun dawo. Ya sake cewa Mallam “kar ka damu In sha Allahu komai ya kusa zuwa karshe”. San nan yayi masa sallama ya nufi mashin dinsa da abin Karin da masoyiyarsa ta bashi.
To ita fa tana wan nan kujiba kujiba ne kuma Momi ta kai saranta wajen mahaifinta na kinyi masa godiyar tsarabar da tayi karyar ta bata. Duk suna zaune kuwa a dinning suna karyawa ya kira ta. Ta tsugunna da ga gefe kamar yadda ta saba. Nan kuwa ya rufe ta da fadan da ba ta san dalilinsa ba. Fadi yake yi “ni kin raina ni kin dau bakin cikin ‘yan uwanki da sukaci gaba kin dorawa ranki. Kuma na fada miki in dai ni kina son mu shirya dake karatu na so kiyi kika yi. Saboda haka banga dalilin da dan anyi musu abu saboda kwazon su za ki dinga bakin ciki akai ba”.
Nan dai ya dinga fada. Ya dauki kusan miti ashirin yana tsattsagar Zainab a wajen.ita dai in ban da sharar hawaye ba abin da ta ke yi. Sai da yayi iya yinsa, san nan ya sallameta ta tafi. Sai da ta gama hidimar abincin rana wajen karfe uku ta shiga daki domin ta kimtsa ta tafi islamiyya, san nan taga miss call din Bala guda goma sha hudu, sai a lokacin ta tuna tayi alkawarin kiransa.
Kafin wayar tayi ringing ya dauka. Irin daukan nan in flashing ka so yi sai an ci katinka. Ta yi sallama ya amsa mata muryarsa can kasa alamun rauni. “yaya na ke jin kamar baka da lafiya”?
“Ina zan yi lafiya Putri Salju? Kwata kwata yau ban ganki ba banji muryarki ba”?
“Subahana Lillahi. Me yayi zafi haka? Kai dai kawai ragwanta ke damunka”
“A kan soyayyarki Zainab ni rago ne na karshe ma kuwa. Kina ganin na shigo wajen aiki na kasa komai. Ga Mujib nan ya sakani a gaba sai tsokanata yake yi. Please Zainab kiyi min izni in zo in ganki ko na ji dadi da sanyi a cikin raina”.
“kayi hakuri aiki ne ya dan sha kaina har na sha’afa da kiran ka da nace zan yi. Wayar kuma na sata a caji a daki saboda haka ban ji tana ringing ba. Yanzu kaci abinci”?
“Ina na kasa shan ko ruwa ne tunda banji muryarki ba”?
Ta yi kasa da muryarata alamar rarrashi, san na tace “yi hakuri Ya Balarabe daure ka tashi kaci abinci. Ka samu ko paracetamol ne ka sha. Duk da dai sauran kwana goma bikin saukar mu, amma yau zan ki zuwa makaranta in jira zuwan ka, in har zaka iya zuwa”.
“Invitiation din da kika bani ya sanya naji na wartsake gaba daya. Nan da la’asar zaki ganni”.
“yawwa jarumi na. ai na san kai jajirtaccen mutum ne. Ina ya Mujib din bashi mu gaisa”.
Yana karabar wayar yace “ranki dade yau kin kada ‘yan maza har kasa warwas”.
“ ni kuma ba zan amsa gaisuwar kaba, saboda naga kamar kana sakaci da amanar da na baka. Kana kusa zaka bari har yaya na ya wuni bai ci komai ba”.
Dariya ya yi, san na yce “gaskiya kin so dora min laifi ne kwai. Amma ina ce ko ciwo ne ya kamaka ai akwai liktan kowanne irin ciwo. Shi nasa ciwon ke kadai ce maganinsa”.
Murmushi tayi san na ta ce “Yanzu dai na baka aiki ka tabbatar ya ci abinci sosai ya sha magani. Nan da awa daya da zaku zo in ganshi garas. In ba haka ba, tarar da zan dora maka bankin duniya ma ba zai iya biya maka ba”.
“tuba nake gimbiyar Balarabe. Yanzu za ki ga aiki da cikawa”.
Ya ajiye wayar ya juya wajen sa ya ga yadda ya takarkare yana cin doyar data zuba masa tun safe. Dauke kwanon yayi yana fadin yanzu saboda Allah dama akwai wan nan better dish din in this office kana jina ina ta kirarin yunwa nake ji, amma kayi min shiru”.
Shi ma ya fisgo flask din yana fadin “let go ka jira yanzu zan tura gidan yaya A’I a aiko mana da abinci this is for me alone”.
La’asar kuwa a masallacin layin su Zainab suka yi sallah. Tun da suka hau mashin nan zuwa gidan Mujib yake mitar shi fa ya gaji da hawa mashin, saboda haka yau idan sun je su nemi turo iyaye saboda ayi mai kankat.
Kafin isowarsu ta salla wanka ta feshe jikinta da turaren Tommy hilfigre da kuma splash dinta na Victoria secret garden. Ta sa atamfar ta mai dan kyau daga cikin kayan da Farida ke bata. Ta dakko dogon hijabinta da yayi matching da kayan ta saka.
Tana gama azkar kiran wayarsa na shigowa. Ta kofar baya ta bude ta nufi wajensa a inda suka saba haduwa. Yana ganita ya saki murmushi. Bayan sun gaisa kafin suce wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login