Showing 30001 words to 33000 words out of 63333 words
Chapter 11 - MAJANUNI Book 1 by Binta Umar Abbale.pdf
auranta ba domin ba
ka da komai! mahaukaci kawai." yana kai k'arshen maganar ya ja hannunta suka shiga motar
da ta tsaya a gabansu.
Ya jima a tsaye a bakin titin yana nazari da tunani akan al'amarin, can kuma na ga ya tsallaka
titin ya bi wata hanya ya mi'ke......
*****
"Ranka ya dad'e ina sauraranka. d'aya daga cikin yaransa ke wannan maganar yayin da yake
tsugune a gabansa.
Ya ajiye jaridar dake hanunsa a nutse ya ce." Sule kai ne kasan gari sosai kasan wata unguwa
Ja'in a cikin garin nan.?"
Yayi jim na minti biyu kafin ya ce." Eh ranka ya dade ina dai jin sunan unguwar amma ban ta'ba
shigar ta ba amma wani lokaci muna bi ta hanyar tare da kai idan za muje babbban kamfanin ka
na sumunti dake sharad'a."
Ya ce." To ai ta kwana gidan sau'ki tunda ka san hanyar wani aiki za kayi min akan wani
mutumi ina so kayi min binkice sosai a kansa.
Ya ce." To ranka ya dad'e babu damuwa ya sunan mutumin?" shuru yayi na minti biyu, sunansa
Jamilu idan bai manta ba domin can da dadewa ya taba bugun cikin yarinyar ta fada masa
sunansa da kuma unguwar da yake zaune.
"Sunansa Jamilu amma akwai wani suna da jama'a ke kiransa ya kwanta min a rai amma hakan
ba zai zama matsala tunda mutumin sananne ne a cikin unguwar binkice a kansa ba zai yi
wahala ba."
Ya ce." To babu damuwa ranka ya dade insha Allah zanyi k'okari sanin wanene mutumin domin
kawo maka cikakken labari a kansa."
Ya ce." To Allah ya taimaka ina tsumayinka daga nan zuwa gobe da safe.
Ya mike da fadin." Insha Allah ranka ya dade .'' da sauri ya nufi parking spece ya fito da mota
domin cika umarnin maigidan nasa.
Na jima ina kallonsa ina hango nagarta da dattijantaka a tare dashi, cikakken mutum ne kamili a
zahiri da bad'ini domin yanda yake tafiyar da rayuwarsa a nutse shine zai tabbatar maka da
cewa ya san abinda yake.
*Binta tana mik'a sak'on gaisuwa ga ilahirin masoyantaí ½í²¯â¤â€í ½í´¥*
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K7QH4idftZS5fSw7m2Rueb *Ku yi joinig domin samun damar
karanta littafi na d'aya*
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALEí ¼í½’*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____
_Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin
zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu
lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya
k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar
sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga
sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya
mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da
wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal
zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI
GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah
duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu
'batawa kai lokacií ½í¹í ¼í¿»_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!
infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula
mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi
amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_
*29&30*
Da wuri ya dawo gidan, ya umarci Jamila cewa ta shirya da sauri kada magariba tayi ta je ta kira
masa Shahida maza su zo tare yana nemanta.
Tunda Talatu ta ji haka ta san da wata a kasa. sai ta bishi dakin ta same shi a kishingide yana
zan can zucci.
Gefan sa ta zauna da fadin." Na ga ka aika a kira maka wannan yarinyar a jikina na ji ruwa baya
tsami banza."
Ya kalle ta na second biyu kafin ya ja tsaki da fadin." A nan ki ka fi kauri gulma da tsugudidi
dube ki don Allah kamar ba mace ba, wannan tufafin na jikinki idan ban mance ba yau
kwanansa hudu a jikinki."
Hannu ta daga masa da fadin." Ya isa kada ka ci min mutunci, shin da kake wannan maganar
ka siya min sabulun wanka ko omon wanki ne."?
Shuru yayi mata banda hararar ta babu abinda yake.
Tace." Da fatan dai yarinyar nan ba gidan nan za ta dawo da zama ba domin wallahi ba zan iya
rike ta ba nima naji da nawa."
Tsakaninta da Allah take maganar.
Ya gyara zamansa da fadin." Aure zanyi mata itama ta huta da wannan cin mutuncin naki."
Tabe baki tayi kafin ta ce." Au ashe ta samu mijin aure amma babu labari."
Ya ce." Wannan mutumin ne da yake bina bashi zan bashi kyauta a madadin kudinsa, kin san
yarinyar nakasashiya ce za'a sha wahala kafin a samu mai auranta shiyasa na yanke shawarar
aura mata Saminu tunda dai shi din ma kansa d'aya da rabi ne.
Farin ciki ya cika zuciyar Talatu, babban burinta a duniya a ce Shahida ta wulakanta, a
maimakon ta nuna masa kuskuran abinda yake shirin aikatawa sai ta cigaba da karfafa masa
gwiwa cewa hakan da yayi daidai ne, domin shi yake da iko da 'yarsa.
Cikin wannan halin Shahida da Jamila su kayi sallama a gidan.
Talatu ta fito daga daki tana washe baki, abin mamaki cikin sakin fuska ta amsa gaisuwarta, ita
kanta Shahidan abin ya bata mamaki mutuka.
Durkushe take a gabansa gabanta in banda faduwa babu abinda yake, tun kafin yayi mata
magana ta karanci komai a fuskarsa, labarin gizo baya wuce na koki saura kwana uku wa'adin
da ya bata ya cika, wasu zafafan hawaye suka shiga tsere a saman fuskarta.
Fuska a murtuke ya daka mata tsawa! da fadin.'' Ba kuka na ce kiyi min ba Shahida ki saurare
ni da kyau! kina jina ko."? ya k'arashe maganar da karfin gaske wanda har sai da su Talatu su
ka ji sautin muryarsa.
"Ina fatan baki mance magana ta dake ta karshe ba."?
Murya na rawa da yanayin maganarta ta ce." Ban man ce ba Baba."
Ya ce." Wa ki ka tsayar a matsayin wanda za ki aura."?
Kai tsaye ta ce." Babu kowa."
Ya jima yana kallonta kafin ya ce." To ba zaki mayar da ni mutumin banza ba, kina yawo
godai-godai a gari ni ba shashashan uba bane, tunda kin kasa tsayar da mijin aure ni a
matsayi na na wanda ya haife ki zan aurar dake ga wanda ya cancanta, saboda haka ki zauna
cikin shiri ki kuma shedawa kakarki cewa nayi miki miji zan had'a ku tare da Hadiza na aurar
daku a lokaci guda."
Wani irin kuka ne ya k'wace mata murya a sarke ta ke fadin." Baba ka da kayi min haka mana
kayi min adalci ka sake bani dama a karo na biyu insha Allahu zan fito da wanda na keso."
Kafin ma yayi magana Talatu ta bankad'o dakin ta shigo domin duk abinda ke faruwa suna ji ita
da yaranta, ta ce." Wa ne irin adalci ki ke so ayi miki ? ai ki godewa Allah tunda har ki ka samu
wannan bawan Allah ya amince da cewar zai aure ki a matsayin ki na muskiniya, ki daina
daukar kanki cikakkiyar mutum kamar kowa."
Maganganun Talatu sunyi mata zafi sosai! a shari'ance ma sunyi tsauri da yawa, jahili ne
kadai ya ke bambamce jinsin mutum wanda Allah ya hallita mai lafiya ko mara lafiya, duk wata
hallita da Allah yayi akwai manufa kuma ba don baya sonka ya hallicce ka hakan ba, shi ya fi so
ya gan ka a hakan ne.
Da k'yar ta iya yunkurawa ta tashi. hanyar fita kawai ta nufa hannunta kunshe a bakinta kukan
da take dannewa ya'ki dannuwa sai fita yake hawaye kuwa a saman fuskarta sai tsare suke.
A bakin titi adaidaita sahu ya sauke ta, yanayin tashin hankalin da take ciki ya sanya ba ta lura
dashi ba, yana daga can tsallaken da jarkar ruwa a hannunsa zai je ya samu ruwan alwalwa a
tuka-tuka! shi ya gan ta a firgice! hankalinsa kuma ya tashi ainun! ganin yanda take kuka! ya bi
ta da kallo lokacin da take karya kwanar layin gidansu, sai da ta k'urewa ganinsa sa'an nan ya
tsallaka titin cikin damuwa ya nufi in da tuka-tukar take yana tunanin abinda ya ke damunta.
Cikin matsanancin tashin hankali da damuwa ta shiga gidan, kai tsaye rugume kakar tayi tana
rera wani irin kuka mai tsuma zuciya! duk da ta kasance nakasashiya ba zata so ayi mata irin
wannan auran ba, gabadaya al'amarin bai kwanta mata a rai ba wannan shine dalilin da yake
sanya ta zubda hawaye.
Baba Asabe ta rike ta suka shiga daki a tare, ita kuwa Saliha ko a jikinta ta'be bakinta ma tayi
ta cigaba da aikin gabanta.
Da kyar Baban ta rarrasheta ta dora da fadin." Dama tun da naga wannan kiran na gaggawa na
san akwai abinda zai faru, Jamilu ba shi da kirki ko kadan kiyi shuru ki fada min abunda sukayi
miki."
Tasa hannu ta goge hawayen dake gudana a saman fuskarta, ido jawur! ta kalle ta da fadin."
Wai aure zai yi min ."
Baban ta zuba mata ido cike da mamakin maganar
"Aure kamar yaya ."? ta sake tambayarta domin jin cikakken bayani.
Murya na rawa da yanayin maganarta ta fara sheda mata hukuncin da baban nata ya yanke a
kanta cewa lallai zai had'a ta aure da wanda yayi ra'ayi.
Baba Asabe tayi tsalle ta dire! ta fara surfa bala'i ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, ta
ce." Wato yanzu ne zai nuna iko a kanki saboda bashi da kunya an gama yi masa wahala kin
girma kin zama mutum shine zai shigo da wannan maganar to wallahi bai isa ba mutukar ina
raye ba za'ayi wannan auran ba."
Kawu Musa ya shigo gidan ya riski maganar ya zauna Baban tana sake jadadda masa cewa
Jamilu bai isa ba yayi kadan sai dai duk in da za su shiga su shiga amma ba zata bari ba.
Ya ce." Baba musulunci ne ya bada damar hakan, ai budurwa ce mahaifinta na da ikon za'ba
mata mijin aure bazawara ce kadai ke da 'yancin za'bar mijin da take ra'ayi, saboda haka babu
ruwanki, ki cire kanki daga wannan maganar."
Ta ce." Ka san Allah ba zan lamunta ba, domin dai yarinyar nan ba ta da cikakkiyar lafiya to ba
zan bari garin san zuciyarsa ya aura mata bara gurbi ba, a jikina nake jin akwai dalilinsa na
aikata wannan abu."
Ya ce." To shikkenan yanzu abinda za'ayi shine zanyi binkice akan lamarin idan ya kasance shi
wanda ake so ayi auran dashi mutumin kirki ne ya tara duk abubuwan da ake da bukata haka
akeso, amma idan akwai mishkila a tare dashi nima ba zan bayar da goyon bayan tabbatuwar
al'amarin ba."
Ta ce." Eh hakan yayi na baka wuka da nama kayi min binkice akan shi Jamilun da kuma dalilin
da yasa yake so ya aura mata wanda ba ta so."
Ya mike da fadin." In sha Allahu zanyi kokarin gano yanda al'amarin yake.
A daran ranar Shahida ba ta iya rintsawa ba sallar dare ta kwana ta nayi tana kuka da rokon
Allah yayi mata za'bi na alkairi a cikin ranta take jin za ta iya auran Baban-baba akan dai ta auri
mutumin da mahaifinta yake kokarin aura mata, tun bata ganshi ba take masa wata irin tsana!
Da yamma tana daki a kwance tana tunanin rayuwarta ta tsinkayi muryar yaro." Wai ana
sallama da Shahida in ji Saminu Abbatuwa."
Gabanta yayi mummunan faduwa! Baba Asabe ta harari yaron a fusace! ta ce." Ka je ka ce
bata nan."
Yaron ya juya ya fita yana dariya! daman ya san za'a rina, tunda mutumin ya aiko shi gidan
zuciyarsa ke raya masa cewa ba zai samu ganin budurwar da yake so ba duba da irin hallitarsa
da tarin munin da Allah yayi masa.
A she bata hakura hijab ta zura a wuyanta ta kama hanyar fita tana surutai akan al'amarin, so
take ta ga mutumin tayi masa cin mutunci!
Shirgegen mutum ta gani da katon ciki a tsaye a kofar gidan nata.
Ta kalli tafkekekiyar kafarsa da dunduniyar take waje sakamakon takalmin da yayi masa kad'an
farce zako-zako kafafun sunyi wata irin daud'a da kaushi da faso abin babu kyawun gani!
Ta kalli sumulmulallan kansa da fuskarsa dake zuba uban kyalli 'kwayar idonsa jajawur gasu
cike da kwantsa da alama dai yana da matsalar ido.
Hankalinta bai tashi ba sai da ya wangale bakinsa yana dariya babu ha'koran sama dana kasa
sai turame a gefe da gefe! mummunan wawulo ne dashi! ya zube har kasa yana gaisheta.
Gefe ta matsa gabanta na dukan uku-uku! lallai Jamilu bashi da mutunci ina yarinya
kankanuwa kamar Shahida za ta kai wannan katoton mutumin.
Ta gaza furta komai sai kallonsa take tana tunanin yanda zata bullowa al'amarin.
''Baba Asabe Ina wuni." Maganarsa ta dawo da ita hayyacinta.
Ta amsa "Lafiya lau kai ne kake sallama da Shahida."?
Ya ce." Eh ni ne sunana Saminu Abbatuwa ina sana'ar siyar da dabbobi a kasuwar Abbatuwa
dake cikin wannan gari namu mai albarka."
Ta girgiza kai da mamaki a tattare da ita ta ce." Waye ya turo ka gurin Shahida? ko kuma kai ka
ganta ka ga kana so."?
Yayi shuru yana nazarin maganar, fuskarsa ta sauya da bacin rai! ashe hujaj bai daidaita
komai ba amma yasa shi zuwa domin a ci masa mutumci.
Ta sake maimaita masa tambayarta ta farko "Shin turo ka akayi ko kuma kai ka ga yarinyar kake
so."?
Ya ce." Mahaifinta ne ya fansar min da ita a madadin kudin da nake bin sa."
Gabanta yayi wani irin fad'uwa! dama tasan ruwa baya tsami banza!
Ta kalle shi rai! a 'bace ta ce." To ka koma ka sheda masa cewa ni Asabe yayi 'karya bai isa ba
ya sanya yarinya a caca na Shiriya zuwa kotun koli dashi a kan wannan al'amarin."
Ya sa hannu ya sharce gumin dake saman goshinsa ya kalle ta da mummunar fuska ya ce .''
Dama ba ni na nema ba shine yayi min kyautar ta a madadin kudin da nake bin sa kimanin
dubu dari uku da hamsin saboda ya kasa biya na, don haka yanzu daga nan gidansa na nufa
domin muyi wacce za muyi."
Ta ce." Wannan kuma ya rage naku." gida ta shige tana bambami da mamakin al'amarin.
Dawowarsa kenan daga kasuwa Saminu yayi masa dirar mikiya.
Tunda ya fito ya ga yanayin fuskarsa ya tabbatar da cewa lallai akwai matsala ya bude baki
kenan zai yi magana ya katse shi ta hanyar fadin......*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALEí ¼í½’*
MANAZARTA WRITES ASSO..
*33&34*
*KANO*
Unguwar giginyu.
Shukura cikin matsatsun kaya ta fito da wani 'karamin mayafi a kafad'arta wanda dashi gwara
babu. hannunta rike da mukkulin mota tare da handbag tana wani irin k'amshi mai fizgar
hankali. Shukura karatun low ta yi yanzu haka ta kammala, tana ta fafutukar aiki, mahaifinta ya
ce ba da yawunsa ba, domin dai babban burinsa bai wuce a ce ya aurar da ita, duba da yanda
ta kai munzalin auran, bayan haka kuma tana aikata abubuwa marasa kyau irin wanda ba ya
so, hakan kuma baya rasa nasaba da sanya hannun uwarta akan dukkanin abunda take.
Ganinsa a zaune a gurin hutarsa ya sanya jikinta ya yi sanyi sai ta hau duru-duru! ya kalle ta
tun daga kasa har sama! yanayin fuskarsa ya sauya da 'bacin rai!
Yarinyar na so ta zubar masa da mutunci a gari domin ya jima yana hana ta shigar kaya irin
wannan amma taki ta daina a kullum burinta ta fitar da tsaraicin ta waje.
Cikin 'bacin rai ya ce ." Shukura ba kya jin magana ko?
A sanyaye ta ce." Daddy kayi hakuri don Allah."
Ya daga mata hannu da fadin." Koma cikin gida."
Sai ta fashe da kuka da fadin "Daddy kayi hakuri ka bar ni don Allah." A shagwabe take
maganar.
Ya duba a gogon dake d'aure a hannunsa shida da rabi na yamma daf ake da a kira sallar
magariba.
Ya ce." Ina za ki ji? Hanci ta ja da fadin" Bikin 'kawata a can karkasara."
Girgiza kansa ya yi da fadin ." Ki koma gida babu in da za ki je." yanda ya fadi maganar babu
wasa ya sanya ta juya a guje! tana kuka!
Ta