Showing 15001 words to 18000 words out of 38761 words

Chapter 6 - RABON KWADO Book 3 End By Nana BMB.txt

18 Jan 2025

2800

junanmu soda kauna da kulawa, har Allah ya azurtamu daku, don haka kadena wasu magan ganuma don bakasan me Allah zeyi gaba bah"


"Mom kufa na mussam manne yaza ayi ki hada kanku da waccar mara class din ma don Allah kidena maganar ma yanzu donni bazan taba kaunartaba wlh"


"Kace wlh son rantsuwa fah kayi"


"Eh Allah mom bazan iya son kowace maceba tunda aka rabani da farin cikina"


"Son Allah yayi itace farin cikinka dama tunda Allah ya musanya maka da ita kaga zuwanka Adamawa abin alfaharine a gareka daga zuwa anbaka 'ya sukutun"


"Mom nayi dana sanin zuwa garin nan tabbas bazantaba mantawa da zuwansa bah ashe tsautsayine yakawoni cikinsa ashe iftila ei ne ze fadamin,"
Mikewa mom din tayi tana cewa," lallai son kayi nisa to ni bazan biye makaba haryanzu yarinta na ibarka,Allah yaganar dakai gaskiya" tayi ficewarta abinta tabarshi zaune yanata kun kuni.




Mimi tafiya take cikin sanda harta isa cikin bedroom din dasuke kwana,sauke ajiyan zuciya tayi dataga duk sunyi bacci tayi hamdala don kuwa tasan suka ganta ahaka bakaramar kunya zatajiba ita kanta tasan a birkice ta dawo sauri tayi tashige wanka tayi maza tafito tashirya ta daure gashin kanta data gama busar dashi yanzu, a kasa tayi shimfida tayi kwanciyar ta saboda yadda boobs dinta ke mata zafi bazata iya hawa bed bah su fama matasu, rigingine tayi a kwance idanunta nata tsiyayar hawaye sosai takejin haushin mujaheed yanzu komai daya faru tsakaninsu yake dawo mata gani take komai dayayi mata da mugunta yaringa hadawa abin nashi.


To shima mujaheed koda yashiga makwan cinnasu yata rar da muhammad zaune kan sallaya, koda shigarsa yasau baki galala yana masa kallon mamaki, hakanne yasa mujaheed cewa.


" To CCTV camera! wani munafin cinne yahanaka bacci?"


"Mujaheed kada kacemin seyanzu kadawo daga garden" muhammad yay maganar cikeda mamakin mujaheed da tuni yashige wanka abinshi,


Koda yafito a zaune yasamu muhammad kan bed yana rike da haba yana kare masa kallo yace.
"Babbar magana abin harya kaiga wanka,waishin mujaheed ina auren dole akayi maka harda zaka soma nunawa yarinya rashinta ido,baiwar Allah zatayi fama da jaraba a gurin nan kwazzababbe kawai"

Dariyace taso kwacewa mujaheed amma seya basar don yasan jira yake ya tofa kala ya hayayya ko masa, yanaji yakaraci babatunsa ya kwansa.


To asuba tagari mutan gidan fulani.






TAKU A KULLUM NANA BMB.


08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣ RABON KWADO....!!


BOOK 3


NA NANA BMB


GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{ Marubuta masu garkuwa da alkalami domin fadakar da al'ummah }



page 31 - 32


Bayan sallan ishah amare gaba daya angama shiryasu an cancada musu ado naman mamaki duka angama jidar kowa zuwa gurin dinner se amare ne kawai suka rage dukda irin kyawun da nana tayi fuskanta babu amrashi saboda halinda take ciki tunanin yousep kawai take don tasan baze zoba,meenal kuwa zalki kawai take sotake kawai taga waye wan nan mijin nata,mujaheed ne yafara kiran mimi tafito cikin yaukinta dukansu babu kawayensu bare a rakasu mimi bawasu kawaye, ita kuma meenal nadiya ce kuma tana can tana nata shirin,haka nana sam babu duriyar mardiyya kome yahana hallata oho! cikin shagala da kallonta mujaheed yabude mata mota ta shiga abinta shima yazauna sameer ne yayi driving nasu suka tafi,


Ba jumawa muhammad yakira meenal tafito kuwa da saurinta kamar zata tashi sama,sotake kawai taga dawa Allah ze hadata koda yabude mata motar saurin zura kanta tayi ciki sukayi gware kuwa yay saurin rike goshin nasa yana bude baki alamun yaji zafi, sam meenal bataji zafin bah saboda mamaki tayi turus tana kallonsa,


" Ya muhammad ina mijin nawa kuma?"


Tayi masa tambayar cikin mamaki.


Tsayawa yayi da danna gishin nasa yana mallonta kawai,wato yarin yar nan bata duba takaddar auren suba haryanzu kenan kuma ma duk invitation din da aka buga bata fahimtaba ko yaya kodan babu na daurin aurene? katse tunanin sa yayi yace.


"Ayya sorry sweet mijinki baze samu hallata bah ne yarokeni alfarma zan tafi dake yanzu"


"Lallai ma ya rainani wani irin aiki ne yake dashi dayafini? to wlh bazan yardaba ahaka kake cewa yana sona ya muhammad"


Meenal tayi maganar cikin jin haushi,shikuwa ganin zata bata masa lokacine yasa shi jawota jikinshi yana cewa


"To komeye kibari semun dawo sekiyi nizan ma kira miki shi"


Fahad abokinsa dake gaban mota sosai yake kunshe dariyar sa jin drama din tasu dayake haka yajasu suka tafi tanata ruwan baka ei,


Gida yarage saura nana kawai ita kadai kamar mayya hawaye tuni yasoma kwaranya ah idanunta gaba daya tasada kar da zuwan yousep tanata kallon time jikinta yana karayin sanyi se 9 da wasu mintina mah wayanta tafara ruri, jikinta na bari kuwa tadaga saboda ganin mekiran nata murya a sanyaye tace.


"Hello!"


" Fito mutafi"


Shine kawai abinda yousep yace da ita yakashe wayansa, jiki ba kwari tafito hannunta dauke da tissue tana dan gyara face dinta, nadiya tasamu a bayan mota suka gaisa san nan tabude gaba tashiga cikin ladabi ta gaisheshi ya amsa batare da ya kalletaba yaja mota suka tafi,inda zaka tabbatar da dole akawa yousep zuwa nan kananun kayane ajikin shi ba manya bah fuskar nan babu annuri ko kadan,har suka isa gurin kowa shiru kamar kurame bame cewa wani kala,
Abinda yaba yousep mamaki shine suna shiga MC yasoma koda su hakanne yasa nana rike masa hannu tamau har suka isa mazau ninsu kana yajanye hannunsa yanajin kamar yakama da wuta, auntie kuwa kufular duniya tayita inbanda harara babu abinda take antaya wa yousep jira kawai take a tashi a gurin tasameshi tayi masa wankin babban bargo don sosai taci alwashin cin mutum cin yousep yau,bakin ciki yataru yamata yawa harta rasa inda zata saka kanta kowa ya halkara banda daddy kuma yace mata yau ze dawo.


Cikin farin ciki da kwanciyar hankali gamida jin dadi suke shagalinsu batare da wata rashin da ah bah komai bisa tsari suke sha aninsu gurin taro yakeru kana gani zakasan na 'ya'yan wane da wana ne, meenal cika kawai take tana batsewa itama sotake kawai sukoma gida rashin mutumci kala kala ta tanadarwa mijin nan nata yau, sosai taji bata kaunar sama tunkan tagansa,


Su nana basu juma da isowa bah wata bakar mota itama tasawo kai cikin gurin ta parker, wasu kyawawan matasan samari ne suka fara fitowa daga cikin mota din wanda a shekaru bazasu wuce 14 years bah, kallo daya zakai musu kasan twins ne su saboda tsananin kamar dasukeyi da juna sunsha farar shadda tanata zuba kyalli sekayi musu kallon tsaf zaka ga kamanninsu da muhammad, daga gaban mota wata mata tafito dauke da diyar ta da bazata wuce shekara 6 bah zuwa 7 dukansu sunsha abaya an dau rolling tamkar larabawa, ( kai me karatu tsayawa fisalta kyan dasukayi bata lokacine)


Abin mamaki daga bangaren driver kuma daddy ne yafito cikin tashi shigar na al farma shima, hannun sa matar takama shikuma yarikewa yarinyar hannu ahaka suka nufi cikin gurin wadan nan samarin suna take musu baya gwanin sha awa,


Dama daddy yasa an sanar wa MC gashi nan shigowa da iyalansa yanzu,habawa malam guri fah ya dauka ya kaure da zuzutawan MC kaf jama ar gurin kuwa poster akayi ana kallonsu kamar anga wani abin al ajabi,


Kai tsaye gurin amare suka isa samarinne suka fara gaisawa da amaren cikin harshen turanci fuskar kowan nansu dauke take da murmushin farin ciki da jin dadi,gurin muhammad da meenal matar ta tsaya tanata sauke ajiyan zuciya na farin ciki, ganin abin kaunar tata datayi, cikin shauki da kaunarsu take kallonsu tamika wa muhammad hannu tace.


" congratulation my muhammad auntie safiyyan ka tazo tayaka murnar aure dakayi"


Rintse idanuwan sa muhammad yay yana jero Addu o i, hakanne yasata sakin murmushi takalli meenal datake ta faman kallon ta, tace.


" congratulation my Dota, tsawon shekaru ina jiran wan nan rana dazan sake ganin ki a rayuwata,hakika ina kaunarki dayawa kullum cikin begen ki nakeyi yarinya ta ashe da rabon zan kuma ganin wan nan ranar dazan kuma ganinki"


Safiyya tayi maganar cikin gubar hawaye taname tallafo fuskarta,
Dariya daddy yayi yarike wa muhammad hannu yace.
" My son bude idanun ka mana auntie safiyyan takace bakason gani ko kuwa kannen kah? bazakayi farin ciki da dawowar su garekuba?"


Ganin muhammad yaki bude idanun sa har yanzu yasa shi sakin murmushi yace.


"My lady taho muje mu gabatar da kanmu tunda kowa yakasa gasgatamu"
Tana murmushin itama sukabi bayansa gurin da MC yake suka karasa ya amshi speaker din hannunsa yay gyaran murya gamida gyara tsayuwarsa yafara mika gaisuwar sa da kowa da godiya kadukkan wanda ya halacci wan nan taro nasu,kana kuma yasoma zayyano bayanai akan matarsa ta biyu safiyya wadda take zaune a dubai da yaransu uku, hassan da usain, se autarsu nabiha,


Seda yagama zayyano jawabansa tukanna yamikawa safiyya speaker din ta amsa itama cikin sanyinta tasoma mika godiyar ta ga daukacin mutanen dake gurin, ko ina muryan ta yake karadewa,jikin muhammad a sake ya bude idanun sa cikin wani irin yanayi tabbas wan nan muryan nata baze taba gushewa a zuciyan saba,


Tana cikin jawabinne taji anmata wata irin rumguma, kukan ta dataji ne yasata sanin ko wacece nan danan idanun ta yaciko da hawaye koda ta juya sukayi 4 eyes da ummi tana kuka, kara matseta tayi a jikinta tana kuka sosai tana cewa.


" Ni nasan safiyya kina raye baki mutuba kawai kinmin nisane bayadda zanyi da rayuwata, wallahi koyanzu Allah yadauki raina burina yacika yadawo min dake,taho zo muje gurin iyayen mu kullum cikin begenki suke suma"


Tunkan su karasa hajiya ta nufosu tana sharbar nata kukan itama cikin tsatstsan farin ciki ta rungumesu suka hadu sunata rafsar kuka,


To muhammad kuwa yatasa twins a gaba da tsananin mamaki don seyanzun ma yaga yadda suke kama dashi haka mujaheed suna tsaye sunyi cirko cirko kallon twins din kawai sukeyi cike da al jabi, daddy gurin 'yan uwa da abokan azziki yaje anata gaggaisawa masu tsiya namasa kan cewa yaje yaboye amaryarsa.


To mekaratu lamarin auntie gwanin ban tausayi halin da tashiga saboda sosai take ganin kamar tana mafarki tarufe idanun ta ta bude yafi sau bakin bunu, dakyar take iya fisgo numfashin ta saboda tsananin bugawar da zuciyanta yakeyi duhu tasoma gani a halin yanzu ga yadda takejin wani irin yama yama a kwa kwalwar kanta da hannu biyu tasa ta dafe kanta don bakaramin girgiza tayi da wan nan al amarin bah, kuma sam babu wanda yakula da halinda take ciki mah saboda anmata ma dacewa wata dinner akazo guri ya kacame,


Kowa yana rububin daukar nabiha wadda taketa kwalo idanu kamar zatayi kuka don tunda take seyau ta taba ganin hausawa haka dayawa, haka twins mah,


Meenal tana zaune kamar an dasata a gurin don itama bakomai take fahimta ba yanzun saboda halinda tashiga, daddy ne yakula da hakan yasashi zuwa yakamo hannun ta yaje inda su safiyyan suke yasaka hannunta cikin diyar tata yace.


" Meenal mamakin ya isa haka mahaifiyar kice ta dawo gareki daman tana nan a raye bata rasuba kamar yadda kowa ya dauka a da amma banda yanzu"


Wani irin numfashi meenal take fitarwa hawaye nabi mata fuska tana kallon safiyyan cikin muryan kuka tace." daddy wai meyasa life dita take fuskantar irin wan nan rayuwar ne?" tana maganar tana shirin fashewa da kuka, " Haryanzu nakasa yaddama kaina cewar bakaine ka haifeni bah, kuma yanzu gashi kacemin wai mahaifiyata tana raye! taya haka zata kasance a gareni, mahaifiyata tana raye bata taba zuwa inda nakeba seyanzu, wan nan waca irin uwace daddy?" takarashe maganar tata cikin kuka!


Jikin kowa kuma seyay sanyi saboda yadda tabasu tausayi, dafata daddy yayi yace.


" Doguwar magana ce wannan meenal kiyi hakuri idan mun koma gida zakiji komai kinjee, mahaifiyar ki tana matukar kaunarki don kece farin cikinta akoda yaushe"


Cikin wani irin yanayi meenal tasauke ajiyan zuciya tajanye hannunta daga na safiyya ta matsa kusa da daddy ta rikeshi tana girgiza kai tace. " Sam banajin sonta nikuma, daddy ko kadan ma banason ta rabe ni, bana bukatar ta agareni yanzu gara nayi rayuwata a yadda na taso daddy!"


Ayadda take maganar ne zakasan batasan ma metakeyi bah a yanzu, rumgumeta kawai daddy yayi sosai idanun sa suka ciko dakwalla, don tabashi tausayi sosai, itakuwa safiyya kuka tacigaba dayi jin furucin da diyarta ta keyi mata,duka kuma Dr da imam sune sadiyyar faruwar komai, hakanne yake kara saka safiyya kuka tasan meenal sam bazata saurare taba yanzu kam.


Ta dole muhammad da mujaheed suke son gano cikin twins waye hasan, waye usain sun kuma kasa, sedariya suke musu sukuma


Seda akaci aka sha tukunna taro ya tashi rabin shi kuwa koke koke ne akasha, har inda auntie take daddy yaje yakamo mata hannu zuwa lokacin kuwa tadena fahimtar komai sedai idanu yasakata cikin motar dasukazo da safiyya tana ciki itada ummi sannan ya dora mata nabiha akan cinyarta yarufe motan yazaga mazaunin driven yashiga....




TAKU A KULLUM NANA BMB.


08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣ RABON KWADO....!!


BOOK 3


NA NANA BMB




GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{ Marubuta masu garkuwa da alkalami domin fadakar da al' ummah}




page 29 - 30


BAYAN WATA BIYU


Yau takama juma ah, ranar kuma dinner din su muhammad ranar dazasu fara nasu taron kenan, bayan gidan fulani sungama nasu shagalin suka dungumo suka taho kano kuma, gida yayi cikar kwari babu masaka tsinke ga family din auntie da mutan bauchi duka an hallara,amare sunsha gyara matuka se daukar idanu sukeyi dama mimi tasha gyaranta tundaga gida,sedai sam taki yarda su hadu da mujaheed wanda shikuma jida kai yahanashi zuwa inda take yasame ta sedai hange daga nesa,
To meenal tun randa muhammad yabata takaddar aurensu bata duba taba saboda yanda takejin zuciyanta tabarwa zuciyanta idan wan nan lokacin yayi taga koma wani maha lukinne, shima muhammad bekuma yimata maganar bah kallonta kawai yake saboda ta kuma yimasa maganar mardiyya yace taje takirata su fuskancu junansu tukun tun ranar take neman mardy tagaza samunta har kawo yanzu haka daddy shima kallonta kawai yake,


Nana kuwa harkawo i yau yousep betaba kiranta a wayaba sema ita da take nacin kiransa karshe inya gaji yasakata a black list kamar mayya kuma seta canza number takira shi duk tabi tarame saboda damuwan datake ciki kowa yaganta yasan tana cikin damuwa,abin yana matukar damun auntie itama tana tausayin 'yar tata sosai kowa angonsa ya hallara amma banda na 'yar ta, tome hakan yake nufi?
General da Daddy da daddyn mujaheed se Abban su mimi su hudu suka hadu suna gudanar da tarukan nasu bisa tsari da kwanciyar hankali,
Sameer ma se a yaudin ya iso shida matarsa da inty dakuma mom dinsu don ragowan abokanan na mujaheed ma sun rigashi isowa,se antayawa mujaheed din harara yake don yaki gaya masa komai yace idan yazo yagani dakansa muhammad nata musu dariya,masauki na musam man aka basu da abinci kala kala suna cikin cin abin cinne su mimi da meenal suka shigo domin tarbarsu, cikin mamaki inty taje tarike musu hannuwa tana kallinsu don tarasa wadda zata kira da meenal kamar sha sha haka take kallonsu,
Mujaheed yasaki murmushi mesauti yace.


"Yadai! inty tun yanzu harkin fara shiga rudani haka"


Tana kallonsu tace." ya mujaheed dama su twins ne baku taba gaya manaba,don Allah wacece meenal din acikin ku? don bazan iya tan tancekuba gaskiya."
meenal ta kalli mimi sosai tajuya ga inty tace.
" Dama sister muna kamar da za ah kasa ganemu ne?"
Salma tana daga gefe tana kallonsu tace, " Meenal"
suduka biyun suka juya suna kallonta,mimi tana murmushi takarasa inda take zaune tace. "lah! auntie salma babyn mune wan nan ashe kin haihu"
Zama tayi gefenta ta anshi affan tana murmushi ganin yadda har yay wayau, murmushi salman tayi tace.
"Ok kece meenal din kenan"
hannunta mom tariko itama tana cewa "diyata meenal meyasa baki taba gaya mana cewar ku twins bane"
Meenal tana gefe tana kallon salma saboda bata taba ganinta bah seyau,maganar da mom din tayine yasata cewa "mom ay ba twins bane mu 'yan uwane"
"Tabdijan gaskiya wan nan kamar taku ta baci matuka babu wanda zece ba twins bane ku" cewar inty kenan sosai suke mamakinsu se kallonsu suke,matsowa kusada mimi mom tayi tace "meenal meyake faruwane? mungani a TV mujaheed ya auri 'yar matemakin gwamna na adamawa,garin ya hakan yakasance? mujaheed be aure kiba"


Murmushi mimi tayi ta kalli mujaheed daya zuba mata maya tattun idanunsa,ta sauke ajiyan zuciya cikin sanyinta tace.


"Ay nice 'yar tasa"


Dawani irin kallo suka shiga binta mussam man sameer daya zuba musu idanu tun dazu,


" Meenal me kike nufi?" mom tayi mata tambayar cikin rashin fahimta tana kallonta,


Meenal tana daga zaune tace." mom ay nice meenal ita mimi sunan ta"
Kasa rike dariyarsa muhammad yay ya cusa fuskansa cikin pillow na kujare saboda yadda kowa reaction dinsa yabada abin dariya,


"Meenal kina nufin mimi mujaheed ya aura bakeba?" mujaheed yay tambayar cikin wani yanayi na kaguwa dasanin meke faruwa haka,


Meenal ta kawata murmushin fuskanta tace.
" Aydama da ita suke soyayya bani bace"
"What!"
Sameer yafada yaname mikewa tsaye don zuwa yanzun abin yasoma fin karfin kansa sosai ya zubawa mimi idanu haka su mom

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login