Showing 30001 words to 33000 words out of 163126 words
hassadarki ta motsa wato kin so ne ke da kika zo kika aure mata miji sannan kuma ki zama ke ce ke ta haihuwa ita kuma ko oho ko? Sai ga shi ba ke kaɗai ke da Allah ba. Ubangiji na kowa da kowa ne. Ta samu ciki kin kasa ɓoye hassdarki shi ya sa kika zo za ki yi ma mutane rashin kunya. To ba sa'an ki anan kuma duk tsiya dai a baya kika zo sai da aura ta rage sannan kika samu."
"Ke Munnira"
In ji Anty Bahijja. Maman Farko ba ta yi magana ba Anty Maimuna ce ta ce" Munnira ke ba za ki ba da haƙuri ba sai hura wuta! Wallahi kar na ƙara jin bakin ki"
"Ta yi magana dole fa a mayar mata da martani domin rashin kunya ce za ta yi ma mutane."
Munnira ta faɗa a fusace. Anty Zabba sai ta yi aikin hankali ta kama hannuna tana faɗin" Ta ho mu je Sadiya kin ga ba ke kaɗai ba ne. Ɓaçin rai kaɗan zai iya shafar abin da ke cikin ki. Munnira ai ta gama mgana taho mu je."
Har na bi ta, saboda raina ya ɓaci har wani duhu duhu na ke gani amma tabbas Munnira ta faɗa masu zafi shi ya sa ta kasa magana amma Gimbiya ba ta so mganar ta tsaya nan ba sai ta fara masifa har tana fizge hannunta a cikin na Naja da ke riƙe ta, tana faɗin kar ta tanka mgana ta mutu har Maman Farko sai da ta roƙe ta da kar ta ce komai a bar mganan hakanan
"Ahayye. Nanaye baƙin cikin me zan yi niSaudatu! Ai duk haihuwan da za a sake yi ma Daddy sai dai ta biyo bayan haihuwar da na yi masa. Biyu ne amma kamar da goma ne. Irin kuma haihuwar da ba a taɓa masa ba sai da ya auro ni sannan na haifa masa.'"
"Ke Saudatu me ya sa ke b a ki jin mgana ne?
Maman Farko ta faɗa a fusace tana cigaba da faɗin" A na cewa a bar mganar kina ƙara magana?
"Kyaleta Mama ba riba za ta ci ba domin kowa a nan wajen ya san ba ta da gaskiya."
In ji Suwaiba saboda kowa ran shi ya ɓaci da mganganun Gimbiya. Har na ci burki da zan juya na bata amsa Munnira ta ƙara fansana
"Wallahi ƙarya kike yi. Ai am gama yi ma Tafida farar haihuwa tun haihuwan Jidda. Kin san soyayyar a haifa ma ɗa kana tashen samartaka! Kin san girman soyayya auran saurayi da budurwa? Wallahi ko goma za ki ta haifa maza sai dai ki biyo baya amma ba dai ki zo a gaba ba. Kuma in Sadiya ta haihu ki rubuta ki ijiye sai kin gane cewa ke dai kin yi irin na ki haihuwan amma ba dai ki yi irin na Sadiya ba."
Na so na yi shuru amma sai na kasa saboda na biyu kenan ta na faɗin ta yi haihuwan da ba a taɓa yi ma Tafida ba saboda ta haifi maza ni kuma ban iya haihuwan namiji ba shi ne ban iya farar haihuwa ba.
kawai sai na juya na fizge hannuna daga na Anty Zabba na isa gaban Gimbiya ina kallonta kafin na ce.
" Sau biyu kenan ina jin kina nuna bambamci tsakanin su Khalipa da su Jidda. Ban yi miki magana a farko ba amma yau na kasa haƙuri sai na tanka. Gimbiya ni fa Yusuf kaɗai na aura kuma soyayyace ta sa na yarda da shi har ma iyayena suka aminta da shi muka zama a ƙarƙashin inuwar aure. Yau ko mata dubu zan haifa da ɗigon jinin Yusuf wallahi ni Allah ya gama mini komai Gimbiya. Ya tsamoni cikin duba ya yi mini ni'imar da ba kowa ya yi ma wa ba. Haihuwan namiji ko mace ni ban ɗauke shi a wani abu ba. Ɗaya na ɗauke shi. Mata suna da matuƙar tasiri a rayuwar mu da addininmu. Kin manta cewa mace ce ta fara karɓan addinin musulunci a mata? Kin manta da tarihin matar Firauna? Hasiya da irin gwagwarmayan da ta yi domin addinin Allah. Ko kina da labarin Allah ya gina mata gida a Aljannah? To kamar yadda Maza suke da tarihi a cikin addininmu haka ma Mata ke da wannan tarihin. Saboda haka ni in mata Allah zai ba ni ina so in ta haihuwarsu ina roƙon Allah ya shirya mini su. Ya kuma sa su yi ma addininsu hidima. Ke kuma da kike son Mazan saboda tunanin su ne ke da gidan Allah ya yi ta baki ko dubu za ki haifa wallahi tallahi ba zai tsole mini gefen ganina ba Gimbiya. Gargaɗin da zan yi miki shi ne ki daina ƙoƙarin mayar da ƴa'ƴana a baya. Suma ƴa'ƴa ne dai-dai da irin haihuwan da kike tunanin kin yi a kan su Khalipa."
Ina gama faɗin haka na wuce. Maman farko ta jinjina kai tana na faɗin" Shi kenan Sadiya kin gama mgana."
Kowa sai ya yi shuru ya yi sanyi ita ko Gimbiya sai ta fashe da kuka jin yadda har Hajiya iya da ba ta san farkon faɗan ba ta na salla sai da ta ce Gimbiya ce ba ta da gaskiya.
"Ko ba ta girme ki ba ai tana gaba da ke a aure."
"Balle ma wallahi Sadiya ta girme ta. Sai dai ta yi sa'ar ƙanwar ta Amina."
In ji Munnira, Suwaiba ta karɓe da cewa" Tsaya tsaya ma ko da ma a ce ba ta girme ta a shekaru ba a gidan aure ita ce babba. Kuma bai kamata ta girmama ta ba? Ai kowa ya ji wannan abin da ya faru a san ba ki ta ki gaskiya ba Gimbiyan"
Ni dai ban tsaya ba na ce zan tafi gida. Yau ma tun safe rabon da mu yi waya da Yallaɓai. Anty Maimuna ta ba ni mamaki har da ita a masu ba ni haƙuri Anty Bahijja kuma ta rufe Gimbiya ta faɗa tana kukan munafunci. Tare da Marwa da Munnira muka fita Hauwa ta ce Muttaƙa zai zo ya ɗauke ta. Anty Zabba kuma gidan su ta ce za ta je ta kwana. Amaryan ta ma tun da suka sauka daman gidansu ta sauka bikin ma daga can ta zo.
Muna cikin adaidaita Munnira sai jaraba take yi tana ce mini wai ina yi ma Gimbiya sanyi sanyi shi ya sa ta raina ni.
"Wallahi ta ba ni mamaki ko kunya ba ta ji ba."
Marwa ta faɗa cikin mamaki. Munnira ta ce"To daman tana da kunyar ne! Wallah ba ta da kunya ta daɗe tana neman da man da za ta ci kasuwa a kan Sadiya."
"Sai me? Don Allah ku bar mganar ni wallahi raina ma ƙara ɓaci yake yi "
Na faɗa ni a ƙokarina su bar mganar amma Munnira ba ta bar ta ba sai masifa take yi tana cewa na faɗa ma Yallaɓai domin ya dauƙi mataki.
"Ni ba ruwana ba ki ji ta ce kar na kai ta gaba ba."
"Ki kaita ɗin domin ta san kin isa."
Shuru na yi ban yi magana ba. Saboda ni ba halina ba ne wannan surutun, abubuwa da dama sai dai ya ji su can a bakin ƴan gidan su. Ni bar ni da mgana in na ga za a cuce ni ko magana kan lamarin da ya shafe ni amma ba ruwana da mganar kishiya. Ko kafin ma ya yi aure ko hatsiyar mu da yayyen shi ban taɓa faɗa masa sai dai in ya ji labari ya zo ya tambaye ni amma ba dai ni na kwashi jiki na je ina ce masa an yi kaza an yi kaza ba. Shi ya sa yau ɗin ma na yi shuru amma har a ƙasan raina ba zan faɗa masa ko da kuma ba zai ji labari ba amma dai ina da yaƙinin tabbas zai iya sani.
Mu mai adaidaita ya fara saukewa sannan ya wuce da Munnira. Allah ya so ni ga Marwa ina komawa gida na kwanta sai zazzaɓi ita ce na samu ta dama min kuni na sha ya zauna a cikina. Ni saboda bacin rai ko Baby ban nema ba da zamu taho. Sai kawai na ce gobe sai su dawo tare da Jidda. Haka Yallaɓai ya zo ya same ni a kwance ya yi ta faɗan sai da ya ce ba ya son na je Anty Zuwaaira ta matsa sai an je da ni gashi nan na dawo ba ni da lafiya sai da na ce masa ba fa komai ba ne aman da na yi a can sai ɗan zazzaɓi kuma ya san ina yin zazzaɓi haka daddare sannan ya ɗan sarara da faɗan da ya fara
Paracetamol ya ba ni na sha na yi sallah na kwanta sai na ji daɗin jiki na zuwa safe kuma sai na ji ya sake ni. Marwa ta gyara minI gida ta yi mana abin kari itama da safen ta wuce Ɗorayi za ta gai da su Gwaggo. Daga can ta wuce gidan su ta kwana da safe ta wuce Rano. Iya kwanakin da Kawu ya ba ta kenan. Ni kaɗai a gida domin Yallaɓai da hantsi shima ya fita, sai can bayan la'asar dai ga shi an kawo su Jidda. Ita na samu ta yi girki ni kuma na ce ta dama mini kuni domin wanda Marwa ta dama min tas na shanye shi kuma shi kaɗai na ke samu ya na zama a cikina sai ganye haka irin su Kabeji, latas da allayahu. In a ka sanya su a cikin abinci ina samu na ci sosai. Amma wani kifi wani nama ko warin shi ba na so balle su ƙwai da sauran nau'ikan abincin da ba na so ma na ji warin su in ana dafawa. Ni warin ma maggi mai star ne kwata kwata ba na so shi ya sa na daina ma giftawa ta Kitchen ɗin na bar ma Jidda ne ban san yadda yake ciki ba, domin na daɗe ban shiga cikin sa ba.
Har a ka kwarari kwana huɗu da dawowata gida ban ji Yallaɓai ya yi mini wata mgana ba. Sai ranar jumma'a ranar ma ba a gidana yake ba yana gidan Gimbiya ne.
Yau Mubeenan Musbahu ta zo ta yinin mini ita ta yi girki da gyaran gida. Tun da ya ga ba ni da lafiya yana yawan turo ta gidana kuma ina jin daɗin haka. Sai dare Musbahu ya zo ya ɗauke ta shi ya sa na koma ɗaki na kwanta saboda na ji na fara jin sanyi sanyi. Ina cikin bargo ina shafa kasan marata cikina ya shiga wata na huɗu kuma har ya fara turowa. Ina jin ƙaunar abin da ke cikina sosai wata ƙila don irin wahalan laulayin da na ke sha ne na tuna kafin bikin Suhailat maganar da muka yi da Yallaɓai.
"Yallaɓai in na mace na haifa sunan Mama za mu saka mata."
"In kuma Namiji ne to sunan Alhajin Ɗorayi za mu saka masa ko?
Ya ƙarishe mini yana dariya. Nima dariyan na yi kafin na ce" Ka yi gaskiya. Tabbas haka ne a raina."
A lokacin jawo ni jikinsa ya yi yana faɗin" Kar ki damu fata na ki sauka lafiya duk sunan da kike so shi za mu sanya kin ji ko?
Sai na ji daɗi har ina ba shi sumba.
Vibration ɗin waya ta ne ya dawo da ni daga tunanin da na faɗa. Ta na gefen in da na ke kwance ne na saka hannu na ɗauko ta sai na ga Yallaɓai ke kirana. Ban kawo komai a raina a tunanina sallama zai yi mini kamar yadda ya ke yi in bai samu zuwa ba.
"Zan taho da Daughter yanzu ina so mu yi mgana gabaɗaya."
Abin da ya ce minI kenan bayan mun gaisa. Sai na ce masa sai sun taho. Har muka gama wayar tunanina bai hasaso mini kan abin da ya faru ba ne sai daga baya na fara tunanin wataƙila kan haka ne amma kuma a ina ya ji? Ko wa ya faɗa masa? Watsar da tunanin na yi saboda ba ni da mai ba ni amsar su.
Sai da suka zo gidan sannan na fito daga ɗakin na saka hijabi amma duk wanda ya gani ya san ina fama da azaban laulayi duk na yi fari na lashe na kuma rame. kullum ina fama da bushewar baki da maƙogwaro. Ina ganin Gimbiya sai na tuna da faɗan da ya shiga tsakanin mu da ita shi ya sa na yi kamar ban gan ta ba kamar yadda itama na ga ta yi, sai wani cin magani take yi tana wani hura hanci.
Shima gogan ransa a ɓace na gan shi da ga gani sun yi ta ne kafin su ƙariso. Jidda ya haɗa da yaran gabaɗaya da cewa su koma falon su za mu yi mganam ita ta tattara su suka bar mana falon. Shi yana saman kujera mai zaman mutun uku ni kuma ina zaune a mai zaman mutum biyu a gefen sa ita kuma sai ta zauna kan mai zaman mutum ɗaya muna fuskatan juna ni da ita. Ai ni tun da ta yi mini wannan wulakancin na yi alƙwarin duk in da za mu haɗu in ba ta ce sannu ba ba zan tanka ta ba. Da mutumcina ba zan zauna wacce ba ta isa ta zubar mini da ƙima ba.
"Ba ku gaisa ba?
Ya faɗa bayan ya kore shurun namu gabaɗaya.
"Tsakanin ni da ita wa ya zo ya samu wani?
Na tambaye shi ina mai kallon shi da idananuwa da suka ƙanƙance.
"Ita ce "
Ya faɗa yana kaɗa kai, ni ban yi magana ba sai shi ne ya kalleta kafin ya ce" Ki gaishe ta mana."
Ta yi shuru taƙi mgana ni dai kaina na ƙasa ina wasa da gefeb hijabina da ya sani bai ɗauko mini ita ba. Ta zo har falo na tana yi mini Taƙama.
"Ba da ke nake mgana ba."
Na ji ya da ka mata tsawa.
"Ina yini."
Ta faɗa kamar dole. Ko da ya ke ai dolen ce ya saka ta.
"Ke kuma ki amsa tun da ta gaishe ki."
Ya faɗa muryansa a sama daga gani yau an taɓo zuciyar ƴan maza.
"Lafiya lau."
Nima na faɗa a tsume saboda ni ba gan amfanin wannan zaman ba tun da wacce ta yi laifin ba ta ji a karan kanta ta yi nadamar abin da ta yi ba.
"Hakan da kuka nuna shi ne ya ƙara tabbatar mini akwai wani abu da ya faru a tsakanin ku wanda kuka rufe ni ba ku gaya mini ba. Ban sani ba ba domin Kawu Abba ya kirani ya faɗa mini ba, sannan Maman Farko ma ta kira ni ta ce na tara ku kun samu yar hatsaniya ranar a gidan Bahijja amma cikin ku a ka rasa me faɗa mini wani abu ya faru? Me ya sa haka?
Dukkan mu muka yi shuru. Ni sai da ya faɗa sannan na gano in da ya fara samun labari. Wato Marwa ce ta sanar ma da mijinta shi kuma ya kira Yallaɓai ya faɗa masa. Sai Maman farko da ta yi masa mgana ashe ita ma mara kunyar ba ta faɗa masa ba.
"Daku fa na ke mgana?
"Me ya sa ba ku faɗa mini ba?
Ya faɗa yana ɗan sausaauta fushinsa saboda ya yi ƙasa da muryan sa.
"Kasan daman ni ba halina ba ne na tare ka da mganar an yi kaza an yi kaza. Ballatana matarka daman ta ce ni ce ke kai ta gaba a wajen ka."
"Wannan ba Hujja ba ne. Ke ce babba bai kamata ki same ni ki faɗa mini wani abu ya faru ba?
Ba na so mganar ta yi tsayi ya sa na ce" Ka yi haƙuri na yi kuskure."
"Gaskiya ban ji daɗi ba. A ce sama da kwanaki ban san wani abu ya faru da matana ba sai wasu ne za su kirani suna faɗa mini ? Kun yi mini adalci kenan?
"Ka yi haƙuri."
Na sake faɗa ita hajiyar tana zaune tana karkaɗa kafa ba ta yi mgana ba.
"Ya wuce. Amma kar a ƙara irin haka ba na so. Duk abin da zai faru da ya wuce ku biyu wasu suka sani to nima ya kamata na sani ɗin"
"In sha Allahu."
Na faɗa ina muskutawa domin na gaji da zama duk na takura.
"Me ya faru ne a tsakanin ku da a ka ce kun yi sa'in sa a gaban mutane? Yaushe kuka fara sa'in sa a tsakanin ku ni ban sani ba?
Tambayar gabaɗayan mu ya yi mana. Amma ni ban ce komai ba ita kuma sai ta fara faɗin" Ai na ɗauka ka san duk abin da ya faru."
"Na sani zan zo in tara ku ina tambayar ku?
Ya faɗa a ɗan fusace ganin ya harzuƙa ya sa ta fara mgana a ƙoƙarinta na ta juya mganar tun da ta fara faɗin wai na ce na yi mata mgana ta yi banza da ita. Ita ba ta ji ba ne amma shi kenan na fara faɗa ina faɗin ta ji da gangan ne.
"Sadiya"
Ya katseta da kiran sunana sai na ɗago kaina ina amsawa.
"Na'am"
"Ki yi mini bayanin abin da ya faru daga farko."
Na buɗe baki zan yi mgana ta tare ni da cewa" Ni ba ka yarda da ni ba sai ita kenan?
"E. Ai ita na fara sanin kafin ke. Saboda haka ita zan fara ba ma Amincina kafin na baki "
Sai ta yi shuru bayan ta koma ta haɗe rai tana faɗin.
"To ai shike nan."
Ni dai ban bi ta kanta ba na yi masa bayanin duk abin da ya faru tun daga farko. Ban ɓoye masa komai ba har mganganun da na gaya mata da wanda su Munnira suka faɗa mata duka na faɗa masa na ƙarishe da cewa" Na yi ƙoƙarin na danne zuciyata amma na kasa. Saboda na ga ta na ta nuna bambamci tsakanin su Khalipa da su Jidda. In su ta ce farar haihuwa ne su kuma su Jidda ɓakar haihuwa take son ta kira su? Ta fada mganar nan ba sau ɗaya ba kuma sau biyu ba. Shi ya sa na tanka mata har ta kai mu ga sa'in sa"
Sai ta taso mini tana faɗin" Ni yaushe na ce su baƙar haihuwan? Ni fa ba haka nake nufi ba. Munnira ce ta ce wai ina bakin ciki da kin samu ciki ni ko na