Showing 3001 words to 6000 words out of 63472 words
Chapter 2 - Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel By Hanne Ado Abdullahi.txt
ya fita da komai. Tafi son zama star a duk inda ta ratsa.
Amma kyan Khadija ya tsorata ta. Mace kamar ita ta zabi duk wani bangare na jikinta.
Tsayi daidai misali. Kirar jiki abar tinkaho. Kala abar alfahari. Gashi burin 'yanmata. Murya muradin mawaka. Sai kuma uwa uba hali irin na salihan bayi.
Wadan nan qualities din su suka janyo tsanar da Rumaisa tayiwa Khadija. To kuma sai aka dada rashin sa'a. Duk wadan nan martabobi duk da Zainab karama ce, amma sun fara huda a jikinta.
Ai da farko dawowarta gidan , aji daya aka saka su da kannenta. Gashi dai daga local government tazo , amma ba a yi wata guda ba ta zarce kowa a ajin har da kuwa Farida da kuma Farisa. Saboda tsiransu wata goma ne kawai ya saka aka saka su a makaranta tare.
Kwazon ta shine abin da Mummy ta fara attacking ta hanyar tabbatar dabata samu damar zuwa makaranta a kowacce rana ba. Ko hana ta damar yin home work da dai sauransu.
Duk da cin mutuncin da tayi wa Khadija bai ishe taba. Maigidan na shigowa ta tare shi da kukan ta tana rattaba masa wai Khadija tazo ta kare mata zagi da cin mutunci. Akan wai ance tana zaluntar Zainab.
Sai da ta fyace majina san nan cikin muryar kuka tace "yanzu saboda Allah duk yadda nake kokari na akan yarinyar nan amma ba'a gani. Yadda nake tattalata har yafi yadda nake wa su Farida amma duk da haka yarinyar nan da bakinta ta kalle ni a gaban uwarta tace wai ina wahalar da ita. Kuma ni ba wan nan ne yafi bata min rai ba irin gaya mata da tayi wai kana banbanta, ta da sauran yaran gidan nan".
Sai da ta fashe da wani kukan san nan ta sake marairaecewa tana fadin "yaushe aka yi. Me aka yi wa su Farida ba a yi mata ba. Wannan magana ta bata min rai. Amma ai ita Khadijan ta fi kowa data dauki maganar yarinya ba tare da ta binciki
Komai ba".
Tafasa yake ita kuwa tana dada tunzura shi. Habawa ai kuwa da ya tashi a fusace dakin yaran ya nufa. Zainab na kudundune a kasa tana kukan raba ta da mamanta da aka yi,"sai saukar bulala taji. Tayi ihu tayi magiya tayi afi amma bawan Allah nan bai san tana yi ba.
Mummy da mugunta tana karasowa da gudu abu na farko da ta fara yi shine jawo kofar ta rufe ta kuma rike handle din tana fadin "don Allah Abban Farida ka bude kofar nan".
Tabbas ba shi ya kulle kofar ba ita ta rufe amma bacin rai ba zai barshi ya tuna mai ya faru ba.
Sai da yaga Zainab bata motsi san nan ya fice daga dakin yana fadin "don uwarki gobe ki kara. Sai na miki abin da ya fi haka".
[8/6, 23:12] +234 814 948 5104: FINI A UBA👨👧👧 IN FIKI A MIJI💑
PAGE 4
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Khadija ta dade tsaye a bakin gate din gidan su Zainab ba tare da ta san abin da zata yi ba. Shi kansa maigadi shock din abin da matar gidan tayi ya hana shi magana.
Ta daure ta bude jakarta ta daiko wayar ta nokia 3310 ta kira mijinta Mallam Usman tana mai sanar da shi cewar ya gayawa abokinsa da ya kawota ba zata tsaya jiran sa ba zata dawo on her own.
Yayi kokarin tambayarta ko wani abu ya faru amma ta katse shi da fadin yayi hakuri sai ta dawo.
Ya buga ya sanar da abokinsa Malam Buba mai golf abin da Khadijan ta fada.
Take kuwa ya fasa lodi ya fita daga layin lodin da ya hau ya dawo gidan Dr Abdullahi Zubairu.
A halin da ya ga Khadija shi kansa hankalinsa ya tashi. Ta na ganinsa sai a lokacin kuka ya kwace mata.
"Shiga mu tafi maman Hafsa" ya fada yana mai bude mata gidan baya. Shi kansa ya rasa kalmar da zai bata hakuri da ita.
A kundila ya tsaya gidan wani abokinsa. Ta shiga tayi wanka matar gidan ta bata wasu kaya ta sa.
Hankali tashe su ka tarar da Malam Usman yana dakon zuwansu. Sai a lokacin shi kansa Mallam Buba ya san abin da ya faru.
Duk kan su sun yi bakin cikin jin wulakancin da aka yi mata saboda kawai ta kaiwa 'yarta ziyara.
Ya bata hakuri wan nan ta wuce. Ba sai kuma ga tsohon miji sun hadu da sabon miji a gidan su Alhaji Abdullahi.
Duk da aurensa da Khadija ya rabu hakan bai raunana zumunci tsakanin mahaifin Khadija da kuma na Abdullahin ba.
Shine ma waliyyin ta a auren ta na biyu da shi Mallam Usman din.
Kanwar Abdullahin ce ta rasu, Allah ya hada su a zaman makoki. Ya riga yaji famfon matarsa ga shi dama kuma yana kullace da shi kansa Usman din.
A cikin gida suka hadu shi da Usman din ya shiga ciki gai da iyayen su mata.
Bai ko lura ya hankalta da jama'ar dake dankare a tsakar gidan ba ko kuma ya na sane niyyar ci masa mutunci yayi oho.
Mallam Usman na kokarin mika masa hannu domin su yi masabiha yaji kalaman Abdullahi mahaifin Zainab sun dake shi kamar bulala. Yana buda baki sai yace "dawa zan gaisa da kai?ai kai kanka ka san nafi karfin gaisawa da matsiyaci irinka".
Kowa ya san Malam Usman, Usman din ne har a sanyi hali. Ga kuma kunyar gidan surukai dake dawainiya da shi. Domin yadda yake mutunta mahaifin Khadija haka yake yiwa tsohon surukinta.
Saboda haka yana budar baki cikin sanyin murya yace "kaga Dr kayi hakuri koma menene mu tattauna cikin fahimtar juna. Ni da kai ai mun zama daya".
"Dawa ka zama data ? Kaga Mallam dakata ka kalle ni da kyau ai ka san ni ba sa'anka bane."
Ya na fadin haka ya cakumo wuyan rigarsa yana fadin cewa "kuma ka gayawa matarka ta kiyayi mata ta. Ranar da duk ta sake taka min gida sai na sa an wulakanta ta yadda bata tsamm........"
"Sakarwa mijina rigarsa ko kuma infasa maka kai da tabarya".
Yaji ihun muryar Khadija ta nufo su kuma dauke da tabaryar. Duk su biyu basu ankara da cewa hayaniyar su ta fito da Khadija da kuma mahaifiyar Dr da ma sauran mutanen da ke cikin dakin ba.
Ta kuwa nufi shi dauke da tabaryar gadan gadan. Da hanzari mahaifiyarta watau kakar Zainab ta wajen uwa ta karbe tabaryar tana fadin "ke Dije baki da hankali ne".
Yayin da shi ma cikin mamaki yace "Khadija ni ki ke son wulakantawa akan wan nam banzan talakan mijin naki"?
"Ga ka nan banza wanda bai san ciwon kansa ba. Kuma ka zauna ka tace haram din da ke cikin kudin da kake ikirarin kana da shi ka gani ko bayan yin hakan halastacciyyar dukiyarka za ta kai tasa"?
Inna mahaifiyarta ta ce " kar in sake jin bakin ki a nan".
"Amma inna kina jin zagin da yake min bayan wulakanci da matarsa tayi min".
"Ke Khadija wuce ki tafi gida. Kar in sake jin kince wani abu". Mallam Usman yace da ita.
Ta yi tsai na dan lokaci ta kalli mijin nata sai taji ba za ta iya yi masa musu ba. Takaicin ya hana ta gayawa Abdullahi bakaken maganganu da ta tanada sai kawai hawaye ya fara zuba a idonta.
Kallon baban Zainab kawai tayi ta saki wani dogon tsaki. Takaici ya kama shi ya daga hannu da niyyar kai mata mari wani irin riko aka yi wa hannun nasa wanda bai taba jin irin sa ba.
Ya juya ya kalli Mallam usman wanda ya rike masa hannu yana fadin "sake ni in koyawa yarinyan nan hankali".
Shi dai bai bashi amsa ba amma kuma bai saki hannun nasa ba.
Innar Khadijan ce ta sake cewa "baban Hafsa kuzo ku wuce gida kai da Dije ba na son rigima".
"Su wuce ina"? Mahaifiyar shi Abdullahin ta fada watau kakar Zainab ke nan ta wajen uba.
Taci gaba da cewa "ita kuwa Dije ai nan gidan ubanta ne ba kuwa wanda ya isa ya sa ta fice daga cikinsa.
Shi dai da yake jin rashin mutunci ya iya ficewa. Shi kuwa baban Hafsa gidan surukansa yazo. Kuma tunanin haka ya sanya ka kuma ci darajar hakan har ka iya shake masa riga bai nuna maka banbancin karfin tuwon dawa da na samanbita ba.
In bai cin haka har kai ka isa ka taba jarumi irin sa. Ka tambaya a kauyen nan kowa ya san irin jarumtarsa."
Ita dai Innar su Khadija sai faman jan ta take tana bata hakuri yayin da shi kuma ya juya yafice daga cikin gidan cike da takaicin abin da mahaifiyarsa tayi masa. Kuma har sai da ya kai kofar gida bai daina jin zafafan kalaman da ta raka shi da su ba. Fadi take "yarinyace ka gaji ka sakota. Kace ba ka so. Wani kuma ya aura. Ka tsaya kanawa mutanen bakin hali. Ai duk wan nan zafin da ka daukan na san na takaicin rashin Khadijan ne".
Ita kanta Khadija da Mallam Usman sai da suka dawo suna bata hakuri saboda ganin yadda ta dauki zafi.
Ta kalli Malam Usman tace "kaga ai gaisuwa kazo min. Koma kofar gida ka zauna ka ci gaba da amsar gaisuwa idan yayi wani yunkuri ka daka min shi a wajen. Ke kuma shiga ki ci gaba da aikin abincin da kuke yi. Ban kuma yarda ki tafi ba sai sanda kuka saba tafiya idan kunzo".
Innar Khadija tace "don Allah ki yi hakuri ki bar zancen nan haka. Da wanne zamu ji da rasuwa ko kuma da shirmen yara"?
"Shi da ya dago fitinar ai bai tuna kanwarsa ce ta jini ta rasu ba. Tun da shi duk abin da matarsa ta dora shi a kai hawa yake ya zauna daram".
Ai kuwa takaicin abin da aka yi masa shi a Kera tsaf akan Zainab ya sauke shi.
Ita bata da masaniya ma na abin da yafaru. Yana cikin mayarwa da Rumaisa irin wulakanci da Khadija ta jawo aka yi masa ita kuwa ta shigo da saurinta tana fadin "Abba kaga da muka je Kera Abba Mallam ya ban....."
Ba ta kai karshen zancenta ba ya kuwa yi mata dukan da Mercy da Ronaldo sukewa Ball. Yarinyar nan sai da ta dangana da bango ta tsaya. Duk da haka bai hakura ba dukanta ya shiga yi kamar Allah ya aiko shi.
Sai da Mummy ta tabbatar ta daku san nan ta tashi ta rike shi tana ba shi hakuri.
[8/6, 23:12] +234 814 948 5104: FINI A UBA 👨👧IN FIKI A MIJI 💑 PAGE 4
BY HANNE ADO ABDULLAHI
Kwanan Zainab uku tana jinyar dukan da mahaifinta yayi mata. Wanda ba komai ne ya hassala shi yayi mata
dukan kawo wuka irin haka ba, sai kyawun da ya ga Khadija tayi.
Ta yi shar da ita kamar ba matar kauye ba. Shi ko zaman su da ita a kasar waje bai ga tayi wan nan kyan da kuma kuruciyaba.
Tafi masa kama da budurwa 'yar shekara ashirin ba uku zuwa da hudu amma ba wai matar malamin makaranta kuma uwar 'ya'ya biyar ba.
Ya dade kwarai bai hadu da ita ba. A tsammani sa tun da talaka take aure zai ganta yarkace yarkace.
Amma sai ya ganta tsaf da ita.
Ga kuma kalaman mahaifiyarsa da ta dinga fadin "mata ce an bashi yace baya so ya sako ta. Wani kuma ya aura shi ne zai zo yana nuna wa mutanen bakin hali".
Ba karamin tunzura yayi da kalaman mahaifiyar ta sa ba.
Yadda ta kwana uku tana jinyar jiki, haka ya debi wannan lokaci yana jinyar zuciyarsa.
A wan nan ma dare sambatunsa ne ya tayar da momi ta jiyoshi yana fadin "sai na wulakanta Khadija. Ita har ta kai matsayin da zan fadi magana ta mayar min da martani".
Momi ta kamo shi ta zaunar da shi a bakin gadon dakin. San nan ta nufi fridge ta debo masa ruwa a kofi ta bashi ya sha.
Sai da ta ga ya dan natsu san nan ta tambaye shi abin da ke damunsa. Take kuwa ya gaya mata niyyarsa ta daukar fansa akan tshuwar matarsa.
Dariyar jin dadi tayi saboda itama tana da burin ta tsawwalawa wa rayuwar Khadija. Saboda a nata tunanin son da dangin Daddy su Farida suke mata ne ya hana ita din su sota a matsayin ta na matar mai kudin dangin.
Ta ki fahimtar cewar su wadan nan fulani da ta ke gani bamasu zalama bane. Kudin ta dana mijinta ba zai sa su dauki raini da wulakancin ta da kuma na 'ya'yanta ba. Hakan ne ya sa suka ja baya da ita.
Ita ma kuwa tayi niyyar ramawa. Take tayi murmushi tace "kana director a finance. Kira na Education kawai ka sa a sallami mijin nata daga aiki. Ai dai dama karyarta ta sa ce. To datse samun nasa muga tsiya".
Jikinsa har kyarma yake saboda jin dadin wan nan gurguwar shawara da matarsa ta ba shi.
Takwas na safe kuwa a gidan Murtala tayi masa. Ya kuwa nemi abokinsa ya kuma nuna masa abin da yake son ayi kuma yama kara da son abata takardunsa kar ya samu damar neman aiki. Summary dismissal yake son abashi.
To shi ma na education din akwai voucher cuwa cuwa da ya ke son ya tura finance din ayi masa approving kuma shine mai sa hannu.
Take suka yi trade by bater.
Voucher a nan office din aka sa masa hannu ba tare da an sha wahalar kaita ba.
Yayin da shi kuma yakira education secretary na zone din ya bada dokar a sallami mijin Khadija daga aiki.
Kafin sha daya na safe kuwa takardar sallamar ta isa ofishin principal din Garko science. Har kuma da sharrin dalilin korar tasa saboda kama shi da akayi yana soyayya da daliba a makarantar.
Shi dai principal na Garko ya samu bakuncin ES na zone din su da kuma bakar takarda korar karen da aka yi wa Mallam Usman.
Ya tambayi dalili ES yace masa "kafar manya ya taka."
"To kuwa ko zan tozarta kowa banda Mallam Usman. Saboda haka ina mai shawartar ka da ka canza lafazin cikin wasikar ka. Kora kuke so to ku sauke shi ba dalili amma banda kazafi". Principal din ya fada.
ES ya tashi zai masa jan ido shi kuwa ya hado masa gangamin sauran malaman .
Take kuwa 'yar karamar zanga zanga ta fara faruwa a makarantar. Shi kuwa Mallam Usman baima san abin da ke faruwa ba saboda ya fita da wasu dalibai kai ziyara kafin ciri dam.
Ya dawo ya tarar da hatsaniyar da ake a cikin makarantar Inda sauran malamai suka dage in dai aka kori Mallam Usman to suma kuwa sai dai su ajiye aiki.
Shi kuma ES YA DAGE IN DAI principal bai sa hannu a takardar sallamar nan ba to kuwa sai dai duk su rasa aikinsu.
Vice ne ya daure ya fahimtar da Mallam Usman abin da ake ciki. Ba shiri kuwa ya gano fada da tsohon mijin matarsa shi ya haddasa masa rasa aikinsa kuma har yana neman ya zamo sanadin da abokan aikinsa zasu rasa nasu.
Ba tare da doguwar shawara ba ya dau takarda ya rubuta shaidar ajiye aiki ya kuma tilasta principal ya sa hannu.
Principal ya karba amma yayi masa alkawarin taya shi neman wani aikin ya kuma umarce shi da ya kawo takardun matarsa su dauke ta temporary tun da shi yana da hurumin daukar irin wadan nan ma'aikatan.
Da wan nan mummunan labari ya isa wajen matarsa. Ya dai shaida mata cewar yana cikin malaman da gwamnati ta rage.
Amma ya nuna mata ta kawo nata takardun za a taimaka masa ita a samo mata aiki.
Ya kuma samu ta yarda da maganarsa. Har kuma ta yarda zata ba da takardun.
Kwana biyu a tsakani ta kaiwa matar principal ziyara saboda ta yi mata barkar matar kaninta da ta haihu.
Anan ta samu labarin abin da ya faru. Da tsananin bacin rai ta dawo gida.
Nan kuwa ta tarar da mijinta. Ba ta bata lokaci yi masa bayani ba tace da shi "abban hafsa aramin wayarka".
Ba tare da tunanin komai ba ya mika mata wayar. Shi dai yaga tayi kira sai kuma yaji ta sake cewa " yi hakuri zamu gaisa an juma. Yanzu nambar yayanki zaki tura min".
Bai ji me akace daga daya bangaren ba amma yaji ta ci gaba da fadin "zan miki bayani ba wani abu bane".
Daga haka ta kashe wayar.
Shigowar sako da kuma kiran data dora shi ya sanyi shi fahimtar me take yi.
Cikin kakkausaurya yaji tana fadin "sannu shugaban ma'aikatan duniya. Zauna ka dawwama aikin gwamnati. Amma ka sani ko ba retire akwai mutuwa. Kuma kai din nan kayi kadan ka iya kuntatawa rayuwarmu. Aiki an bar maka shi. In har kana ji ka isa ka hana mu shakar numfashi san nan zan san ka cika sunanka Abdullahi dan Zubairu. Amma ka sani ......." wuf taji an fixge wayar daga hannunta.
Ta juya takalli mijinta wanda shi ma alamun bacin rai sun bayyana karara a fuskarsa.
"Ashe baki da kunya ban sani ba. Ashe ko ba komai ba zai ci arzikin da ya kasance yaya a wajenki ko kuma ki duba darajar Zainab ba . Amma kika rufe ido kina gaya masa duk abin da ranki ya ayyana miki. Kin je kawai kin jiyo tsegumi a waje kika hau kai kika zauna."
"Ke nan akwai abin da ya faru ka boye min".
"Ni ban san komai ya faru ba. Aiki ne Allah ya kaddara abincina ya kare a kai sai kuma me".
Shiru tayi ta kasa bashi amsa. Maganganu ne dankare a ranta amma ta kasa gaya masa.
Tarbiya yayi mata ta mutuntuwa bata fadi in fada ba. Saboda haka ta kasa mayar masa da martani ko kuma ta ci gaba da yi masa musu.
Sai kawai hawaye da kezuba a fuskarta na takaicin abin da daddy Zainab yayiwa mijinta.
Ganin tana kuka sai kuma ya sassauta muryarsa ya kamo hannunta.
Cikin muryar rarrashi yace da ita "kin ga Khadija ki yi shiru mu zauna mu tattauna yadda zamu shawo kan lamarin. Kuma kin ga principal yayi min alkawarin zai taimaka miki ke ki samu aikin a makarantar".
Haka ya dinga rarrashinta sai da yaga tayi murmushi kuwa san nan shima ya murmusa yace "haba kin bi kin daga min hankali. Sanadin 'ya'yanki su dawo su tarar da ke cikin yanayi na bacin rai su dauka nine ba su san baban su director ne ya jawo ba".
Ranar kuwa kwana tayi tana