Showing 27001 words to 30000 words out of 63333 words

Chapter 10 - MAJANUNI Book 1 by Binta Umar Abbale.pdf

cikin 'bacin rai ya ce." Wai ke Talatu yaushe zakiyi hankali ne.? ta'be
baki tayi ta nannago 'bakar magana ta ya'ba masa domin har yanzu da ragowar haushi da
takaicin abinda yayi mu su, haka kawai ya kwashe nama ya bayar, sun tashi a tutar babu.
Babu ladabi a maganarta ta ce." sai ranar da akayi hankali ni ma zanyi." Ya tsira mata ido yana
kallo.

Ta ce." Tun shekaran jiya wannan mutumin yake zuwa sallama da akai, ya ishi mutane nace
yau dai tunda kana gidan sai ka tashi kaje domin kaji abunda yake tafe dashi."

Yana kokarin tashi zaune ya ce."Ki aika Jamila ta fada masa cewa bana nan."

"Wane irin na aika Jamila bayan na sheda masa cewa kana nan, shin ko dai baka da gaskiya
ne?"


Yana k'o'karin magana su ka ji wani yaro ya shigo yana fadin." Wai Saminu Abbatuwa yana
tsaye fa yana jiran Maigidan a waje."

Hadiza dake zaune a tsakar gidan tace." Dallah kaje kace gashinan zuwa." Yaron ya fita yana
k'unk'uni.


Talatu ta kalleshi taga duk ya had'a zufah! sai muzurai yake, ta ce." Da alama dai wannan
mutumin kudi yake bin ka."

Ya kalleta da fadin." Talatu wannan mutumin kudi yake bina kimanin dubu dari uku da hamsin
gashi bani dasu a yanzu wannan ne dalilin da ya sanya nake shakkar fita gurinsa.

Ta ce." Kai har mai ka saya da wannan kudin? Jamilu ka girma baka san ka girma ba har yanzu
ba zaka daina d'aukowa kanka bala'i ba, kana da surukai a cikin unguwa masu bu'katar auran
'Ya'yanka ko kunyar hakan ba ka ji."

Ya ce." Kin ga kada kiyi min maganar banza fita ki bani guri."

Ta buge zaninta da fadin." Ko ba kace na fita ba ai zan fita dama, Allah dai ya shirye ka." Ta
kama hanya ta fita daga dakin tana surutai.

Jallabiya yasa ya fita.


Wani shirgegen k'aton mutum ne tsaye a jikin bango fuskarsa sai mai 'ko take, gashi da wasu
irin ido mitsi-mitsi duk kwantsa a ciki, Saminu Abbatuwa ne.

Ya mi'ka masa hannu da fadin." Barka da yamma Saminu kwana biyu kana ta zuwa baka samu
na wallahi na d'an yi wata 'yar tafiya ne yau din nan na dawo."


Ba tare da ya ri'ke hannun da ya mika masa ba ya ce." Alhaji Jamilu ka bani mamaki wallahi
ban ta'ba tunanin haka halinka yake ba."

Ya sosa kai yana 'yar dariya da fadin ." Haba Saminu ai ka bari mu gaisa tukkuna ka ji Uzuri na,
ni ba 'karamin mutum bane da zan dinga wasa da hankalinka."


Ya d'aga masa hannu da fadin." Babu wani Uzuri naka da zan duba domin ba haka mu kayi da
kai ba, ni mutum ne mai girmama al'kawari shiyasa bana mu'amula da wanda bai san
muhimmancinsa ba, ban d'auka za kayi min haka ba wallahi, kazo neman alfarma a gurina nayi
maka duk da cewa a lokacin akwai wad'anda suka zo da kudi a hannunsa domin na siyar musu
na'ki na ajiye maka alhalin baka bani ko kwabo ba, na rufa maka asiri, shine ni zaka tona min
nawa asirin."
Ya k'arasa maganar yana numfarfashi tare da taruwar wata kumfa a gefan bakinsa.


'Yar dariya yayi irin wacce ya saba ya ce." Allah ya huci zuciyarka! na san dole wannan
al'amarin ya 'bata maka rai amma kasa ranka a inuwa insha Allah yau da daddare zanzo har
gida na kawo maka kudinka ni kaina na fi so mu yi rabuwar arziki saboda haka ka samu
nutsuwa kuma kada ka yarda da jita-jita mutane a kaina, ni mutum ne mai cika alkawari,
matsala aka samu wallahi nima hakan bai min dadi ba.

Ya sauke ajiyar zuciya yana dan jin sassauci a zuciyarsa, amma dai duk haka babu fara'a a tare
dashi yace." Jama'a da yawa sun yi min magana mara kyau a kanka, amma a yanzu a karo na
biyu zan kara yarda da kalamanka, mutukar baka cika alkawari ba to duk abinda ya biyo baya
kada kayi kuka da kowa kai ka janyo, don haka yau da daddare ina jiran zuwanka."
Ya dafa kafad'arsa da fadin." Kada ka damu mutumina zamu rabu lafiya da ikon Allah."

Ba tare da yace masa komai ba ya kama hanya yana tafiya tinkis-tinkis naman jikinsa yana
rawa ya bishi da kallo yana hango yanda kansa yake zuba k'yalli d'igon gashi babu kan sumul
sai uban 'kyalli yake.

Sai da ya 'bace da ganinsa sannan ya sauke zazzafar ajiyar zuciya ya shiga gidan yana tunanin
hanyar da zai bi domin ganin ya samu kudin da zai biya mutumin nan hakkinsa.


****
Tana so tayi magana amma tana gudun abunda zai biyo baya, da yammacin ranar Kawu Musa
wato mahaifin Saliha yazo gidan ya ci mata mutumuci har da su zagin mahaifinta, duka ne
kawai bai yi ba, saboda kawai tana taimakawa Baban-baba, shine suke kiranta da
mahaukaciya.

Ta goge wasu hawaye masu zafi da suka gangaro a saman fuskarta. Wai shin meye laifinta
anan? don ta taimaka masa, a ganinta shi din abin a tausaya masa ne, to wai mahaukaci ba
mutum bane? ita fa har yanzu ba ta dauke shi a wannan matsayin ba, har yanzu kallon mai
hankali take masa. A sanyaye ta kira sunanta." Baba." ta juyo da muburgin kad'a miya a hannunta, yau towo tayi
sha'awa shine ta tu'ka musu na masara."

"Don Allah kada ki biye maganar Kawu Musa Allah ne kad'ai ya san irin ladan da kike samu
gurin ciyar da wannan bawan Allah ki daure ki cigaba da bashi abinci."

Saliha ta dinga zabga mata harara can kasa tace." Banza mahaukaciya kawai k'arshen so ki
aure shi kawai zaki dinga damun mutane."

Ita kuwa Baban jikinta ne yayi sanyi ta ce." Shahida ba wai bana so bane. A'a ni bana son kina
zuwa gurinsa duniyar nan babu yarda har yanzu mutumin nan bai kwanta min a raina ba
wallahi."

Ta ce." Ni kuma wallahi bana mugun tunani a kansa, domin nayi imani da cewa babu wani abu
da zai min wanda zai yi tasiri tunda ni alkairi nai masa, to bana tsammanin sharrinsa zai yi tasiri
a kaina."

Ta gyada kai da fadin." Ai shikkenan Allah ya sawwake."

Shuru tayi bata amsa ba ita kuwa Saliha sai maganganu 'kasa-'kasa ta keyi, ba tayi da 'karfi ba
wanda ta san idan taji to ba zasu kwashe lafiya ba.


Ta kalleta da fadin." Ki d'auko kwanon da aka ware masa na zuba masa abincin."

Da sauri tace." To.'' ta tashi tana jin dadin yanda Baban ta fahimci ta.

Baba Asabe wani lokacin tana da tausayi sai dai wani sa'in Kawu Musa yana sauya mata
ra'ayi domin shi din wani irin mutum ne mara kan gado.


Ta zuba masa towon da yawa da miyar 'kubewa kafin ta kawo miyar tattasai da nama mai yawa
ta zuba masa har da manshanu.

Shahida dadi ya lullu'beta ta je ta sanyo hijabi ta fito da azama ta d'auki abincin za ta fita, Baban
ta kalleta da fadin." Anya Shahid ba za'a samu almajiri ya kai masa ba.

Ta girgiza kai da fadin." Yanzu zan kai masa na dawo idan almajiri ne zai iya zama a wani gurin
ya cinye ya dawo yace ya kai masa.
Tana gama maganarta da gaggawa ta fita domin ba ta son Baban ta sake wata maganar.


****
Saminu Abbatuwa ya yi ta tsumayin zuwan Hujaj kamar yanda ya yi masa alk'awari, shiru
malam ya ci shirwa, b'angaran Hujaj din kuma yana can suna bugawa, har yanzu nasarar bata
fad'o kansa ba, ya cire tsadaddan agogon dake daure a hannunsa ya ajiye aka cigaba da
fafatawa, cikin hukuncin Allah abokin karawarsa ya ci agogon, gumi mai zafi ya dinga karyo
masa, babu abunda yai saura a jikinsa sai riga da malin-malin, sai kuma takalmin kafarsa, dan
tun a karon farko ya cire hular kansa ta kimanin dubu ashirin da biyar ya ajiye aka cinye.

Bai saduda ba, zai sanya tsadaddiyar wagambarin dake jikinsa wacce taji ubar aiki, shaddar
wankin ta d'aya a k'iyasi da shaddar da dinki sun tasar wa dubu arba'in! Ya kalli al'kalai da
fadin." Wasan yanzu muka fara na sanya wannan kayan na jiki na, saboda haka muje zuwa.

Ba tare da 'bata lokaci ba suka cigaba da bugawa.

*Tofa wannan sana'a dai ta marasa tunani ce😳*
*MAJANUNI!*
(The Unknown Rich Man)
NA
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
MANAZARTA WRITES ASSO..
_____

*31&32*
"Ka ga dakata Malam." ya katse shi ta hanyar daga masa hannu. ya cigaba da cewa." Ashe
dama ba ka gama daidaita komai ba ka sanya ni zuwa aka tozarta ni." Cikin tsantsar bacin rai
ya kai karshen maganar.

Hujaj! ya girgiza kai a cikin ransa ya san hakan sai ta faru, to wannan karon dole ne ya nuna iko

akan 'yar sa, babu wani mahaluki da isa yayi masa karan tsaye akan abinda yake da iko dashi,
yarinya dai shine ubanta saboda haka zai ga wanda ya isa ya hana shi iko da ita.

"Ka gan........bai bari ya k'arasa abinda yake shirin fad'a ba ya sake katse shi a karo na biyu ya
ce." Na gaji da wannan yawo da hankali Hujaj nayi hakuri iyakar hakuri saboda haka na rantse
da zatin Allah yau ba zaka kwana a gidan nan ba sai ka fito min da kudi na." yana huci! da
numfarfashi yake wannan maganar bai kuma jirayi jin ta bakin Hujaj d'in ba fuuuuu! ya bar gurin
kamar kububuwa!

Wani zazzafan gumi! ne yake karyo masa! yasa hannu ya share na saman goshinsa hankali a
tashe ya shiga gidan!


Talatu ta bishi da kallo a lokacin da yake k'okarin shiga dakinsa, duk yanda akayi akwai matsala
ganin yanda ya shigo gidan cikin tashin hankali.


Yana 'kokarin fitowa daga dakin ta shiga "Wai lafiya na gan ka duk a hargitse?

Ya ce." Baba Asabe ce take nema ta tona min asiri a gari saboda haka yau zan nuna mata
k'arfin iko na a kan 'ya ta."

Ta ce." Me take nufi to?

Yana k'okarin ratse ta ya wuce ya ce." Yanzu bani da lokacin yi miki bayani saboda Saminu ya
fusata! komai yana iya faruwa idan ban yi wa tufkar hanci ba saboda haka sai na dawo za muyi
magana."


Ta biyo bayansa tana surutai "To ai 'yar ka ce don ka yanke hukunci a kanta sai ya zama laifi
gaskiya wannan karan ka nuna mata cewa ba fa ita ce take da iko da yarinyar ba kai ne ubanta
dole ne ayi hakuri da hukunci da ka yanke."

Bai ce mata komai ba ya kama hanyar fita yana gyara babbar rigar jikinsa. kai tsaye can gidan
Baba Asaben ya nufa.


Dama ta shirya masa ko da ya gaishe ta a dakile ta amsa ta cigaba da sabgogin gabanta, ya
juya ko'ina bai ga Shahidan ba sai Saliha dake wanke-wanke a bakin rijiya. ko kallonsa ba tayi
ba ballananta ya samu arzikin gaisuwa.


Fuska a tur'bune ya ce." Kan maganar yarinyar nan ne na zo na tafi da ita domin na yanke

hukunci a kanta wanda hakan alkairi ne a gare mu baki daya."


Ta kalle shi a wulakance kafin ta ce." Rufe min baki shakatafe! shashasha wanda bai san ciwon
kansa ba, ai dama na shiryawa zuwanka saboda baka da mutunci shine ka sanya yarinya a
cha-cha wato kai abin kunya gaba ka bashi ba baya ba, ka turo wani mummunar hallita da
sunan mijin aure kaji kunya Jamilu wallahi kayi faduwar 'bakar tasa!"

Gumi! ya dinga karyo masa! ransa yayi masifar 'baci da irin cin mutuncin da take masa ya ce."
Wai shin ke kika haifar min yarinyar nan ne da kike min iko da ita, iya kawaici da kara nayi miki
mai zai sanya ki dinga k'okarin wuce gona da iri, ki zauna a matsayinki mutukar kina so na
cigaba da ganin mutuncinki."

Ta ce." Jamilu cin mutuncinka ai ba sabo bane a guri na, ka saba dama kai hanyar da mutunci
yake baka bi gurin ba, to bari kaji na shirya tsaf wallahi tallahi ba zaka wulakanta yarinyar nan
ba sai inda karfi na ya 'kare akan hakan."


Ya ce." Auran da zanyi mata shi ki ke kira tozarci! a tunaninki waye zai aure ta da wannan
lalurar? yarinyar fa ba cikakkiyar mutum ba ce wannan ma sa'a aka ci da zai aure ta."


Fashewa tayi da kuka ta nuna shi da ya tsa da fadin." 'Yar cikin ka ce fa Jamilu, saboda Allah
ya halliceta a haka sai kake neman kai da ita har ka sanya ta a cha-cha! mai yasa baka sanya
d'aya daga cikin 'ya'yan Talatu ba kada fa ka manta duka kai ka haife su kuma ranar lahira sai
Allah yayi muku hisabi."

Ko gezau! ya ce." Ni dai na gama yanke hukunci wannan yarinya ba ta da miji sai wanda na
za'ba mata a matsayi na na ubanta yana da kyau a bani hakkina wannan shine magana ta daku
ta karshe ku zauna a shirye daga nan zuwa sati biyu komai zai guda na.''


Shuru kawai tayi tana kallonsa hawayen tausayin yarinyar na tsare a saman fuskarta tunda
take a duniya bata ta'ba ganin maciyin mutunci irinsa ba, shekara da shekaru yake 'kunsa mata
'bakin ciki har yanzu ta rasa maganinsa.


Shi kuwa rigarsa ya buge! ya fita daga gidan cike da cin alwashi akan abunda ya niyyata.

Saliha na kife kwanuka a kwando ta ce." Wai Baba ina ruwanki ne! don Allah ki kyale shi yayi
iko da 'yarsa mutumin nan bai da mutunci wallahi saura kiris na d'ura masa ashar saboda
takaici!


Tana goge hawaye ta ce." Saliha har yanzu kuruciya na damunki baki san duniya ba amma
mutumin da yake k'okarin hada aure da Shahida bai cancanta ba."


Ta ce." To ai gwara shi akan wancan mahaukacin na bakin titi, kamar yanda ya fadi hakane
yarinyar nakasashshiya ce da wuya ta samu mijin aure dole sai mara galihu."

Girgiza kanta kawai ta ke hawaye na zuba a saman fuskarta, saboda kawai yarinyar na da
matsalar kunne shikkenan ba ta da wani farin ciki da jin dadi a duniya ba za a duba cancanta da
abinda ya da ce ba, to ita muddin tana numfashi ba zata bari ayi mata auran tozarci ba.



Tana fitowa daga kantin Lurwanu ta hango shi ya fito daga gidan.

Gabanta yayi mummunar fad'uwa! sam ganinsa ba alkairi bane mussaman yanda ta hango
tsantsar tashin hankali a fuskarsa.


Babu damar guduwa tunda ya riga ya gan ta, fuska a tur'bune ya k'arasa in da take. sai ta
sunkuyar da kanta cikin rawar murya take gaishe shi. bai amsa ba kawai ya rike hannunta ya ja
ta sukayi gaba.


Jan ta yake tana bin sa har suka fita bakin titi bai ce mata komai ba gabanta sai fad'uwa yake
tana kiran Innalillahi wa'ina ilahi raji'un!


Suna tsaye a bakin titin suna neman abun hawa Baban -Baba ya 'karaso gurin dugujaja! ya
tsaya gefen ta. Hujaj din ya razana kad'an! yana kallonsa ita kam ba ta tsoro ta da ganinsa ba,
sai ma wani irin kallo da take masa hawaye na sauka a kumatunta tafi jin tausayinsa akan
kanta."

Kallo guda ya yi masa ya sha jinin jikinsa idan ba mahaifinta ba to wani shak'i'ki ne a gurin ta
saboda yanayin kammani da ya gani a fuskokinsu.

Da yake mutum ne mai kyauta sai yasa hannu cikin aljihu ya d'auko dari biyu ya bashi domin shi
duk a tunaninsa abinda yake bukata kenan.''


Girgiza kansa ya yi kafin ya ce." Ina zaka kai min mata ta?"

Maganar ta dinga yi masa amsa kuwwa! a kunne "Ina zaka kai min matata? ya sake maimaita
maganar, itama ta tsorata da jin furucinsa hawayen idonta ya bushe ta dinga kallonsa gabanta
na dukan uku-uku!


"Kai ba na son hauka! kar'bi nan ka matsa ka bani guri." abinda ya fad'a masa kenan ya sake
mi'ka masa gudar dari biyun.



'Kin 'karba ya yi maganar dai ita ya sake maimaitawa "Ina zaka kai min mata ta?"


Cikin fad'uwar gaba ya ce." Don Ubanki waye wannan maukacin! meye hadin ki dashi.?


Da yake da 'karfi ya yi maganar yasa da sauri ta ce." Ba mahaukaci bane sunansa
Baban-Baba a 'karkashin waccan motar yake kwana Baba Asabe tana bashi abinci."


Ya ce." Okey shiyasa kuka k'ulla soyayya a tsakaninku.? ido ta tsura masa tana auna
maganarsa. Ya buga mata muguwar tsawa! da fadin." Ba zaki bani amsa ba.? ta ce." Ba
soyayya muke ba Allah ne kawai ya hada jininmu nake tausayin........Ya wanke fuskarta da wani
azababen mari! yana huci! ya ce." Ni zaki mayar mutumin banza ko? wannan d'an iskan
mutumin ban yarda dashi ba kina tausayinsa shi zai iya cutar dake saboda haka aure zanyi
miki, kai kuma ka saurare ni da kyau."

Ya tsura masa idanunsa dake cike da tsantsar b'acin ran marin da yayi wa yarinya ya ji ciwon
hakan har cikin ransa.

Cikin isa ya cigaba da cewa." Wannan yarinyar tafi 'karfinka ba zan baka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login