Showing 36001 words to 39000 words out of 52687 words
Chapter 13 - DACEWA Book Complete Document by M amuhagge .pdf
tabada kantaba ta juyawa mamar baya.
Murmushi mama tayi tace,
You see neesah nasan matsalarki duk da khadija bata zayyane min komaiba but you see
khadija nason taimaka miki amma bazan bar hakanba until nima zakiyi min wani Abu 'daya.
Idan kin amince I promise to stand wit you until you bring them down,
Koma meyene zanyi danki samu yanda kikeso just promise me zaki barwa khadija Jamaal ta
aura.
Cikin wani sabon baqin cikin sunan Jamaal kawai data kira yasata miqewa idanuwanta na
rinewa da qiyayyarsa datakejin tana qara kama kowace kusurwa ta jikinta takalli mamar murya
a shaqe tace,
And why will I trust you bayan abubuwan dana gani da idanuwana suna faruwa da mutanen
dana yarda dasu gashi na rasa Ahmed..
Kuka tasaki mai cinrai tanajin tsananin kewar Ahmed na cinta har cikin jininta.
Neesah keba maqiyiyata bace kuma banason kizama maqiyiyata shiyasa nake baki wannan
damar domin dukkaninmu musamu abinda mukeso cikin ruwan sanyi after all koma mezakiyi
you need evidence kuma this is the only option for you to get it.
Cikin kuka da takaici tace,
'Yarki na 'daya daga cikin mutanen dana tsana sbd she knows everything amma taqi fada gashi
yanxu na rasa Ahmed bakusan ya nakeji ajikin zuciyataba jinake gwara na mutu nabi Ahmed
sbd shikadai ne me sona and now I can never be with him.
Share hawayenta tayi tareda kallon mamar cikin ido tace,
Na yarda da shara'dinki sbd bana buqatar ko jin sunansa bare buqatar cigaba da zama dashi
sbd zamana dashi ya qare har abada so you can take him all for your daughter but let me clear
sumthing to you,,don't double cross me sbd zuciyata yanxu a bushe take nima zan iyayin komai
ga duk Wanda yayi gangancin sukata, And for you daughter zanji da ita idan nagama da manyan sbd wannan alqawarine na 'dauka
duk Wanda keda sa hannu ko sanadin mutuwar Ahmed will pay ciki harda Jamaal,ummi kawai
nacire duk da itama bazan iya cigaba da zama a gurintaba.
Idanuwan neesar take kallo tabbas banda qiyayya da bala'i babu abinda take hangowa a
tsakiyar idanuwan.
Ajiyar zuciya tasaki tace,
Well let's say the deal is sealed..
Sabbin hawaye ne suka gangaro mata ta kwanta tana sheshekar kuka ahankali tana kiran
sunan Ahmed ahankali sbd she's ready ta fight them koda zata rasa ranta.
Shigowar mamy yasa mama miqewa tana cewa,
Bari naje gida Nima na 'dan miqe.
Cikin murmushi mamy tace,
Ai kuwa angode sosai.
Tana fita a mota ta tarar da khadija bayan tagamo ganin likita dataje.
Harta tada mota ta hango zeey zaune cikin wata ash corolla8 tai saurin kallon mama taga
hankalinta baya wajen taja jiki ba qwari sukabar asibitin.
Da daddare mama takalleta tace,
Khadija inason kifa'damin duk wasu bayanai dazaki bawa neesah idan ta warke.
Cikin kallon mamaki tace,
Mama karki shiga wannan alamarin idan neesah ta warke zan fa'da mata komai da kaina dan
ko suwaye ma yanxu nafasa fa'da miki sbd banason kisa kanki a rigima.
No khadija kifadamin komai ina son nasani sbd inason protecting 'dinki takowane hali,
Inason nizan bada bayanin sbd koma suwaye su fuskanceni bakeba sbd karsu cutatar dake.
Jikin khadijar ne yayi sanyi ta miqe tareda cewa,
Zan fa'da miki komai gobe insha Allah mama.
Harsun kwanta taji takasa barci sbd zeey data gani a asibiti 'dazu.
Saukowa gado tayi ahankali tareda zura dogon hijab ta 'dau wayarta da kudin mashin ahankali
ta fice.
Asibitin ta nufa ta tsaya 'daga nesa ka'dan da 'dakin.
Wata nurse taga tazo tashiga saikuma taga mamy tafito 'dakin.
Bataga fuskar nurse 'dinba saitaji tsoron abinda yasa mamy tabaro nurse
Ita kadai a 'dakin.
Ahanki ta lalla6a ta isa qofar 'dakin ahankali ta tura qofar.
Zaro ido tayi jikinta na rawa sbd ganin fuskar zeey sanye da kayan nurses ta na kallon neesar
dake bacci tana dariyar mugunta ahankali.
Wayarta ta zaro ahankali ta danna video recording.
Sosai fuskar zeey tafito ta zaro wani qaton dogon syringe zata yiwa neesah allurarsa saikuma
ta tsaya tana tunani alamar ta manta wani Abu saita ciro wayarta daga aljihu ta danna kiran.,,
Ayeesha gani nasamu shigowa na manta a ina leloh yace na soka mata.
Cikin qaguwa ayeesha tace,
Ki soka mata koma a ina kika samu mudai ta mutu mu huta konasamu kan Jamaal nikadai.
Kashe wayar tayi ta 'daga syringe din zata da6awa neesah wayar kiran mama data duba bataga
khadijarba yashigo wayarta
A tsorace zeey tajuyo sukai ido biyu da khadijar ta zaro ido cikin tsoro sbd ganin recording take.
Da gudu khadija tabar jikin qofar zeey tabiyota da mugun gudu.
Cikin mugun tsoro khadijar ke gudu gashi dare yayi kuma zeey a mota take.
Daqyar tasamu mashin jiki na rawa ta hau tafada masa inda zai kaita.
Pls qara gudu takusa kamomu wlh zata iya komai idan takamani.
Gudu mai mashin 'din yaqara sbd shima ya tsorata matuqa.
Gudu zeey keyi sosai dan ta kamosu tabi ta Kansu da mota kowama ya huta.
Wayar ayeesha takira tasanar da ita komai.
Suna isowa gidan tun bai tsayaba ta dira ta fa'da gidan tareda qalgama sakata ta nufi sashensu
Jamaal da gudu sbd shi ka'dai takeson gani yanxu ta miqa masa wayar sbd harzancen ayeesha
saidaya 'dauku.
Daf dazata isa taji saukar wani qaton ice a tsakiyar kanta tayi baya ta zube kanta na jini.
Janta cikin flowers ayeesha tayi kafin ta Lalla6a taje tabudewa zeey gida sukazo suka jata suka
fitar waje zeey ta 'dago syringe 'din da dah neesah zasu sakawa ta sokawa khadijar shi tareda
tatse mata ruwan ciki tsaf suka wuce suka barta gurin yashe tana shure shure.
Mamuh💋
🌲 *R H F W F*�
_Don't forget to vote, follow and comments_
*_DACEWA_*
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*_Viawattpad@mamuhgee_*
*54-55*
Kasa zama mama tayi tasake danna kiran khadijar.
Motsin dayaji yasa ya tashi baiga ayeesha ba amma yaji qarar ruwa a toilet alamar tana ciki
saiya fito Palo.
Sakejin motsin yayi a waje ya ta6a qofar palon zai bude ya fita ga mamakinsa saiyaji qofar a
bu'de.
Fitowa yayi yafara dudubawa daidai lokacin da mama tasake kiran khadija saiya hango hasken
waya ahankali ya qarasa ya tsaya ya kalli wayar ganin hoton khadija gaban wayar yasashi
'dauka dan ya tabbatarda tatace ta yadda.
Juyawa yayi yakoma ciki daidai shigowar ayeesha ta gate tazo gurin tayita dudduba wayar bata
gantaba ta lalla6a takoma.
Turus tayi jikinta na 'dan rawa ta ha'diye wani mugun yawu ganinsa tsaye tsakiyar 'dakin.
Cikin mamaki ya kafeta da ido sbd har lokacin ruwan toilet 'din aiki suke ya tsammaci tana ciki.
Tun kafin yayi magana tarigasa da cewa,
Am dama dana Shiga nan toilet 'din ruwan ciki ya tsaya sainaje na bedroom "dina ashema na
manta nabar wannan akunne gashi yanxu ya kawo bari na kashe.
Qala baice mataba sai ido daya bita dashi yana naxarin yanayinta daya nuna duk a ru'de take
da ganinsa a farke.
Hankalin mama yakai qololuwar tashi ta fito Palo tafara dudduba ko Ina ba khadija tuni tsoro da
fargaba suka shigeta.
Motsinta ya fiddo da inna Rabi nan itama hankalinta ya tashi suka bu'de qofar palo suka
dudduba harabar gidan.
Ummi ce itama ta taso jin motsi Allah yasa dady yakoma tana 'dakinta na qasa shiyasa tajisu.
Tuni mama jikinta yafara sanyi hawaye na Neman tsinke mata.
Wayar Jamaal ummi takira ta sanar dashi ba 6ata lokaci ya fito tareda wayar khadijar a
hannunsa yace,
Yanxu bada da'dewaba naji motsi nafito amma wayarta kawai nagani a qasa.
Da hanxari mama ta kar6i wayar jikinta na mugun rawa tace,
Daidai ina ka tsinci wayar?
Nuna mata gurin yayi taqarasa gurin da sauri ta duqa tana dubawa taga jini kwance a gurin.
Durqusawa shima yayi cikin mamaki dan da farko Sam bai luraba,,
Jinin suka farabi har bayan flowers kafin kuma suka cigaba dabi inda jinin yabi har gate.
Jiki na rawar tashin hankali mama ta bude gate 'din tareda sakin wani razanannen ihu ganin
khadija kwance shame shame cikin jini kamar gawa.
Cikin sauri Jamaal ya fito da mota gaba 'dayansu suka 'dunguma zuwa asibiti.
Suna isa aka kar6eta cikin gaggawa duk da tsakar dare ne asibitin akwai wadataccin doctors.
Zaman 'yan bori mama tayi tana risgar kuka zuciyarta na tafasa.
Jamaal kuwa zama yayi tareda dafe Kansa yana tunanin alamarin.
Idan har yanda sukabi jininta to tabbas
A daidai inda ya tsinci wayarta adaidai gurin akai mata koma menene kafin aka jata bayan
flowers tukuna kuma aka kuma 'daukarta ya jefota wajen gate.,,
Idan kuma hakan ne to koma menene ko wayene hakan na nufin 'dan cikin gidan ne tunda aciki
komai yafaru.
Lumshe ido yayi tareda tunano ranar da aka shigo gidan lokacin da akazo ta windon neesah,
Ko a wannan lokacin tabbas wani daga ciki ne ya bude musu gida a zatonsa Ahmed ne to
yanxu Ahmed bayanan to waye?
Ana kiran sallar asuba doctors 'din dasuke ciki suka fito kowanne fuska ba da'di.
Dr sulaiman Wanda case 'din neesah ke hannunsa yanxuma na khadijar a hannunsa ya fa'da
shiya kirasu office 'dinsa bayan ya zauna ya 'dago ya kalli mama dake tsiyayar hawaye kamar
numfashinta zai 'dauke
Maida kallonsa gurin Jamaal yayi murya a sanyaye yace,
Captain maganar gaskia akwai matsala sbd patient 'din nan ba qaramar buguwa kanta yayiba
dan harsaida mukai mata 'dinki yanxu.,,
To duk madai ba wannan ne babbar matsalarba
The biggest problem is she was injected by par*****POI's.
Murya na rawa mama tace,
Me hakan ke nufi Dr?
Girgixa kai yayi cikin tsananin jimami yace,
Jikinta ya mutu gaba 'daya,
Bazata iya tashiba,
Bazata iya motsiba,
Bazata iya maganaba kawai banbancinta da gawa shine numfashi..
Yanke jiki kawai sukaga mama tayi a sume.
Nurse Dr yakira suka 'dauketa aka nufi emergency da ita.
Ummi ma jikinta rawa ya 'dauka gashi dama yanxu lafiyartata sai ahankali tun rasuwar Ahmed.
Riqeta Jamaal yayi shima idanuwansa a rine sbd alamarin gidansu yafara basa tsoro.
Kallonsa Dr yayi yace,
And one more thing shine wannan alamarin is a serious case sbd allurar laifine saida ita dan
haka zamuyi involving hukumar bincike ciki domin agano waya siyeta,gurin wa aka siyota kawai
dai ka duba inda kuka 'daukota ka samo mana syringe 'din da akai allurar zamu fara tracing
hannun daya riqe syringe 'din.
Ahankali yace,
Yes Dr nima zanyi farin ciki idan akayi hakan sbd alamuran sunfara zama ru'du sosai.
Bayan gari yayi haske ansamu mama ta dawo hayyacinta su ummi suka nufi 'dakinsu neesah
dabaida nisa dana khadijar Duk a amenity suke.
Sosai hankalin mamy yatashi lokacinda ummi tasanarda ita halinda ake ciki
Neesah dake kwance zuru batareda sunsan tuni ta warkeba hankalinta yatashi matuqa idonta
suka cika taf da hawaye shikenan ta rasa only hope datake dashi akan munafurcinsu ayeesha
kuma tasan bako tantama wannan aikinsu amma tasan dole akwai dalilinsu nayin haka dole
akwai abinda suka aikata khadijar tagani. Zataso tayi magana da mama amma batasan ya zatayiba.
Jamaal kuwa gida yakoma ya koma ko shiga gate baiyiba ya fara tsayawa bakin qofar gidan ya
fara dudduba syringe 'din.
Harya fidda ran ganinsa sai gashi yagani saidaya saka gloves tukuna ya daukesa yakoma
asibiti direct office 'din Dr yaje yakai masa.
Kallonsa Dr yayi bayan ya kar6a yasaka cikin wata leda bag yace,
Well yanxu zuwa gobe zamu cire Tom print 'din dake jiki
Su kuma patients 'din zamu sallamesu gobe kafin daga baya zamu San yanda zamuyi mu samu
Tom print na duka members 'din gidan.
Har aka sallamesu neesah batasamu ganin mamaba saida suka fito domin tafiya gida.
Mamy ce riqeda hannunta sai inna Rabi dake gefenta 'daya.
Khadija kuwa kamar gawa haka aka 'daukota aka saka cikin ambulance sukuma suka shiga
motar Jamaal duk da jitake kamar xuciyarta zata qone sbd ganinsa.
Koda suka isa gida ayeesha ta qyalla ido tagansu hankalinta ya tashi takira zeey tasanar da ita.
A 'daki aka kwantarda khadija neesah ma 'dakinta mamy takaita.
Har dare neesah na buqatar ganin mama amma mamar bata fitoba tana gaban khadijarta
datake gani kamar gawa.
Tsakar dare bayan mamy tayi bacci ta lalla6a ta sauko gado tareda fitowa ta fa'da 'dakin
khadijar.
A zabure mama ta tashi tareda zaro shar6e6iyar wuqa qarqashin filonta.
Ganin neesah tasaki siririyar ajiyar zuciya tareda maida wuqar ta sauko gado tana kallon
neesah tace,
Meyasa kika fito idan wani ya ganki aka gano kinwarkefa.
Khadija ta kalla cikin jimamin dama ita mugunta fitsarin fako ce amma kuma ta tausaya mata
duk da haka.
I'm really sorry mama akan abinda yasamu khadija but abinda nakeson fa'da miki shine nasan
dole akwai dalilin dayasa sukai mata haka idan son samu ne inason nasani.
Shiru mama tayi cikin nazari kafin tace,
I must say my khadija is right this people are very dangerous amma zan nuna musa komai na
duniya akwai na gaba akwai na baya.
Mamuh💋
🌲 *R H F W F*�
_Don't forget to vote, follow and comments_
*_DACEWA_*
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*_Viawattpad@mamuhgee_*
*56-57*
Washe gari mamy tayi shirin komawa Jamaal yakaita airport ta wuce dama neesah a matse
take da mamy takoma sbd sam batason su ayeesha su cutatar mata da ita.
Yana dawowa ya tararda yusuf a gidan..mamaki yayi sosai yana kallonsa sbd koda safe sunyi
waya amma bai fada masa zaizoba.
A palon ummi suka zauna suna Yusuf 'din na fira da ummi kafin Jamaal 'din yashiga 'dakin
neesah don fito da ita Yusuf ya dubata.
Zaune gaban mirror hawaye take sosai sbd kewar Ahmed data taso mata.
Half rubber gown ce ajikinta sky blue mara hannu sai gashinta da ummi ta 'daure mata tsakiyar
kai.
Kallonta yayi sosai yanajin wata muguwar kewarta na cinsa sbd rabon daya ganta in one 'dinta
tun kafin cikin ayeesha ya zube.
Danne 6acin ranta da tsanarsa tafara qoqarin yi tareda miqewa taje bakin window ta tsaya
tareda folding hannayenta.
Matsowa yayi ahankali tareda kai hannunsa ya riqo nata.
Ajiyar zuciya ya sake tareda lumshe idanuwansa.
Rintse idanuwanta tayi sbd jitayi kamar wutar lantarkice ta jata.
Sakinta yayi tareda bude wardrobe ya 'dauko dogon hijab yasa mata tareda riqo hannunta suka
fito palon.
Zaunar da ita yayi kusada ummi.
Kallonta tsaf Yusuf yayi tareda yimata sannu da jiki batace qalaba saidai idanuwa data bisa
dasu.
Ummi ce ta miqe tashiga 'dakin khadija Jamaal kuwa wayarsa datai qara ya 'daga sbd ganin
dady ne.
Fakaitar idonta yayi ya karka6a handkerchief 'dinsa ka'dan..
Tari tafara sosai Jamaal yayi saurin katse wayarsa yana kallonta Yusuf yayi saurin miqa masa
glass cup cikeda ruwa yace,
Bata tasha zata samu relief.
Kar6a tayi da sauri tasha sbd sosai taji mugun tarin kamar maqoshinta zai fita.
Tana shanye ruwan ta aje cup 'din tareda miqewa ta fa'da bedroom 'dinta.
Sake kiran dady Jamaal yayi Yusuf ya fakaici idanuwansa ya 'dauke cup 'din da neesah tasha
ruwa ya jefa cikin briefcase 'dinsa.
'Dakin khadija suka shiga nanma saidaya samu ya fakaici idanuwan kowa ya samu ya 'dauke
remote 'din Ac da mama ta kunna ta aje.
Sosai yakeson Tom print 'din khadija amma ba dama can idanuwansa suka hango masa
wayarta gaban mirror batareda kowa ya luraba ya zurata aljihunsa suka fito palo ya 'dauki
remote 'din palon da ummi tai amfani dashi.
Harzasu fita ya bude murya yace,
Inna Rabi empty cup zanje dashi masaukina zanyi amfani dashine.
Kallon mamaki Jamaal ya aika masa amma baice komaiba suka fito daidai ayeesha zata shiga
gurinsu ummin.
Dariya Yusuf yasaki yana cewa,
Amaryar captain kinsamu kinshigo kota kanmu kindaina bi.
Cikin sakin fuska tace,
Wlh aa hankula ne wlh sunqi su kwanta shiyasa,,yaushe kashiga garin namu.
Yau 'din nan nashigo wani aiki amma insha Allah zuwa nextweek nagama aikina nakoma sbd
aurena nima dayake gabatowa.
Kallonsa Jamaal yakumayi sbd shi Sam baisan da wata maganar aurensaba.
Wata waya ya fitar ya miqawa ayeesha yace kinga matata dazan aura.
Kar6ar wayar tayi tareda duba hoton tace,
Eh tanada kyau Allah yabada sa'a.
Ameen yace tareda kar6ar wayar suka wuce.
Key 'din motar Jamaal 'daya Yusuf yakar6a har zai shiga saiga zeey tashigo gidan sanyeda
dogon hijab
Kallo 'daya Jamaal yayiwa gefen ya 'dauke kai.
Yusuf kuwa kallonta yayi dakyau yacewa Jamaal wannan tana yawan zuwa nan gidan ne?
Yes and why did you ask?
Nothing I just want....kawai bari na tunkareta.
Matsawa yayi da 'dan hanzarinsa ya tareta yana murmushin yace,
Yan mata naganki ne kuma nakasa hkr sbd zuciyata ta kamu yanxu dai ina sauri rubuta min
number ki I will call anjima saimuyi mgna.
Cikin mamakinsa ta kar6i pen 'din dayake bata ta rubuta masa ta wuce.
Yana barin gidan direct asibiti ya nufa a office 'din Dr sulaiman ya fito da komai suka hau aiki
akai.
Tashin farko tomprint 'din zeey yayi matching dana jikin syringe 'din.
Shiru sukayi na tsawon lokaci kafin Yusuf