Showing 3001 words to 6000 words out of 6095 words

Chapter 2 - Mutum Da Aljan Book 4 Littafin Yaki By Abdulaziz Madakin Gini.txt

shi kuwa sarki sai yaci gaba da kalllonsa yana murmushi kawai yace
bazan taba hanaka yin soyayya ba tunda ka riga ka kamuda son namrita amma ka sani cewa babu abinda yake janyowa jarumi rashin nasara a rayuwarsa face soyayya kaje ka nemi tarihin manyan mazajen duniya wadanda sukayi shuhurar da har yanzu ba a sami kamarsu ba
irinsu HANTARU NA BIRNIN MISRA MAI TAKOBIN SAIFUL LUJARA soyayyace ta kai su izuwa ga hallaka dakuma SADAUKI SHADDADU DA HULKAS NA BIRNIN KUFAAA...
duk sun mutune ta sanadiyar soyayyah na sani cewa duk abinda ya faru jiya a tsakanina da wannan muguwar dabba a lokacin damuka je gasar farauta a dajin darul samjul da kuma su namrita duk ka gani duk da cewa baka cikin hayyacinka sosai.
To ka da zuciyarka ta karaya akan karfina da daukakata saboda ita wannan muguwar dabba data gagareni ba dabba bace aljanine kuma ya kasance daya daga cikin manyan zakwakuran jaruman sarki masarul Anjana kawai an turo shine domin a jarraba iyakar karfina
.
Aljanin yayi amfani da karfin sihirinsa ni kuma karfin damtsena kawai nayi amfani dashi saboda a dokar wannan gasa tamu ba aikin sihiri ko tsafi
su kansu su namrita sun samu nasarar kashe aljanin ne da karfin sihiri ba wai da karfin damtesnsu ba na tabbata cewa yanzu shi kansa sarki masarul anjana ya tsorata da lamarina tunda ya gani da idanunsa yadda babban jaruminsa ya kasa hallakani da iya tsagwaron karfin damtsensa
duk wannan lamari na gano shine bayan nayi bincike mai zurfi a cikin mudubin tsafina
lokacin da sarki alkasim yazo nan a zancensa sai yarima kamsus ya kamu da matukar farin ciki don haka sai ya rungume sarki alkasim yana mai cewa ina alfahari dakai ya kai abbana
hakika nasan cewa ruwa baya tsami banza domin nayi matukar mamakin yadda akayi dabba ta gagareka sarki alkasim ya janye jikinsa daga cikin na yarima yana murmushi yace ai na gaya maka tuntuni ko mutum ko aljan a cikin wannan duniya bana shakkarsa
bare wata dabba in dai a fagen yakine ko gumurzu ba za a iya kaini kas ba sai dai da yaudara
da ma sukayi amfani da ita da suka ga na ajiye sihirin tsafina a gefe daya amma daga yau bazan sake yin irin wannan kuskuren ba har yarima ya budi baki zaice wani abu sai ga kuyangi su biyu dauke da farantin abincinsa na kalaci
Al amin Ahmed Misau Guyson Sunana kenan
daga zauran labarai page nake magana
bisa mamaki sai yaga yau abincin mai yawa ne ba yadda aka saba kawo masa ba koda kuyangin suka ajiye farantin abincin biyu a gabansu yarima sai suka juya suka fice daga cikintantin fitarsu keda wuya sarki ya dubeshi yace tashi da sauri kaje ka wanke bakinka muyi kalaci domin yanzun nan zamuyi shirin ci gaba da tafiya
da jin haka sai yarima ya tashi da sauri ya bude akwatinsa ya dauki asuwakinsa kuma ya dauki battar ruwa ya fice
da fitowarsa wajan tantin sai yaga ashe kowa ya dade da tashima an gama kimtsawa shine kadai ya makara ai kuwa sai yayi sauri ya goge bakinsa ya kuskure da tafin hannayansa ya koma cikin tantin da sauri ya zauna suka kama cin abincin shi da sarki
rabon da yarima yaci abinci da sarki anfi shekara guda don haka sai ya kamu da mamaki dalilin da yasa sarki yazo har tantinsa domin suci abinci tare nan dai suka ci gaba da cin abincin cikin nishadi da nutsuwa.
Tsawon yan dakiku dayansu baice uffanba sannan yarima yayi gyaran murya yace
yakai abbana menene dalilin da yasa yau kayi sha awar cin abinci tare dani koda jin wannan tambaya sai sarki alkasim ya tsame hannayansa daga cikin abincin yayi shiru kansa na sunkuye kamar ba zaice komai ba daga can kuma sai ya dago kai ya dubi yarima a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla sannan yace kafin mahaifiyarka ta rasu ta bar min wasiyya akanka guda uku wasiyya ta farko itace kada na kuskura na hanaka duk abin
Da kake so a cikin wannan duniya bisa wannan daliline na kasa hanaka yin soyayya da abokiyar gabata namrita
guyson nake magana
wasiyyata ta biyu itace lallai na baka horo na tarbiyya mai kyau domin kasan gaskiya da karya bisa wannan daliline nake yi maka horo idan ka aikata laifi ko da kuwa ni ka yiwa laifin ba wani ba
wasiyyata ta karshe itace naja ka a jikina na nuna maka soyayya irin ta da da mahaifi bisa wannan daliline nake cin abinci tare dakai a cikin kwana guda
ka sani cewa akan mahaifiyarka na fara yin soyayyah kuma a kanta na kulle soyayya
daga ranar da mutuwa ta rabamu kawo i yanzu ban sake sha awar naso wata ya mace ba bare na sake yin aure
ba komaine ya janyo hakan ba face nayi imani a cikin zuciyata cewar idan mutum ya rasa masoyiya ta farko ba zai taba samun kamarta ba
mahaifiyarka ta fara kaunata tun bata san cewa ni dan sarkine ba a daji na hadu da ita kuma da kiyayya muka fara muka zamo abokan gaba wannan al amari ya farune kimanin shekaru talatin da biyu da suka shude.---
----
YAMMACI NE MAI KYAN YANAYI DOMIN DAJIN YA KASANCE A CIKIN WATA IRIN NI'IMA
ta wata irin iska mai dadin bugawa wacce bata haddasa sanyi ba kuma ta kore zafi
bishiyoyi da koramai sai rangaji suke yi abin gwanin ban sha awa
a dai dai wannan lokaci ne jarumi alkasim ya shigo cikin dajin rataye da kwari da baka a gadon bayansa a kuibin cinyarsa ta hagu kuwa wata sharbebiyar addarsa ce a daure ko riga babu a jikinsa sai gajeran wando iya guiwar kafafu wanda akayi shi da fatar damisa kyakkyawar surar jikinsa ta sadaukai duk ta bayyana a fili karara.
Tun safe jarumi alkasim ya shiga cikin wannan daji da niyyar yin farauta amma baiga wata babbar dabba ba ko guda daya face kanana irinsu zomo da sauransu a tunanin yarima Alkasim a matsayinsa na babban jarumi kuma dan sarki guda daya jal tilo abin kunyane a gareshi ya shigo daji farauta ya koma gari a ganshi da karamar dabba.
Bisa wannan daliline ya ci gaba da kutsawa ta cikin wannan daji har yamma ta riskeshi yana ta sanda gami da dube dube
kwatsam ba zato ! Ba tsammani sai ya jiyo wani irin gurnani gami da sauti wanda ke nuna alamun cewa ana fafata gumurzu acan cikin wata sarkakiya mai duhuwa
dake can gabansa nesa kadan
nan take farin ciki ya kamashi ya ayyana a ransa cewa lallai wadansu manyan dabbobin dajin ne guda biyu suke yin gumurzu a tsakaninsu don haka ya samu damar da zai jefi tsuntsaye biyu da hoge guda
kai tsaye alkasim ya ci gaba da durfafar wannan duhuwa yana mai ci gaba da yin sanda
koda ya isa daf da wajen yaga abin dake faruwa sai ya kamu da tsananin al ajabi ba wani abu bane ya gani ba face wata zukekiyar santaleliyar kyakkyawar jarumar mace tana kokwawa da wani murtukeken zaki.....
.
Wow ni kaina guyson da nake typing ganin wannan kyakkyawar yarinya yasa na kasa ci gaba da typing
kuma nake cewa mu tara a gobe idan Allah ya kaimu zaku jini da ci gaban wannan labari
.
Al Amin Misau ke magana
Mutum Da Aljan
Littafi Na Hudu (4)
Part C.

.
Author- Abdul madakin gini
AA Misau ke Magana
.
Labarin ya isowa Guyson cewa..
Lokacin da zukekiyar jarumar macen nan mai kyawun gaske ta ci gaba da gumurzu da wannan zakin sai ya zamana cewa idan zakin ya danne ta yana kokarin turmusheta ya kafa mata hakoransa sai ta juye dashi itama ta turmusheshi tana kokarin shake masa wuya
duk da cewa zakin na karta faratan hannayansa a sassan jikinta amma ko kwarzane ya kasa yi mata saboda karfin sihirin tsafinta.
Tun da sarki Alkasim yake yawo a duniya bai taba ganin mace mai karfin damtse kamar wannan ba don haka bai san sa adda yaci gaba da kallon taba kawai yana ganin ikon Allah
sai da wannan jaruma da murgujejen zakin suka shafe kusan rabin sa a suna bakin artabu amma dayansu ya kasa samun nasarar hallaka daya ga dukkan alamu dai karfi yazo daya
har jarumar ta yunkura ta zaro wata sharbebiyar wuka ta daga sama zata kirbawa zakin a makoshinsa sai kawai taga kibiya ta taho da gudu ta soke zakin a goshinsa ta faso keyansa
maimakon zakin ya fadi kasa sai ya juya yayi arba da wanda ya harbo kibiyar ba wani bane ba face ALKASIM kawai sai zakin ya daaka tsalle saama izuwa kan Alkasim da nufin ya raromeshi su yi mutuwar kasko amma kafin zakin ya fada kansa tuni ya sake dana kibiya a cikin bakarsa ya sakar masa wani harbin
ai kuwa sai kibiyar ta huda idon hagu na zakin ta sake bullowa a bayan kansa take zakin yayi sama yana ruri da kururuwa sannan ya fado kasa tim yana shure-shure.
Ba a jima ba sai zakin ya zama gawa a sannan ne aka fara kallon kallo tsakanin sarki Alkasim da wannan bakuwar jaruma wacce bai santa ba kuma bai san daga inda tazo ba.
Fuskarta a murtuke take sai daka masa harara take tamkar tana tsaye a gaban babban makiyinta na duniya kai kace ubanta ya kashe ba zaki ba
yayin da alkasim yaga wannan tsaleliyar budurwa tana harararsa kuma tana yi masa wani irin kallo tamkar daga taga bakin kumurci sai kawai yayi murmushi ya mayar da takobinsa izuwa gadon bayansa ya sakaleta sannan ya nufi inda gawar zakin take ya sunkuya da nufin ya dauki zakin ya sabashi a kafadarsa
kawai sai ji yayi anyi masa wani irin wawan naushi a gadon bayansa saboda karfin naushin sai da yayi tsalle can gefe daya fuskarsa ta gwaru a jikin wata bishiya ya fado kasa da rub da ciki kawai sai ji yayi jini na yoyo akan hancinsa da bakinsa.
Cikin fushi alkasim ya mike tsaye zumbur kafin jarumar ta tako kafafunta sau biyu ya daka tsalle sama izuwa kanta ya doki kirjinta da kafarsa guda jarumar tayi taga taga da baya har sau uku kamar zata fadi kasa amma sai ta tsaya kyam a tsaye tana karkade kurar da kafar Alkasim ta sanyawa rigarta.
Al amarin da yayi matukar girgiza hankalin alkasim kenan domin ba wai ya mace ba komai girman kato idan yayi masa irin wannan duka a kirji take yake faduwa kasa ya kama aman jini amma yau gashi ya mace ta shanye wannan duka nashi
anya kuwa wannan mutumce? Tambayar da alkasim ya yiwa kansa kenan kuma ya rasa amsarta
kawai sai alkasim da wannan jaruma suka kama zagaya junansu suna yin kallon kallo a karo na biyu har izuwa tsawon yan dakiku kwatsam kuma sai suka ruguntsuma da masifaffen fada suka wanzu suna masu kaiwa junansu naushi da bugu hannu da kafa ba tare da dayansu yayi yunkurin zare makami ba
wohoho idan karfi ya hadu da karfi dolene kowa yaji a jikinsa haka dai wadannan jarumai suka ci gaba da gabzar junansu suna hadawa kansu jini da majina gami da jigata
da zarar dayansu ya samu nasarar naushin daya sai kaga shi ma dayan ya rama babban abinda ya firgita alkasim shine ganin yadda karfinsa dana wannan jaruma yake neman zuwa daya sai da suka shafe kusan rabin sa a suna wannan bakin artabu har ya zamana cewa sun galabaita ainun
tun suna yin fadan da kuzarinsu har saida karfinsu ya kare suka durkushe kasa bisa gwiwowinsu suka ci gaba da fadan kamar zakaru
masu magana sunyi gaskiya da sukace dole itace kanwar naki babu shiri alkasim da jarumar suka baje a kasa suna haki kamar ransu zai fita saboda tsananin jigata sai bayan wata rabin sa ar sannan sukayi zumbur a tare kamar hadin baki kowannansu ya kaiwa kofar mataccen zakin sura a lokaci guda
koda taja shi ma yaja sai suka tsarge jikin zakin tamkar takobi aka sa aka datsashi kawai sai jarumar ta dubi sarki Alkasim tayi masa wani dan guntun murmushi na mugunta tace mun rabawa kanmu gardama yanzu tunda mun raba zakin biyu dai dai amma ka sani cewa daga yau nidakai mun zama abokan gaba tunda kaso ne kayi min kwace alhalin nice ta kamaci mallakar wannan zakin gaba dayansatana gama fadin hakan
saita saba rabin zakin a kafadarta ta juya da sauri ta falfala da azababben gudu izuwa cikin wannan duhuwar daji cikin hanzari alkasin ya bita da gudun amma ko hangota baiyi ba domin ta bace bat tamkar walkiya sai da ya shafe yan dakiku masu yawa yana ta gudu a cikin dajin yana waige waige da dube dube ko zai ga wannan jaruma amma ko alamunta bai gani ba
al amarin da
Yayi matukar bashi mamaki kenan ya fara zancen zuci yana mai cewa anya kuwa wannan jarumar mutum ce? Idan har ta kasance mutum dole ne ya kasance tana da zuri:a
Al amin Ahmed Misau
Guyson sunana kenan nake magana
daga zauran labarai page
ina ne gidansu ko kuma ina ne garinsu ko kuwa a cikin wani ayari take na fatake? Amsar da alkasim ya kasa baiwa kansa kenan
haka dai alkasim yayi ta wannan hasashe da zulumi a cikin zuciyarsa har ya dawo cikin birnin misra da shigarsa cikin gidan sarautar sai ya wuce kai tsaye izuwa fadar sarki inda ya zube gabansa ya kwashi gaisuwa
guyson sunana ko kuce Al amin Ahmed Dan misau
Daga zauran labarai
shikuwa sarki sai ya dubeshi cikin alamun matukar mamaki yace yakai dana abin alfaharina ya kai dodon maza zaki uban dawa kuma guguwa mai baje birane yau kuma me ya faru
naga ka dawo daga farauta babu komai a tare dakai shin babu sauran dabbobine a cikin dajin namu ko kuwa ka fasa yin farautar ne ka juyo da baya?
Lokacin da yarima Alkasim yaji wadannan tambayoyi guda biyu sai yayi ajiyar numfashi cikin alamun karayar zuciya nan take ya kwashe labarin duk da ya faru tsakaninsa da wannan bakuwar jaruma ya zayyane masa
koda jin wannan labari sai sarki ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya yana mai tsananin farin ciki tamkar wanda aka yiwa albishir babba
Al amarin da yayi matukar baiwa kowa mamaki kenan daga can sai sarki ya tsuke bakinsa yayi shiru ga barin yin dariyar sannan ya dubi yarima alkasim cikin murmushi yace wannan bakuwar jaruma itace matar da zaka aura har ka samu haihuwa da ita
toh Guyson nake magana
gobe ka sake yin shiri ka tafi daji ba don kayi farautar dabba ba sai domin farautar wannan mata taka duk wahalar da zaka sha da duk irin wulakancin da zaka fuskanta ka juresa
yayin da alkasim yaji wannan batu sai shima fuskarsa ta fadada da murmushi ya mike tsaye ya dafa kirjinsa da hannu guda ya dubi sarki cikin dakakkiyar zuciya yace yakai abbana idan har na cika jininka nayi maka alkawari cewar duk irin gabar da zamu yi da wannan jaruma sai na siye zuciyarta ta kaunaceni''
typing by me Al amin Ahmed Guyson
daga zauran labarai
koda jin haka sai sarki ya sake kamuwa da matukar farin ciki ya mike tsaye daga kan karagarsa ya rungume alkasim yana mai cewa ina alfahari dakai yakai dana nasan zaka iya
har dare ya raba alkasim bai rintsa ba domin da zarar ya rufe idanunsa baya ganin komai face fuskar wannan bakuwar jaruma a yinin gaba daya ka kasa ci da shan komai
ko a zaune ko a tsaye sai yayi ta tuno da abubuwan da suka faru a tsakaninsa da bakuwar jarumar a daji
dakyar dai alkasim ya samu yayi dan barcin amma alfijir na ketowa ya farka nan take yasa kuyangi suka shirya masa ruwan wanka da abincinsa na kalaci ya kimtsa kafin gari ya soma haske tuni ya gama shirin tafiya farauta ba tare da bata wani lokaci ba yarima ya hau dokinsa ya fice daga cikin gidan sarautar ya nausa izuwa cikin wannan daji wanda ya hadu da bakuwar jaruma a cikinsa jiya
alkasim yaci gaba da nausawa cikin dajin yana ta dube dube da waige waige kai wani lokacin har saukowa yake daga kan dokinsa yana duba kasa ko zaiga sahul bil adama amma ko alamarsa bai gani ba
sai da ya shafe sa a biyu da rabi yana ta kai kawo a cikin dajin banda dabbobi da tsuntsayebabu abinda yake gani
da yake wannan karon ba tasu yake ba sai dai su wuce ya wuce abinsa babu mai tankawa wani hakanne yasa alkasim yaji ya kosa kuma zuciyarsa ta fara karaya da saran cewa zai sake haduwa da wannan bakuwar jaruma duk da mahaifinsa ya gaya masa cewa itace matar da zata zamo abokiyar rayuwarsa
lokacin da rana ta kwale sai alkasim ya nufi wata katuwar bishiya mai yawan ganyaye domin yaje ya zauna a karkashinta ya huta da isarsa bakin bishiyar sai ya sauka daga kan dokin ya daure dokin a jikin bishiyar sannan ya zauna a lokacin da wata irin iska mai dadin sanyi ta fara kadawa hakan ne yasa ya kishingida yana mai jingina gadon bayansa a jikin bishiyar
saboda gajiyar dake jikinsa sai kawai ya fara yin gyangyadi faruwar hakan keda wuya sai yaji wani abu na yawo a jikinsa tun daga kan kafafunsa
a firgice alkasim ya yunkura domin zare takobinsa amma sai yaji an kanannade jikinsa gaba daya kafin yayi wani yunkuri tuni wannan bishiya ta dare saiga wata kofa ta bayyana nan take wata iska mai karfi ta fito daga cikin kofar ta zuke alkasim a lokacin da yaji wata irin kasala ta shigeshi yadda ko hannunsa ba zai iya motsawa ba ashe wata murtukekiyar macijiyace ta kanannade shi gaba dayan jikinsa
kawai sai gani yayi an fyadashi da kasa a tsakiyar wata kasaitacciyar fada.
Fadar ta kawatu ainun da kayan kyale kyale kai kace fadar birnin misra, Al amin Ahmed Guyson sunana' koda alkasim ya dago kansa cikin matukar karfin hali sai yaga ashe babu kowa a cikin fadar face mutum daya jal kuma ba kowa bane face wannan bakuwar jaruma ita kadai zaune aakan wata katuwar karagar mulki taci ado irin na 'ya 'yan sarakai.
Koda yarima Alkasim yaga jarumar a cikin wannan hali sai ya kidime yaji ya kara kamuwa da tsananin sonta fiye da ko yaushe..
Don haka sai ya kura mata idanu yana murmushi ita kuwa saita murtuke fuskarta ta dubeshi a fusace tace mazaka bani amsar tambayar da zanyi maka yanzu in ba haka ba kuwa zan gana maka azabar da ba a taba yi maka irin taba
koda jin wannan batu sai alkasim yayi murmushi yace ''

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login