Showing 1 words to 3000 words out of 52687 words
Chapter 1 - DACEWA Book Complete Document by M amuhagge .pdf
_*DACEWA*_ Elhajj
( _when east meets west..._ )
_By_
_Mamuh geee_
*1*
Yan mata biyar ne a 'dakin
Wasu a zaune suna kwalliya wasu kuwa a tsaye suna shiryawa.
Hayaniya suke sosai a 'dakin sbd shirin nasu na bikin babbar aminiyarsu ne wato *ANEESAH*.
manyan 'yan matane masu class da burgewa ga ilimi da wayewa tareda tsantsar Hutu,
Dukkaninsu idan ka tsaya ka kalla babu mummuna aciki saidai banbancin kalar fata wasu farare
wasu chocolate.
Qofar toilet 'din 'dakin aka bude wata kyakkyawar dirarriyar budurwa ta fito 'daure da towel
wadda zatakai kimanin shekaru ashirin da shida.
Kyakkyawa ce batada jiki amma hips dinta da boobs 'dinta sun girku sosai a jikinta duk da
batada jikin.
Ahankali tazo gaban mirror ta zauna tana kallon 'yan matan tace,
Wai Ku ko kunya bakwa ji sai rawar jikin shiryawa kukeyi ni danake amaryar wanka kawai
nayo.
Eh wannan kuma kinga dama ne..'dayar ta fada tana gyara eyebrow 'dinta.
Wadda ke tsaye gaban wardrobe tana saka undies ta 'dan dakata ta juyo tace,
Are you guys seeing wat I'm seeing?
Neesah yanda kike farin ciki da rawar jikin auren nan naki da Mr perfect amma tun jia na lura
sai delaying komai kike yanxu.
Ajiyar zuciya aneesar ta sauke ta matso lotion 'din jarggens tafara shafawa a jikinta kafin tace,
Amirah I just don't know why but I'm having this strange feeling like am gonna lose sumtin,
Sumtin that is so precious to me.
May b kin fara tunanin yanda zaki rabu dasu Umma ne ki tafi gidan.
Cigaba tai da shafa manta batareda ta qara cewa komaiba.
Amirah,Hafsat,siyams da asmy sune sunayen 'yan matan kuma friends na Amarya aneesah.
Friends ne su tun a primary school har zuwa yanxu dasuke university.
Dukkaninsu iyayensu masu arziki be sosai
Hakama kowacce akwai ilimi da wayewa sosai a gidansu,
Amirah da siyams ba farare bane sa6anin asmy da aneesah dasuke farare.
Dukkaninsu 'yangayune wayayyun 'yan mata masu tsantsar class da burgewa
Duk wayewarsu da bokonsu hakan baisa sun 6ata rayuwarsuba irin ta 'yan matan zamanin
yanzu dansu tarkacen samari ma bai damesu ba har gwara Aneesah tanada soulmate kamar
yanda take fada.
Aneesah na matukar son taheer kamar ranta kamar yanda yakesonta.,
Sun hadu ne a airport 'din qasar Germany lokacin dasukaje dubo qanwar mamynta da akaiwa
aikin zuciya acan.
Soyayya suke sosai wanda har kowa mamakinta yake sbd Sam bata kula duk wani namiji
amma yanxu kowa na mamakinta akan tahir soulmate 'dinta.
Aneesah su biyu kacal mahaifansu former chief justice Alh sanda da Dr maryam suka haifa
Daga ita aneesah sai qaninta naseer.
Naseer na matakin qarshe a secondary school yanxu.
Dadynta nada qanwa 'daya tilo dayake matukar so sbd su kadai iyayensu suka haifa kuma suka
bari a duniya.
Haj Aysha itace qanwar dadynta tana zaune a Victorian island Lagos sbd mijinta shine chief
commander custom.
Ummi nada yara biyu duka maza _JAMAAL_ shine babba 'dan kimanin shekaru ashirin da biyar
sbd aneesah ta girmesa da kusan shekara biyu,
Jamaal ya gama karatunsa a qasar Europe inda yanxu yazama cikakken US navy captain
kuma acan yake zama.
Jamaal kyakkyawane mai sanyin hali matuqa ga rashin son hayaniya sbd Sam ko zama bai
cikayi a qasarba sbd yanayin aikinsa,
Rashin zamansa yasa iyayensa ke matuqar sonsa sbd bama kamar dadyn aneesah dake jinsa
kamar 'dan cikinsa.
Ahmad shine qanin Jamaal Wanda shi yanxune yake degree 'dinsa anan Lagos.
Sai khadija 'yar qanwar dadynsu Jamaal da ummin ke riqo wadda zatakai 19 to 20 years.
Taheer ma hadadden namiji ne iya haduwa wanda zai kai shekaru talatin da biyu da haihuwa,
Taheer kwararren gynecology Dr ne a babban hospital anan abj.
Taheer na matuqar son aneesah sbd komai nata yayi masa hundred percent saidai Sam
momynsa bata sonta sbd 'yar qawarta takeson ya aura dan kawai ita gani take Aneesah batada
tarbiya sbd ganin wayewarta tai yawa.
Daqyar taheer da dadynsa suka shawo kanta ta yarda akan auren nasa da aneesah gashi har
anfara shirye shiryen biki.
Bayan dukkaninsu sungama shiryawa suka fito gabaki 'dayansu daga bedroom 'din aneesah
suna daria sbd siyams data dizga wani a waya yanxun.
Umma suka tarar a parlo zaune tareda wata baquwa suna tattaunawa akan shagulgulan bikin.
Aneesah ta zauna kusada umman tace,
Umma zamuje wata 'yar siyayyane bazamu 'dau time ba zamu dawo.
Kallon tuhuma umman tajefawa su amirah kafin tace,
Yanxu dan Allah da rana tsaka zaku fita wata siyayya alhalin kuna sane sarai baikamata
ana gyaraba kuna fita yawo tunda dai bikin nan yariga ya matso.
Asmy tai saurin cewa,
Insha Allah Umma bazamu da'deba.
Yanxu dai Ku kuka sani idan umminta tazo Ai nasan bazata bar wannan shashancinba.
Tashi sukai suka fice daga palon zuwa harabar gidan
A motar siyams suka fita sbd ita tabiya gidajensu ta 'daukosu.
Ceddi plaza suka nufa
Suna isa gurin suka fara shopping 'dinsu hankali kwance cikin 'yar hayaniyarsu ta qawaye.
Wayar aneesah ce tai ringin tana dubawa taga taheer ne ta saki wani lallausan murmushi
tareda 'daga wayar tace,
Soulmate ni Allah nayi fushi.
Sorry Luv I was very busy ne throughout the day...
Oh so ure telling me aiyuka sun sa ka manta da ni.
Heyy don't say that Luv,
U know that's not true.
Naji nidai pls my Dr kazo yau I'm missing you so bad.
Hmmn bby kobaki fadaba dole nazo sbd nima am missing my Queen so badly da bazan iya
bacci ba yau idan bangantaba.
Mamuh馃拫
[3:19AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: _*DACEWA*_
( _when east meets west..._ )
_By_
_Mamuh geee_
*2-3*
Har suka gama shopping suka bar gurin aneesah waya take da angon nata cikin nisha'di su
kuwa su amirah sai tsokanarta suke.
Saida suka biya gidansu amirah ta 'dauko kayanta sbd ita tace agidansu aneesah zata kwana
har agama bikin.
Tun a harabar gidan suka shedarda baqi sun fara sauka a gidan dan haka su asmy ajesu kawai
sukai suka juya sbd yamma datai sosai.
Qanwar mamynta ce tazo daga kano tareda 'yayanta uku dukkaninsu yarane.
Da hanzarinta ta isa jikinta cikin murnar ganinta tace,
Anty Mamee oyoyo.
Kallon mamy Antin tayi tace,
Amaryar kenan anty kika barta tana yawo shine harsai yamma suka dawo.
Ai daga yau bazata qara fitaba tunda dai gashi kinxo idan umminta ta iso saikui ta fama dan
Sam wlh aneesah batason zama kullum cikin qaryar zasu karbo saqo suke.
Sorry mamy daga yau andaina insha Allah"" cewar amirah data fito daga bedroom bayan takai
kayanta.
Daki suka wuce sukai sallah magriba amirah tafito Palo gurinsu mamy
Aneesah kuwa toilet ta fada tayo wanka.
Ado tai sosai cikin wata maroon Turkey's gown bayan ga qamshi dake tashi ko ina ajikinta.
Palo ta fito ta zauna kusada Anty tana turawa taheer text na cewar ya shigo Palo yafara
gaidasu mamy sbd yace mata ya iso.
Knocking yayi a parlon kafin yashigo tareda sallama.
Cikeda kunya ya gaidasu mamy kafin ya juya ya fita ta miqe tabi bayansa.
Qaramin palon gidan suka shiga ya zauna yana jifanta da wani kasallen kallo yace,
Amaryan Dr you look gourgeus.
Ajiyan xuciya tasaki ahankali sbd ganinsa gaba 'daya ya sanyaya mata jiki tace,
Soulmate kwanakin nan ina having wasu strange feeling narasa gane meke damuna.
Tsura mata ido yayi tsawon lokaci yana karanto fuskarta shima sai yaji jikinsa na Neman yin
sanyi yace,
Kwantar da hnklinki luv it's nothing or may be kina tunanin yanda zakiyi missing su mamy ne.
Firar soyayya suka hauyi sosai kafin ya tafi bayan amirah tazo ta kar6i kudi masu matuqar yawa
a hannunsa na fara shirye shiryensu.
Washe gari tinda safe gidan suka tashi fresh milk kawai tasha Anty Mamee tafara gyaranta dan
dama tana gyaran amare.
Su asmy ma sunzo tun safe sai hayaniyarsu suke.
Bayan angama komai tashiga wanka tana fitowa saita jiyo hayaniyar isowar ummi.
Doguwar riga tasaka mara hannu ta fito palon cikin tsananin farin ciki ta isa gurin ummin ta
zauna tace,
Ummi sannu da hanya?
Cikeda qaunarta ummin tace,
Thank you baby,ya shirye shirye?
Murmushi tayi kafin tace,
Ummi wane shirye shirye za'ayi bakyanan.
Bari kedai baby wlh naso zuwa tun last week amma Jamaal yace najira yananan zuwa sai
mutaho tare saigashi wani aiki ya riqesa
Yanzunma bazuwa yayiba na tahowata shizaizo 'daurin auren daga baya.
Murmushi kawai tayi batace komaiba sbd Jamaal Sam ita batama tunanin idan tagansa zata
ganesa sbd sun dade basu haduba dama kuma ko magana bata hadasu sai gaisuwa shima ba
kowane lokaciba dan Sam ita batason halinsa sbd girman kansa ko kallon arziki bayayi mata
duk da tana antynsa bare tasamu gaisuwa shiyasa bata damu dashiba Sam bareshi da bazai
iya cewa ga kamanninta ba.
Daki ta raka ummi bayan tayi sallah taci abinci suka hau fira ummin na bude mata tsarabar
wasu tsinannun English wears da nights gowns data kawo mata akwati guda.
Washe gari gidan ya qarasa cika sosai sbd ranar ake bridal eve,
Makeup sosai Amarya tasha cikin wani tsadadden drylace dark blue
Friends 'din amarya ma ankon peach lace sukai da blue head.
A babban hall 'din dake cikin bistry saga mall za'ai evening 'din
Hall ya cika ya tsaru matuqa sbd gaba 'daya gurin masu ilimi da wayewa ne agurin sai abin yayi
tsari sosai.
Lokacin da ango da Amarya suka shigo gurin aka fara biki dai dai isowar habib qanin umman
tahir.
Tunda idanuwansa suka sauka akan neesah gaba 'daya yaji nutsuwarsa ta kunce sbd wata
zazzafar qaunarta da sha'awarta yaji lokaci 'daya sun damqesa.
Yawu ya hadiye yana lumshe fitinannun idanuwansa yana qara budesu akanta.
Habib qanin umman tahir ne kuma gogaggen 'dan duniya sbd tsaf ya kware a gun neman mata
duk da kuwa yanada matarsa.
Da gayya ya ringa 6arar da kudi duk lokacin da Amarya neesah ta fito fagen rawa Wanda ita
kallo 'daya tai masa ta 'dauke kai tana ta6e baki sbd irin kallon qurullar dayake mata taji ta
tsanesa nan taken.
Har aka tashi gurin bikin Habib hadiye yawu yake qarshe dai yabar gurin yana sakin wani
fitinannen murmushin manufa.
Duk wasu shagulgulan biki an gudanar dasu cikin farin ciki ana gobe 'daurin aure ne sukai
dinner da daddare Wanda har anyi an watse neesah na zaune cikin mota tana jiran tahir
yagama sallama da wasu friends 'dinsa yazo sutafi.
Waya take da amirah tana fada mata idan tahir yakawota ta tsayar mata dashi zatai magana
dashi.
Jitayi anbude motar anriqo hannunta ba musu ta fito dan ta 'dauka tahir ne,
Tana fitowa saitaga Habib ta fizge hannunta da qarfi tareda tamke fuska sosai tana masa kallon
qarin bayani.
Manyan lovely eyes 'dinta suka rikitasa yaji wata muguwar sha'awarta na neman haukatasa sai
kawai ya fiddo handkerchief ya shaqa mata wani Abu a fiska nan ta sulale ya tarota jikinsa ya
cicci6eta ya saka motarsa yabar gurin da sauri.
Mamuh馃拫
[3:19AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: _*DACEWA*_
( _when east meets west..._ )
_By_
_Mamuh geee_
*4-5*
Taheer na zuwa motar yaga bata ciki
Yayi saurin danna kiran numbarta sbd tunanin ko gajiya tai da jiransa tabi wata motar ta wuce.
Ringin 'din wayarta yaji daga bayansa ya juya saiya hango wayar a qasa.
Dauka wayar yayi ya fara dubbuba harabar gurin cikin mamaki.
Amirah yakira tana 'dauka yace,
Pls amirah bby ta iso gida kuwa?
Nope, akwai wani abu ne?
No kawai dai nazo mota bata ciki and I called her phone but abin mamaki wayar a qasa na
tsinta.
Gaban amirah yafadi ta tashi daga kwancen datake tai qasa da murya sbd kada wani yaji ayi
making big issue out of it.
Kadaka fadawa kowa bari ganinan tafe gurin yanxu.
A sulale ta fice ta hau napep
Tana isa ta tarar dashi duk hnklinsa ya tashi idanuwansa sun qada jajir sbd tashin hnkli.
Sake dudduna ko ina agurin sukai basu gantaba harsun juyo sai amirah ta hango head 'din
neesah cikin flowers ta ruga da gudu ta 'dauko gabanta na faduwa
Tahir kuwa jikinsa ne yaqara 'daukar rawa ya damqi head 'din yana jin tsoron abinda yake shirin
faruwa dashi ace amaryarsa ta 6ata a daren 'daurin aurensu.
Amirah wayarsu asmy tahau kira tana tambayarsu ko suna tareda neesah amma kowaccensu
tace aa.
Wayar mamy takira ta tambayeta ko neesah ta iso gida.
Mamy tace,
Aa, amma yakamata ace tadawo sbd fa dare yayi kuma dai Ai anriga angama dinner metake
jira ne haryanzu.
Datse kiran amirah tai sbd batamasan me zata cewa mamyn ba.
Sake kiranta mamy tayi takasa 'dagawa sai abin yaba mamy mamaki sosai nan take ta zargi ba
lafiya ba ta qara kiran amirar.
Murya na rawa amirah ta dauka.
Amirah lapiya kuwa?
Ina aneesah bata wayar zanyi magana da ita.
Hawayen datake dannewa suka gangaro mata ta bude baki murya na rawa tace,
Mamy wlh an nemi neesah an Ras.....
What? Mamy ta fada da qarfi kafin tace,
Kamarya amirah?
Ba mumbarku a gurin ba?
Ki kira tahir may be suna tare.
Mamy gani nan tareda tahir gaba 'daya ma baya cikin nutsuwa mun duba ko ina,mun kira
mutane da dama amma duk ba'a gantaba.
Sulalewa mamy tayi ta zauna da6as a kujesa cikin tsantsar tashin hankali.
Saurin riqeta Anty Mamee tayi ummi kuwa wayar ta kar6a da sauri tana cigaba da sauraren
bayanin amirah.
Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun,,,,
Shine abinda ummi ke maimaitawa cikin tashin hankali.
Wayar abban neesah takira yana 'dauka tace,
Yaya kadawo kuwa?
Alh sanda dake zaune a babban palonsa yana kallon news yace,
Eh tun 'dazu nadawo ina Palo na.
Fita tai da sauri ta nufi palonsa tana shiga ta fara fada masa halinda ake ciki.
Sakato yayi yana kallonta cikin rashin fahimta yace,
Aysha ki nutsu ba abinda zai faru bari nakira tahir 'din naji.
Yanda yaji yanayin muryar tahir yasashi tashi tsaye yace,
Tahir menake ji yanxu?
Abba wlh kaina a 'daure yake da wannan alamari sbd acikin mota nabarta dan na sallami wasu
baqina sai kawai na tarar da batanan.
Kwantar da hnklinka tahir insha Allah za'a ganta.
Fitowa sukai dukkansu suka ha'dudasu tahir 'din sukai station.
Acikin daren 6atan Amarya neesah ya ya'du har gidansu tahir
Wanda wasunsu ke cewa tadai gudu ne bawani 6ata.
Kasa zama umman tahir tayi tafara kai kawo a 'dakinta cikin dogon tunani da wasi wasi,
Gskia bazata iya bari tahir 'dinta datake masifar so ya auri neesah ba sbd ga abubuwa nan
marasa kyau na qara faruwa.,
Duk iya yanda ake tsammanin tashin hankalin to abin ya wuce nan dan tuni gidan bikin yakoma
kamar gidan makoki gashi dare ya tsala sosai amma ba Wanda yasamu damar ko kwantawa
bare rintsawa.
Duk iya yanda mamy taso daurewa kasawa tayi saidata zubarda hawaye sbd fargabar menene
zai faru da aneesar dan bakowa zai yarda da duk abinda zai biyo bayan ganin nataba.
Ummi kam kuka take reras dan sosai Allah yasamata so da qaunar 'yar 'dan uwantaba.
Su Abba da dadynsu Jamaal tareda tahir 'din da babban amininsa jafar kuwa har gabanin
asuba suna can tareda jamian tsaro cikin tashin hankali gurin nemanta.
Amirah kuwa tasha kuka har idanuwanta sun kumbura hakama su siyams acikin Daren duk
suka iso gidan aka zauna jigun jigun jiran tsammani.
Koda akai sallar asuba da qyar kowa yatashi jiki a sanyaye sukai sallah
Har lokacin duk Wanda ka kalla idanuwansa a kumbure gashi har lokacin su Abba basu
dawoba.
Qarfe shida na safe su Abba suka dawo zuciyoyinsu a dugun zume da tashin hankali.
Mamuh馃拫
[3:19AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: _*DACEWA*_
( _when east meets west..._ )
_By_
_Mamuh geee_
*6-7*
Zama sukai a babban palon Abba suna sauraren bayanin da dady ke musu akan iya binciken
dasukai.
Tahir kuwa yana isa gidan ya tarar da wani sabon tashin hankali dan kuwa ummarsa ta yanke
hukuncin ko anga neesah bazai aureta ba sbd itadai