Showing 6001 words to 9000 words out of 13874 words
Chapter 3 - Subul Da Baka Book 3 Complete by Zainab Dahiru Wowo.txt
Ya
miqo min littattafan kusan guda 20, a sama
wani sabon littafin mu2niyar ne, wato xeedee
wai shi 'INA XA MU JE?' daga jin sunan littafin
nasan dole ya yi dadi. Na yi murmushi "na
gode qwarai". "ga kuma hausa films xo in
koya miki hada kayan kallon yadda xa ki ringa
sauyawa daga DVD xuwa satelite wataqila ba
xa ki iya gane connection din ba duk da a
hade suke ko da remote sai ki sauya". Nace
"to". Tare da matsawa cikin doki da murna,
saboda gaskiya xaman kadaici ya ishe ni kam.
"abin ma ba wuya".
Na fada ina yar dariya. Ya yi murmushi. Gare
ki mai saurin fahimta ba...... Akwai sairan
abinci? Wallahi yunwa nake ji. Eh na dafa
wancan babu na ga ba ku rage komai ba.
Yauwa bari na watsa ruwa, hada min kafin na
fito Na shirya masa hadadden farfesun 'yan
ciki da fried taliya, sai kemon kuskus mai
madara da kwakwa a ciki. Ya kwashi girkin
nan da kyau, da ma kadan na yi daidai ni da
shi, ya cinye nasa duka. Na yi yar dariya tare
da kallon empty kwanonin da farantin, sai ya
kyalkyace da dariya. Me kike son cewa? Na
kwashe kawai na wuce kicin. Ya ci gaba da
cewa. Ko fiddo maganarki yarinya, so kike
kice ina da ci ko? Kin manta garinku kenan
lokacin da kike ba ji abinci halan? Daren ranar
mun yi hira da kallon wani fim na Hausa mai
ban dariya na dan Ibro. Washegari kuwa
tunda ya fita da safe sai yamma ya dawo, sai
ga shi da uwar tsaraba kayan daddawa,
kuka,kubewa sauran tarkace wai in ji Inna. Na
yi ta murna, tamkar Inna ce gabana. Goma na
safen washegari ya bar gari da alkawarin bai
wuce sati daya ko biyu. Nanji dadin tafiyarsa
saboda na sami damar sakewa in yi karatun
littattafan da ya sawo mini da fina finai.
Maimartaba ya bada kayan itatuwa kwando
kwando aka kawo tare da dumbin godiyar
dawainiyar da ake da shi. Kullum idan Yarima
bai kirani sau hudu biyar ba, ya kira ni sau
uku karanci. Kamar daga sama ranar wata
asabar, sai ga mahaifiyarsa da wasu barorinta
guda biyu. Na ji dadin zuwanta sosai, saboda
itace wadda ta fara kawo m8n ziyara daga
bangarensa. Na zubo mata abonci dankayan
makulashe, abin mamaki ta ci komai tana yi
tana mini nasihar na rike mijina, kuma na
dage da addu'a. Da za ta tafi na zubo mata
dambun naman kaji cikin wata katuwar
samira, sannan na kunso mata snack na ba
daya daga cikin barorin na ce ta rike mata. Ta
dinga yi min addu'a sannan ta tafi. Kwanan
Yarima goma da tafiya ya yo mini waya ga shi
nan zai hau jirgi yau zai dawo. Nan da nan na
fara shirye shiryen tarbarsa. Ga mamakina har
kusan karfe biyun dare ban yi bacci ba ina
sauraron zuwansa, amma shiru! Na kira
wayarsa sau wajen uku a kashe, hankalina yayi
matukar tashi. Baccin da ban sami yinsa ba
kenan har garin Allah ya waye.
Da safen ma har kusan karfe sha biyu ba wani
labari. Haka na ci gaba da aiki kamar wadda
kwai ya fashewa a ciki. Ina cikin harhada
kayan abincin maimartaba na jiyo alamun
budewar kofa, da hanzari na fito. Ya shigo a
hargitse kamar ba shi ba, gabana ya fadi,
kada dai ace maimartaba ya rasu? Ya kamo
hannuna idanunsa jawur, muka zauna bisa
kujera. Humaira tare muka zo da Zarina,
kuma yau maimartaba zai koma fada. Na saki
ajiyar zuciya a hankali. To mene ne abin
damuwar a nan? Na fada a zuci. Ya karkace
kai kamar mai shirin yin kuka, ya ci gaba da
cewa. A dalilin kyautatawarki da abin da kike
aika masa tun zuwansa yanzu haka ya ce zai
zo a yi miki godiya, kuma har da Zarina yanzu
haka... Na dafe kirji tare da zaro ido ina
shirin yin magana muka jiyo bugun kofa. Da
sauri ya mike tare da lekawa, ya dawo da
gudu. Wallahi su ne! Take na ce Innalillahi
wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma laa sahlan
illa maa ja'aktahu salan, wa'anta tij'alik hazna
iza'shi'ta sahlan. Na je na bude ina kara
karanta adduo'in neman sauki a kan duk wani
tsanani a zuciyata. Su Umma ne a gaba kafin
wasu dattawan mata gudu biyu, sannan shi
maimartaba wasu manyan mutane hudu na
bin bayansa. Sannan dogarawa, a bakin kofa
dogarawan suka tsaya. Rakube nake jikin
oofa, ban da kyarma babu abin da nake yi
kaina kas. Kutumar uba! Aka biga wannan zagi
da karfi, a firgicr na dago kaina. Ganin
Gimbiya na yi kusa da ni da alama ita ce
karshe wajen shigowa. Munafuka! Algunguma!!
Kowa yayi cirko cirko tare da kura mata ido,
amma ban da Umma da ta sami kujera ta yi
zamanta. Da ma ke ce matar abokin Yarima
yar iska? Makircin da kuka hada ke nan ke da
uwarki? To wallahi ba ku isa ba, ina Yarima?
Na rantse da Allah yau sai ya sake ki..... Ke
wai lafiyarki kalau kuwa Zarina? Duk wannan
cin zarafin da kike wa yar mutane na mene
ne? Shin ko kin san dalillin zuwanmu wurinta
kuwa? Cikin dattawan matan nan daya ta
katse ta da fadin haka. Ta hankado keyata na yi
taga taga zan fadi,
kawai na ga mutum ya tare ni na fada jikinsa.
Da sauri na kalle shi sai kawai muka ga
maimartaba ya zauna a duke. Ganina jikin
Yarima ya kara harzuka Gimbiya, ta fara
zubda ruwan rashin mutunci ba tare da ta yi
la'akari da wadanda ke wurin ba, tana fada
wa dattawan kobji wace ce, saboda suna da
masaniya kan maimartaba ya haramta aurena
da Yarima ko bayan ransa. Sau biyu tana
kawo harin za ta dake ni yana tarewa, ni kuwa
banda kuka babu abin da nake yi, saboda
tashin hankali. Ni ba na Gimbiyar ya fi
damuna ba, irin hukuncin da maimartaba zai
yanke a kaina kawai na ke ji. Wuri ya
harmutse, fada tsakanin Yarima da Gimbiya
su kuma dattawan wasu na goyon bayan
Gimbiya su kuma dattawan wasu na goyon
bayan Gimbiya, wasu na nuna cewa ba ta
kyauta ba ta yi rashin kunya sosai, tunda ta
aibanta Yarima gaban iyayensa. Duk wannan
hargitsin su Momy da Maimartaba ba su ce
komai ba Ganin abin ya ki ci ya ki cinyewa yasa
maimartaba daka musu wata irin tsawa da
kowa da ya yi mamaki. Nan da nan kowa ya
na'abba. Wannan ai hauka ne! Ya fada,
sannan ya ci gaba da cewa. Ba ku da
bambanci da dabbobi, musamman kai. Ya
nuna Yarima. Gabana ya yi wani mummunan
faduwa, ya kira dansa DABBA ni kuma mai
zan koma. A matsayinka na namiji yausha
zaka biye wa mace musamman lokacin da
kishi ya turniki zuciyarta? To kowa ya zauna
zan yi magana biyu zuwa uku, amma kafin nan
zan fara da abin da ya kawo mu. Ya kalli
Yarima, Ya sunanta? Kansa duke ya ce,
Humaira. Humaira zo daga nan. Ya nuna min
kusa da shi daga kasa, tsoro ya kama ni
saboda na san kaina kawai zai sare da adda
shi ne sakamakona.
Ina kyarma na karasa har lokacin kukan nake.
Godiyar da na zo yi miki ba zan fasa ba. Na
gode, Allah ya yi miki albarka. Wane ne
mijinki kuma?.saboda har da wannan
tambayar na zo yi miki, domin kullum Yarima
ce min yake yi matar abokinsa. Wayyo duniya!
Wayyo Iñna! Wani sab9n kuka ya zo na ji
kamar na zura a guje. Ko ba kya iya magana?
Na ce wane ne mijinki? Wane ne fa banda
Yarima. Gimbiya ta fada a hasale daga inda ta
ke zaune. Cikin tsananin bacin rai maimartaba
ya kalle ta.. Kada ki yarda na gane ba ki da
da'a domin za mu bata, batawa mai tsanani.
Ta zumburi baki ta kauda kai tana gunguni,
abinda ya ba wa kowa mamaki. Ya kalle ni,
Humaira ko zan san wane ne mijinki?
Na dukar da kai ina wani irin kuka, da kyar na
iya furta. YARIMA NE! Amma don Allah ka yi
hakuri, wallahi ba laifina ba ne, ni ma ba da
son.......Dakata! Bari kukan kada ki sarke.
Yanayin yadda ya fadi maganar cikin tausayi
ya sa ni da Yarima saurin kallon juna. Ya mike
tsaye, sai kowa ma ya mike, ni ma dole na
mike saboda an bar ni ni kadai a zaune.
Sakamakon abin arzikin da kika yi kin na yafe
wa Yarima, kuma na aminta da aurenku ko
lahira wani yana cin arzikin wani, to shi ma ya
ci arzikinki, domin tunda ya yi auren farko ban
taba shan riwan gidansa ba sai a nan. Sai ka
tattara matanka ka hada su wuri guda, shi zai
hada kan iyalanka. Yana fadar haka ya yi
hanyar waje, saura kuma suka mara masa
baya.
Wani yayan Yarima ya banko mini harara
wacce ta sa dole na yi kasa da kaina. Karaf! A
kan idon Yarima, ashe hankalinsa na gurinmu
da ma. Gimbiya ta fara zazzaga masifa, tana
fadar maganganu har tana ikirarin plan ne aka
shirya da ma don a ci mutuncinta. Yan baya
suka ji abin da ta ke fada, amma shi
maimartaba tuni ya fice, har ya kai a mota. Ta
yunkura tare da shako wuyana ta makare ni
jikin bango, Yarima ya taso lokacin har ta
kwada min abin fulawa ta fasa min goshi. Da
kyara ya kwace ni tana faman dukana da
harbi, ni kuwa sai kuka nake. Hayaniyarta ta
dawo da su Momy, da kyar suka fidda Zarina
gidan tana ta hauka. Jikina sai rawa yake yi
saboda tsoro duk na firgice sai bari nake. Da
kansa ya wanke min jinin ya sa auduga ya
daure da bandeji.
Wayarsa ta fara kara ya dauka tun bayan da
ya yi sallama, ban da kalmar TO babu abinda
yake fada har ya ajiye. Ya kalle ni asanyaye.
Maimartaba ne ya ce kar k8 sake ki kara
kwana nan gidan, na maida ki can gidana inda
Zarina ta ke ku..... Wallahi Kano zan tafi, ba ni
kara kwana nan garin, ban iya masifar
Gimbiya ko kadan nan din ma kana ganin ga
manya ba ta j8 kunyar raunata ni ba, ina ga
nan ware daga ni sai ita? Aure ne na yi na
Allah, amma ba zan kuma ba. Idan ita ba ta
da hankali ke ma....... Kwarai ni ma haukan
nake a kan komawa gidanka kam, kai auren
gaba daya ke bana yi, ko dole ne? Na fashe
da kuka. Da ma tun farko ni wannan masifar
nake gudy wallahu. Ya langwabe kai. Allah ya
baki hakuri.
Na hayyako masa. Eh da man duk wanda ka ji
ana ba hakuri ai an gama cutarsa. Haba
Humaira 8na hankalin ki ne yau? Daga turu na
fito karewar hauka. Na mike ina faman hada
kaya a jaka. Ya karaso murya a raunane ya ce.
Don Allah ki yi hakuri, mu gode wa Allah da
matsalar ta tsaya gurin Zarina kadai, kin ga
alherinki ne ya sanya mahaifina ya yafe mini
kan rashin bin maganarsa, shu ya sa aka ce
YADA ALHERI BAYA ka tsince shi gaba.
Wallahi.na tabbatar da lallai ya ji dadi sosai a
kan abinda kika aikata, domin ni ina tunanin
fushi da wulakanci wanda zan fuskanta a
lokacin da ya gano abin da nake boyewa, don
ko mahaifiyata ba za ta tsira ba. Shi ya sa na
nace wa aurenki don na san ke alheri ce a
wurina. Wallahi ba ki ji yadda hankalina ya
kwanta ba..... Dole ka sami kwanciyar hankali
mana, ni tunda ka ti silar tada nawa.
Xaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Subul da baka 3 page 2
Posted by ANaM Dorayi on 05:17 PM, 21-May-15
Under: Subul da Baka
Ya yi murmushi,
"ya xa a yi na yi silar tada hankalinki?" "ban
sani ba". Na fada lokacin da nake qoqarin
rufe jakar. "Allah ya ba ki haquri, kin ga
maimartaba ya yaba hankalinki kada ki yi
abinda xai sanya ke ma ki fita ransa kamar
xarina". "dole kuwa in yi, domin na tsira da
raina da lafiata.. A gabanka ta fasa min jiki, to
ina ga ba ka nan?". "nima ai bayan idonta
gashi kina mini tsiwa mai ya hana ki rama? Ko
kin san xarina ta gane kin tsorata da ita? To
wallahi ni ba xan tare miki fada ba, domin
akwai lokacin da dole ba na nan kinga kuwa
dole ta ringa ba ki wahala, amma idan ta ga
cewar ke din ba ki tsoronta, to lallai xa ta
shafa miki lafia, don Xarina ba ta fi qarfinki ba ni
a ganina.
Abin mamaki kishiya...". "ka ga malam ni ba
fitina na xo yi ba...". "nima bana son ki yi
fitinar, amma ya kamata ki amsar wa kanki
'yanci, ki nuna ke ma fa MATA ce ba baiwa
ba. Maganar gida kuma wallahi babu inda xa
ki tafi yau a gidana xa ki kwana ke da
axara'ilunki xarina ta qarasa ki". Na fashe da
kuka, sai kawai ya shige bandaki. ***** *****
*****Tashin hankali ba a sa masa rana,
kwana 2 da komawata gidan aka kawo mini
dattawa guda 2 wadanda xa su ringa tayani
aiki, sabanin gimbiya da nata yara-yara ne
majiya qarfi, kuma aqalla xa su kai su 9 ko 10.
Qaton gida ne da babban 'gate' sannan
kowace bangarenta guda. Yau xan amshi girki
don haka magariba na
yi na fara kimtse-kimtse, 2n 6:pm na sallami
su dagwayye ana gama sallar isha ya shigo.
Na kawo masa abinci ya kalleni. "yo ina en
aikin?". Ba tare da na yarda mun hada ido ba
na ce, "sun tafi sashensu na sallame su".
Murmushi ya yi, "to dauko abincin mu tafi
sashena". Gabana ya fadi, amma ban yarda ya
fahimta ba. A falonshi muka xauna mai tattare
da kayan more rayuwa, kujerun kansu sun ishi
mu2m kallo, ban iya tsayuwa fasalta falon
amma ina iya cewa komai ya ji na more
rayuwa, hmmm! Jin dadi sabo na fada a xuci.
(kun ji mu2niyarku an kile an fara 2nanin jin
dadi). Allah sarki su inna qwalla suka kwanta
suka kwanta a idona da na tuno inda na baro
su. Na duqa xan fara xuba masa abincin
kenan naji an ingijeni nayi baya- baya na fada
qasa da qarfi, kafin na yi wani motsi ta biyo
ni da qafa tana harbi, a rude ya taso tare
da ture ta wuri guda ita ma. "ke wace irin
dabba marar 2nani ce fareeda?". "wallahi
wannan munafukar sai na hallakata a
gidannan, don uban...". fas! fas!! tasst!!! ya
wanka mata kyawawan mari guda 3 a jere.
"kar ki dauke ni sakarai, shashasha mana, ke
me ya sa kike da fitina da rashin son xaman
lafia ne? ko don kin ga ina tausaya miki
saboda abinda ke jikinki?". ta harxuqo masa
kamar ta rama marin da ya yi mata. "mene
kai din in ba sakarai shashashan ba?". ya
qara wanka mata wani marin guda 2 qwarara,
ya juya xai dauko kebul (cable) ta ko dauki
wani abin fulawa ta kwada min a goshi. "bari
in kashe ta don ubanta in ga abin da xa ka
yi".
Tana qoqarin qara rusa min shi ya riqe da
sauri. 2ni jini ya balle yana son dauko
tsumma yana tsoron kada ta qara min wani
dukan. Ya fige ta ya 2ra waje kafin ya rufe
qofa ta banko da qarfi. Ganin idan ya biye
mata ni kuma xan rasa jini da yawa ya sanya
shi qyale ta, ya nufo gurina da sauri. Cak! Ya
dauke ni xuwa bandaki sai kyarma nake ina
kuka, tsoro da fargaba sun fi yawa a gabana.
Muka fito, ya janyo wani akwati sai ga kayan
dressing ya ci gaba da gyarawa. Ta xo kanmu,
"aikin banxa aikin wofi, an asirce ka, an
magance ka er talakaka ke wa wannan
kyarmar kuma don ubanki yau na ga yadda xa
ki kwana dakinnan. Na rantse da Allah ko
gawarki ba a yi mata wanka nan dakin domin
ba na hada daki da ke, banxa talaka". Ya
kalleta a wulaqance saboda yau da fareeda
ba ta da ciki, da Allah kadai ya san illar da
xai mata, ya ce "ga ki nan talaka wacce ba
gaji arxiki ba, maimartaba da ya tilasta ya sa
na aure ki Yau saboda munanan dabi'unki na
tsiya
yana dana sanin aurena da ke, 'yar talakar da
ki ke qyama ki ka raina kuma a yau ita ake
alfahari da ita a matsayin suruka". Bai rufe
baki ba ta hargitso masa qa2war talabijin da
ke manne a bango, ta fado bisa sauran
tarkacen kallon da abubuwar glass ji kake
ratsatsatsa!!! Ya dauki waya kamar mahaukaci.
"hello sahabi kana ina? Don Allah idan kana
iya fitowa yi sauri ka xo gidana yanxu". Ni
kam ina can rakube jikin bango kaina kamar
ya bare, ga wata masassara da ta taso mini,
ko tashin hankali ne ya hana ya yi min allura,
ko ya bani magani? Oho! Shi ya fada ita ta
fada, da ya matsa kusa da ita ta nuno shi da
kwalbar glass ya
rasa inda xai billowa tashin hankalin, iyakar
qarshe ya kai. Sallamar sahabi ya sa duk suka
yi shiru daga ita har shi din "Subhanallahi,
innalillahi, Hameed mene haka ya faru? "mtsew!
Shigo idanunka su gane maka
barna da asarar da yarinyar nan tayi min, duk
goshin er mutane, marainiyar Allah...".
"shegiya dai! Domin mun dade da sanin
shegiya ce ba ubanta ya mutu ba..." "haba
gimbiya don...". "yi min shiru munafuki, ina ce
da kai aka hada baki duk abin da aka qulla.
Ni xa a yi wa makirci? ayi wa plan? xa a
qirqira dafa abinci ana kaiwa sarki don
munafunci, wallahi yau sai dai ayi wacce xa a
yi". "Me fa xa a yi bayan na shirge ki kamar
jaka, don ba xan tausaya miki ba 2nda na ga
abin naki ya wuce 2nani...". "haba yarima har
sau nawa xan fada maka ka daina biye wa
mace?". "ka san Allah na dauka wa raina sai
dai yau na kwana prison, amma lallai gab na
ke da na lalata rayuwar wannan...". In taqaice
muku, haka muka kwana a tsaye ana abu guda
1, ko sallar asuba sai da yarima ya fara yo wa
sannan sahabi ya tafi gudun kada ta qara ji
min wani raunin. Suka dauke ni muka bar
gidan, amma sai da yarima ya tare ta sannan
sahabi ya fidda ni dakin, saboda yunquran da
take yi sai ta caka min gilashi a ciki. Iyakar
firgita da kaduwa nayi, 2n ina kuka har na
koma xare idanu, ni kadai na fige kamar
wacce tayi ciwon shekara. Gidan sahabi muka
je, na yi wanka na yi sallah, na nemi ciwon kai
da masassara na rasa, har qara kan da ya yi
min wani jummm! Allah ka raba bawa da
tashin hankali da fitina. Da qyar na sha rabin
kofin tea shi ma don Hafsat ta matsa min
matar sahabi. Ina kwallonta tana goge qwalla,
ta tausaya min. Xuwa can wajen 12 sai ga su
sun dawo. Ban san me suka tattauna ba, tayi
juyin duniya ta fita na qi fita, saboda sam
bana son ganin yarima, don a ganina shine
musabbabin haddasa min wannan fitinar, 2n
farko da bai dawo rayuwata ba kamar yadda
muka haqura da juna da farko, da hakan ba
ta faru a gare ni ba. Ganin ba ni da niyyar fita ya
sa ta ce, ya
shigo dakinta ya same ni. Baqin cikin
shigowarsa ya sanya ni kuka. Ya yi shiru kusan
mintuna aqalla 8-10, kafin ya fara magana
cikin sarqewar numfashi. "kiyi haquri humaira,
na san cewa ke ba mai son magana ba ce,
ballantana tashin hankali irin wannan, amma
komai ya xo qarshe, mai martaba ya amince
da na raba muku gida. Yanxu haka har ya
bamu wani a lowcost cikin estate din da ya yi.
Don haka ya sa kika ga mun dade sai da
muka kammala komai, yanxu haka ana can
ana sauran gyare- gyaren da ba a qarasa
ba". Ke dai da ke kara2 idan na tanka kin
tanka, ya matso kusa da ni, "ko sai xuwa dare
idan kin qara hutawa nan? Na ga can din ma
ba hayaniya, sannan babu aikin da xa ki yi,
saboda su malama dagwayye na can 2n
daxun". Ko motsi ban yi ba. Ya matso tare da
xama bakin gadon.
.....Farko da kuma kullum lallai tana kan
hanya, 2nda a duk lokacin da muka hadu sai
ta nemi xubda jinina. Ka sallame ni na tafi
gida don girman Allah, bana sha'awar xama
da kai ko da da