Showing 21001 words to 24000 words out of 63333 words

Chapter 8 - MAJANUNI Book 1 by Binta Umar Abbale.pdf

gabanta na wani irin fad'uwa!

"Insha Allahu bai mutu ba."
Ta furta hakan a fili.

Da sauri tasa hannu ta goge hawayen da ya zubo ta kira wani yaro da hannunta.

Yaro yazo ya tsaya gabanta da ledar kankana da lemo a hannunsa da alama aikensa akayi
kuma da azumi a bakinsa yana sauri ya isa gida yace." Gani."

A sanyaye tace." Don Allah ko kasan inda Baban-baba ya koma da zama?"

Cike da rashin fahimta yace." Waye Baban-baba?"

Ta nuna masa tsohuwar motar da fadin." Mutumin dake zama a waccan motar."
Ya kalli gurin da take nuna masa ya juyo da tsoro a tare dashi ya ce." Ni ma ban sani ba.'' bai

jira jin abinda za tace ba yayi saurin barin gurin yana waiwayenta.

Ba ta ha'kura ba ta sake tarar wani yaron tana tambayarsa, yaron irin marasa kunyar nan ne,
kawai sai ya fashe da dariya yana gwada irin maganarta ta kurame! "habbbaba! ya nu na ta da
yatsa yana kyalkyala dariya ta bishi da kallo tausayin kanta da kanta ya lullubeta, wai shin ita
din abar tausayi ce ko kuma Baban-baba?
Hawaye masu zafin gaske suka ciko idonta, tayi namijin k'okarin hanasu zuba, da saurin gaske
ta bar gurin tana addua a zuciyarta.

Koda ta koma gidan ma 'bacin rai ne! don fad'a ta riska, Baba Asabe ta inda take shiga ba ta
nan take fita ba har da cewa idan ba tayi a hankali ba to za ta kai ta asibitin dawanau a duba
kwakwalwarta, to itama a lokacin da Baban ke fadin hakan ba taji haushi ba domin ta fara
zargin kanta anya kuwa bata samu matsalar kwakwalwa ba.
Washe gari aka tashi da sallah, jama'a nata walwala da farin ciki mussaman wanda Allah ya
hore wa abin layya ciki har da Baba Asabe domin babban (rago) na dubu sittin ta saya tayi
layya dashi, wadatar zucci ne da ita tare da 'ko'karin faranta ran jikokinta dake gabanta.


Uku ga sallah ta shirya tsaf fuskarta babu walwala ta fito daga d'aki da hijab dinta a hannuta.

Baban ta kalleta da fadin." Kin shirya kenan? ai da nace Saliha ta shirya kuje tar.....Salihan ta
katse ta da fadin." Ni babu in da zani bacci zanyi na huta, sannan kuma da yamma Kamalu zai
zo muje gidan yayarsa ziyara." Kamalu shine saurayinta wanda akayi musu baiko.

Baban ta ce." Ayyo! to shikkenan Shahida kinji abinda ta ce."

Babu damuwa a tare da ita ta ce." Babu komai.'' Hanyar fita ta nufa da fadin." Sai na dawo."

Ta ce." Ki gaishe su ba dan halinsu ba, maganar naman sallah kuwa ba zan ce ki tafi musu
dashi ba dalili na fi kowa sanin waye Jamilu da burgar tsiya yanzu idan baki take ba yana nan
ya kayar da manyan shanu yana neman suna a unguwa."

Bata tsaya taji 'karshen maganar ba tayi saurin fita daga gidan, a ranta tana jin haushin irin cin
mutuncin da Baban ke wa mahaifinta.


Ilai kuwa tana shiga gidan taga zahiri domin kaca-kaca ta samesu suna ta aikin suyar nama
tare da daka dambu a k'aton turmi Hadiza ce mai wannan aikin.

Can gefe kuma ganda ce tare da kan sah! da rago a babbake akan buhu an shanya k'udaje sai
tashi suke a gurin da wari mara dadi.

Jamila ce kawai ta amsa sallamarta tana fara'a tace." Aunty Shahida ashe kece dama kwana
biyu kina raina."

Ta saki fuskarta da fadin." Nima saboda ke nazo gidan."

Hadiza ta kalleta da fadin." 'Yar iska bebiya kawai." da yake a hankali tayi maganar ba ta ji ba ta
dai ga bakinta na motsi a lokacin da take maganar amma Talatun da sauran 'ya'yanta duk sun
ji."

Babu wani 'kulli a cikin ranta ta ce."Talatu ina kwana anyi sallah lafiya?

A dakile ta amsa ta cigaba da juya zallar tsokar naman dake cike da kaskon suya.

Jamila ta shimfid'a mata tabarba tana zama ya shigo gidan fuskarsa a tur'bune!
kamar koda yaushe yana sanye da tsadaddiyar shadda wacce taji uban aiki irin na manyan
mutane, hula da takalmi da agogo duka babu na banza kamshinsa kuwa tuni ya cika gidan.

Gabad'aya su kayi masa sannu da zuwa ya amsa babu walwala ya bud'e d'akinsa ya shiga
babbar rigar ya cire ya rataye ya zauna kasan kafet zugum! da ka gani yana da damuwa.

Sallamarta ce ta katse tunaninsa, ya amsa yana bin ta da kallo har ta samu guri ta zauna tana
sake gaishe shi.


Ya amsa yana mata wani irin kallo kafin yayi kwafa da fadin." Sai yau ki kayi ra'ayin zuwa gurin
da nake?"

Shuru tayi tana wasa da yatsun hannunta.

Ya cigaba da cewa." Maganar aure ce ba kya so na yi miki shiyasa ki ka d'auke k'afarki daga
gidan nan ko?"

Ta kalleshi da fadin." Baba aure nufin Allah ne idan lokaci yayi zanyi aur......ya katse ta, ta
hanyar daga mata hannu da fadin." Ni zaki fadawa lokaci? zaman me kike kin zama uwar mata
shekara ashirin kanwarki Hadiza saura wata shida bikinta ga Jamila nan itama nayi magana
da yaron da yake son auranta mun tattauna da mahaifinsa, ke da kike babbarsu kina zaune to
wannan itace magana ta karshe da zanyi miki wata biyu kacal na baki ki fito da mijin aure tunda
kin kammala secondary kinyi saukar al'kur'ani to kuma me ake nema?"

Tana shashshekar kuka ta ce." Wallahi Baba tunda nake babu wanda ya ta'ba cewa yana sona,
duk wanda yake so na yi aure ba kamar ni ba, na dai fi tunanin saboda lalurata maza suke gudu
na."

Ya girgiza kai da fad'in.'' Mace bata kwantai matsalar ki ba zai hana ki auruwa ba, ki na da duk
abinda ake buk'ata saboda haka ni ban yarda da wannan maganar taki ba."

Sai ta kasa ce masa komai domin duk abinda zata fad'a masa ba zai yarda ba, bahaushe ya
ce." Mai d'aki shi ya san inda yake masa yoyo, gaskiya ne tunda ta taso babu wani namiji da ya
taba cewa yana sonta.

Hannu tasa ta goge hawayen fuskarta, ta kalleshi har yanzu fuskarsa bata sassauta ba."

"Zan tafi Baba." tafad'a tana k'okarin tashi. ya ce."Ki bari sai yamma idan an kammala soya
naman ki tafi da naki."

Ya sosa mata in da yake mata 'kai'kayi cikin fargaba ta ce."Baba ina ka samu kudi ka yanka
*SAH!* har da *Rago?"*

Ya kalleta yana sake tamke fuskarsa." Ke ni kikewa wannan tambayar don ubanki."
Ya fada yana zazzare mata ido!

A sanyaye! ta ce." Kayi hakuri." Hanyar fita ya nuna mata da hannu cikin tsawa! yace." Tashi ki
fita ki bani guri."

Da sauri ta tashi ta fita gabanta na wani irin fad'uwa! akwai dalilin da yasa ta tambaye shi
saboda sanin halinsa mugun dan rigima ne zai iya zuwa yaci bashin mutane duk domin yazo
yayi bajinta da burga! da neman suna a cikin unguwa babban burinsa ace masa ya isa shi mai
kudi ne.
Hasashenta ya tabbata domin kuwa bayan fitar ta, ya zurfafa cikin tunanin hanyar da zai bi
gurin ganin ya biya mahaucin da ya kar'bi *SAH!* da Ragon a gurinsa.

Yayi nazari ya hanga ya hango a yanzu dai bashi da dubu dari uku da hamsin din da zai biya
mutumin idan ba gidan da yake ciki a zaune zai daga ya siyar ba.

Dama yasa ran samun wasu kud'i ne sai kuma asara ta same shi, domin hak'ansa bai cimma
ruwa ba, a gurin sana'ar tasu shine ya tashi fanko fayau!(ziro) hatta da motarsa bata tsira ba sai
da aka 'kwamushe haka ya dawo gida a motar haya.

Kwabo yanzu babu a cikin asusunsa sai 'yan canjin dake hannunsa, gabadaya tunaninsa ya
ta'allaka gurin ganin hanyar da zai biya mahaucin kud'insa.

Talatu ta shiga d'akin tana gyara d'aurin zanin jikinta da yayi muguwar daud'a sai karni take
fuskarta na maiko.

'Kerere ta tsaya a kansa da fadin." Babu icce ya 'kare ga kuma uban 'kashi can da za'a soya
yanzu dai abunda ake bukata icce da man gyada."

A sakarce ya kalleta yaji wani mugun takaici ya turnuke shi, ta tsaya masa aka kerere! ba ta
san halin da yake ciki ba, girgiza kansa yayi yace." Je ki zan fito yanzu na bada kudin."

Ta juya ta fita bagazan-bagazan!

Ya fito tsakar gidan yana nazarinsu. babu Shahida a cikinsu ta tafi, wato da yace ta tsaya ta tafi
da nata rabon shine ta kama hanya ta tafi, shikkenan ai tayi wa kanta, waje ya fita minti biyar ya
dawo gidan tare da zaratan samari biyu, a yanzu dai bashi da kudin icce ballantana wani man
gyada, saboda haka ya yanke shawarar bada sadakar naman da niyya biyu.
Ganin abinda yake shirin faruwa yasa ta fito afujajan! baki na rawa tace." A'a ya haka kuma?"

Bai saurareta ba ya cigaba da loda zallar tsoka da k'ashi cikin buhu yana fad'in gidajan da za'a
kai musu.

Talatu kamar ta dora hannu ka ta kurma ihu! jikinta sai rawa yake tana fadin." Ya haka ina za'a
kai kuma?"

Ya ce." Na bayar sadaka dama haka Allah ya ce ayi saboda haka wannan na cikin kaskon ya
ishe ku."

Idonta ya ciko da ruwan hawaye ta dinga zabga masa harara! wannan ai wulakanci ne! duka na
cikin kaskon bai fi ya cika bokin fenti ba.

Su Hadiza ma jikinsu ne duk ya mutu saboda ganin yankan k'aunar da mahaifin nasu ya yi
musu.

Kaf ya kwashe naman ya bayar, ya bar musu kadan hatta da kawunan dabbobin da gandar
dake shanye a buhu bai bari ba sai da ya bayar, dalili baya bukatar ta sake zuwar masa da wata
bu'kata ta siyan icce ko man gyad'a da makamantansu.
*BINTU*


_Akwai ingantaccan maganin�� gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin
zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu
lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya
k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar
sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga
sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya
mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da

wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal
zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI
GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah
duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu
'batawa kai lokaci�🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!
infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula
mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi
amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_Follow this
link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ku yi
Joining domin samun damar karanta littafi na d'aya*



*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____


_Akwai ingantaccan maganin�� gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin
zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu
lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya
k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar
sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga
sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya
mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da
wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal
zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI
GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah
duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu
'batawa kai lokaci�🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!
infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula
mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi
amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_

*23&24*
Cikin nutsuwa yake musabaha da jama'a bayan idar da sallar asubahi a massalacin dake jikin
gidansa wanda ke unguwar giginyu, cikin kamala ya fito daga massalacin da cazbaha a
hannunsa yana sanye da farar jallabiya mai k'aramin hannu kansa sanye da hula mai raga-raga
irin ta larabawa kamar ko da yaushe ya nad'e kansa da farin rawani. Can tsallake ya hangi wasu matasan samari a tsaye, jikinsa ya bashi cewar shi suke jira ya fito
daga massalacin, aikuwa dai gabanshi suka zube suna gaishe shi, ya saki fuskarsa tare da
basu umarnin tashi.

Bayan sun gaisa sai kuma su kayi shuru suna sunkuyar da kai dukkaninsu da alamun magana
a bakinsu.

Gyaran murya yayi cikin kamala da dattako yace." Ko meye yake tafe daku kada kuyi shakkar
fada min ina sauraranku."

Na farkon yace." Alhaji Taimako nake nema a gurin ka, kayi min suttura kamar yanda Allah yayi
maka, tabbas nazo gurin da za'a share min hawaye na." Da rawar murya yake maganar.

Ya dafa kafadarsa da fadin." Menene bukatarka? fadi kanka tsaye."

Yaji kwarin gwiwa a tare dashi yace." Mata ta ce ta haihu yau kwana bakwai kenan bani da
abin hakika da goro da Alawa hankali na ya tashi sosai Alhaji domin maula ba hali na bane,
kawai don bani da yanda zanyi ne kasancewar gwamnati ta yanke min albashi na, babu laifin
tsaye bare na zaune wannan dalilin yasa wahala tayi min yawa yara na biyar gashi karamin
ma'aikaci ne albashin duka dubu talatin da biyar nake dauka amma yanzu tsayin wata shida
kenan da gwamnati ta zabge rabin albashin ya koma dubu goma sha bakwai, to wannan dalilin
yasa duk wani karamin ma'aikaci yake cikin tashin hankali."

Ya dinga girgiza kansa yana jin wani irin zafi a zuciyarsa. ido ya tsurawa mutumin yana tunanin
wani al'amari daya faru a cikin shekarun da suka gabata lokacin ma da duniya take kwance
kenan Malam me za'ayi da mulkin Najeria.

Numfashi ya sauke kafin yace." Kada ka damu komai yana da sanadi kuma kowane bawa
akwai hanyar abincinsa saboda haka ni zan taimaka maka daidai gwargwado Allah ya rufa
mana asiri."

Gabadaya suka amsa da "Ameen."

Ya kallesu kafin yace."Abokansa ne ko kuma tafiyar kowa daban?"

Hada baki sukayi gurin bashi amsa da cewa." Abokansa ne."

Sai yayi murmushi wanda yake fitar da zahirin kyawunsa ya umarce su da su bi bayanshi zuwa
gida.


Dubu dari cash ya bashi da fadin." Ya je yayi hidimar haihuwa, ya kuma yi masa addua sosai.

Shi da abokansa suka rasa bakin godiya.

To ganin gari ya soma haske yasa a gaggauce ya shige cikin gidan ya bar su a bakin gate tare
da masu gadi sai godiya suke na irin alkairin da akayi musu.

****
Yau haka kawai ta tashi da kwad'ayin cin wainar gero, kuma mai soya wainar a can bakin titin
Jakara take.
Ta fito tsakar gidan ta same su, a zaune suna karyawa da kunu da kosai jawur dashi, sam bai
bata sha'awa ba, wainar geron dai take 'kulafuci.

Ta kalleta da fadin." Baba bani naira d'ari zan sayi waina yau kwadayinta nake ji."

Ba tace komai ba ta zuge zif din lalitar dake daure a jikinta ta dauko 'yan hamsin biyu ta mika
mata.

Kar'ba tayi da sauri tasa hijab d'inta ta fita tana adduar Allah yasa ta samu kada taje ta tarar ta
'kare tunda yanzun tara ta wuce ana zancan goma.


Wani mugun farin ciki ne ya ziyarce ta sakamakon tozali da ta yi dashi a kwance a k'asan mota
akan wani tattararan buhu wanda yayi datti da kasa da k'azanta har da kashin awakai."

Mantawa tayi da abunda ta fito siya, ta tsallaka titin kai tsaye gurinsa ta durfafa fuskarta cike da
annuri.

Yana daga kwancen ya hangota sai yayi saurin rufe idonsa kamar mai bacci.

Tana isa idonta ne ya sauka kan kafafunsa, gabanta ya fadi! ta tsurawa kafafun ido tana
mamakin abinda ta gani. wata lafiyayyar kafa ce kamar bata taka k'asa, jikinta yayi sanyi
lokacin da take kallon fuskarsa da hannuwansa kamar sansanin kanikawa saboda tsabar baki
da maik'o sai ka rantse da Allah cewa 'kafafun ba'a jikinsa suke ba.

Tsoro yasa ta d'an ja baya amma ba ta daina kallonsa ba, kuma ba tayi masa magana ba.

Ya bud'e idonsa tare da k'okarin tashi zaune, fuskarsa a murtuke yake kallonta.

Bakinta na rawa ta kirayi sunansa.
Uffan bai ce mata ya dauki wata tsohuwar buta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login