Showing 18001 words to 21000 words out of 52687 words
Chapter 7 - DACEWA Book Complete Document by M amuhagge .pdf
secret?
Saurin rintse ido yayi yanajin 6acin rai da fushi.
Zamewa yayi ya kwanta idanuwansa a lumshe yana fatar wannan tunanin na Ahmed da
kowama yafita ransa.
Da safe da wani mugun ciwon kai khadija ta tashi amma haka ta daure ta girka breakfast sbd
ummi datace tayi.
Komai ta gama ta ha'da nasu neesah a basket ta aje tashiga 'dakinta tayo wanka ta shiryo dan
itace zatakai abincin duk da zuciyarta ba qaramin dauriya takeba gurin ganin ta danne baqin
cikinta da damuwarta.
Doguwar Riga baqa tasaka tareda siririn yellow Vail ta fito ta 'dauki basket 'din ta nufi 'dakin
ummi.
Zaune ta tarar da ita a gado ta gaidata tareda cewa,
Ummi zan kai musu breakfast 'din daga can inason naje gurin saloon.
'Daga kai ummi tayi sbd yanda kan ke mata ciwo itama na rashin bacci da damuwar data kwana
da ita jiya akan bala'in dataga na shirin afkowa tsakanin 'yayanta dan Abinda tagani jiyan a
idanuwan Ahmed ya tsoratata sosai hakama tasan tsaf Jamaal ya dame Ahmed ya shanye
fagen taurin rai da zuciya mai tsanani.
A hankali ummi ta bu'de baki tace,
Ki gaidaminsu kafin na qaraso anjima Insha Allah.
To,,tace tareda ficewa jiki a sanyaye.
Tana Sanyo kan motarta wajen gate din gidan daidai zeey zata shigo amma mai gadin ya
dakatar da ita akan neesah batanan.
Tsayawa khadija tayi tareda sauke glass takalli zeey ba 'daurewa ba sakewa tace,
Neesah na asibiti tun jiya idan xaki ne muje can zani.
Shiga motar zeey tayi tana mamakin yanayin khadijar sbd yanda take ba wata walwala atareda
ita.
Har suka isa ba Wanda yayi mgn
Tanayin parking suka fito atare suka nufi 'dakin gaban khadija sai tsananta nauyi yake duk
taqara taku guda na zuwa 'dakin.
Har lokacin barci take Inna kuma na zaune tana gyangyan'di.
neesah zeey ta nufa kamar zatayi kuka tana cewa,
Neesah Allah ya sassauta miki wannan jarabawa.
Ameen inna race tana karbar kayan hannun khadija.
Ido khadija ta kafawa rigar Jamaal dake jikin neesah tanajin karyewar zuciya da hawaye na
yunquro mata.
Abincin inna ta 'diba ta fita waje dan taci
itama khadija juyawa tayi ta fice jiki ba kwari.
Miqewa tsaye zeey tayi tana shu'umin murmushi ta bu'de handbag 'dinta taciro wata kwalba
tana dariya ta nufi abincin ta bude flask 'din ruwan tea tazube gaba 'daya abinda ke cikin
kwalbar ta rufe flask 'din
Tana juyowa gabanta yayi mummunar yankewa nan take jikinta ya'dau rawa sbd khadija data
gani tsaye bakin qofa tana kallonta.
Zufane ya yanko mata cikin rawar murya tace,
Um um um maganin.....
Wuceta khadija tayi ta zura hannu cikin basket 'din data kawo musu abinci ta 'dauki mukullin
motar ta tafice cikin wani irin yanayi bawai dan bata ga abinda zeey 'din tayiba
Bata buqatar sanin koma meyene manufar zeey akan neesah dan tun kallon farko dataiwa zeey
ta fahimci babu alkhairi a tattare da ita amma koma meyene ba abinda ya shafeta koma kashe
neesah zatayi.
Yawu zeey ta ha'de tareda sakin ajiyar zuciya dataga khadijar ta fita batace komaiba alhalin ta
ganta sarai.
Komawa kujera tayi ta zauna tana share xufa cikeda mamakin khadija.
Ahankali neesah ta bude idanuwanta daidai shigowar Ahmed tareda Dr da nurses guda biyu.
Kallonta Dr yayi yana murmushi yace,
Finally sleeping beauty ta tashi.
Ahmed dake kallonta cikin murmushi yace,
Dr inajin kunyanka fa sbd wannan sunan yayi maka nauyi.
Dariya sukai dukkaninsu ita kuwa lumshe idanuwa tayi tanajin wata irin matuwar jiki.
Fita Dr da nurse 'din sukai bayan ya duba file 'dinta yayi rubutu aciki.
Matsowa kusa yayi tareda kafeta da fararen idanuwansa hannuwansa a har'de cikin wata
sabuwar lallausar murya yace,
Antynahhh..
Har cikin ranta taji yanda yaja sunan ta bu'de lumsasun idanuwanta ta 'dora akansa.
Kashe masa jiki idanuwanta sukayi ya tako ahankali ya zauna bakin gadon kafin yayi wata
magana ummi da Jamaal tareda khadija data dawo suka shigo 'dakin
Kyakkyawar fuskarnan ta Jamaal a ha'de.
Kujeja inna Rabi ta jawo masa tana murnar ganinsa
Zama yayi tareda amsa wayarsa dake ringin kallo 'daya yayiwa gurin dasuke ya 'dauke kai bai
kuma 'dagowaba yacigaba da wayarsa.
Ahmed ma 'dan tamke fuska yayi yana gaida ummi dake binsa da kallon tsoro da firgici.
Zee ma a ladafce tagaida ummin.
Amsawa tayi tana shafo kan neesah cikin kulawa tace
Baby Yaya jikin naki?
Kai ta 'daga alamar amsawa sbd batadaqarfin jiki ko ka'dan.
Inna Rabi kawo guri ta wanke bakinta ko tea ne tasha.
Da sauri inna tashiga toilet ta 'dauko bucket zeey ta 'dauko robar faro 'daya a fridge ta kama
neesah ta tashi zaune ta wanke baki Ahmed sai sannu yake mata cikin kulawa.
Ummi da kanta ta hada mata thick tea ta matso tafara bata ahankali tanasha.
Zeey ji take kamar ta kar6i cup 'din tajuyewa neesah gaba 'daya tashanye.
Sosai tasha tea 'din hartaji tasamu qarfi sosai ajikinta.
Kallon ummi tayi ahankali tace,
Ummi zanshiga toilet fitsari xanyi.
To tace tana qoqarin kamata tace,
No ummi kibarshi zan iya.
Ahankali take takawa saita tsaya cak tana hadiye yawu
Dafe cikinta tayi tana qoqarin kiran sunan ummi amma kumfan jinin daya fara fita bakinta ya
hana sai kawai ta zube sai ajikin Jamaal jini na fita bakinta tareda kumfa.
Ummi,Ahmed da inna atare sukayo kanta cikin tashin hankali saidai wani matsiyacin kallo da
Jamaal ya watsawa Ahmed ya hanasa qarasowa sbd wata kyakkyawar runguma yayi mata data
fa'do jikinsa.
Dr Ahmed ya fita da gudu yana qwalawa wani mahaukacin kira.
Ummi kuka tasaki tana kiran sunan neesah duk a rude.
A sace zeey takalli gefen khadija suka ha'da ido tai saurin 'dauke kai tana gyara tsayuwarta
cikin hawayen tausayin neesah na kissa.
Khadija kuwa sinne kai tayi cikin hawayen dasuka 6alle mata na ganin neesah kwance jikin
Jamaal tasamu kyakkyawar runguma daga garesa ga wani tashin hankali datake hangowa cikin
idanuwansa duk da ba kowa ke iya gane fushinsa da 6acin ransaba bare tashin hankalinsa
kasancewarsa miskili amma yau ita tana iya hango tashin hankalinsa..
Ficewa tayi da Sauri tana sakin wani wahalallen kuka
A kuma lokacin doctors kusan Biyar da nurses hudu sukayo 'dakin a gaggauce.
_Ayshart bellow naga saqonki na tabayar wayafi wani mugun hali,hassada,baqin ciki da zama
maqiyin gaske a tsakain Ayeesha,,,zeey da khadija_
_gskia yanxu banida amsar baki saidai kiyi nazari ki tantance da kanki sbd dukkaninsu cutarsu
a 6oye take_
_Kuma maqiyi mafi ciwo shine Wanda kasani yake cutarka a 6oye_
*_Hassada mugun ciwo CE Allah ya karemu_*
Mamuh馃拫
馃尣 *R H F W F*馃悇
_Don't forget to vote, follow and comments_
[3:22AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: *_DACEWA_*
_when east meeta west_
_By_
_Mamuh geee_
*_Via wattpad@mamuhgee_*
*32-33*
Emergency room aka koma da ita a gaggauce sbd jinin dake tsananta fita baki da hancinta.
Ummi zuwa lokacin banda sharar qwalla ba abinda take hakama inna Rabi da duk tsoro ya
kamata.
Zeey ma dake tsaye sharar qwallar take afili amma cikin ranta adduar take Allah yasa hanjin
neesar sun riga da sun karkatse.
Jamaal kuwa barin gurin asibitin yayi gaba 'daya dan bayajin zai tsaya matuqar Ahmed na
gurin.
Ahmed kuwa saida ummi ta taso da kanta ta zaunar dashi da sbd tashin hankalinsa na qarfin
hali dataga na Neman yardashi daga tsayen.
Awa uku suna jiran tsammani kafin doctors biyu suka fito fuskokinsu a tsuke 'dayan Dr ya kalli
Ahmed dashine namiji cikin 6acin rai yace,
Bansan meyasa kuke wasa da lafiyar yarinyarnan ba hartakeson kashe kanta,
Jiya ta shiga ruwa danta kashe kanta and today kuma poison.,
Look inason kusani koma meyene takeso ko takeson arabata dashi to kuduba Alamarin sbd
idan yanxu munsamu damar saving 'dinta to bamusaan mai zaifaru next time ba,,
And I'm really sorry to say poison 'din dataci yanada Qarfi sosai and she lost alots of blood dan
haka first thing yanxu shine muna buqatar jini.
Will she be alright Dr?
Well I can't say anything about that for now all we need shine jinin kafin komai.
Kiran Jamaal jmmi tafara qoqarin yi cikin sauri saiji tayi Ahmed na cewa,
Muje Dr zan bayar da ko duka jinane asa mata matuqar zaiyi.
Riqosa ummi tayi yana lokacin da zaibi bayan Dr cikin qoasawa da sabon halinsa tace,
Ahmed meyasa za'a d'ibi jininka bayan akwai Wanda yafi cancanta da bayarwar,
Kaga ka aje wannan sabon halin naka tun kafin kakai qarshen hakurin Jamaal sbd banason
rigima ko wani tashin hankali musamman nasa tunda zuciyane dashi so stay away from his wife
ok.
Takaici da wani baqin cikin Jamaal da zancen ummi ne suka qulesa yace,
Ummi naji yafini cancanta amma shi Darling son 'din naki yana ina yanxu?
Bayanan sbd baya wannan tunanin da kikeyi sbd bata gabansa wama ya sani qila maiqi ta
zarce ba sbd yaji da'din more rayuwarsa da wadda yakeso dan haka ni 'din da bakyason
kusanci na da ita nine zan kula da ita to any extend,,for god sake ummi for how long zaki ringa
tureni daga abu kina tura Jamaal sbd ko yaushe kinfi sonsa akai.....
Tasss,,,,
Ta saukar masa da lafiyayyen mari tana tsiyayar hawayen tashin hankali.
Bai motsaba saima kallonta yayi da jajayen idanuwansa yace,
Ummi for the first time yau kin 'daga hannunki akaina sbd Jamaal.
Juyawa yayi zuciyarsa a karye yabar gurin zuciyarsa na quna banda tsanar Jamaal ba abunda
yake cinsa a rai.
Baya ummi tayi cikin tsoro da tashin hankali ta zauna da6as inna Rabi tayi saurin dafata tana
matsar qwalla itama.
Zeey dake tsaye ta sulale tabi bayan Ahmed.
Har aka 'dibi jininsa bai bar jin ransa na qunaba sbd ji yake duk duniya ba Wanda ya isa ya
rabasa da neesah koda kuwa ita kanta neesar zai iya yin komai idan tace zata rabasa da kanta.
Murmushi take tana tunin ba shakka sun samu hanya mafi sauqi dazasuyi amfanin da ita gurin
wargaza Jamaal da neesah sbd wannan mahaukaciyar soyayyar da Ahmed keyiwa
neesah,,hmmmn wat a foolish mistake Mr Ahmed.
Qarasawa tayi cikin 'dakin dayake kwance bayan an 'dibi jinin nasa qwalla tafara sharewa tace,
Mr Ahmed Allah yasaka maka da alkhairi daka bawa qawata jini kuma itama na tabbatarda
idan ta tashi babban farin cikinta ne ace Ahmed 'dinta ne yabata jini,
Ahmed 'din datake tsananin fa'dar yanda take sonsa cikin ranta.
Bu'de rinanun idanuwansa yayi akanta da Sauri.
Cikin kissa ta rufe bakinta da hannuwanta tana zaro ido tace,
Dama idonka biyu I'm really sorry pls hope bakaji abinda nake fadaba sbd sirri ne tsakanina da
neesah.
Bude baki yayi ahankali yace,
Abinda kike fada gskia ne neesah naso na? Tell me pls.
Wani murmushin samun nasara tayi duk da tasan qaryace take tsara masa tace,
Yes Mr Ahmed neesah na tsananin sonka duk da banbancin shekarunku saidai kullum kukanta
Jamaal ne daya zama babbar katangar qarfe a tsakaninku saidai babban tashin hankali da
damuwar sune bazaku ta6a kasancewa atare ba matuqar Jamaal na Raye.
Shiru tayi tana kallon yanda ya kar6i zancen nata ta gefen ido.
Ficewa tayi tabarsa cikin dogon tunani akan zancen Nata domin zancen ya shigesa matuqa.
Tana barin 'dakin fita asibitin tayi gaba 'daya
Direct gidansu ayeesha ta nufa..
Saida tayi wanka kafin ta zauna gaban mirror tana kallon ayeesha daketa tsoki fuskarnan
masifa na cinta sbd tun jia Jamaal bai 'daga waya daga bayama ya kashe wayar.
Murmushi tasaki tana kallon ayeesha tace,
Eshaaaa,,eshaa Jamaal bazai ta6a 'daukar wayarki ba ayanxu sbd babban abinda muke yaqi
akansa kamar ma muna kusantasu da juna ne da kanmu bamu saniba sbd nafara hango wata
zazzafar soyayyar neesah a idanuwan Jamaal saidai takaicin halayenta da girman kansa suke
danne soyayyar.,
Lallai wannan matakin damuke akai bazai haifar mana 'da mai idoba dan haka tun wuri mu
canxa tsari duk da na 'danawa Ahmed tarko zamu riqa amfani dashi batareda yasaniba sbd
soyayya data rufe idanuwansa.
Kallon zeey ayeeshan tayi da idanuwanta dasukai jajir tanajin kamar ta kama da wuta sbd
masifa.
Hummmmnn zeey kenan to Ai wannan tarkon dakike tunanin kin na'dawa Ahmed nice nafa
na'da masashi sbd ganin zai kawomin matsala a aiki,
Da farko nayi niyyar aikasa lahira saina bari nafara cin amfaninsa tukun.
Kallon tambaya zeey ta watsa mata tace,
Banganeba...
Matsowa tayi gabanta ta zauna cikin kashe ido tace,
Zaki tuna ranar da husnah takawomin magani nasawa Jamaal zai qara sona?
To aranar naji tana waya a toilet Ashe itada Ahmed suka hada baki sbd maganin husnah ta
kar6o musu subani nasawa Jamaal yasha yafara tsananin son matarsa neesah ya qyaleni
batareda na zargi komaiba.
Hakan danaji saina juye maganin nazuva mata wani a robar
Maganin kuma har school naje nabawa wani bokinsa maqudan kudi akan yasan yanda yayi
Ahmed yasha maganin.
Miqewa zeey tayi cikin jinjinawa qawarta tace,
Hmmmm kenan da Jamaal ne yasha haka Zara faru kenan?
Gashi yanxu Kansu sukaiwa dan kuwa mahaukacin so yakeyiwa neesah Wanda nasan yana
gaf da neesah ta tsanesa matuqar ya bayyana mata soyayyarsa.
Tsaki ayeesha tasaki tana cewa,
Bazan iya jiran wannan tarkon yayi wani aikiba sbd komai zai iya faruwa tsakanin captain da
neesah and I can't take this anymore
dan haka gwara kawai na aika su liloh suyimin maganin matsalata for gud.
Wat bakida tunani be zakiyi hakan,?
Idann mukasaka su liloh za'ayi bincike kuma za'a iya ganowa dan haka kibari muyi mata irin
kisan da bakowa zai ganeba za'ama 'dauka ita takashe kanta.
Yes kumafa hakane qawata.
****
Kodata farfado ummi kasa daina hawaye tayi sbd tausayin kanta Dana 'yayanta su kuwa Ashe
neesah ce qaddararsu.
Kallon ummi da idanuwanta suka kumbura da kuka tayi taji duk jikinta yayi sanyi da tsantsar
qaunar da ummin ke mata amma haryau takasa mayar mata da qaunar datake mat..
Lumshe idanu tayi tana karanto jamaay a ranta,
Tabbas zata danne qiyayyarta ta rungumi Jamaal 'din sbd ummin kawai.
'Daga hannu tayi ta riqo hannun ummi
Murya a sarqe tace,
Ummi ki kwantarda hankalinki naji sauqi kuma I promise I won't do this again.
Qago murmushi tsyi murya a sarqe tace,
Naji baby amma dan Allah karki kuma gwada haka harda shan poison kinji ko?
Batareda ta fahimci xancen wani poison ba tace,
Bazan sakeba ummi.
Ahmed ne yashigo 'dakin ummi ta tamke fuska ya qaraso gabanta cikin karyar da kai zai fara
magana Jamaal yashigo yana zuba sanyayan qamshinsa.
Kallonsa sukayi dukkansu banda neesah data lumshe ido ahankali.
Ahmed cikin basarda ganin da yayi masa ya maida hankalinsa kan ummi da idanuwanta ke
kawo hawaye yace,
Ummi dan Allah karkiyi fushi dani harki xubarmin da hawaye wlh aikin xuciyane da sharrin
shai'dan.
Kallon ummin Jamaal yayi da sauri sai alokacin ya lura da fuskarta dake kumbure ya tabbatarda
tana cikin damuwa.
Tabbas Ahmed ne yake neman sawa umminsa ciwon damuwa amma zai maganin abin tunda
neesah ce matsalar zai mayar da ita cikakkiyar matarsa yaga abinda zai faru coz tsaf zaisa
arufe masa shege a prison 'dinsu na us yanda ma ko dady bazai samu damar ganinsaba.
Hannu ya zura a ajihun wandon black jins dinsa ya fara dosarta cikin takun qasaita
Ahmed dake bawa ummi hkr yaji gakasa qarasawa ya maida hankalinsa kansu Jamaal yana
yaba tsantsar kyau da burgewa tareda class irin na Jamaal 'din amma yakasa tantance maiyasa
zuciyarsa ke neman kaisa gun da ba gurinsa ba.
Jin qamshinsa na kusantota yasata bude fararen danuwanta akansa.
Cikin idonta yake kallonta tareda sakar mata murmushin dayasata qasa da kai.
Ba zato taji ya zauna kusada ita tareda riqo hannuwanta duka biyu yana kallon cikin idonta ya
manna mata lafiyayyen kiss a tafin hannu Wanda yasata lumshe ido bataredata saniba.
Fuskarta ya nufa da tasa fuskar yana kallon pink lips 'dinta zai 'dora nasa akai sai jin qarar
zubewar kuloli sukai dukkaninsu suka waiwaya suna kallonta jikinta banda rawa ba abinda
yake da sauri ummi tace,,
Lafiyanki khadija?
Ahmed kuwa ball yayi da kulolin ya fice 'dakin afusace
Khadija ma bayansa tabi da gudu tana sakin kuka mai qarfi.
_wai wai wai zeey, ayeesha da khadija maiyasa bakuda masoya ne_馃
Mamuh馃拫
*R H F W F*
_Don't forget to vote and comments_
[3:22AM, 4/1/2018] 鈥�+234 816 253 8316鈥�: _*DACEWA*_
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*Viawattpad@mamuhgee*
*34-35*
Baya yayi da kansa tareda sakin 6oyayyar ajiyar zuciya yana kallon fuskarta data rufe
idanuwanta..
Mamaki yake yanda yau tayi sanyi babu wata masifa ko harara a tsakaninsu.,
Gefen ummi ya kalla yaga fuskarta 'dauke da murmushi tana 'dan kallonsu inna Rabi kuwa
abincin da khadija tayi 6ari take kwashewa.
Lumshe idanuwa yayi har lokacin hannunta na sarqe cikin nasa yana matsawa ahankali.
Kwanto da ita jikinsa yayi yana tallabo fuskarta
Ummi na ganin haka ta fice annuri fal a fuskarta Wanda dukkaninsu sun