Showing 66001 words to 69000 words out of 76736 words
Chapter 23 - MIJIN ALJANAH 1 to end Complete Hausa Novels by King Boy.txt
king boy isah๐
|
|
__________________________
๐ZAMANI APR 2017 ๐
|_________________________|
***** zamani *****
๐ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ ยฉZ.W.A
***** zamani *****
. _*DEDICATED TO UR|โ> AUNTY NA FATIMA USMAN (MMN ALI)*_ ๐๐ฝ *Na gaida ki kyauta na gode da kulawar da kike bani hakika kece lamba daya a fagen kaunar wannan littafin. Mmn hisham bazan manta dake ba.*๐๐ฝ๐
washe gari da safe:
Zainab tare suka shiga ban daki da al ameen wankan janaba din ma bai iya ba duk sai da gyagyara misha ta kuma kara koya mishi karatun. Zainab tayi wanka ta saka kaya ta feshe duk jikinta da turare tukun ta fito ta nufi kitchen a parllo ta iske yasmeen a kan sofa a nan ta kwana. bata tayar da itaba kitchen din ta wuce ta hada musu kayan breakfast ta kawo ta jera a kan dineeetabal.
Wajen yasmeen ta koma ta tada ta a hankali bayan yasmeen ta tashi tace "ke malam a name mutun na barcinsa zaki tashe shi."
Zee tace. "aunty ki tashi kin kusan makara fa yanzu har karfe 7 ta kusa naga bakiyi sallah ba shi yasa na tashe ki"
"Yasmeen tace to naji na kuma gode amma daga yanzu karki sake cemin aunty Dallah dube ki to anan me al ameen ya gani ma da har ya auro ki in ba dan jarabarsu irib ta maza ba"
"Haba aunty me yayi zafi haka Ni a tunani na ai duk wacce ka iske a gida dole ka kirata aunty kuma kishi ba abunyi bane domin kishiya yar uwa ce. kuma bazan daina ce miki aunty ba tunda ke na iske a cikin gidan nan."
yar dariya Yasmeen tayi tukun tawa zee kallan sama da kasa. "Wato ke a tunaninki har kin sama wajen zama ne a gidan nan da har kike tunanin kishi nake dake. Ai ni banga abunda Zanwa kishi a nan ba. Domin idan naga dama a yau-yau zaki bar gidan nan. marar aikin yi kawai mtsewwwo taja wani dogon Tsaki hade da mikewa ta nufi hanyar dakinta. Maganar da Zee take ne yasa ta dan rage Sauri domin jin me take Fada.
"Ba Damuwa aunty ni bazan daina yi miki biyaya ba domin ko zaman aure bai hadamu ba ni ina girmama na gaba dani kuma karki Raina mutum koda yaya yake domin ta iya yuyuwa yafi ki a gurin Allah. Kuma Da kike maganar Fitar dani daga gida wannan bazai dameni ba domin ni na yarda da Allah kuma komai na Rayuwar mu a rubucr yake duk abunda zai faru dani nasan can dama haka Allah ya tsara." Yasmeen najin haka ta sake yin wani tsakin da niyar ta wuce cikin dakin. "Aunty kiy sauri ki fito ga Breakfast nan na shirya mn ke muke jira".
Tafi Sukaji Raf! Raf! Raf! Al ameen ne ashe yana jin duk Abunda ke Faruwa Tsakaninsu. "Yasmeen dawo ki Zauna zamuyi magana." Al ameen ya fada ko juyowa batayi ba ta shige dakinta. Al ameen yazo ya zauna kusa da Zee ya juya yana kallanta yana murmushi ya dan Shafa gefan kumatunta yace. "A Ina kara godewa allah daya bani ke a matsayin mata. gaki da Tarbiya hakuri da juriya ga natsuwa" Kiss ya manna mata A goshi tukun yace Ina sanki zeena. "Love u too" kawai ta fada cike da kunya ta Rufe idonta Domin tuno abunda Ya faru jiya a tsakaninsu duk sai taji kunya ta Rufe ta. hannuwanta ya kama ya bude idon yace. " Amarya kenan to miye na kunya bayan kuma na... Duka ta kai mishi da sauri ya goce ya tashi yana Tsokalarta suna zagaya Parllon cike da nishadi.
Yasmeen tana jinsu Bakin ciki ne da Kishi ya kara kule ta. Kan gado take A zaune tama Rasa me keyi mata dadi ko wankan ma ta kasa shiga.
Su Al ameen sun dan dade A parllon hat kusan 7:30 amma Yasmeen bata fito ba. hakan yasa yaje ya tura dakin yaji a rufe ya kwankwasa tana jinsa amma tayi Shiru ta kyale sa. har ya gaji ya koma yace wa Zainab.
"Amarya muje mu karya wannan bata da niyar fitowa kuma kinga gun Aiki Zan tafi. Ba gardama zee ta tashi suka nufi dinner din domin karyawa. Shayi mai kauri sai indomie da taji kayan hadi gefe Daya ga soyayen dankali da doya da kwai. ga kuma wainar kwai a gefe. Al ameen tun kafin a zoba mishi kanshi ya isheshi ya fara zumudi. ciyar da juna suka dinga yi Abunda ya kara bawa Kursiyya haushi kenan Batt suka bace suka bayyana a wata katuwar kuka wacce take a tsakiyar wani kogi.
'Al ameen sai zuba uban santi yake Tambaya yake Shin wai wama ya nuna mata kitchen kuma ita da take amarya ai bai kamata ta fara Girki tun yau ba. Zainab murmushi tayi tace angona kaidai ci abinci karfa ince Santi kake.
"To in nayi santin ma ai ba laifi bane. nifa gaskiya nama fasa futa ba inda zanje"
"Ah to nima dan kar inyi maka katsalandan ne angona amma da tun dazu zance maka ka fasa Zuwa gurin aikin nan mu tsaya mu..." kuma sai ta kasa karasa maganar.
Al ameen yace kunya ko. uhm idan "kunya tayi yawa fa tana hana a kyautatawa miji yanda ya kamata kinsan hakan ba"
"Yes na sani kuma zan kiyaye my oga. amma fa kar amarcin mu yasa muci haram ya kamata dai ka sanar da shugaban Hospital din"
"Ai baya da matsala zan sanar da shi kuma zan gayawa brox ya duba patients dina."
*Su kursiyya ne zaune kan kuka duk Sun koma wata irin hallita mai suffa abun Tsoro jikinsu irin na mutun kai na jaki Ga kuma wani wagegen baki da Jini ke kwaranya daga Ciki Wayarta Ta jawo ta kira Al ameen bugo Daya ya dauka domin yarinyar ta fara bashi haushi gwara yayi mata baro-baro ko ta rabu dashi haka yace a zuciyarsa.
ko sallama batayi ba ta fara magana.
"Haba mijina al ameen dina ya zaka min haka kwana biyu baka kirana kama Daina daukan kirana dama haka auren yake?".
Dariyace ta kubce wa Al ameen domin har saida ya rike baki.
"Ke tsaya wai ke wace irin jahila dakikya ce me kike ma kursiyya ko kur.... me ma to wallah bari kiji in gaya miki..................... ......................................
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
โ๐ผAutan marubuta โ๐ผ
๐King boy๐
๐๐ฟโ MIJIN ALJANAH โ ๐๐ฟ
page 134 - 135
|
|
na king boy isah๐
|
|
__________________________
๐ZAMANI APR 2017 ๐
|_________________________|
***** zamani *****
๐ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ ยฉZ.W.A
***** zamani *****
. _*DEDICATED TO UR|โ> AUNTY NA FATIMA USMAN (MMN ALI)*_ ๐๐ฝ *Na gaida ki kyauta na gode da kulawar da kike bani hakika kece lamba daya a fagen kaunar wannan littafin. Mmn hisham bazan manta dake ba.*๐๐ฝ๐
Dariyace ta kubce wa Al ameen domin har saida ya rike baki.
"Ke tsaya wai ke wace irin jahila dakikya ce me kike ma kursiyya ko kur.... me ma to wallah bari kiji in gaya miki Ba sanki nake ba kuma bazan taba Sanki ba. Wama yasanki da har zaki dinga kiran mutum da mijinki auu! wai dan anyi auren wasan nan a grp to bari in gaya miki gaskiya wannan ma Ni a Matsayin nishadi na dauke shi ba komai ba. kuma Ina so in gaya miki Ki Rabu dani dan allah domin ni magidan ci ne Mata na biyu a halin yanzu.
Cikin kuka Kursiyya tace Ni zakawa haka Al ameen Dama kai mayaudari ne ashe Ban sani ba. Shin kasan ko ni wacece kuwa. Saboda kai na Rabuda ahalina na rabu da Masoyina wanda Zan aura dan uwana. Ba ina fadi maka haka bane domin ka so ni Aa ina fada ne kawai domin takaicin da ke cikin Raina. Wato kai mayaudari ne ko To ka yaudari Wata wacce ita ba'a Yaudara Dan haka ka jira Daukar Fansa bazata zo maka da Kyau ba. Domin ni ba Mutun bace Ni Aljana ce.
"Banza mahaukaciya Da yawa na hadu da irinki masu cewa su aljanune kuma ba abunda ke faruwa daga Karshe dan haka wannan bazai Taba tsorata ni ba." Katse wayar yayi tukun yayi Tsaki yace Shirmamiya kawai. Block din number yayi.
Kursiyya Wulli taya da wayar cikin Ruwan dake kasan kukar Hawayen Jini ne suka fara kwaranya a kan bakaken idanunta masu ban Tsoro. Marsiyya kuwa ta shiga Rarashinta Taba bata Hakuri. Wasu irin Muryoyi na dinga ji Na dariya na tashi a gurin wanda su kansu su kursiyya saida suka Rude suka kama waige-waige Domin ganin mai Dariyar Sai can daga bisani wani dan-kareran Aljani ya bayyana yana Zagaya su Yana dariya Ba kowa bane face Dursum. "Kursiyya! Kursiyya! Cikin wata iriyar murya marar Dadin ji yake maganar.
"Na so Ki So mai tsanani na kula da ke na rike ki amana Amma kika guje ni ta Dalilinsa kuma kika hanani daukar Fansa a kansa To yanzu gashi ke da kanki naji kina maganar Daukar Fansa A kansa Saboda kawai ya iya kalaman soyayya kika guje ni a kansa Bakiyi tunanin komai ba kika Tare a gidansa kika guji iyayenki _hahahahahah_ ya karashe zancen da kwashewq da wata irin dariya.
Nuni tayi da hannuta bangaren sa kawai Sai ga wata irin bakar sarka ta fito daga hannunta da sauri ta nanado wuyan Dursum sama ta daga shi yana Reto " Yi dariyar ta kara cewa ci gaba da dariyarka mana. wato bazaka barni da abunda ke damuna bama sai kazo ka kuma dasa min wani bakin ciki? mai makwan ka min jaje ka kuma Rarashe ni ka tayani daukar Fansa sai dai kazo ka cika ni da surutai ka kuma kara tunzura Zuciyata shin haka Salon son naka yake? Idan kayi wasa a yanzu zan batar da kai daga fadin duniyar nan".
Dursum kam idanunsa sunyi jajur har baya iya magana domin sarkar ta shake shi Sosai. tari ya Fara kamar Wanda zai mutu marsiyya na ganin haka ta fara rokon aunty nata ta Sake shi Zai mutu fa in bata Sake shi ba. sakinsa tayi ya fada ruwa Tunjum! Ya lume Zuwa can naga ya fito a suffar wani dodo mai ban Tsoro gashi kato Jikinsa Duk Sulbi ne Idanunsa hancinsa baki da kunne Wasu kwaruka ne ke fita yan kananu bakake. magana ya fara wacce muryar in mutun yaji kamar Dodon kunnansa zai fashe. " Kursiyya ni kikawa haka? Ni kike nema ki kashe domin kawai na fada miki gaskiya. Lalai yau badan ina Sanki ba kuma inq jin kunyar babanki Da sai na koya miki hankali na nuna miki banbancin Mace da Namiji. Kinci Darajar Mahaifinku da kuma San da nake miki. kuma sako yaje wa mahaifinki daga wajena Dan haka yace yana nemanku Daga ke har kanwarku Maza-Maza kuje gida.
"Tabbas zan koma Gida amma sai na dauki Fansa ta tukun nan" cewar kursiyya
"Allah ya bada Sa'a amma ina baku shawara kuyi gagawar dawowa gida Domin Fushin mai Martaba ba kyau ina jiye muku Tsoran afkawa cikin Fushinsa"
Batt dursumm ya bace. Su Kursiyya kuwa suka dawo gidan Al ameen. yau kam su al ameen sun shakata haka suka wuni suna kai kawo tsakanin daki da parllo da kuma kitchen suna wassanni suna farantawa juna Rai. Yasmeen tana daki tana jinsu amma taki Budewa wai ita tayi fushi. duk yau bata ci wani abu ba Sai lacasera dake cikin dan fridge dinta da kuma cincin su kadai take ci in ta ji yunwa ta matsa mata.
Gaba dayan gidan suka ji yana girgiza duhu ya mamaye ko'ina Al ameen da Zainab ma da suka Rike wa juna hannu basa ganin junansa. Yasmeen na daki a tsorace ta mike ta nufi kofa da lalubr ta bude ko far ta fito a guje tana ihoo tana kiran sunan Al ameen karo taci da kujera hakan ya tabbatar mata data iso Parllon. Su Al ameen kuwa kara makalkale junansu Sukayi Zainab kuwa ta fara jawo Suratul Baqara.
Dariya suka ji anayi Ta ko wane bangare na gidan suka jin dariyar na fitowq. gidan kuma yaci gaba da girgiza kamar da. Haka itama Zainab a tsorace take karatun da karfi.
"Ke!! kimin shiru ki tsaya da karatun nan bada ke nake yi ba idan kuwa kina so abun yq shafe ki ne to bismillah ci gaba". Kursiyya ce ke maganar Cikin wata irin murya wacce ita kanta ta isa ta tsorata dan adam uku-uku take fitowa. jikin Zainab Ya hau bari Ta fara karkarwa Amma taki daina karatun Sai dai ta Rage ba kamar dazu ba da take yi da karfi.
kursiyya ce ta bayyana A jikin bango da wata irin hallita mai Firgitarwa wacce idan ka ganta ko kai waye sai ka firgita
"Keeeeeeeee!! kina cika min kunne fa da karatun nan naki ki dakata ko kici na jaki yanzun nan." Shiru Zainab tayi domin ta kadu bata taba ganin wata hallitaba irin wannan. sulalewa tayi daga jikin al ameen ta fadi a kasa sumama. yasmeen tana ganin halittar itama ta kwada kara ta rufe idanunta da karfi. Al ameen Rudewa yayi gaba daya ya fita hayyacinsa yama Rasa dame Zaiji................................................................
Duhun yayi yawa gashi da rana ne hakan yasa na fito a guje fada da Aljani ba dadi fa. ba dan hk ba da na shigar musu ๐
๐ฐ๐ฐ๐ฐ๐ฐ๐ .lolz
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
โ๐ผAutan marubuta โ๐ผ
๐King boy๐
๐๐ฟโ MIJIN ALJANAH โ ๐๐ฟ
page 136 - 137
|
|
na king boy isah๐
|
|
__________________________
๐ZAMANI APR 2017 ๐
|_________________________|
***** zamani *****
๐ZAMANI WRITER'S ASSOCIATION ๐ ยฉZ.W.A
***** zamani *****
. _*DEDICATED TO UR|โ> AUNTY NA FATIMA USMAN (MMN ALI)*_ ๐๐ฝ *Na gaida ki kyauta na gode da kulawar da kike bani hakika kece lamba daya a fagen kaunar wannan littafin.๐๐ฝ๐
๐ค BAN MANTA DAKU BA๐
๐นUSAINI 80K๐น
๐นUMAR D UMAR๐น
๐นAbdul King Article๐น
๐นMUFEEDAT๐น
๐นSAJEEDA BATULA๐น
๐น Mmn islam๐น
๐๐ฝ๐ I love u oll my friends ๐ ONE LOVE
"Keeeeeeeee!! kina cika min kunne fa da karatun nan naki ki dakata ko kici na jaki yanzun nan." Shiru Zainab tayi domin ta kadu bata taba ganin wata hallitaba irin wannan. sulalewa tayi daga jikin al ameen ta fadi a kasa sumama. yasmeen tana ganin halittar itama ta kwada kara ta rufe idanunta da karfi. Al ameen Rudewa yayi gaba daya ya fita hayyacinsa yama Rasa dame Zaiji.
Ana cikin haka sai kawai al qmeen yaji an shaki wuyansa ta baya an daga shi sama. kan iska. kokarin kwacewa ya hau yi nan ya fahimci da sarka ce aka dauro wuyan nashi. Dariya aka ci gaba dayi hahahahaha ๐คฃ kamar bangwayen dakin zasu tsage dan karar dariyar. abunda ya kara dugunzuma hankalin Al ameen kenan Tsoro ya sake mamaye shi ga dakin har yanzu masifar duhu,
Kursiyya ce ta bayyana tana dariya ta cikin wani haske ita kadai ake gani a duk dakin sai kuma al ameen dake makale a sama wanda lunfashin sa har ya fara daukewa dalilin daurin da aka mishi sai wuntsile-wuntsile yake da kafafu.
wata Rudadar murya Kursiyya ke magana da ita " hahaha Al ameen ka tafka babban kuskure na yaudarana da kayi. ka saba yaudara a net ka yaudari mata da yawa naga wannan a bincike na da niyi wasu sun tsani maza ta dalilinka sau da yawa wanda basu taba soyayya kake yaudara. wannan yake karya musu zuciys suji sun tsani soyayya bama ta net ba har ta face to face.
Garin kwashe-kwashrn ka kuma ka debo ruwan dafa kanka ks ballo mayunwaciyar Zakanya kuma dole ta cinye ka. hahahaha Al ameen wato yanzu da mutun ce kawa abun da kamin shikenan kaci bullus ko. to wannan ba mutum bace kursiyya kenan yar gata gurin sarkin aljanu. daga kaina baza ka sake Yaudarar wata mace ba mutun ko Aljan domin yanzu zan kashe ka na batar dakai haka kuma suma wannan matan naks bazan barsu ba bayan na kashe ka suma kashe su zanyi ka sani yanzu ba ko birbishin Sanka a cikin zuciyata.
Yasmeen najin anyi batun kashe su Tayi Zumbur ta mike ta nufi dakinta da gudu da niyar tserewa. kafin ta kai kofa. Yasmeen ta aiko mata da wata Sarka ta nanade ta tajata Sama itama tana lilo sai iho take kwadawa.
Al ameen yana ganin haka Ya kara Rudewa cikin karfin hali yace.' "Naji na kuma amince ki kashe ni ni nayi miki laifi na cancanci hakam amma ina hadaki da allanki ki bar matan domin kuwa Su basuyi miki komai ba."
"Al ameen ka kyale ta marar mutunci ta kashe mu din ai itama Allah bazai kyale taba banza kawai Shedaniya macuciya kawai. in ba dan Zalinci da Fin karfi ba kije ki nema jinsinki kuyi Aure mn mu me Ruwan mu dake."
Maganar yasmeen tayi masifar batawa Marsiyya Rai har itama kursiyyar. Kursiyya ta kara matse matse mata ciki da Sarkar. Wani uban ihuuu! yasmeen tayi wanda bata yi kalansa ko a baya ba. Tace "Yah Al ameen ka taimake ni Ta matse min ciki kuma ina Dauke da juna biyu." A takure ta Fadi maganar tana kara
Al ameen kara Rikicewa yayi ya fara kokarin kubcewa daga shake war da sarkar tayi mishi. amma ina Sarkar ko dan motsi batayi. da ya kalli yasmeen yaga halin da take ciki hawaye ke Zuba a idanunsa Ya fara Rokon Kursiyya yana mata magiya a kan ta sakar mishi matarshi kuma karta kashe mishi da'.
Kursiyya wata mahaukaciyar dariya ta sake yi wacce ko ina na dakin yake amsawa. Ohh! Al ameen me da ashe kasan ciwan da' to bari kaga. jikin bango ta gwara Yasmeen kanta ya bugu ta Fado kasa sumama.
Wani ihuu! na takaici Al ameen yayi Tukun ya fara fadi mata bakaken magan ganu wanda yasa taji mugun haushi wata muguwar wukace ta bayana a hannun kursiyya wacce takobi ce takai tsawan mutun kallo daya zaka mata kasan duk inda aka bugata a jikin mutun sai ta wuce wato Zata Raba mutum biyu ba tare da ta tsaya wani gargada ba. Kursiyya a fusace ta daga takobin da niyar ta Raba Al ameen gida biyu.
Wani mahaukacin kara su kursiyya sukayi Inda lokaci daya naga komai ya Canza Al ameen ya fado kasa tum!