Showing 6001 words to 9000 words out of 52687 words

Chapter 3 - DACEWA Book Complete Document by M amuhagge .pdf

12 Mar 2025

5664

Jamaal sakamakon tozarci da akaso yimana ta hanyar fasa auren aneesah yasa ni

mahaifinka na yanke hukuncin nema maka aurenta ayau dan haka yanxu aneesah matarkace
ina fatan ka fahimceni kuma zaka zamo maiyimin biyayya.

Abban neesah ya kar6i zancen da cewa,

Kuma idan ma kanada wadda kakeso ko ayau zamu iya nema maka aurenta mu hadamaka da
ita..


Sosai su abban suka hango tsantsar 6acin ransa duk da Jamaal din namijin gaske ne gurin iya
6oye 6acin ransa saidai idanuwansa ne suka nuna sbd ka'dawar dasukai.

'Dagowa yayi yakalli dadynsa kafin ya duqar da Kai a maze yace,

Shikenan Abba ngd Allah ya qara girma.

Yana fadar haka ya miqe tareda ficewa a harabar gate din gidan ya hadu da Yusuf
Kallo 'daya yamasa ya 'dauke kai ya nufi mota Yusuf ya qaraso suka bar gidan.

Ta gefen ido Yusuf ya kallesa dan tabbas ran Jamaal din a 6ace yake,

Where are we going Yusuf ya tambayesa a tausashe?

Airport,
Yafada tareda lumshe kyawawan idanunsa cikin wani yanayi.




Neesah bata farkaba sai wuraren 4,
Wanka Anty mamy takaita toilet tayi kafin amirah takawo mata tea mai zafi tasha tareda
magani.

Sallolinta ta ranka tana idarwa ummi da mamy suka shigo.

Ya jikin baby? Ummi ta fada tana dafa kanta.

Kwantarda kanta tayi a cinyar ummin tana cewa,
Ummi jikina da sauqi amma zuciyana ba da'di.

Mamy ce ta fita 'dakin dan kuwa taso itace zata fadawa neesah maganar aurenta da Jamaal
dan tasan neesah straight forward take bata 6oye 6acin ranta tsaf zata fadawa ummi batason
'danta.

Ummi kuwa cikin farin cikinta tace,
Baby dama dole zakiji rashin jin dadi sbd fasa aurenki but koyaushe dama Allah maji roqon
bawane domin kuwa Allah yayi miki sauyi da mafificin alkhairi insha Allah.

Ummi ciwo nakeji sosai a zuciya na,
Ummi inason taheer to the extend da bazan iya aure idan badashi ba.

Cikeda tausayi duk da zancen ya daki zuciyarta ummi tace,
Baby kidaina fadar haka domin kuwa ke yanxu matar waninsa ce,.

'Dagowa tayi daga jikin ummin tana kallon fuskar ummin tace,
Ummi.....
Yes baby dadynku ya daura aurenki da Jamaal ayau.

Wani murmushin takaici tasaki kafin tace,
Ummi wane Jamaal 'din?

Jamaal 'dan uwanki mana.

Zabura tayi tsaye cikin tsananin baqin ciki da tsantsar takaici tace,

Wallahi bana sonsa har cikin raina,
Kuma ma dan ba'a sona ba'a qaunata a rasa da Wanda za'a hadani aure dan an fasa aurena
sai Jamaal,yaronda na girma dan cin fuska.

Kamota ummi tayi jiki a sanyaye tace,
Baby kadaki 'daga hankalinki tunda kinga bakyajin dadi indai akan Jamaal ne wlh bazan ta6a
bari yayi miki wani cutatarwaba indai ina raye....

Wlh ummi bazan zauna dashiba dan wlh bana sonsa kuma....

Saukar mari taji ta juyo a tsorace.

Mamy ce tsaye tana watsa mata kallon takaicin yanda take ciwa ummin fuskar wai batason
'danta.

Sai alokacin wasu hawayen takaici suka gangaro mata ta durqushe qasa tareda sakin kukan
takaicin Jamaal da kowama daya hada auren.



*R H F W F*

Mamuh馃拫
[3:20AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: *_DACEWA_*
_(when east meets west)_



_By_
_Mamuh geee_


*12-13*
Duk iya yanda su mamy suka tsammani aneesah to ta wuce nan dan kuwa kuka take tamkar
ranta zai fita.

Amirah da ummi sunyi lallashinta harsun gaji amma ta kafe akan lallai ita bazata zauna da
Jamaal ba.

Lokacin da Abba yakirata palonsa tsayawa yayi kallonta cikin takaici.

Kuka take sosai ga ummi datai zuru tana qara lallashinta duk da tanajin damuwar yanda neesar
ke kukan qin Jamaal.

Ajiyar zuciya Abba ya sauke cikin sigar lallashi yace,

Neesah kiyi hkr kema kiyi mana biyayya tinda shima dayake namiji bai bijirewa hukuncinmu
bare ke da kike mace,

Koba komai ba ga umminki nanba zaki zauna tareda ita tunda burinki kenan koda yaushe.

Hawayen baqin ciki ta goge da hannunta cikin dasashiyar murya tace,

Abba dan Allah nidai Ku za6amin wani zan zauna dashi amma wlh ni Sam banason Jamaal ko
kadan amatsayin miji.

Harara mamy tasakar mata cikin takaicin taurin kai irin na neesah.

Tsuke fuska abban yayi ahankali kafin yace,
To naji ra'ayinki saidai ni ba ra'ayinki na tambayaba dan haka ba ruwana da ra'ayinki kije
kifara hada kayanki dan wlh aure babu mai warwaresa.

A razane ta kalli abban tana qoqarin danne baqin cikin dake barazanar fixge numfashinta.

'Daki takoma ta zauna bakin gado idanuwanta dasuka kumbura na qara tsiyayar hawaye.


Amirah ce ta matso cikin sanyin jikin tausayin qawarta dan gskia badan girman kan aneesah da
shegen son girmanta da saitace to babu kamarta a fagen samun miji domin kuwa Jamaal ya
damesu ya shanye a fagen class da duk wata wayewa da girma dasuke ganin sunada shi uwa
uba ga kyau da naira.
Neesah dan Allah kidaina 'daga hankalinki domin kuwa tashin hankalin nan bazai baki abinda
kikeso ba saima lalata abubuwa dazaiyi.

Koba komai kiduba yanda ummi ke tsananin qaunarki duk tabi ta damu akanki amma ba kunya
kike dagewa da bakya qaunar 'danta a gabanta,

Ni aganina ma dakinbi abin a tausashe to saiki ga ummin da kanta tabi bayanki kin samu
abinda kikeso.

Kallon amirah tayi da kumburarrin idanuwanta tana qoqarin danne takaicinta tace,

Wlh bazan iya Rayuwa da wannan baqin cikinba,
Yanxu kamarni a kallen ace wai anhadani auren da mutumin danake masa kallon qani agurina,
Cutatuwa zamuyi mu duka dan wlh bazan kwantar da kaina nayi biyayyaba gun qanina
Haka shima yanda nasan shegen girman kansa bazai ta6a kwantarmin da kaiba,
Kinga kenan antarwatsa min burin rayuwar danaso tsarawa a gidana na aure,meyasa taheer ya
cuceni ya fasa aurena alhalin munyi alqawarin gina kyakkyawar Rayuwa a tare.

Su siyams ne suka shigo dukkaninsu fuska qunshe da daria sbd sanin a kwai qura agun
neesah.

Fahimtar zasu iya kawo mata rainin wayo yasa ta miqewarta ta shige toilet.

Cikin kanne daria amirah tace,
Allah kukai mata daria fada zakuyi dan gskia she seems very serious akan zancenta na
bazata yarda da aurenba.

Asmy na tu6e doguwar rigarta tace,
Neesah is different, dan nikam hundred percent captain Jamaal yayimin koba komai ai ba
kowa yasan itace ta girmesaba sbd yanayin jikinsu ma ba 'dayaba.

Cikin daria siyama tace,
Koba komai da gani zai iya haukata mace a fagen making love sbd yanayin qirarsa ta

ingarman namiji.

Daria suka sheqe da ita gaba dayansu.




*******
Zaune take bakin gadon 'dakinta idanuwanta sunyi jajir sbd kukan data kwana ta yini tana sha.

Kallon wayarta tayi a karo na ba adadi tana jiran kiransa amma shiru.


Miqewa tayi ta isa bakin window ta tsaya cikin sabon takaicin halin ko inkula irin na Jamaal.

Jamaal kayi babbar sa'a zuciyata ta riga tayi mugun nisa akan sonka da wlh saina zamar maka
masifa da bala'in da bazakaga tahowarsaba
Amma ko ayanxu saika 'dan'dani mugun baqin dafina dayafi na kunama zafi,
Ko wacece ka aura saina zamar mata baqin macijin da bataji bare tagani saidai taita jin dafina
acikin jininta.


Toilet ta fada tayo wanka tana fitowa ta shirya cikin doguwar riga ta fito palon inda ta tarar da
umman ta nata faman fira da aminiyarta haj shema'u.

Kwanciya tayi a two seaters tareda danna kiran wayarsa.

Shiru number bata shiga saita kira ta qasar wajensa.

Ringin tafara harta katse bai daukaba.
Qara kira tayi harta kusa katsewa ya 'daga.

Taso yimasa rigima amma yanayin muryarsa dake a 'daure yasa ta fasa dan gudun 6ata ransa,
cikeda kissa a kasalance tace,
Captain ka koma without informing me?

Shiru yayi mata,tasake cewa,
Lafiya kuwa captain or.....

For god sake ayeesha how many times zan fada miki banason yawan tambaya just tell me
dalilin kiranan.

Siririn kuka tasaki a hankali harda shesheka.

Shiru yayi yana sauraronta duk saiyaji tabasa tausayi sbd yasan dole ne tadamu akan aurensa
kai tsaye.

Jingina yayi da kujerar palonsa dayake zaune ahankali cikin cool voice dinsa yace,

Eshaah,
Eshaah meyasa kikeson kuka akoda yaushe bayan kinsan babason kuka.

Cikin muryar kuka tace,
Koyaushe kukana akanka ne captain sbd soyayyarka dake azabtar dani.

Yanxu gashi kayi aure ni yanxu banida stand akan.....

Ok naji daina kukan sai muyi magana.

Share hawayenta tayi cikin son qara samunsa tace,
Pls captain don't leave me, I promise I can wait har time 'din daka shirya kar6ana.

Tausayinta ya qara shigarsa sbd hakurinta yasa koda yaushe yake qara sonta.

Naji ammadai yanxu kidaina kuka I will call anjima sainaji idan kin daina kukan saina fada miki
sumtin sweet OK?

'Daga kai tayi kamar yana kusa da ita.

Tana aje wayar ta kalli Umma data nutsu tana kallonta cikin farin cikin yau tasake tadaina kuka.

Ita kuwa murmushin fara samun nasara tayi cikin shirinta na tarwatsa rayuwar neesah datayi.




*********
Zaune take a palo tana waya da asmy mamy na asibiti burin aiki Anty mamy ma takoma,ummi
kuwa tana 'dakin mamy waya takeda Jamaal.

Abba ne yashigo palon ta datse wayar datake ta gaidasa tareda cewa,
Abba dama inason gobe zan koma makaranta kuma gashi motana taqi tashi.


Neesah keda zaki bar gari wace makaranta kuma,
Kibari idan kinje can saiki dora.

Cikin dakewa tace,
Abba ni anan nafison na qarasa karatuna Kuma dan Allah Abba kabarni nayi zamana anan.


Kallonta yayi ganin da gaske take yace,
Naji amma nama fasa abinda nayi niyya na barinki anan har Jamaal ya dawo tashi jeki ki
hada kayan gobe zakibi ummi Ku koma can kafin Jamaal 'din yadawo.


Magana zatayi ya daka mata tsawa tayi dakinta cikin baqin ciki da takaici.




*R H F W F*



Mamuh馃拫
[3:20AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: *_DACEWA_*
_(when east meets west)_



_By_
_Mamuh geee_



*_Viawattpad@mamuhgee_*



*Balkeey Shuwerh I sincerely heart you*鉂�



*14-15*
Tun acikin daren take kuka shiyasa koda ta tashi da safe idanuwanta sun kumbura.

Fushi take da kowa a gidan dan haka ko breakfast bata fitoba.

Ummi taso zuwa ta rarrasota amma mamy ta dakatar da ita ta hanyar miqewa ta nufi 'dakin.

Zaune ta tarar da ita gaban mirror 'daure da towel alamun wanka ta fito.


Akwatinanta mamy tajawo ta bude wardrobe ta kashe kayan ciki tsaf ta jere matasu a akwati ta
rufe akwatinan ta matsar gefe tareda zama bakin gado ta fuskanci neesah.

Hawayen datake dannewa suka gangaro mata ta 'dauke kai daga kallon 6angaren mamy.

Neesah,
Neesah hakan dakike qoqarin yi baida banbanci da abinda su taheer sukai mana na fasa auren
'yarmu a ranar 'daurin aure.

Mune iyayenki dasukafi duk wani mai sonki qaunarki amma kike qoqarin bijirewa buqatarmu
akan wani dalilinki na banza,

Shi Jamaal 'din da kike rainawa kina masa kallon wanda kikafi qarfi tabban idan bakiyi ahankiba
wataran saikin zubar da hawaye akansa illaima na sonsa illaima na qaunarsa.


Jajayen idanuwanta ta kalli mamyn dasu murya a karye tace,

Mamy dan Allah Ku tausayamin kadaku yankemin hukuncin dazai lalata farin cikina wlh ba
laifina bane dana kasa sonsa,

Nayi iya qoqarin dannewa amma na kasa kodan sbd ummi amma wlh mamy bana son ko
sunansa naji ana fada amatsayin mijin danake aure.

Takaicin neesar ne yafara kama mamy amma sbd son ta rarrasheta saita dake tace,

Neesah ki daure kiyiwa iyayenki biyayya kodan yanda dadyn Jamaal yayi saving 'din abbanki
daga humiliation 'din dasu taheer suka tanadar mana a idon mutane,

A 6angare 'daya haka zaki sakawa ummi da tsantsar soyayyar datake yi miki tun kina
qanqanuwa,

Neesah ko kunyarta bakyaji na yanda kika fito kai tsaye kika nuna bakya qaunar 'danta datake
matuqar so.

Hawaye suka gangaro a fuskar neesah batareda ta gogeba murya a qarye tace,

Mamy har abada bazan qi jinin ummi ba amma wlh mamy bana sonsa amatsayin abokin

Rayuwa.

Tsuke fuska mamy tayi tareda miqewa tsaye tace,

Tunda lallashi baya yimiki sai ayimiki yanda zakifi ganewa,
Ki tashi ki saka kayanki 10:00 flight 'dinku zai tashi zuwa Lagos.
Kuma wallahi a matsayina na mahaifiyarki ban yafe ki ce komai ba akan tafiyar nan.

Ficewa tayi a fusace takoma Palo.




Baqin ciki da takaicin datake ciki bamai faduwa bane ta danne abinta cikin ranta tareda
'daukarwa kanta mugayen alqawaririka akan Jamaal dabaimasan tanayiba danshi tuni ya aje
zancen auren a gefe ya maida hankali akan alamuran gabansa.


Abba sosai yayi mata nasiha hakama mamy duk da tana fushi da ita.

Nasir ma na gida a ranar sbd Saturday ce ba school
Sosai yashiga damuwar tafiyar antynsa duk da kullum sai sunyi fada sbd shegen son girmanta
da rainasa datayi Wanda shi kuma bayason hakan dan yace so yake shima Idan ya qara girma
yazama handsome cool guy kaman Jamaal.


Har suka iso Lagos batace qalaba hakama batai ko guntun hawayeba sbd alqawarin datai na
bazata qara zubar da hawayenta a banxa ba.



Ahmed yazo 'daukarsu daga airport danshi tuni suka dawo tareda dady.


Anty nee ya hanya?

Qin kulasa tayi sbd akwai 'yar tsokana a tsakaninsu itada Ahmed 'din sbd shi ya iya bi da ita a
yanda takeso.


Murmushi ummi tayi tace,

Ahmed kadaka dami baby bata cikin yanayin tsokana yanxu.

Tofa ummi yanxu fa sai kowa ya kama kansa sbd 'yar gaban goshi tazo kowama yanzu mai
laifine Idan ya ta6ata.

Harara neesah ta 6alla masa duk da tana cikin damuwa.

Daria yayi dan yaga hararar yace,
Sorry Anty babba kada idon su juye.

Koda suka iso gida dady baya nan mai aikin ummin ce inna rabi ta iso tana musu barka da
zuwa cikin farin ciki.


Babban gidane mai 'daukeda part uku,

First one na Jamaal ne mai 'daukeda parlour da qaton bedroom aciki,

Second one 'din kuma na Ahmed ne kusan irin na Jamaal shima,

The third and last one 'din shine babba sosai na iyayensu,

Babban Palo ne a qasa da 3 bedrooms kowanne da toilet,

'Daya shine na Ummy sai 'dayan na khadija ne 'yar qanwar dady da ummin ke Riqo.

'Dayan kuma na saukar manyan baqin ummin ne,.

Sama kuma gaba 'dayansa na dady ne.

Ko'ina acikin gidan ka kalla abin burgewa ne gashi koyaushe qyal qyal a tsaftace sbd dukkanin
'yan gidan masu tsaftane uwa uba inna Rabi datake kula da tsaftarsa dan a yini zatai gyara ba
adadi duk da bawai wata 'daudar yayiba.

Inna Rabi dattijuwa ce datake aiki a gidan tun Jamaal na yaro Wanda yanxu ta zama tamkar
'yar uwa a gidan sbd sabo da yarda dasukai da ita bama kamar Jamaal da yake qaunarta har
ransa sbd yanda take tsananin qaunarsa tun yana yaro haryanxu daya girma muddin yana gari
to duk hidimarta tasace.

'Dakin ummi neesah tashige dan dama ko zuwa tayi anan take sauka dan haka yanxuma anan
zata zauna.

Tsabar karma ayi mata maganar zama inda ba nan 'dinba ta bude 'dayar wardrobe 'din Ummy

ta Jere kayanta.

Tu6ewa tayi ta shiga toilet tayo wanka tana fitowa tayi sallah kafin ta zauna gaban mirror ta 'dan
shafa mai sbd yanayin garin da sanyi.

Doguwar rigar shaking material tasaka mai yankaken wuya da qaramin hannu ta zari wayarta ta
fito Palo sbd yunwa datakeji.


Daidai qofa sukai kusan karo da khadija dazata shigo bedroom 'din sbd dawowarta kenan daga
schools ta tarar dasu ummin sun dawo shine takeson mata barka da dawowa cikin farin ciki.

Cak ta tsaya ganin neesah batareda ta tsammata ba,babban abin mamakinta neesah dasu
ummin sukaje aurenta itace tafara fita harta biyosu.


Jiki a sanyaye tace,
Anty neesah barka da zuwa.

Daqyar neesah ta amsa tana qaqalo murmushi kafin ta wuce zuwa palon tana kiran inna Rabi.


Khadija kasa qarasawa 'dakin tayi ta juya 'dakinta jikinta a matuqar sanyaye ga hawayen datake
qoqarin maidawa.


Tana shiga 'daki tai wurgi da handbag 'dinta tareda zama bakin gado zuciyarta kamar zata
qone.


Khadija ba mummuna bace hakama bazaka kirata da kyakkyawa sosaiba saidai tanada diri mai
matuqar kyau da 'daukar hankali,

Khadija tun tashinta ta taso da tsananin hassadar aneesah sbd ganin gata,kyau,dukiya,wayewa
duk neesah tasamu uwa uba tsananin soyayyar da kowa ke mata bama kamar ummin wadda
ita bata samu koda rabinta agurin ummin ba.,

Duk wa'innan abubuwan kanta tasowa sbd babban burinta ne tazama rich,
Pure natural Beauty,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login