Showing 150001 words to 153000 words out of 163126 words

Chapter 51 - TURKEN GIDA BOOK 3 COMPLETE BY JANAFTY.txt

Janafty   

18 Dec 2025

1077

da na yi dariya.

"Na zama abin dariya ne?

Ya tambaya a daƙune ganin ya ji haushi ya sa na ce" Ni tsarin ne ya ba ni dariya wai ranar girkin ki da key ɗin turaka ki je ki gyara in kin fita ki rufe"
Shima sai da ya yi dariya  kafin ya ce" Maganin ƙorafi na yi. Kowa da turakanta magana ta ƙare."
To ni dai ko rawan jiki ban yi ba tun asali na tsani turakan miji wallahi, Shi ke nan Yallaɓai ya fara buɗa jiki in kina da girki sai dai ki bi shi har dining ya saka a bangaren na shi duniya sabuwa. Ni fa ranar girkina mantawa na yi na yi barci a bangarena da safe na tuna tsarin har abinci a can za ki haɗa masa ke fa can za ko tare sai kin fita girki ni ko na ce ba zan iya ba ya'yana fa. Yallaɓai ya ce to na yi ta kwana a bangarem nawa shi dai ya gama bin kowacce daƙinta tana yi masa yanga.

Ina gani Rabi'atu da Gimbiya ana gogawa. In suna da turaka aka kasa zaune aka tsaye. Rabi'atu in ranar ta ce ƙamshi turare har haraba. Ita da Salima kanwar Antyn tasu su zage a yi ta girke-girke. A sauya zanin gado a yi wannan a yi wannan haka itama Gimbiya sai suka koma suna gasa shi ko Yallaɓai na jin daɗi sun zaɓi dakunan su ni na karshe suka bar mini, na san dai in dai ranar girkina ne da safe zan je na gyara ko na saka Baby  ta gyara na kuma shiga ɗakin na gyara na wanke tiolet a bangarena na ke yi abinci na kwasa na je na jera masa bana yin wannan rawan jikin na su to Allah na tuba wani kuma dare ne jemage  bai gani ba  ai sai daran mutuwarsa? In muka kwana da asuba nake gudawa bangarena sai dai in zai fita ya biyo ni ranar har ce mini ya yi in bana son  kwanan nan ne na faɗa masa.

"Aa kawai dai ban saba ba ne wallahi ina jin wani iri."

Wani kallo ya yi mini kafin ya ce" Gwara ma ki saba malama turaka yanzu kika fara zuwa."
Shuru kawai na yi, ni bai san ban wani damu ba ta kaina na ke yi, duk da wannan rabawan da ya yi bai hana an samu matsala ba Gimbiya ta ce Rabi'atu tana ɓata kitchen da falo ba ta gyarawa haka take fita tun da can take girki, saboda da daga Rabi'atu sai ni ne daga baya abin ya birkice ni na dawo farko, sai Rabi'atu sai Gimbiya, rigima sosai sai da ya tsawarta musu da cewa zai kori kowa a turakan na shi sannan aka zauna lafiya bayan an yace kowcce ta zo ta ɓata waje ta gyara kafin ta fita ni ina gefe ban shiga ba ina ruwana na yi magana ya ce ina yi masa shissshigi. Na koma gefe na zama yar kallo tsakanin Rabi'atu da Gimbiya ne suke ƙwama film acikin gidan nan wani abun ma kamar ka yi ta dariya wani abun kuma hauahi ka ji kamar ka yi ta dukan su.

Cikin Rabi'atu har ya fito wata biyar amma ya yi girma sosai. Har ni kaina ina mamaki, sai da ta yi scan Yallabai ya zo bakin shi kamar  zai kai kunne yana faɗa mini an ce yan biyu ne a cikin Rabi'atu mace da namiji. Sai a lokacin ya ke faɗa mini wai maman Rabi'atu yan biyu ne namijinta ya rasu ne. Labarin yan biyu Rabi'atu za ta haifa kusfa kusfa Yallaɓai ya kai labarin nan da man fa yana da shegen surutu da faɗi ba a tambayeka ba. Gimbiya ko ta ce ya dai bar murna domin likita ba Allah ba ne, shi ko ina ruwan shi yana ta shirin haihuwa kamar an ce gobe ne ballanta yanzu da kuɗi suke huda shi ai komai ma zai yi.
Haka nan muke zaune muna gungura rayuwar mu, ba a sati Gimbiya da Rabi'atu ba su yi tsiya ba, kuma duk fa kan turaka da miji, ni wallahi har na gaji da baa su haƙuri na saka musu ido, kuma in dai aka yi sai Gimbiya ta zama mara gaskiya saboda ta cika ƙorafi da mgana ita kuma Rabi'atu wayau da bariki da haka take cutar da ita ba ta sani. Ni dai ba mai yi da ni Yallaɓan ma kan shi isata yake yi na tattara shi na bar musu ranar har mgana ya kwaɓa mini wai ya fahimci na koma gefe yanzu na yaye shi kamar ba mijina ba, ba na damuwa da al'amuran shi.

"Ba haka ba ne. Gani na yi bayan ni kana da biyu irina masu kula da kai."

Hararata ya yi kafin ya ce" Wato ina da biyu! Ai ko goma ne ina nan a matsayin mijin ki kuma dole a ce ma mijin iya Baba."

"Dole ne wannan"

Na faɗa ina masa dariya ganin ya shaƙa sai kawai ya jinjina kai yana faɗin"Na gano ki wato kin gama cin moriyar gangan za ki yada ƙwaron ta ko?
Dariya har ina faɗowa daga kan kujera.
"To wallahi ba ki isa ba."
Yallaɓai da karfi hali shi wai a dole ban shiga ana kishin sa da ni ba a raina na ce ba kuma zan tusa kaina ba, ai ni tun da na yi karatun namiji na daina ta yar da hankalina a kan shi.
Ya gaji da mitan shi ya haƙura domin ni kam ta kaina na ke yi, haƙkin shi dai ina ba shi ina iya bakin kokarina amma ba na rawan jiki da na ƙafa a kan shi. Na gama yin wannan tun a baya yanzu duk abin ma ya fita kaina. To jiya ai ba yau ba.

Siyayyya kayan haihuwa komai biyu aka siya dangin Yallaɓai kowa uwar biyu yake kiran Rabi'atu  da shi har Nene fa in ta kira waya sai ta ce ina uwar biyu? Na ce lalle duniya juyi juyi yanzu uwar biyu ce a layi ba mai farar haihuwa ba. Cikin Rabi'atu na wata bakwai ya yi ƙasa ga shi ya girma yana rinjayan ta, ba ta aiki komai da man daga kwanciya sai in za ta shiga makaranta ya ma hana ta driving shi ya ke kaita ko Sadi, Salima na nan tare da ita tana kula da ita amma da wannan ƙaton ciki ba ta fasa zuwa turaka ba tana ganin ƙya shin ta haƙura har sai ta haihuwa na ce yar wahala kawai in dai namiji ne ke ce a baya ba shi ba.  Danginta sun yi maganar a al'adansu gida za ta koma ta haihu megidan ya ce bai amince ba da kan shi ya zo yana faɗa mini na ce Allah ya kyauta ban san yadda suka ƙare ba daga baya ya ce mini in ta haihu an yi suna za ta je can Maiduguri ta yi wanka tun da sun matsa a raina na ce to ni ina ruwana? In na yi magana ya ce ina yi masa shisshigi ni dai iyakata Allah ya kyauta da Allah ya raba lafiya.

Ciki na kai wata tara ta daina fita ko'ina saboda ta yi nauyi ba sai an faɗa maka ba kana ganinta sai ka ce amma dai yan biyu ne acikin nan ko? Saboda girman shi ya yi yawa gaskiya Rabi'atu ta zama ɓukekiya ciki ya ma yar da ita babban mace. Edd ɗinta bai gama cika da kwana goma ba aka yi mata aiki ta haihu a wani daran jumma'a.  Da ya kama 13 Nov. 2023.
Ni Yallaɓai ya taso ina barci lokacin da ta fara naguda da man cikinta na shiga wata tana ya tara mu ni da Gimbiya ya ce zai riƙa kwana a bangaeen Rabi'atu saboda cikinta ya shiga watan haihuwan shi, ni dai ko a jikina na ce Allah ya ba da sa'a. Gimbiya ce ta ɗan nuna ba ta yadda ba ya shi ba yardanta yake bukata ba shi ya sa ba ma amfanin mganar tun da abin da ya  yi niyya ba zai fasa ba.

Ta kasa haihuwa da kanta sai da aka yi mata C.S an fito da jarirai biyu mace da namiji. Kwana muka yi zaume a asibitin nan ni da Yallabai da Salima sai da safe aka fito da ita sannan ya kikkira jama'a ya sanar da su. Da safen na koma gida ni na ke ma faɗa ma Gimbiya da yara Rabi'atu ta sauka an samu yan biyu. Su Baby suna ta murna, Sai da huta can da yamma na koma asibitin Gimbiya ta ce mini sai gobe za ta je shago za ta leka.
Ko da na je asibiti ta cika makil da dangin Rabi'atu da na Yallaɓai su Anty Bahijja  ana bakin gadon mejogo ana ta yi ma jarirai hotuna. Faɗi take yi an yi haihuwan da ba a taba yi a gidan Tafida ba haka ta yi posting ma a status. Shi kan shi angon ƙarnin ya kasa sukuni ina jin all contact ya yi wajen tura sakon an yi masa haihuwa saboda yadda yake yini amsa wayoyin yan barka.
Washegari tare muka koma da Gimbiya da yamma da yara ai ko ta sha mamakin ganin su Anty Maimuna ana ta rawan ƙafa a gabanta ma sun sake faɗa an yi ma Tafida haihuwan da ba a taɓa yi masa ba ta cika ta yi fam har tana ba su amsa da cewa sai dai a kira su da ƙannen su Khalipa Anty Maimuna ta ce ta yi mata rashin kunya ba aure gare ta ba ta san ita kanwarta ce dukan tsiya za ta yi mata suka bar Gimbiya da tura baki tana ƙwalla ni dai ban tofa ba amma da man na san wata rana itama za ta ji irin abin da na ke ji a can baya.

Kwanan Rabi'atu shidda a asibiti aka sallamota suka dawo gida. Yayenta biyu sun taho daga Maiduguri da kanwar babansu Yakumbo ita za ta zauna da ita har bayan suna. Gida fa sai kamshin masu jego, an shirya suna gagarumi tun da haihuwa ce da ba a taɓa yi ba. Kuma mun ga haka mukan mu kowaccen mu 100k Yallaɓai ya ba mu ni da Gimbiya na fitar kayan suna. Jidda ma ta zo gida lokacin ai dole ta zo Yallaɓai fa haka ya dinga kiranta wai ta zo gida ta ga k'annenta yan biyu. Kuma yara sun ci sunan Sulaiman da Aisha. Ya cika alƙawari ya yi ma Alhajinmu takwara. Alhajinmu ko har gida ya taho barka ya kuma turo Gwaggo. Tun da an yi ma ubana takwara ai dole na ware kudi na yi hidima cikin kuɗin da ya ba ni ne na siya ma yaran riga da pampers uwar kuma atamfa na yi mata. Gimbiya dai kayan jarirai kawai ta yi ni kuma ba ni da da man zillewa Yallabai ya gama yaɗa ma Duniya Alhajinmu ya yi ma takwara shi ma can Alhajimmu ya gama yaɗawa shi ya sa kaf yan  gidanmu sai da suka zo barka na nesa su Amina suka kira waya.

  Sa guda Yallaɓai ya gada da raguna biyu, shagalin suna abinci ma daga reataurant aka dafo shi. An yi kayan rabo su robobi jaka memo da hotunan yara, Jidda dai ta yi kayan fulawa su cake da donut uban kuma ya ba da kuɗi ta yi har da cake, Rabi'atu kuma ta shiga ta fita da kayan alfarma. Ni dai kala biyu na saka da man ina da su Gimbiya ko da man tana da sutura ina tunanin ba ta yi ma sabon ɗinki ba. Yan uwansu na Maiduguri ba su zo da yawa ba gaskiya saboda nisa sai dai dangin Yallaɓai ne suka cika gidan har da mai kiɗan kwarya su Halima suka kira suka cashe, wata zabiya cikin masu kiɗan ƙwarya tana waƙe mai jego.

"Ina mai jegon ta ke ne? Rabi'atul badawiyya farar mace alkyabban mata. Farar mace fitilar gida. Amaryan Yusuf mai yan dubu dubu kin iya haihuwa da kika tashi biyu kika haifa ki shigo fili ki taka domin yau ranar ki ce"

Anty Maimuna ta fito da maijego  suna ta mata barin kuɗi sai ga Yallaɓai ya zo gidan zabiya na ganin shi hau yi masa kirari.

"Ga ni ga Alhajin Naira. Alhaji yusuf angon Rabi'atu mijin fara baban farare. Mijin mai kyau daga Maiguduri, uban biyu kake dole dai a ce da mijin iya Baba."

Nan fa Alhajin naira ya zaro bandir ɗin yan dubu dubu yana ta ɓari waje ya ruɗe da murna da ihu. An yi hotuna mai hoto kam ya haska ya fi kala ɗari, mu dai muna gefe muna mirmishi in ka yi baya ace kana bakinciki Gimbiya tana bangarenta ma ba ta fito ba. Su Anty Bahijja sun kuma haɗa ma Rabi'an kayan suna ya kai atamfa goma ga kayan jarirai ga kuɗi, Mimisco kanta da ba ta kasar suna spain ita da megidanta super ta aiko Naja da shi da less mai tsada. Ana ta ɗagawa ana yabawa,  Baban biyu ma ai ya yi wasa da naira yana da shi yanzu komai ma zai yi ba ya ƙya shi.

An yi suna lafiya an gama an yo soye soye kuma duk sun ba mu domin lokacin ma da suka gama sai da suka kirani na ce su dibar ma mejego da mijinta sai na bangaren su da namu bangarem mu dai yan gida gabaɗaya suka dibar mana da yara na dangin Yallaɓai Gwammaja akai tare da yaji mai yawa da turaruka. Na Yallaɓai kam har naman sai da ya kai ma Alhajinmu da kan shi na sunan takwaran shi kuma Alhaji shima za a riƙa ce masa. Alhajinmu haka ya zaunar da ni da na je yana yi mini faɗan na zauna lafiya kar ya ji kar ya gani na zama silar tashin hankalin mijina ai ba ni da ta cewa. Yallaɓai ya gama kama Alhajinmu a hannu da makircin su na maza

Macen kuma Ayush za a riƙa kiranta. Tariq ya zo ya ga jarirai ya yi barka haka ma Kawu. Abokan aikin Yallabai duk sun zo barka shi ya sa sai bayan suna da wajen kwana goma Rabi'atu da y'anuwanta biyu da Yakumbo suka bi jirgi zuwa Maiduguri sauran kuma suka bi motar haya da kaya. Sun yi mana sallama da za su tafi muka rabu da faɗin Allah ya sa mu gana.

Tun da Rabi'atu ta tafi sai da ta yi wata biyu a gida  sannan Yallabai ya je ya kwana biyu suka dawo tare. Su Alhaji sun yi kiɓa ɓulɓul kamar Yumna tana ƙarama sai dai su farare ne irin su uwar su, bayan ta dawo kuma ta fara ɗan zaga gidajen dangin miji ga shi kuma da man karatunta ma ya tsaya na ji Yallaɓai na faɗin diparing za ta yi. Rabi'atu ta dawo da sarkan ƙafa na kwalliyar mata da hudun hanci Yallaɓai kuma ya ce ya yi mata kyau ta yi kiba ta ƙara yin kyau sannan ta dawo s da wata yarinya Zafira ɗiyar yayarta ce wata kila a wajenta za ta zauna megidan dai bai ce mana komai ba.

Satin da ta karɓi girki Yallaɓai kamar zai yi hauka saboda rawan ƙafa, har zuwa ya yi ya same ni wai tun da ta daɗe ba ta nan mai zai hana mu bata sati ɗaya na ce ni na bata sati biyu ma sai dai Gimbiya. Itama ban san Aljanun sukunin da suka shiga kanta ba ta ce su yi ma wata ba ta damu ba ina ga itama ta fara dawowa daga rakiyan Yallaɓan ne shi ya sa aiko ya ji daɗi suka yivta gwangwazan amarci, daɗin da ya ji ne a watan ya sauya ma Gimbiya sabuwar mota balle ma mun shiga sabuwar shekaran 2024 harkoki suna ta budewa. Yallaɓai yanzu sai godiya ya samu kwangila ginin wani kamfani a zaria zai je ya yi kwana biyu ba kwana kwana ya ce Rabi'atu ta raka shi muka ce Allah ya tsare baban biyu da uwar biyu sun fi kwana huɗu sannan suka dawo Jidda ta ce sun kawo mata ziyara ita yanzu ajin ta uku a Jami'a Baby ce ke SS3 Yumna da Ammar tuni an saka su a makaranta.

Watan su Ayush shidda Gimbiya ta fara laulayi da azumin watan ramadana ashe ciki ne. Bawan Allah ya yi ta murna domin Yallaɓai na son yara a rayuwan shi. Nima yana ta mini dan biki wai ban gama sai na ƙara ko ɗaya ne, ba ni da sanin gaibu amma sai na ke jin kamar na gama haihuwa tun daga kan Yumna. Itama Gimbiya cikin na ba ta wahala kuma tabbas itama ya kula da ita amma fa uwar biyu da biyunta dabam suke, su ke shan sharafinsu na ɗauka son da yake yi ma su Khalipa na daban ne sai da biyu suka zo na gane su Khalipa ba su ga komai ba in dai gata ne.



*Janafty**Ƙarshe*

Yau ta kama asabar ɗin karshen mako ne tun bayan da na idar da sallar asuba na koma barci kamar ƴar maye, sakamakon a gajiye na ke, wancan satin muka yi bikin yar gidan Ya Aina ƙanwar Marwa ta biyu, tun da satin bikin ya kama ba mu huta ba muna ta zirga zirga da shirye-shirye, sannan Amarya Katsina muka kaita ni da Ma'u da Rahila muka je, bayan mun dawo kuma aka yi mana rasuwa a Yashe ƙanin Muntarin Rahila ne ya rasu magidanci kwanan mu uku acan sai jiya da daddare muka dawo, na kuma dawo gidan na iske Yallaɓai baya nan yana Abuja kan wani project da man mun yi mgana a waya ya ce mini sai yau asabar yake saka ran dawowa.

Barcin gajiya na ke so na yi shi ya sa ma da safe da Baby ta ce za su je Gwammaja su yini na ce ta tattara yaran su tafi gabadaya. Yan biyu kaɗai aka bari wajen uwarsu, Gimbiya kuma ba ta fita kwana biyu megidan ke faɗa mini ta yi ta fama da zazzaɓi sannan itama da ta kira ni ta ƙara yi mini gaisuwa na ji muryanta shake nan take ce mini ba ta da lafiya mura da zazzabi. Jiyan dai da na dawo sun shigo ita da Rabi'atun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login