Showing 27001 words to 30000 words out of 38761 words

Chapter 10 - RABON KWADO Book 3 End By Nana BMB.txt

18 Jan 2025

2803

ko shakku"
Sam meenal tama rasa awani hali take ciki yanzu ko hawayen ta nemesu ta rasa kallon imam kawai takeyi shikuwa matsowa yakarasa ze rungumeta cikin wani irin firgici tayi baya tana masa wani kaskan tancen kallo, cikin sanyin jiki yatsaya yana girgiza mata kai harda magiya
" Kiyi hakuri 'yata kada kiyimin haka kutemaki ni don Allah keda mahaifiyar ki ku kadaine farin ciki na wlh"
" Allah yasawa kah! koda wasa ko a mafarki bazamu taba zama farin cikin kaba kada ka kuma kirana da 'yarka domin ni bansan kaba, bansan waye kaibah duk duniya banida mahaifin da yawuce daddy nah wanda yasan fadi tashi nah a rayuwa saboda haka kada ka kara danganta kanka da mahaifiyata don tafi karfin kah, kakuma tafi kabar mana gidanmu! domin kai ba alheri bane a gun kowa!" meenal takarashe maganar cikin kuka!


A lokacin kuma su muhammad suka dawo gidan kasan cewar motocin Abban su mimi tacike parking space dinne yasa basusamu damar shigowa da tasu motanba sosai suna dai hangen abinda yake faruwa bude kofan motan mujaheed yay zefita muhammad ya riko masa hannu yana girgiza masa, yana cewa." Fara kiran mimi muji abinda yake faruwa naga meenal tana kuka" dawowa yayi yazauna mujaheed din yakira mimin, tsaki kawai muhammad yay yace ba lallai sun fito da waya bama kawai muje don bazan iya jurewa bah ganin meenal tana wan nan kukan" kafin ya rufe baki kuwa an daga wayan sedai be tantance muryan wayeba yace." Wai meyake faruwane awaje? suwaye sukazo?"
Ba ah bashi amsa bah yaji an yanke wayan, bebi takan hakan bah suka fita a motan suka karasa inda kowa yayi dako dako a tsaye, mujaheed ne ya tsaya gefen mimi yana tambayar ta lpy? sedai kanta bashi amsa mahaifiyar zarah ta karaso gaban imam fuskarta babu alamun annurin rahama tasoma sauke masa maruka dukda haka be isheta bah seda ta cakumi kwalar rigar sa tana huci tasoma magana cikin fusata!
"Tabbas yau nakara yarda da cewar kai butulu ne bakin muna fiki macuci! namaka dare dole kayimin rana, dama ance kaji tsoron wanda kafiya temakawa dayawa, ashe har mata ce dakai harda 'yah saboda muna fiki ne kai daya sa aka kamaka bacemin kayi harkallar kudi bace ta hadaku ashe karya kakeyi" Abban su mimi lokaci da yakama imam yasanar dashi yasaki safiyya.


Mari lafiyayye shima imam ya sauke mata wanda yasata kara gigicewa takara shake masa wuyan riga tana cewa." Wlh yau imam taka takare a duniya sekayi nadamar abinda ka aikata min rayuwar ka ma a gidan yari zaka karasa ta"
Fitowan safiyya kenan domin ganin abinda yake faruwa sabida itace ta daga wayan mujaheed,tayi mummu nan gani, ganinta da imam yayi ne yasashi dena jin abinda maman zara take cewa ma kallon ta kawai yake,
Girgiza kai kawai daddy yay cikin takaici yaje yakama hannun ta suka shige ciki, tsaki Abbah yayi yaname cewa." Ay kuma shike nan tunda haka yafaru gara komai yazo karshe yau, hajiya kisake shi yanzu dai dole mushiga ciki a kashe wan nan kurar data taso sabida haka idan kuntafi kwacigaba da rigimar ku kome zakiyi masa kimasa"
Dakyar imam yakwaci wuyan rigarsa a hannun ta se faman haki yakeyi don ya shaku kam ba karya rankayawa akayi parlour kuma kowa ya hallara, ummi tana ganin imam tasoma sallal lami tana cewa." Haba tunda naga daddyn ku ya haye sama da safiyya nasan ba lpy bah ashe bala ei ke kuma tunkarar mu"
Dakatar da ita Abbah yayi kan tayi shiru kada takara cewa kala, haka kuwa tai gum da bakinta se uwar harara datake antaya masa haka muhammad kallon sa kawai yake, dakyar Abbah yashawo kan daddy ya fito da safiyya aka zauna gaba daya kuka kawai take tamkar numfashin ta ze fita, bayani daddy yamasa kan cewar shida safiyya yanzu shikenan har abada domin matar sace a yanzun harda yaransu ma, 'yar sace meenal gata nan sedai bashida da iko da ita sam seyanzun hassan da usain dasukaji wan nan batu sukasan ma abinda yake faruwa, saboda kululun daya tsayawa imam hawaye kawai yafara yanajin kamar yahadiye zuciya ya mutu jiyake makar yashake daddy,


" Macucin banza da wofi dole mana dama kayi hawaye, mummu nan kaddara ce nima tasa na aure kah amma kasani yau taka takare bayan sakina dazakayi zakaga abinda zanyi maka"
Sam bebi takan taba yamike ya tsugunna a gaban safiyya yanajin kamar ya hadiye zuciya yace." Safiyya kiyi hakuri ki gafarceni kaddarar rayuwar muce ahaka mutum baya taba gujewa kaddarar sa arayuwa" tunda yafara magana kukan nata ya tsananta nan danan numfashinta ya canza, dafe kanshi daddy kawai yayi don yasan za ayi haka dama kafin yagama tunani kuwa sejinta yayi ta fado jikinsa a sume! cikin kidi ma kuwa ya rarumeta yana jijjigata yana ambaton sunan ta,
bodyguards Abbah yakira yace suzo su fitar da imam daga gidan domin anyi anyi yafita sam yaki hankalinshi nakan safiyya, su hudu suka shigo kuwa suka cukwi kwiyeshi kamar kayan wanki sukayi waje da shi, maman zarah tamike taname cewa " kusamin shi a mota mutafi kai tsaye police station zamu tafi yau duk kudina dayacimin seya biyani kuma yasakeni inba hakaba kuwa sena daureka imam"


Dr bello daddy yakira a waya cikin gaggawa kuwa ya iso yaduba yanayin jikin safiyya hankalin kowa a tashe yake ba ita tafarka ba kuwa se wajan la asar tayi wani iri da ita dakyar ummi tabata tea ta amsa aka bata magun gunan ta tasha shine yasa tadanji dama dama bugun da zuciyan ta yake yadai daita yanzu,
9 tanayi nadare safiyya ta tubure musu tace a zo a mika meenal dakin mijin ta bazata kuma kwana a gidan suba se a dakin mijinta, tariga taji sauki ita saboda batada lpy baze yi wu ace za ah fasa kaita dakin tabah, Ya Allah! meenal koda tajee wan nan batu wani sabon shafin kuka tabude tanaji tana gani ummi tasata a gaba tayi wanka tafito tashirya ta tsaf tanata bazaza kamshi abinta, cikin zuciyan meenal lugude kawai take tsoro yana kara kamata da nauyin abin datake gani wai itace za ah mika gidan Ya muhammad a matsayin matar sa, a gaba suka sakata suna mata fadan tabi mijinta sauda kafa,seda suka gama aka kaita gurin daddy mah yay mata nasa nisiho hin masu ratsa zuciya hartaji zuciyan ta ta karaya sosai ta saduda saboda taga babu sarki se Allah wan nan al amarin haka yake,
Dukda ga gida ga gida hakan be hana su ummi shiga motaba meenal ta rike ta sosai tanata gunjin kukan ta gefensu mimi ce se nana gaban motar kuwa inty ce itada zara se mujaheed daya jasu zuwa gidan suna fita gateman ya bude musu gate suka shiga, seda suka tsaya sukayi addu o i tukunna a bakin kofa kuma ummi tace tashiga da kafar ta ta dama, gida nata tashin kamshi gana amarya kuma seya hade har cikin bed room suka kaita kowa yazauna abinsa anata bata baki har 10 ya wuce san nan ummi tasa akaiwa meenal wayau kowa yasilale a hankali suka tafi dama mujaheed yana ajesu yakoma, koda meenal ta farga da hakan kuwa da mugun gudu tayo hanyar parlour din sedai tamakaro gam taji kofan a rufe hakanne yasata zubewa a jikin kofan tacigaba da kuka,


To ango kuwa yana can yashirya abinsa yace babu katon daze rakashi dakin sa, koda mujaheed yaji haka tabe baki yayi yace." Nima naga 'yar kafarka tazomin rakiya" muhammad yay murmushi yace" kaika huta ay" yay gaba abinsa, jikin mimi sosai yayi sanyi tunda suka dawo gida take tunani tunda itace akan layi goce da wuri za ah dunguma a tafi bauchi itama akaita nata gidan, ita kuwa nana abinne ya hade mata biyu ga tunanin yousep dana auntien ta tanason sanin halin da take ciki,
11 muhammad yashiga gidan nasa yana bude kofan parlour yaji yabuge abu, hakanne yasashi zuro kai a hankali yaganta ta bingire tanata bacci, murmushi kawai yayi don yasan tunda aka fara shagalin bikin nan basu samu ishasshen bacci bah, ledojin hannun sa yaje yasaka a fridge, kana yadawo yadauke ta a kasan yaje ya shim fideta a makeken bed din, fuskanta kawai yazubawa idanu cike da shaukin so da kauna ahankali yaketa shafa gefen face dinta kasancewar baccin ta yayi nisa sam ko motsi batayi, mikewa yayi yakashe light din parlour yarufe ko ina san nan yadawo yashiga bathroom yadauro alwala yafito yasoma jero nafil fil yana me mika godiyar ga ubangiji daya cika masa wan nan buri nasa, sebayan ya idarne yasoma karatun Al kur'ani me girma seda yajima yana karatun tukunna yatashi yasoma cire kayan jikinsa dagashi se boxer ya haye bed din a hankali yasoma raba meenal da sutirar jikinta har ya rage daga ita se pant da bra ya manna ta da kirjinshi yaja musu bargo, dake shima gajiyar ke nukur kusar sa nan danan bacci yadauke sa,


To asuba ta gari amarya da ango.




TAKU A KULLUM NANA BMB


08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣ RABON KWADO....!!


BOOK 3


NA NANA BMB




GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{ Marubuta masu garkuwa da alkalami domin fadakar da al'ummah }




page 47 - 48


Tunda mimi ta tashi taketa kiran ummi a waya sam taki dagawa harta gaji tayi mata text akan pls kada sutafi tanason ganinta ko yaya ne kafin su tafi, nanma shiru babu amsa hakanne yasata kiran meenal tana kuwa dagawa tasa mata kuka har hankalin meenal yatashi, dakyar ta iya saita kukanta tace." Pls sister na rokeki ki kira ummi a waya tashigo part dinmu inason ganin ta kada sutafi sam taki picking call dina" ajiyan zuciya tasaki meenal tace." Insha Allah yanzu zata shigo kwantar da hankalinki,don yanzu muka gama waya da ya muhammad yace yanzu zasu taho" sake rikecewa mimi tayi takuma saka kuka tana cewa." i beg u sister ki kiramin ita yanzun"
" sister na meya sami voice dinkine bata fita sosai? sorry kinji kidena kuka kina dagamin hankali sosai" turo baki mimi tayi harda harara tana cewa." wan nan mugun yayan nakine mana jiya yahanani bacci san nan yau ya hanani zuwa inyi sallama dasu ummi" murmushi meenal tayi donta fahimci abinda take nufi tace." Kai sister Allah ya shiryeki ya mujaheed dinne mugu kawai saboda ya anshi hakkinsa" tsaki mimi tayi tace "wai hakki zakiga hakki yarinya nidai ki kiramin ita" murmushi meenal kawai tayi ta kashe wayan takirawo ummin bata daga ba seta kira auntie safiyya tashida mata abinda yake faruwa,murmushi kawai tai ta nufi bangaren nasu.


Tasan ummi kota wani hali bazata shigo bangaren 'yar tatabah yanzu, rarrashin ta tayi sosai takara kwantar mata da hankali takara gasata sosai a ruwa medan zafi ta lallabata tayi shiru sedai kuma ta makale ta taki saki tace ita su tafi tare tayiwa su ummi sallama, sam auntie safiyya taki yarda harseda tayi mata jan ido tukunna tana fa nuna mata aure fah tayi, jikinta asan yaye tasake ta tashige bed room tafada kan bed tasoma sabon wani kukan.
11 da wani abu suka kama hanyar kano, wajan la asar suka iso muhammad ko gidan be shigaba ya wuce nashi gidan, don zumudi kawai yake yaga iyalin nashi,
Farin cikine sosai ya lullubeshi kuwa cin karo dasu dayay a parlour sam basuma san ya shigoba saboda hankalinsu yana kan game din da suke bugawa kallonsu kawai yake yana zuba murmushi, hankalin meenal ne yafara kaiwa kanshi," Ya muhammad!" ta kirashi cikin tsananin farin ciki saboda ganinsa datayi ba tsammani da gudu ta mike tayi gunshi har tana takewa hassan yatsun kafarsa, tun kan takarasa ya tareta da kyakkyawar runguma yana sauke ajiyan heart, a kunne ya soma mata magana." My angel nayi missing dinki over jiya nayi bacci mara dadi" rintse idanun ta meenal tayi don seyanzun abinda yake wakana tsakanin su yadawo mata tasoma kokarin janye jikinta amma sam babu hali sabida rikon daya mata,

" Sannun ku da dawowa! babban yaya, ya hanya?" usain yana murmushi yamasa maganar ganin abindake wakana tsakanin sa da amaryar tasa, shikuwa hassan se tura baki yake don kuwa yaji zafin takun na meenal, murmushi muhammad yay yace." yawwa my brothers hope nasameku lpy"
" Nidai yanzu dawowar ka matarka sabida taganka tawa kafana mugun taku kilama se ankaini gurin gyara" cewar hassan kenan,
Sakinta muhammad yay yana murmushi ita kuwa a sukwane tayi bedroom don kunyace takama ta matuka, gurinshi ya zauna yana kallon kafar nasa cikin tausayawa yace." Ayya! sorry kajee batasani bah ay tayi maka"
Rikeshi nabiha tayi tace "yaya kayafe mata kajee bata saniba"
murmushi hassan yay yace " Tom shikenan my small nahakura saboda ke"


Kuma tunta muhammad yariko yana cewa." Wow yau munci albarkacin kanwarmu Allah nagode maka, yanzu bari nafito wanka naci abinci semuje kuga mamma, nasan kinyi missing dinta sosai koh?" nabiha ta daga masa kai tana murmushi, mikewa yay yana cewa." to bari nafito tsarabar ku tana mota mah sauri yasa ban shigo muku da itaba bari nafito" sukabishi da toh, kuma suka rakashi da idanu.


A kofan fita yaci karo da ita harta gama hada masa ruwan wankan zata fito, salin alin yakama hannunta suma koma bathroom din, nan danan yanayin ta yasauya kamar wadda akawa mutuwa kamar tayi kuka tace." Pls kayi hakuri ya muhammad ni nayi wankana ma fah abinci zanje na shirya maka a dining" cikin kure ta da shanyay yun eyes dinsa ya noke wuyan sa a shoulder dinsa yana tura baki gaba alamun yaki din, aikuwa yaga tana shirin saka masa kuka, hakan yasa yakarasa mannata da bango yahade bakinsu gurin daya yana kissing dinta har seda tagaji da tsaiwa tukunna yasakar mata lips din nata,
Zuciyar ta taf da mamaki idanun ta arufe tasoma laluben kofa zata fita don zuwa yanzun tasoma sallama ya muhammad din nata, da mamaki shima kawai ya tsaya yana kallon ta



" Meenal"


Yakira sunan ta cak ta tsaya batare data juyo bah hannu yasa ya jawota kusa dashi yana kallon fuskanta na few seconds, yace." Bude idonki ki kalleni" seda yakuma mai maitawa tukunna tabude eyes din nata ahankali tasasu cikin nashi, ganin yadda nashin yakoma ne yasa takeson maida nata ta kulle ammah bata samu damar hakan bah, cikin sanyin shi yace " sweetie kina sona kuwa? tell me, kada ki boye min" takasa magana se kanta kawai data daga masa, babu abinda yagani cikin kwayar idonta se zallar tsoro, ajiyan zuciya yayi yasake ta tafice kuwa da saurin ta, kai kawai ya girgiza yana murmushi yace.
" Yarinya zaki dawo kan hanyama"
Ko da tafita zuwa parlour hassan harda rike baki yace. " OH! yaya kuma daga shiga daki kuma semuji ki shiru" hararar burin kunya tamasa sa ta wuce kitchen" murmushi usain yay yace." To mudai yay sauri yazo tafiya zamuyi mu baku guri"

" Tab! wa ina nan ni senaga kul! uwar daka" inji hassan, galala usain yake kallon sa harda rike baki yace lallae kuwa ashe kanada babban aiki" kashe masa ido daya yayi yace "to kabari kagani kuma" meenal tanajiyo iyashegen na hassan sama sama harta fito ta aje masa abincin be wani jumaba yafito yazo yaci abin cinshi yakoshi, kana yamike yace su fito, meenal cikin azar babi aka zari hijab akai waje tanajin dadi,
Suna zuwa parlour suka sami ummi azaune bata juma da idar da sallah bah, koda ta hangosu farin ciki ne sosai ya lulluneta ta mike ta tarbesu ta cafe nabiha zuwa sama tana dariya itama haka atunanin ta taga mamma dinta 😅 seda ta shilla ta sama sannan suka zauna tana cewa." kyakkyawar yarinyata nayi kewar ki dayawa" itama tana murna tace." i miss u too mamma" doss! tadan dora mata kiss a kumatu, kallon twins ummi tayi tace OH! twins ansamu sister an manta da mamma koh! ko ku kirani a waya mugaisa ma" keya usain yasoma shafawa yana murmushi shikuwa hassan dariya yayi yace." mamma sim din mu bazeyi aiki bah a nan anata hidimar biki kuma daddy besamu time bah ya canza mana, ita kuma yaya data kiraki mukace tabamu wayar tahanamu" yadda yay maganar tasa ta karshe zakasan sharota kawai yake meenal yakeso yawa sharri, takuwa soma antaya masa harara, haka ummi itama tace." bawani nan kada kayiwa 'yata sharri"
" Mamma Allah munyi enjoying 1 day din nan sosai damukayi shi da sister dimu rana ta jiya dai zamu dauketa kamar wata kyautace me girma da Allah yabamu mun kara fahim tar juna sosai mamma dama kullum kinsan wan nan ranar muke fatan tazo kuma gashi Allah yakawo ta sedai mugode masa kawai" cikin jin dadi ummi tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login