Showing 1 words to 3000 words out of 6095 words

Chapter 1 - Mutum Da Aljan Book 4 Littafin Yaki By Abdulaziz Madakin Gini.txt

"Mutum Da Aljan
Littafi Na Hudu (4)
Part A.

yan suka taho izuwa kan sarki Alkasim suka tsaya suka yi cirko cirko suna kallonsa kawai
.
Al amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan ya dubesu a fusace ya daka musu tsawa yace menene zaku tsaya a kanmu haka kuna kallonmu kawai ba zaku taimaka mana ba mu mike tsaye mu koma can sansani ba !
.
Koda jin wannan batu sai ramjis da hatyan sukayi girgiza suka juye izuwa kamannin jarumi zaihas da jaruma namrita, cikin kaduwa sarki Alkasim ya mike tsaye zumbur jiri na dibarsa sakamakon jinin dake zuba a sassan jikinsa yayi wuf ya zare takobinsa ya fuskancesu yana mai gyara tsayuwarsa kawai sai yaga namrita ta kyalkyale da dariya
.
Lokaci guda kuma saita turbune fuskarta ta dubeshi a fusace tace ya za ayi mu yakeka kana cikin wannan mugun hali
ba zamu dauki fansa ba a kanka sai kana cikin koshin lafiyarka gami da jin izzarka
.
Ka sani cewa bamu shiga wannan gasa ba domin mu samu damar da zamu hallaka ka ba sai domin mu nuna maka cewa dan hakin da ka raina shike tsone maka idanu ka sani komai karfinka komai mulkinka zaka iya faduwa kasa a ko yaushe saboda ita wannan duniyar fadi gareta kuma abin cikinta yawa gareshi
.
Babuwanda yasan iyakarsa ka tsaya kayi tunani wannan fa dabbace kawai ta galabaitar da kai haka in ba don mun kawo maka dauki ba da sai dai kuyi ragas kai da ita
ka tuna fa cewa ko birnin sarki masarul anjana bamu isa ba inda za a tara gaba dayan jarumai da matsafan duniya
.
Kanka ka sani kawai amma baka san sauran mutanen duniya ba babu mamaki akwai wadanda suka fika da yawa amma kace idan muka sake kawo maka hari zaka kashemu to mu ma mun dauki alkawarin cewa ba zamu sake kawo maka hari ba har sai mun isa can birnin sarki masarul anjana ina mai tabbatar maka da cewa har abada ba zamu taba durkushewa ba a gabanka mu nemi gafararka ba face mun cika burinmu na kashe ka ka kashe mana mahaifinmu kuma mahaifiyarmu ta mutu a sanadiyyar ciwon zuciyar da ka dasa mata na ganin gawar mijinta
.
Ta yaya kake tsammanin zamu iya yafe maka har abada babu yafiya a tsakaninmu dakai
ga wannan dabbar sai ka dauka ka koma da ita can sansanin a matsayin kai
ne ka lashe wannan gasa sai ranar da zamu cika burinmu akanka sannan zamu
sake haduwa koda gama fadin hakan sai jaruma namrita da dan uwanta jarumi zaihas
suka bace bat daga wajen tamkar basu taba wanzuwa ba
a wannan lokaci zuciyar sarki alkasim ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin bakin ciki don haka
bai san sa adda ya takarkare ba ya kurma uban ihu mai tsananin firgitarwa wanda
yasa gaba dayan halittun dake cikin dajin darul samjul suka firgice suka dimauce
babu shiri tsuntsaye suka kama tashi suna sauya sheka dabbobi kuwa da sauran
kananan kwari suka rinka shigewa cikin ramukansu suna buya
kai hatta halittun dake karkashin ruwa lambo sukayi suka ki tasowa izuwa saman ruwa
ashe duk wannan abu dake faruwa tun a farkon fara gumurzun da wannan katuwar dabba sai dabbar ta make sarkin yaki ya fadi kasa
kansa ya gwaru da wani dutse
take kan nasa ya dare jini yayi ta tsartuwa ya baje a kasa sumamme a wannan lokacine da sarki ya kurma uban ihu
sarkin yaki ya farfado daga dogon suman da yayi a firgice ya mike zaune ya dubi gabas da yamma kudu da arewa sannan
ya lura da sarki wanda ke tsaye a gabansa ruke da takobi jikinsa na kyarma ga jini na
yoyo a sassan jikinsa kuma ga gawar wannan dabba a gefe guda, shi kuma
yarima yana kwance a kas a gabansa ya kasa tashi , kawai sai yaji sarki ya daka masa tsawa yace maza ka dauki
yarima ka goyashi a bayanka ka ruga dashi izuwa can sansaninmu domin likitoci su dubaku
cikin hanzari sarkin yaki ya suri yarima ya goyashi a bayansa har ya juya zai tafi sai ya dubi
sarki yace ya shugabana tunda dao ka samu
nasarar kashe wannan dabba ai saika daukota mu tafi tare domin jama a su tabbatar da cewa kaine ka lashe wannan gasa
Al amin Ahmed Misau
guyson sunana kenan
daga page na 'zauran labarai'
sarki Alkasim ya gyada kai yace bani ne na kashe wannan dabba ba makiyanane suka kasheta zaihas da yar uwarsa namrita kuma sun juye
kamannin ramjis da hatyanne suka shigo wannan gasa maza kayi sauri ka kai yarima tantinsa zan jira isowarku a can
koda jin haka sai mamaki ya kama sarkin yaki amma sai yayi shiru bai kara cewa uffan ba ya runtuma da gudu izuwa hanyar da zata kaishi sansanin goye da yarima kamsus a bayansa
nan dai yayi ta gudu ba tsayawa kuma babu waiwaye yana isowa sansanin ya hango sarki zaune a kofar tantinsa bisa kujera likitansa na dinke raunukan jikinsa'
hm kunji aikin tsafi fa wai Guyson nake magana
a guje wadansu dakaru hudu suka taryi sarkin yaki suka karbi yarima suka shigar dashi cikin tantinsa suka kwantar dashi
nan da nan shima nasa likitan ya dukufa a kansa aka shafa masa wani irin magani
na musamman a gadon bayan nasa sauran jaruman gasa dai
Tuntuni daya bayan daya suka rinka dawowa sansanin tun sa adda suka sare
sakamakon azababben gudun tseren da akayi na kece raini ramjis da hatyan ne kadai ba a ga dawowarsu ba abinda ya kara daurewa
jama a kai shine sarki ya dawo dauke da raunuka a jikinsa kuma babu wata dabba a hannunsa shi kuma
yarima an kawoshi a matukar galabaice to wai shin menene yake faruwa ne haka amsar da aka rasa wanda
zai iya bayar da ita kenan
shi dai sarki alkasim tunda ya dawo daga dajin darul samjul baice uffan ba kuma baiyi magana da kowa ba har aka gama dinke raunukan jikinsa aka shafa masa magani
kawai sai akaga ya shige cikin tantinsa yaje ya kwanta gaba dayan
hadiman ma korarsu yayi daga cikin tantinsa kuma yaki ci da shan komai saboda bakin ciki abu na farko
da ya fara tunowa shine maganganun da jaruma namrita ta gaya masa na batun ya kashe mahaifinsu kuma
mahaifiyarsu ta mutu a sanadiyyar bakin cikin mutuwar mijinta abu na biyu kuma shine batun cewa ya daina tunanin cewa yafi kowa karfi
isa da iko domin za a iya samun wadanda suka fishi a cikin wannan duniya mai fadi
idan kuwa hakane ashe ya dade a cikin jahilci irin na iyayensa da kakanninsa wadanda suka tabbatar masa da cewa zai iya ja da kowa a wannan duniya walau mutum ko Aljan
idan maganarsu gaskiyace to ya ya akayi dabbba ma ta gagareshi har ya zamana cewa ta yi kusan hallakashi yanzu a haka ne zai iya zuwa ya tari sarki masarul anjana sarkin da dukkan aljanu da mutanen duniya ke tsoronsa da shakkarsa
koda sarki alkasim yazo nan a zancensa sai wata zuciyar kuma ta ce dashi kai ai ka da mage ba yanka bane yau shekararka talatin da uku
kenan akan mulki ba a taba samun bacin rana ba irin ta yau kuma yau din ma ai ba a kaika kas ba inda ma zaka je kasan saidai ayi ragas
duk maganganun wannan yarinya namrita zancen banza ne idan ka kuskura ka sasu a ranka har sukayi tasiri a cikin zuciyarka
shi kenan ka samu raunin da darajarka zata zube a idon duniya kada ka manta cewa
duk inda kake kuma a duk halin da kake ciki kana tare da rahamar ruhin iyayenka da kakanninka don haka ba zasu taba barinka kaji kunya ba
yayinda sarki alkasim yazo nan a zancensa sai zuciyarsa tayi fari dukkan wata fargaba ta yaye
daga cikin ransa bai san sa adda ya kwalawa wata kuyangarsa kira ba tashigo cikin tantin da sauri
kawai saiya dubeta yace maza kije ki shirya min giya kuma a shirya min makada da masu rawa . Nishadi nake bukata , hm kunji karfin hali' guyson sunana' kuyangar ta risina tana murmushi tace an gama ya shugabana
lokacinda jama ar wannan sansani sukaga an kama yiwa sarki kida da raye raye yana ta nishadi gami da shan giya sai kowa ya cika da mamaki har ni kaina Al amin Guyson kuwa ba komai ne ya baiwa jama a mamaki ba face ganin cewar
ai yanzu lokaci ne na bakin ciki bana farin ciki ba tunda an dawo daga gasar farauta babu nasara
yarima ma an dawo dashi ba lafiya shi kansa sarki ya dawo dauke da raunuka masu yawa amma kamar babu abinda ya dameshi sai sharholiya yakeyi
yarima kamsusu dai bai dawo cikin hayyacinsa ba kuma baiji kwarin jikinsa ba sai da dare ya raba a wannan lokacine
ya farka daga dogon barcin da yayi sakamakon maganin da likita ya bashi yasha
zumbur ya mike zaune akan shimfidarsa cikin kuzari tamkar wani abu bai sameshi ba bisa mamaki sai yaji ko kadan bayan nasa ya daina zugi da radadi tamkar an zare masa ciwon da yake ji tun daga
lokacin da wannan katuwar bakuwar dabba tayi masa mugun duka abu na farko daya fara fado masa a rai shine abubuwan da suka faru a can dajin darul samjul duk da cewa ya tsinci kansa a cikin wani
irin mugun hali mai kama da wani irin mugun hali mai kama da jirkitar hankali ko rabin suma sai yaji yana iya tunowa da duk abubuwan da suka fara tun daga lokacin da suka fara yin bakin artabu da wannan muguwar dabba kawo izuwa lokacin da namrita da dan uwanta suka ceci rayuwar sarki suka murdewa dabbar wuyanta
ta fadi kasa matacciya da kuma lokacin dasu namrita suka rikida izuwa ainihin kamanninsu
nan take yarima kamsus ya kamu da tsananin mamakin yadda wadannan al amura suka kasance haka
a dai dai wannan lokaci ne kuma yaji ya kara kamuwa da tsananin son jaruma namrita fiye da ko yaushe ma tunda gashi sun ceci
rayuwar mahaifinsa ita da dan uwanta duk da cewa suna son ganin bayansa
daga can kuma sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi tsoro ya baibayeshi ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin yadda dabba ta kusan hallakasu a yaki to wai shin kuma
idan suka isa birnin sarki masarul anjana inda za a tara gaba dayan jaruman duniya ya matsayinsu zai kasance ? Koda yazo nan a tunaninsa sai fuskar namrita ta fado masa a rai lokacin da tayi masa wani duba tana murmushi nan take yarima kamsus yaji dukkan fargaba ta kau daga cikin zuciyarsa kuma
yaji babu abinda yake so a duniya a wannan lokaci sama da ganin jaruma namrita
kawai sai yarima kamsus ya mike tsaye daga kan shimfidarsa ya fito daga cikin tantin ya kama kai kawo a cikin sansanin inda ya iske dakarun tsaro akan aikinsu
sauran jama ar sansanin kuwa duk suna cikin tantunansu a kwance suna ta
Ta faman shara barci abinsu kai tsaye yarima kamsus ya nufi tantin sarki tun kafin ya karasa bakin tantin
da tazarar taku biyar ya jiyo munsharin sarki koda ya gane cewa sarki barci yake yi sai ya juya ya nufi kofar fita daga sansanin
da isarsa kofar sai dakarun dake gadin kofar suka dubeshi cikin alamun firgici shugaban dakarun yace ya shugabana ina kuma zakaje a cikin wannan tsohondare kayi sani cewa akwai hadarin gaske ka fita daga cikin sansanin nan kuma sarki ya kafa dokar cewa in dai dare yayi to babu wanda zai fita daga cikin wannan sansani
kafin shugaban dakarun ya gama rufe bakinsa tuni yarima kamsus ya zaro takobinsa daga cikin kufe kawai saiya dubi badakaren a fusace cikin harara yace na rantse da darajar sarki duk wanda yace zai hanani fita yanzu daga cikinku saina sare masa kai ''..........
.
Topha nima jin wannan zance na sare kai yasa
na dan dakata a nan sbd nakasance jarumi
bana son fada ehem
,
Mutum Da Aljan
Littafi Na Hudu (4)
Part B.
.
Author' madakin Gini
typing by' Al amin Ahmed Misau
Guyson sunana kenan

.
Ku bani aron lokacinku....
Marubucin littafin yaci gaba da cewa....
-
koda jin wannan batu sai gaba dayan dakarun suka tarwatse suka baiwa yarima hanya ya bude kofar ya fita yana fita sai suka janyo kofar suka sake rufeta
ba tare da tsoron komai ba sai yarima kamsus ya nausa cikin daji yana tafe abinsa yana kallon bishiyoyi da ganyayensu yana jin nishadi tamkar ba a cikin daji yake ba
kuma ba dare bane sa ar da yayi ma shine babu duhu a dajin sakamakon hasken farin wata amma kuma tsananin shirum dake dajin ya isa ya firgita mutum komai jarumtakarsa
tsulum ba zato ba tsammani sai yarima kamsus ya hango jaruma namrita ta nufoshi tana sanye da wata doguwar shudiyar riga fuskarta cike da annuri da farko sai yarima kamsus ya mari kansa domin a zatonsa mafarki yakeyi abinda idonsa suke nuna masa ba zahiri bane'
bisa mamaki sai yaga har yanzu yana iya ganin namrita tana ci gaba da durfafarshi hakane ya tabbatar masa da cewa lallai ba mafarki yake yi ba don haka shima sai ya kara sauri ya tunkareta a wannan lokaci kowannansu mamakine ya kamashi da yaga dan uwansa saboda abin ya zo dai dai tamkar hadin baki.
Ashe kamar yadda yarima kamsus ya tsinci kansa a cikin tunani da begegn namrita haka itama ta tsinci kanta kuma taji ta kasa yin barci kuma babu abinda zuciyar tata ke so sama da ganin fuskar yarima kamsus
hm Lallaifa wannan shine so gamon jini Al amin guyson sunana daga zauran labarai.
A lokacin data tsinci kanta a cikin wannan hali dan uwanta jarumi zaihas na ta faman shara barci abinsa baima san halin da take ciki ba kawai sai namrita ta mike tsaye ta kama tafiya ta nufi sansaninsu sarki Alkasim tana mai ayyanawa a ranta cewa komai rintsi sai taga yarima kamsus a wannan dare
koda namrita ta hango yarima kamsus a cikin daji saita kamu da tsananin farin ciki saboda tasan cewa ba zata sha wata wahala ba wajen ganinsa
cikin hanzari suka karaso suka riski juna suka tsaya daf da daf yadda suna iya jin numfashin junansu kuma kowannansu na murmushi
kawai sai yarima kamsus ya dubeta yace mene ne dalilin da yasa kika fito a cikin wannan daren alhalin bamu dade da rabuwa ba acan dajin darul samjul?
Sa adda namrita taji wannan tambayar sai ta yi yar karamar dariya sannan ta dubeshi cikin nutsuwa tace ta yaya zan iya zama banzo naga halin da kake ciki ba tunda na barka a cikin mugun yanayi bisa dukan da wannan dabbar tayi maka a gadon bayanka ka sani cewa dan halak ne yake maida martanin halacci ga wanda yayi masa
guyson ke magana
har abada bazan taba mancewa da halaccin da kayi min ba na ceton rayuwata dakayi daga hannun mahaifinka yau zan sanar dakai wani babban sirri wanda baka san dashi ba
yakai wannan tauraro abin haskakawa kayi sani cewa tun muna kanana sa adda ka nuna tausayinka a garemu bisa kisan da mahaifinka ya yiwa mahaifinmu naji ka shiga raina.
Tun daga wannan lokaci a kullum rana ba zata fito ta fadi ba ba tare dana tuna kyakkyawar fuskarka ba wacce a lokacin da take zubar da hawayen tausayi ba.
Ka gaya min iyakar gaskiyarka kada ka boye min komai shin abinda nake ji a kanka a cikin zuciyata kaima kana jin irinsa??
Koda jin wannan tambaya sai yarima kamsus yaji wani irin farin ciki ya baibayeshi irin wanda bai taba jin kamar saba nan take yaji kamar ya kamo namrita ya rungumeta akan kirjinsa amma saiya dake
ya dubeta cikin murmushi
sannan mai taushi yace yake sarauniyar matan duniya kiyi sani cewa ni dake zanice ta tarar da mujemu, ina mai tabbatar miki da cewar duk abinda kikeji a cikin zuciyarki dangane dani bai kai rabin wanda nakeji ba a kanki saboda jina da ganina sun zama naki ne
dukkan bugun zuciyata yana ambaton sunanki ko a kwance ko a zaune a tsaye ko a tafe ke nake tunani dare da rana amma duk sa adda na tuno da gabar dake tsakaninku da mahaifina sai naji zuciyata na daka
kafin yarima kamsus ya gama fadin abindake bakinsa tuni jaruma namrita tasa tafin hannunta a karon farko tun haduwarsu ta toshe masa baki kawai saita dubeshi a lokacin da hawaye ya zubo mata tace daga yau kada ka sake yadda gabata da mahaifinka ta shafi soyayyarmu.
Hm wannan itace bakar soyayyah ko nace makauniya Guyson sunana muje zuwa kawai.
Ka sani cewa koda zaka kasheni bayan na samu nasarar kashe mahaifinka ruhina zai bar gangar jikina yana begenka da ambatonka ni yau na cire sartsen da ya makale a cikin makoshin zuciyata tun da nasan matsayina a wajanka
shawarara da zan baka itace kayi duk iya kokarinka wajan kare mahaifinka daga sharrinmu ni da dan uwana domin ba zaka taba sanin dadin mahaifi ba sai a ranar daka rasashi
da wannan kalami nake yi maka sallama sai mun hadu a cikin birnin sarki masarul Anjana amma ina son kayi min alkawarin guda daya idan har soyayyarka a gareni gaskiyace
koda jin wannan batu sai yarima kamsus ya dubi namrita cikin tsananin mamaki yace ke kuwa wane irin alkawari ne haka kike so nayi miki ?
Guyson nake magana

Namrita tayi ajiyar zuciya tace kayi min alkawari cewar ba zaka hada soyayyata da ta wata 'ya mace ba walau MUTUM KO ALJAN'' Koda jin wannan tambaya sai yarima kamsus yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske kuma ya rasa dalilin faruwar hakan saida ya shafe kimanin dakika biyar baice komai ba sannan ya dago kai yadubi namrita cikin murmushi yace
na yi miki alkawari kece kadai zaki mallakeni a matsayin abokiyar rayuwata hm wai tarar Aradu ba gammo kenan yaji dadin zance fa guyson nake magana
ki sani akan ki na fara yin soyayya don haka taya ya wata zata iya zuwa daga baya ta karbo miki abinda kika rigada mallaka?
Yayinda namrita taji wannan batu sai farin ciki ya kamata ta sake yiwa kamsus sallama sannan ta bace bat tamkar bata taba wanzuwa ba a wajen
--
gari na wayewa sai yarima kamsus ya farka daga barcin da yake yi mai nauyi yana bude idansa ya yi arba da mahaifinsa sarki Alkasim a zaune gefensa ya kura masa idanu yana yi masa murmushi
yarima ya mike zaune zumbur ya dubeshi cikin kaduwa yace ya kai abbana yaushe ka shigo cikin tantin nawa ban sani ba?
Koda jin wannan tambaya sai sarki alkasim ya bushe da dariya sannan yace
ya za ayi kasan lokacin dana shigo alhalin jiya ka bata dare a wajen kulla soyayyarka.
Koda jin haka sai mamaki gami da tsoro suka kama yarima zuciyarsa ta buga

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login