Showing 60001 words to 63000 words out of 63472 words

Chapter 21 - Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel By Hanne Ado Abdullahi.txt

09 Nov 2025

2193

itama ta debo nata bakin cikin. Auren kisan wuta tayi da driver gidan da tayi aure wani Alhaji mai kudi. Karamar rigima ya dankara mata saki uku. Akan tana son komawa ta lallabi driver akan suyi auren sakin wuta. To an yi aure na sati uku amma sama da wata uku yaki saki.
Kuma ga shi da kokari har gida ya kama mata haya ciki da falo da kuma falle guda nasa a nan cikin limawa, ya kuma yi mata iznin tahowa da ‘ya’yanta guda biyar akan zai taya ta rike su. Matsalar sa muni kamar a yankar wukar. Idan ta kalle shi har gabanta faduwa yake.
Ta nemi saki yace bai san zance ba. Ta kai shi kara ta rasa hujjojin da zata bayar na ya sake ta. Kotu kuwa ta bashi aure. To yauma wan nan bakin cikin tazo take zayyanawa Momi.
Ita kam tama rasa yadda zata yi da rayuwarta. Ga Khalifa an neme shin an rasa ga kuma auren ‘yan gata yanda ya kasance. Bilkisu kuwa tayi musu ta ‘yan duniya. Ba ruwanta da kula kowa. Dama ba cikin su daya da momi ba. Ta wurgar da su ta rungumi uwarta da ‘kannenta ‘yan dakinsu.
Ganin bakin ciki da talauci zai daureta ta tattara ta koma Abuja inda ta samu sabon aiki. Nan kuwa Boss dinta ya dinga sakata tana tabargaza da kudin gwamanati.
Haka rayuwa taci gab da Garawa. Zainab ita tasa aka nemo mata Khalifa. Ta sake mai da shi gidan kangarrarun yara. Sai da kuwa ya shekara ya fito ya warke tas kansa ciki da Qur’ani. Nan ta nuna masa son ya koma makaranata. Shi kuma ya nuna yafi kaunar ya tafi Saudiyya ya karanta Islamic studies. Jin wan nan zance Momi ranta ya baci ta fara masifar Zainab ta mallaketa mata da. Ya daina jin maganrta sai ta yarsa. Shi dai bai bi ta kanta ba ya yi tafiyarsa makaranta.
Wan nan karon ma Dadi ya dan yi jinya, su baffa suka zo dubashi. Duk da dai yanzu shi dan gata ne a wajen Zainab. Hatta ruwan da zai sha za ta tabbatar ta ajiye masa. Amma yadda su Baffa suka ga gidan kamar kufai sai ba suji dadi ba. Suka tambayi Momi ya gaya musu ta koma Abuja da zama.
Baffan Nene ne yace “to kai kuma haka zaka ci gaba da zama gida ba mace”?
Shiru yayi bai bashi amsa ba. Shine ya sake cewa idan baza ka ga mun yi maka karanbani ba ai da mun baka mata”.
“Wallahi Baffa ba wani karanbani. Idan zan samu hakan zan gode”.
“ba damuwa kaje ka ganta ku gaisa. Safiya yarinyar kirkice duka duka shekarara ta talatin da biyu bata taba haihuwa ba. Mijin ne Allah ya yi masa rasuwa”.
Da alamun jin kunya yace “Baffa ni ba ma sai na ganta ba. In dai kuna ganin ta dace da ni shi ke nan ayi komai. Momi dai bata da labarin komai saboda ba wanda ya ji zancen auren. Farida ce zata sanr da ita ita kuma ta koma karatu tana Ibadan. Halim da Hanif Zainab ta mai da su wata boarding school inda ake biya musu har karatun ‘Qur’ani mai girma.
Saboda haka week end kawai tazo ta tarar da amarya a gida. Komai kuma ya canza. Dadi ango ya murmure duk furfuran nan ta tafi. Gida ko ina kal kal da shi. Tayi niyyar yin tijara da saukewa amarya Safiyya rashin mutunci, ita ma kuwa ta nuna mata ba kyalle bace. Da shirinta ta zo.
Dadi yaga zata daga masa hankali ya sake ta saki daya. A ranar ta koma Abuja cike da bacin rai. Duk wan nan badakala da akeyi Zainab bata nan ta yi tafiya saboda tana kokarin hattama degree ta na uku a tafsir. Ita kam ai ilmin ta dangin mijinta ba karamin amfana suke da shi ba.
Kaf yaran family a wajenta suke daukar karatu. Babbar islamiyya ta bude sadaka. Tun tana madina Dady ya sanar da ita zancen aurensa. Ta tashi dawowa kuwa ta hadowa ango da amrya lefen na garari. Ta shirya musu dan karamin honey moon inda ta yaudare su da cewar Dadi zai koma check up.
Kafin su dawo kuwa ta sa akayi musu total renovation. Akayi musu sababbin furniture. A wan nan lokacin yaranta uku. Amma’yar shekaru takwas, sai Amir mai shekara biyar sai kuma Maama mai shekara daya. Sai koma babban bebinta da bata hada shi da kowa, watau first born dinta ke nan bala mai gwanjo.
Goggo Safiya kuwa ta kama kowa ta rike a gidan. Su Halim idan sun zo hutu nata ne. Farida kuwa dama I don’t care attitude gareta. Ba ruwanta da harkar kowa. Aikin ta kawai ta sa a gaba.
Albashir zaune a falonsa suna buga game da Amir a Xbox X dinsa Zainab tayi sallama ta shigo. Yana ganin yanayinta yace da yaron “game up. Sai gobe ma karasa”.
Yayi musu sallama ya nufi dakinsu. Yaron na fita ya jawota jikinsa tare da fadin “me ya samu Putre Salju na? na ganta yau kamar akwai abin dake damunta”.
“Farida ce ta bugo min waya tace wai EFCC sun kama Momi”.
Sakinta yayi yaci gaba da buga game din shi kadai.
“Ya Balarabe bakaji me nace maka bane”?
“naji so what. Me kike so inyi miki”?
“Kenan ba taimakon da zaka iya yi min. Shi ke nan na gode zan je in yi iyakar kokarina” ta mike irin ni nayi fushi din nan.
Da sauri ya mike yana riko ya yana fadin “yi hakuri Putri na. idan kikayi min fushi ina zan sa kaina”. Da murmushi ta dawo wajensa ta zauna a gefensa. Shi kuma yace “yanzu gaya min me kike so inyi”?
“wai da ka kirawo yallabai Sa’ad ba shine ogan Abuja ba ko da taiamkon da zai iya yi mana”.
“an gama ranki shi dade”. Waya ya kira ya sanya ta a speaker. Muryar sa’ad taji yana cewa “kaga autan umma angon Zainab baban Amma. Yau ka tuna da ni ne ko zakka ka cire ka tuna da abokinka tsohon dan sanda”?
“Ai ba wata zakka sai dai rigimar Putri da ta tashe ni yanzun nan”.
“a kace amaryar bala mai gwanjo ta murda kambunta”.
“ai ita dama kambunta kullum a murde yake. Gani kuma matsoraci ban iya yi mata musu ba”.
Dariya ya tuntsire yace “yanzu me take so ayi mata mu taimaka mu dafa maka. Kasuwar gwanjo zamu koma, koko wata sana’ar ta samo mana”?
“In bata samo sana’a ba ai ta dauko rigima. Ka tuna matar nan da ta so hana mu auren juna. Ita staff dinka suka kama”.
“subahana Lillahi. Ai kuwa aiki baiyi kyau ba. Suruka guda a hannun surukinta. Bani details din case din.
“ai ba wani details sunan ta Rumaisa a finace take aiki. Sai dai ban san nawa ta sata ba”.
“kai jama’a. yanzu Ya Balarabe don zaka taimaka min sai ka ci min fuska”?
Sa’ad ya jiyo muryarta ta speaker da Albashir ya danna. “Kin ga madam kyale shi. Bani nan da five minutes zan kiraku”.
Minti biyar din ma bata karasa ba ya kira ya ke sanar dasu abin da ya faru. Kudi ne suka fitar ita da ogan ta har miliyan hamsin. Amma unfortunately five million kawai taci a cikin kudin saboda ogan ne ya karbe sauran. Sai dai kuma sa hannunta ne a voucher so ba ta inda zata fita.
Sa’aad ya ci gaba da cewa “idan so samu ne a samu a yi refunding ko da ten ne daga cikin kudin sai a samo guarantor da zai sa hannu a sake ta. In yaso daga baya zan ga yadda za a yi ayi dropping all charges against her”.
“kana maganar 10 mill. Ni ina ga kudin da zan biya”?
Da mamaki ta juya tana kallonsa. Mutumin da don ya ginawa talaka gida ya bashi jari mai kauri ba wani abu bane a wajensa amma yana kukan bashi da as little as 10m.
Tana cikin kuka ta duba balance din account dinta. Kudin ba su kai ba. Saboda bata dade auren Sajida da kuma Faruk kannenta ba. Duk da dai 90% Albashir ne yayi komai. Ga kuma Hafsa da ta itama auren nata ba hustling saboda kanin abokinsa Mujib shi ya aureta, amma dai duk da haka an dan ji jiki. Saboda har gida suka gina masa.
Yinin ranar sam ta kasa sukuni. In ban da kuka ita da Farida ba abin da su ke yi. Ita farida tana da albashi mai dan tsoka, amma kaf hidimar anti Sakina da yaranta a wuyanta suke, saboda haka kafin wata dan abin da aka samu ya kare.
Zainab tayi rokon tayi lallashin amma sam Albashir ya kekasa kasa yace shi ba abin da zai iya yi. Daddy kuwa ko guarantor ma yace ba zaiyi mata ba. Farisa tace ita kuwa she cant waste her money on Momi saboda ita ta jawa kanta.
Albashir ya shiga wajen Umma take tambayarsa yinin yau gaba daya bata ga zainab ba, kuma bata kirata a waya ba. Kwanciyarsa yayi a kan doguwar kujera san nan yace “kyaleta umma rigima take ji shi yasa ma na fito na barmata gidan”.
“haba dan uwana. Don tana ji rigima kuma ina ce ba rarrashinta zaka yi ba. Ita fa mace ba girma take da shagwaba a gaban mijinta ba”.
“umman ba rarrashin take so ba. Wai fa matar gidansu taci kudin gwamnati shine ofis din su Sa’ad suka kamata. Kuma wai ni take so in taimaka in fito da ita”.
Da mamaki Umman ta sake cewa “baka da abin da zaka fito da ita din ne ko kuwa tsiya kawai kake ji”?
Shiru ya kasa baiwa umman amsa. “Anya dan uwana yaushe ka koyi riko haka”.
“Allah Umma don dai baki san irin muguntar da ta dinga yiwa Zainab bane. So tayi kwata kwata rayuwarta ta lalace. Hatta makaranta kin ga sai da tayi mata sanadinta”.
“Kuma da tayi mata sanadin nata sai me ya faru. Yanzu kai ilmin da Zainab take da shi ba daidaikun mata ne suka samu sa’ar yin sa ba. Ina ce ran nan kace min ERC sun nemi ta basu littafin data buga na easy fiqhu akan zasu saka shi a IRK syllabus na makarantu. Kuma duk wan nan daukakar har ace ana bakin ciki bata yi karatu ba. Ashe akwai abin da yafin ilmin addini dadi”.
“umma ni kawai haushin matar nake ji”.
“To ka daina saboda Maryam ta taba tambayarta dalilin da yasa take iya yiwa Momi alkhairi lokacin da ta kai Khalifa karatu Saudiyya. Amsar da ta bata ni kaina naji dadin ta. Tana budar baki tace idan har ta ci gaba da kullatar Momi to tabbas ba ta yi wa Allah godiya da ya hada ta zama da mu ba. Kaga kuwa idan ita tayi wan nan tunani kai ma irinsa nake so kayi. Saboda haka, kaje dan uwana in dai baifi karfinka ba, ka taimaka a fito da ita”.
Suna falonta zaune ita da Farida sun yi jigum jigum, saboda ance idan ba a zo bailing Momi ba tsakanin yau da gobe tabbas jibi kotu za a tura ta. Shigowarsa yana waya inda suka ji yana neman ticket na mutum uku zuwa Abuja, ya sanya suka saki ransu.
Sun sami jirgin karfe daya. Kafin uku suna ofis din Sa’ad. Albashir ne yayi komai, ya kuma tsaya a guarantor, amma fa yana yi yana mitar idan Momi ta gudu aka kama shi, ita ya shafa. Saboda umma da Abba suna da wasu ‘ya’yan ita kuwa shi kadai ne mijinta.
Sa’ad yana dariya yake ce masa “kar ka damu ba inda zata je. Kuma ma ina ga zan yi closing din case din yau din nan. Nan da nan asarar 10m ta hau kan Albashir. Saboda ba shi yayi niyya ba ya sa mata suna asara. Mutumin da riba ke shiga account dinsa bayan kowacce awa daya. Ko sati zai iya hada ribar 10m din.
Inda Allah ya takaita Farida bata tare dasu da ba karamin kunya zata sha ba na mitar da mijinta ke yi. Sa’ad kuwa ya taimaka matuka, saboda a ranar aka gama case din Momi.
Tana fitowa daga inda aka tsareta taga Zainab, har kasa ta durkusa tana yi musu godiya ita da Albashir. Zainab ta dago ta rungunme ta a jikinta tana bata hakuri. Abin mamaki wai yau ita Momi ke shiwa albarka.
An gama case. Sai dai kuma an sauke ta daga aiki. Tare suka juyo zuwa kano washegari. Dadi kuma yayi tsallen arziki yace ba gidansa ba. Ba irin rokon da ba su yi masa ba yace shi kam ba zai maida ita ba.
Akwai wasu kananan gidaje da Albashir kan gina masu dauke da dakuna uku a jere sai falon a karshen dakin farko da kuma kitchen da tsakar gida suna kallon dakunan daura da falon ke nan. Sai kuma daga karshen dakunan akwai dakin waje da toilet dinsa da kuma shago dan madaidaici.
Ko wacce shekara ya kan gina irinsu guda goma ya bayar sadaka. Zainab ta bude daya tasa aka wanke shi. Take ta sayo kayan gida har da su Ac aka gyara gidan sosai. Ba ita ta gama ba sai kusan magariba. A ranar momi ta tare a sabon gidan da Zainab ta bata.
“Eh haka kawai saboda mutum yaga ba a iya fushi da shi sai ya dinga min hawa kawara. To bulukutu maragatan”
Ita dariya ma mitar ta Albashir take bata sai kace Ammace take fada da Amir. Jawo shi tayi jikinta sai da ya samu daidaita natsuwarsa ya fara manta a ina yake san nan tace “kayi hakuri. Ba zan iya ganin Farida cikin tashin hankali in kyale ta ba. Momi kuma ai uwace a wajena”.
Cike da shauki yace “tsokanarki nake yi Putri. Kin san I can do koma meye for you”.
“Alhamdu lillah. Yanzu sauran ka abu daya. Yadda ka sama wa su Hafsa mazan aure nagartattu ka taimaka Ita ma Farida ka samu wani mai hankali cikin jama’arka ka hada ta da shi”.
“kai Putri akwai ki da naci. Kusan shekaru takwas ke nan kullum sai kin yi min maganra in aurar da farida. Yaya ki ke son in yi. In lokacin auren ta yazo ai za ta yi ne”.
To Momi dai daga babbar ma’aikaciya ta dawo zaman shago. Dan provision Farida ta zuba mata take sayarwa tana dan samun na batarwa. Duk da dai Zainab bata barta haka ba. Yadda ta sauke a gidan mahaifin ta haka take saukewa a gidan Momi. Amma yau da gobe sai Allah.
Sai daga baya Farida ta samu auren wani nurse in charge ne a asibitin su . Yana da kirki sai dai matarsa da uwarsa ba bayani. Masifaffu ne na nuna wa sa’a. da sun yi zai barta ta kama gidan ta, amma daga baya matar ta zuge uwar tace mata “inna idan kika barsu suka kama gida su kadai dadi zasuje suna ci mu su bar mu a anan tun da ance babbar likita ce tana da kudi. Ki sa shi ya kawo ta nan ayi komai akan idonmu”.
Haka kuwa akayi. Daki ciki da falo aka bata a gidan sa. Duk tarin da momi tayi na auren ta ya tashi a banza. Momi taso taki auren ita kuwa she is being practical tace “mh mh Momi kyale ni iam not getting any younger. Iam almost thirty”.
Haka ta lallaba tayi auren da take ganin zai zamo mata rufin asiri, sai dai fa abin da kamar wuya. Ba a raba tunuya ba. Haka dole take cefane na mutum goma sha biyar. Inna da kanne mijinta hudu. Mariya da ‘ya’yanta bakwwai. Ga kuma bazawarar kanwarsa da ‘yarta duk a gida daya.
Ba wani cikakken privacy a gidan. Duk wanda yaji ko da sartse ne ita zata kai shi asibiti ta kuma sayo magani. Cefanen gidan ita ce. Shi nasa albashin sai Innar ta karbe ta bawa useless kannensa. Dama shi kadai ne responsible a gidan. Ga ‘yar banzar rashin kunya da suke labta mata. Ga sata. Yanzu haka ta hakura da sayen waya mai tsada ta koma nokia mai torch light. Saboda in dai ta saya yau gobe kuwa zata neme ta ta rasa. Ba kuma ta isa tayi cigiya ba. Saboda ko ganin ta tayi a gidan za ace ai ba ita kadai nasara yayi wa wayar ba.
A haka ta haifi diyarta mai sunan Momi. Lokacin da ta tashi zata saka ta anursery aka ce sam ba za a raba musu makaranta da sauran yayyen ta ba. Saboda tana son Iman ta samu karatu mai kyau, haka ta hakura ta dau responsibility yaran takwas ta hada da tata tara.
She works for like sixteen hours daily just to meet her financial abligations. Ko motar hawa ta kasa saya. Duk ta tsofe kamar ba ita ba. Ranar da Zainab ta haifi ‘yarta ta hudu Khadija, taje mata barka. Haka ta tantsa yaran nan a adaidaita sahu, saboda ta dauko su daga makaranta ke nan, don ta san idan ta koma gida ba zata samu fitowa ba.
Zainab na zaune a falo ta ga yara sai fitowa suke daga adaidaita. Sai da mutum goma suka fito daga cikinsa. Take hankalinta ya tashi na ganin kanwarta ce cikin wan nan situation din. Sai da sukaci abincin dare san nan suka tashi tafiya. Ta fito raka ta driver zai ajiye ta agida, sai kawai ta tuna da sienna LE2004 dake zaune a gidan wai saboda ko da za aiki driver.
Bata san sanda ta shiga daki ta dauko key ba. Har sun gama duruwa cikin motar ta range rover tace wa “Farida sauko ungo wan nan ai dai zata kai ki point A to B. cike da murna ta shiga gida da sabuwar motar da yayarta ta bata.
Washe gari har da maigidan aka fito ana ta murnar samun sabuwar mota. Aka lalauba babu mota babu dalilinta. Ana kakabin an sace sai ga waya daga police station yazo an kama kannesa sun buge wani mutum da mota.
Haka mijin Farida ya nufi police station din. Ashe wai ta window dakinta suka shiga tana wanka suka dauke key din da daddare. Yayi belinsu Farida ta tsaya kan medical treatment din wanda suka buge. Daga ya dawo gida yana musu fada, kishiyar farida Mariya tace tana jin san da Faridan ta zuga shi.
Nan kuwa suka tarar mata. Duk da kokarin da yayi na hansu sai da sukayi mata ligif da jikinta san nan suka kyaleta. Shi ya kaita asibiti yana bata hakuri kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login