Showing 1 words to 3000 words out of 63333 words

Chapter 1 - MAJANUNI Book 1 by Binta Umar Abbale.pdf

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb



*MAJANUNI!*
_(The Unknown Rich Man)_
Na
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____

Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Ubangiji mad'aukakin sarki. Tsira da aminci su 'kara
tabbata ga fiyayyan hallita Annabi Muhammadu S.A.W

*MAJANUNI*
'Kir'kirarran labari ne wanda ba'ayi don a ci zarafin wani ko wata ba. duk wanda ya ga ya yi
dai-dai da rayuwarsa to a rashin sani ne.


TSOKACI:
Kasancewar Ubangiji ya halliceka da ji da ga ni tare da wadatacciyar lafiya, to kada hakan ya
sanya ka d'auki kanka daban da sauran wanda aka hallita da wata larura makamanciyar
wannan, Ubangiji ba yanda baya zartar da ikonsa, kuma yanda ya so haka shi yake faruwa.
tabbas bawa baya shiryawa kansa rayuwa face wacce ya riski kansa a ciki.


*_Da 'ko'kari da jajurcewarki wannan Littafi ya fita. Hasinatu (AUTAR MANYA💯) Binta tana
godiya, rabbi ya tabbatar da zumuncinmu har gaban abada._*


*Am Back Again*
Allah ka bamu sa'a da rabo mai amfani.

*1&2*
*KANO STATE*
*GADAR SALGA* Unguwa ce mai zaman kanta wacce take daura da kasuwar kurmi tsohowar
kasuwa mai d'umbun tarihi a jahar *KANO.*
Cikin rukunin gidajen yaku bayi na cikin unguwar. Matashiyar budurwa 'yar kimanin shekaru
goma sha tara Zuwa ashirin zaune a kan kujera 'yar tsuguno da tarin wanke-wanke a gabanta
tana wankewa tare da kifewa a cikin wani babban kwando. wanke-wanken take tun k'arfi da
alamar sauri a tare da ita.

Cikin rashin kintsi! Saliha Ta iso inda take, ba tare da tunanin komai ba ta kurma mata wani
irin ihu! a cikin kunnuwanta! A Zabure! ta juyo har farantin dake hannunta yana fad:uwa a
kasan gurin, idanuwanta sukayi rau-rau kamar zata fashe da kuka ta fara magana cikin yanayin
na 'bacin rai! tare da yanayin hallitar da Allah yayi mata tace."Saliha menene haka."?
Cike da rashin mutunci tace." Yo idan ba haka akayi miki ba ai ba za kiji magana ba, yaushe
zan dinga wahalar da kaina gurin kiran sunanki ai ihu! kawai shi ya cancanta ayi miki tunda
kunnuwanki a toshe! suke."

Girgiza kanta kawai tayi tare da mayar da kanta 'kasa tana cigaba da wanke-wanken dake
gabanta.

A fusace! tace."Au! Shahida mahaukaciya kika mayar dani ina miki magana kinyi min banza to
bari naje na shedawa wacce ta aiko ni kiran ki.

Hanci ta shak'a ta sanya hannuna ta goge gumin goshinta cikin yanayin magana irin ta
kurame! tace."Saliha kina dai ganin wanke-wanken nake ko."

Saliha ta watsa mata harara da fadin." To ba zaki bar wanke-wanken ba ki tashi ki je kiran da
take miki ba."

A hankali ta ajiye sosan dake hannunta ta mike tsaye hanya ta nuna mata da hannu da k'arfi ta
ce"Wuce muje." girgiza kanta tayi rai a b'ace tayi gaba Salihan ta rufa mata baya.


Baba Asabe tana zaune a tsakiyar rumfa tana d'aura gishiri su ka yi sallama Saliha kai tsaye
cikin uwar d'aki ta shige tabi lafiyar gado. Ita kuwa tsugunuwa tayi a gabanta cike da ladabi
tace."Baba gani Saliha tace kina kira na."

Ta ajiye d'aurin gishirin ta janyo jakarta dake gefe kudi ta dauko daure a leda ta kalleta da
fadin." Bakin asibiti za ki je ki dauko min man gyda tun shekaran jiya ya k'are anata zuwa
nema." bakinta kawai take kallo, nan ta fahimci abinda take nufi, tunda ba wai da 'karfi take
maganar ba, shiyasa ta tsirawa bakinta ido, ta na ji amma ba sosai ba, shiyasa wani lokacin
idan ana magana take bin bakin mutum. nan take fahimtar komai.

Cikin saurin magana da yanayi na harshenta ta ce." Ban gama wanke kwanukan ba."


Ta ce."Ki ajiye idan kin dawo ki k'arasa ai da sauran lokaci."

Ta amsa da "To" Tare da mi'kewa. uwar dakin ta shiga domin dauko hijabi nan taga Saliha a
kwance da waya a hannunta tana game.

Girgiza kanta kawai tayi ta bude ma'ajiyar kayanta ta dau'ko hijabi tasa a wuyanta ta fito falon.
Ta kalleta da fadin."Dubu arba'in da hud'u ne man gyada galan d'aya manja ma galan d'aya
kafin ki isa zan kira Garba a waya na sheda masa zuwanki ya tari a daidaita sahu ya sanya
komai a ciki.

Tace."To shikkenan Baba sai na dawo." Tace." Ki kula sosai da kudin hannunki yau Juma'a
akwai turmutsutsu na jama'a."

Kud'in ta ri'ke da kyau da fadin." Zan kula insha Allah.

Cikin nutsuwa take tafiya har ta fito bakin titi can tsallake ta
hango mutumin ta zaune a 'karkashin tsohuwar motar da yake zama tare da tarkacen kayansa
na mahaukata!

Girgiza kai tayi tana me tsira masa ido yana kwance kan wani tattararran buhu ya takure
jikinsa guri daya jikinsa duk yayi fururu! kasancewar lokacin sanyi ne shiyasa al'amarin ya
tu'azzura.
Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke tana sake jin tausayinsa na bin ilahirin jikinta, hakika da tana da
yadda za tayi da ta taimaka masa ya daina kwana 'kar:kashin mota duk yanayin da ake ciki na
ruwa da iska anan yake wanzuwa tsayin watannin da yayi a cikin unguwar tasu.

Cike da tsantsar tausayinsa ta d'auke kanta daga inda yake ta fara laluben abun hawa Juma'a
ce shiyasa abubuwan hawa sukayi k'aranci a kan titin.

Ihu! da hargowar yara ya sanya da sauri ta mai da kanta gurin, nan taga yara masu yawa sunyi
masa rumfa suna tsokanarsa sai ihu! suke tare da fad'in "Baban- baba kazami! Baban -baba
mai annakiya Baban-baba mai kashi a wando."! Shi kuma
Yana zaune yana kallonsu fuskarsa a sake kamar koda yaushe idan yara suna tsokanarsa sai
ya yi ta murmushi koda kuwa cikinsu za'a samu masu jifansa da duwatsu! ba zai yi 'ko'karin
'kare kansa ba.

Ranta ya 'baci mutuk'a ganin yanda manya mutane ke wucewa wasu a kasa wasu abubuwan
hawansu amma a cikinsu an rasa wanda zai tsawatarwa da yaran akan abinda suke.

Ba tare da tayi tunanin komai ba ta tsallaka titin kai tsaye gurin ta nufa.

Tana zuwa cikin 'bacin rai irin na kurame take musu fad'a tana korarsu........Sai suka kwashe
mata da dariya suna nuna ta da hannu da fadin." Mu bama jin abinda kika cewa ke din kurma
ce ko kuma bebiya?"

Abun yayi mata ciwo sosai ta sake d'aga muryarta cikin yanayin saurin maganarta da yanayin
hallitarta take gargadinsu da fadin." Ita din kurma ce kuma haka Allah ya halliceta idan da
wanda ya isa ya sauya mata hallita a cikinsu sai ya d'aura aniya.

Suka dinga kyalkyala mata dariya sunayi mata ihu! kawai sai ta durk'ushe a gurin ta fashe da
kukan 'bakin ciki a wannan lokacin ledar kudin dake hannunta ta fad'i ba tare da 'bata lokaci
ba wani matashi dake can tsallake yazo ya d'auke yayi gaggawar watsa yaran ya gudu da
kudin a daure a leda.

Ido kawai ya tsira mata tana tsugune a kusa da shi kanta a tsakanin kafafunta sai kuka take.

Sosai yake jin zafin kukanta a cikin zuciyarsa to amma 'kudirin dake cikin zuciyarsa shi ya
hana shi rarrashinta tun ba yau ba ya san da yarinyar a duk sanda zata gan shi a hanya ko a
gurin zamanshi yana hankalce da irin kallon da take masa 'kwayar idonta kadai ita ke nuna
masa da cewar ta damu da shi, duk da cewa wata magana bata ta'ba had'asu ba to amma ya
yi imani da cewa ita d'in mai 'kaunarsa ce, Abinda tayi a yanzu shine ya tabbatar masa da
zarginsa.


A nutse yace."Ki yi hakuri kinji ko." Shiru bata d'ago kanta ba, jim yayi yana nazari wani
'karamin icce ya d'auka ya zungureta dashi.

a firgice ta d'ago kanta idanuwanta sunyi fululu fuskarta har ta kumbura! Tsigar jikinshi ce tashi
ya mayar da kanshi kasa yana wasa da icce hannunsa.

Tsaye ta mike tana karkad'e jikinta gabanta sai dukan uku-uku! yake!

Ta kalli gabas ta kalli yamma kudu arewa sai kawai ta d'ora hannu a ka ta kurma ihu! tare da
fadin." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'una!

Ya mike tsaye da sauri yana kallonta so yake yayi magana amma jama'ar da suka fara taruwa
a gurin suka hana shi idanuwanshi kawai ya zuba mata.

Haladu wanda ya kasance ma'kocinsu ya 'karaso gurin da fadin."Ke Shahida menene? me kike
a gurin wannan mahaukacin."?

Cikin kuka tace." Zuwa nayi na kori yaran da suke tsokanarsa shine suka sace kudin kuma
Baba Asabe ce ta aike ni bakin asibiti na saro mata man gyada."

Yace."In ban da shashanci irin naki da hauka yaushe zaki iya watsa yaran da suka dad'e suna
tsokanar wannan shashashan mutumin nan wanda bai san ciwon kansa ba, shashahar banza
kawai gashinan garin hauka kin janyowa mutane asara to kada kiji da wai sai na fad'a mata
yanda akayi komai ya faru."
Tana kuka take fadin." Don Allah kayi hakuri kada ka fada mata ." Tsaki yaja ya gyara zaman

daddumar dake kafad'arsa ba tare da yace komai ba ya bar gurin.

Ganin haka yasa mutanan dake gurin suka watse.
Komawa yayi ya zauna tare da rungume hannuwansa a kirji, Ta kalleshi da fadin." Baban-
Baba Don Allah baka ga wanda ya daukar min kudi ba?"

Girgiza kansa yayi alamun bai gani ba, hawaye suka sake zubo mata tace."To ko zaka duba
min cikin takarcen kayanka ko Allah zai sanya suna ciki."

Beyi mata jayayya ba ya fara dudduba tsummokaran dake gurin yana musu filla-filla babu
komai sai tarin ledoji na pure water da sauran robobin lemo da yake tarawa.

Ba tare da tsoron komai ba tazo ta tsuguna daf dashi tana sake hargitsa ledojin babban burinta
ace taga ledar dake d'aure da kudin Baba Asabe.

Sosai yake mamakin rashin tsoron yarinyar da yawa yara duk fitsararsu daga nesa suke
tsayawa su tsokane shi, basa iya kusantar gurin da yake duk da cewa baya doke-doke amma
hatta da manya basa iya zuwa inda yake amma abun mamaki ita ba taji tsoronshi ba tazo ta
tsuguna kusa dashi duk da ta san cewa shi din ba mai cikakken hankali bane.
Gabadaya jikinsa ya mutu wata iriyar kasala da kaunar yarinyar suka sanya shi kasa dauke
idonsa daga kanta.

Ta kalleshi da jajayen idanuwanta da karfi tace."Babu kudin sun sace ban san wane irin hukunci
Baba Asabe za tayi min ba."

Da yake ya fahimci kurma ce ita sai ya girgiza kansa ya had'e tafikan hannayensu guri guda
alamun yana bata hakuri.

Tsaye ta mike tana gyara zaman hijab dinta ta kalli hagu da dama babu motar data sako kai
da sauri ta tsallaka titin tana had'a hanya.

Cike da tsantsar tausayi yake kallonta har ta 'bacewa ganinsa, ya sauke ajiyar zuciya mai zafi
tare da sunkuyar da kansa 'kasa yana me cigaba da nazari da tunanin yanayi na rayuwa!


_NA YI AMFANI DA SALO BIYU GURIN RUBUTA WANNAN LABARI, INA FATAN MASU
KARATU ZA SU FAHIMTA_

*BINTA UMAR ABBALE*
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb
Ku yi join don samun dama karanta littafin na d'aya.

*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
Na
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO...
_____

_Fatan Alheri ga marubuta Amanar Binta💯🥰_

*Hasinatu (Autar Manya)*
*Sadiya Rimi*
*Binta Garba Saleh*
*Matar ya sayyadi*
*Real Esha*
*Jamy 'Yar kankia*
*Fatima Sunasi Rabi'u*
*Dr Ms Agadaz*
*Ummu Mahir*
*Jasmine*
*Zee Kumurya*
*Shamsiyya Manga*
*Autar Marubuta*
*Indo Aisha*
*Maman Teddy*
*Zahraty Takwara*
*xayyishatu Humaira*

*3&4*
Tsoro da fargaba! ya sanya ta kasa komawa gidan sai kawai ta samu kan dakalin wani gida ta
zauna tana kallon masu wucewa da nufin zuwa massalaci domin gabatar da sallar juma'a.
Har aka sakko daga massalaci tana nan zaune a gurin, Haladu yazo ya wuce ta yana girgiza
kansa. itama kai ta girgiza tana kallonsa har ya karya kwanar layinsu, k'wafa tayi tare da d'auke
kanta ta san duk wannan saurin da yake yana so ya je ya kai gulmar abunda ya faru babu
shakka sai ta dauki mataki a kansa mutukar ya janyo mata 'bacin rai! dama sun saba tafkawa
dashi a duk sanda yazo sayan abinci gidan nasu.


Da yake gidan ya kasance gidan gandu( na kowa da kowa) ya sanya ba tare da neman iso ba
ya kutsa kansa ciki tare da sallama a bakinsa.

Ta amsa tare da fitowa daga kicin da wani kafcecen ludayi na juya miya a hannunta.
Ta ce."A'a Haladu har an sakko kenan?"

Ya amsa da "Eh wallahi" kai tsaye gurin zamansu ya nufa ya zauna tare da cire hular dake
kansa.

Ta ce." Gurasa da miya zaka saya ko kuma shinkafa da miya?"

Hamma! ya saki ya sosa kansa da fadin." Yau dai shinkafa zan ci domin na gaji da cin kayan
fulawa kwana biyu idan nazo bayan gida sai na rirri'ke kan famfo nake samun damar yi
watarana har ihu! nake kurmawa! kai basir mugun ciwo ne wallahi."

Saliha dake yanka salak ta fashe da dariya tana kallonsa, Fuskarsa ya murtuke yana muzurai!
Ita kuwa sai tikar dariya take sai da tayi mai isarta sannan tayi shuru.


Sai da ya kai loma uku na abincin sannan yace." Uwar towo ina ja'irar yarinyar nan ta shiga
ne?"

Baba Asabe ta ce." Shahida kake nufi?" Yace."Eh kwarai kuwa." Tace."Kaga tun kafin tafiya
massalaci na aike ta bakin asibiti shiru har yanzu bata dawo ba.

Girgiza kansa yayi da fadin." Can na ganta gurfane gaban tsohon mahaukacin nan dake bakin
titi tana kuka koda na tambayata sai take sheda min cewa...........Duk ya kwashe komai ya fada
mata.

Baba Asabe ta dafe kirjinta tana salallami! Ya ce."Wallahi kuwa ai wannan kudi kawai ki fitar da
ranki dasu domin kuwa nayi imanin da cewar babu su an sace."

Jiki a sanyaye ta zaune bakin rijiya da fadin.'' Amma kuwa wannan yarinya ta cuce ni dubu
arba'in da hud'u ne wace irin kaddarace ta ritsa dani a yau."

Ya ce." Hukunci mai tsauri zaki d'auka a kanta domin kuwa ita tayi ganganci har aka sace kudin
idan ba haka ba mai zai sanya ta gurfana gaban mahaukaci irin Baban-baba wanda bai san
kansa ba."

Girgiza kai tayi cikin 'bacin rai tac e."Haladu ni fa ban yarda da wannan mutumin ba, wallahi ban
yarda cewa mahaukaci bane tunda duk abun masu hankali yana aikatawa bayan haka kuma
sallah bata wuce shi bana tamtama shine ya sace min kudina.


Dariya yasa da fadin." In banda abinki Uwar towa ya za'ayi ki kira Baban baba mai hankali in da
yana da hankali ba zaki gan shi a lalace ba. Sallah kuma da ki ke magana dayawa mahaukata
irinsa suna daburawa amma ki daina sanya Baban-baba a cikin masu hankali.

Tsaye ta mike da fadin." Haladu dole naje da kaina na duba kudina yau koni ko shi duk

haukansa wallahi na fi shi sai ya fito min da kudina 'barawo kawai
"

Tsaye ya mike tare da zaro kudi daga aljihunsa ya mika mata da fadin." To ni dai ga kudinki zan
shiga gida na huta zuwa yamma zan shigo domin naji a'ina aka kwana.''

Kudin ta kar'ba tasa cikin lalitar dake d'aure a kugunta da sauri ta shiga daki ta fito yafe da
mayafi.

Saliha ta kalleta da fadin." Baba kada kije ki tunkari mahaukacin mutumin nan kada garin
neman gira a rasa ido ni dai na fada miki.

"Sai naje d'in ba zan lamunci wannan al'amarin ba domin kuwa ban yarda da asara ba." Tana
'kare maganarta cikin zafin nama ta kama hanyar fita da kud'irin zuwa yiwa Baban Baba A tare
a tare.

Tunda ta hango ta gabanta yake faduwa sunkuyar da kai tayi har ta k'araso inda take, "Don
ubanki abinda ki kayi min kenan? ta fad'a tana kokarin kai mata duka! tasa hannu ta kare tana
kallonta da idanuwanta da suka taru da ruwan hawaye. cikin masifa ta ce."Tashi muje gurin
mahaukacin daya sace min kudina."
Cikin k'okarin kare kanta ta bude baki za tayi magana.......ta buga mata tsawa! wacce ta sanya
babu shiri ta mike tabi bayanta tana me cigaba da aibata ubanta wanda bai san abinda yake
faruwa ba.


Har suka isa bakin titin tana surutai! jama'arta sai tambayarta suke abinda ke faruwa tana
tafe tana basu amsa wasu dariya kawai suke su wuce wasu kuwa bin bayanta suke domin
kashe kwarkwatar idonsu.

Yana tsaye da wata jarka a hannunsa da alama gurin yake so ya bari, katamau! ta rike
hannunta suka 'karasa gurin da yake.

Tsira musu ido yayi yana kallo. ta kalleshi da niyyar yi masa tijara! dafin idanuwansa ya sanya
jikinta mutuwa sai ta gaza furta komai kawai tayi 'kasa da kanta.

Kallon yarinyar ya yi suka hada ido da ido, sai tayi gaggawar saukar da nata idon sakamakon
mutuwa da jikinta ya yi a cikin k'wayar idonshi akwai wani sirri wanda shi kanshi bai san yana
dashi ba.
Can 'kasan ma'koshi ya ce." Menene ko za

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login