Showing 9001 words to 12000 words out of 46340 words
Chapter 4 - ARNAN DAJI Book 1 By Feedeen Bash.pdf
anmasa itake masa komai Dan ita matar tasa
saitaga dama shiyasa takara samun damar yawonta bame samata ido Dan itama matar ubanta
tanada kwadayi dataga tafara wanka zata fara lissafi asiyon kaza a tahon da kaza haka zatayta
lissafi itako afra ko ajikinta tunda tasan tana rufa mata asiri babanta besan bin maza takeba
yadauka kawai yawon gidan kawayene (kaji shashanci muje zuwa)
A razane suka juya wazasu gani baban rama ne da mado saurayin aduke Wanda za ay
musu aure bana sunasan junansu so me tsanani anan mado ya durkushe yafara sharar kwalla
duk dauriya irinta mazan ARNAN DAJI hakan besa ya daureba abun yay masa ciwo baban
rama ya duka garin Yaya haka tafaru rama tafara kuka tafara magana muna zaune nida aduke
mungacin farfesun kwadin datay mana mun ajiyewa tenkwai nata saita rigani wanko hannu
bayan ta dawo saina fita Nima saina zaga bayan gida ina fitowa nadinga jin magana sama
sama sai nadanyo sanda na labe sainaji yana cewa ina rama bazaki gayan inda takeba saina
kasheki badu ya temakeka bansan inda rama tayiba Ni Bata gidannan Sam bazaki fada ba toko
zanmiki abunda zanmata amadadinta nayarda kayimun komeye Raina fansane ga Yan uwana
meye amfanin rayuwata inaganin Yan uwana cikin wani hali tana kuka take furta masa haka
Nan ina labe ina kallo yafara cire kayansa ya juya baya saina fito Ashe aduke taga tahowata
tace na koma naki na tsaya saida tahada hannayenta biyu tana rokona sannan na koma
dakinka na buya saidayasha yay mankas sannan ya farwa aduke tana ihu yana zabga mata
mari ahaka ya farkata farkawa ta rashin mutunci ya yagalgalata bakaramin ta adi yay mataba
banjin akwai maganin dazewa aduke aiki harta gyaru takarasa cikin kuka idon mado jage jage
da hawaye way waye waye sukai shiru saida baban rama ya daka musu wata mahaukaciyar
tsawa ba magana ake mukuba waye da wannan danyen aiki me kikai masa ke rama daya
biyoki har gida cikin rishin kuka ban masa komaiba yadade yana neman mu kadaice nakiya
saboda shize auri kawata aminiyata bazan iya cin amanartaba yasha tareni a jeji ina guduwa
shine ya biyoni har gida a yau besamanba sai yasamu aduke shiru na minti biyar ya gifta adakin
inbanda tashin kukan tenkwai da rama da aduke bakajin komai baban rama yay gyaran murya
tabbas hayaki baze hakaba tayayama bayan shine da ze aureku rama bayanan yana daure a
kurkuku saboda shine cikon mutum na biyar daza a yanka nasan kowaye ya aikata wannan
lefin kurufamin asiri kurike alkawarin dakuka daukarmun karku gayawa kowa abunda yasameni
karku bari kowa yaji cewar aduke wadda dakyar maganar tata take fita munmuki alkawari
bameji fitar maganarma zata iya sawa a hallakamu cewar baban rama way waye kugaymun nifa
banganeba cewar mado zan gayama kowaye Amma saikayi alkawarin bawanda zeji wannan
batu mubarshi anan iya mu biyar dinnan Ni Kuma zanje dawa na nemowa aduke magani yanzu
Inasan aduke har Raina bazan taba Bari wani yajiba Amma aransa ya kudurce sai ya dau fansa
ja e ne dan gidan sarki kaho Yay mata wannan aikin kasan aikinsane a razane ya dago abokina
ja e yaci Amanata na rantse da gemun kakana saina dau fansa yasa Kai ya fice sunata kwala
masa Kira be juyoba sai suka kara rushewa da kuka.
Tofa muje zuwa nice taku maikaunarku akoda yaushe.
*FEEDYN BASH*
[9/11, 22:29] +234 810 679 5647: *?ARNAN DAJI?*
*NA*
*FAREEDA ABDULLAHI*
*_?KAINUWA WRITERS?? ASSOCIATION_*??
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
45-50
_*GODIYA DA JINJINA AGAREKI ANTY FAUXY YAR AMANA, AMANA TAKAIMIKI GASKIYA
SAMUN MACE KAMARKI AKWAI WUYA MACE BA HASSADA BA KYASHI ALLAH YA KARA
DAUKAKI DA DUKKAN YAN KAINUWA WRITERS*_
*JINJINA AGAREKI MARYAM DANDAWAKI SANNU DA KOKARI ALLAH YAKARA DAUKAKI
YAKAWO KASUWA ME ALBARKA NAGODE MAKU*????????????
A fusace suka juyo suga wacece wannan? cike da farin ciki ja'e yace "itace ku cimmata
ku kamon ita yanzun nan".
Tariga ta fita hayyacinta kawai gani tai sun yiyo kanta gadan-gadan nan tafara gudu, gudu
takeyi suna binta abaya haka suka dingayi har suka fara shigowa gari, nan suka dakata ita
Kuma ta bazama cikin gari da gudu tamkar zararriya, bata zame ko inaba sai gida, tana shiga
taga haryanzu tenkwai na nan da gudu ta fad'a kanta jiki na rawa bakinta sai karkarwa yake ta
rirri'keta taboye abayanta "lafiyanki aduke menene? "
Sai kallo ba magana nanfa tafara girgizata amma ina bata hayyacinta bata magana, ganin
haka yasa takamata suka fice daga gidan suka tafi nasu gidan suna shiga lamunde tace
"To sarakan yawo daga ina kuke? kunsan munada mara lafiya gashi harya fara motsawa
Amma ya kasa tashi saboda ciwon kansa ya dai bud'e ido yai yun'kurin tashi ya koma"
cike da farin ciki take gaya musu taga duk sun mata shiru ba wanda ya kulata, tenkwai taja
hannun aduke takaita dakinsu tazaunar ta fita ta d'ebo mata ruwa a tulu me sanyi tabata
takarba tasha ba tace komai ba sai had'iyar zuciya take kamar zata had'iye zuciyarta,
daukanta tenkwai tayi ta kwantar da ita batace komai ba sai binta da idol kawai take tamkar
zararriya ganin komai take tamkar a mafarki, "wai ankashe babanta ancinyeshi anwa aduke
fyade tana chan batasan halin datake cikiba" gaba d'aya kwakwalwarta ta dena aiki ta tsaya
chak ta sandare kawai akwance, ganin haka tenkwai ta koma waje taleka d'akin majinyacinta
da tunda tasa Kai Bata 'kara waiwayarsaba sai yanzu taganshi yana baccinsa hankali kwance
ta tsura masa ido tana hango tsantsar kyansa da nagartarsa sabanin wancen Dan iskan ja'en
daba wata nagarta atare dashi sai zallar iskanci ace shizata aura tazauna har karshen
rayuwarta gwara ta mutu data aure shi tana fatan wannan bawa ya kawo wani haske a wannan
garin nasu.
Yadauke idonsa daga kanta cike da takaicin yadda tazama tamkar gunki gaban wanda
bemasan tanayiba shigashi yana tsananin kaunarta Amma Bata saniba gata kyakykyawa me
diri mtsww yaja tsaki sai da jeddah takare masa kallo ta tabbatar da yay mata ? Nan takada kai
takama hanyar fita daga hall din taja hankalin maza dayawa saboda kyanta Amma batasu
takeba tafuce waje tanemi waje tazauna tana jiran taga fitowarsa ayko kafin atashi taga ya fito
da sauri shida wani abokinsa sun durfafo inda take Nan takara suma azaune saida sukazo gab
da ita taga yabude motarsa da hanzari ta tashi ta isa gabansa Tace "sannufa" yay mata banza
kamar badashi takeba, abokinsane yayi karfin halin cemata "sannu y'anmata ya kike? Ta washe
baki tare da qara yauqi ta amsa da "lafiya lau" Nan suka hau zuba dama shine Wanda ya ganta
tun a ciki ta tafi dashi shiko be auraba tunda yaga kamar Yar hannunce yad'ana Amma zefi san
ya aureta, dataga wankin hula na shirin kaita dare saitace "abokinka baya maganane" yadan
kalleshi a sace yaga yadda ya had'a rai ransa inyayi dubu ya baci sun barshi a cikin mota kamar
bawansu, bayasan wargi Sam besan wanna shegen kwashe kwashen na faruk ya jiyo ya kalleta
have "haka yake bikiga ya bude mota ya shigeba" "gsky yay mun" ya kalleta "Ni Kuma kinmun
yaza ayi? " tai far da ido "naima kamar Yaya? " wani murmushi ya sakar mata irin nasu na 'yan
duniya sannan yace "kinmun a matsayin matar aure"
Dariyar ita ma Tayi sannan tace "kaban dariya wallahi ni gaskiya abokinka nake so shi yai
mun shizan aura" ya'ke yayi don maganarta ta sosa masa rai amma ya dake yace "to ni a wane
matsayin zaa ajiyeni?" "Abokina" ta fada da sauri sannan ta qara da "matsayinka kenan Kuma
abokin mijina" Ya kalleta rai bace yace "To wannan da kike gani ansa masa rana Kuma bayasan
babbar mace sannan baya kula mata".
Ta dago ta kalleshi tace "wanne temako zakay mun yasoni ya kulani?"
"Gaskiya babu" Ya bata amsa kai tsaye "zan dai baki card dinsa da number din wayarsa,
Amma Ni mezaki ban?" Ya qarashe zancen da kashe ido irin na yan bariki,
"hmmm me kake so ajikina kafada da kanka zan baka shi? " cike da murna yace "kinyi
alkawari? " bata amsaba ya dora da "kawai so nake ki mallakamun kanki"
Murmushi ta sakar masa na manyan bariki tace "dan dai wannan karka damu ka kwantar da
hankalinka.
"zanbaki complementary card dinshi, yadda zaki same shi a office da Kuma number din
wayanshi shikenan ko? "
cike da farinciki tace "shikenan ngde gaskiya"
"to muje murage muki hanya".
Tana tsaye taga kamar ya motsa da hanzari ta karasa kusa dashi tace "sannu kafarka? "
saitaga ya bude idonsa Nan tacika da farinciki da gudu tafito waje cikin zumudi take kiran
lamunde tana "Ya farka ya bude idonshi" lamunde ma cikin farin cikin tabiyota suka koma suka
kamashi suka zaunar dashi sai binsu yake da ido ba umm ba ummun yakasa cewa komai
kansa yakeji yay masa nauyi ya daure tam ya Kai hannu ya taba sai yaji a kulle yake ashe, yay
shiru ya kasa magana Nan lamunde ta dakko masa maganinsa tabashi yasha shidai bece
komaiba kawai binsu yake da ido, bai sansuba betaba ganin halitta irinsuba to Amma wayema
shi meyake anan? beda amsar tambayarshi sannu suke ta doka masa yanata kallonsu kamar
gumaka chan lamunde tace "begama hutawa be dawo hayyacinsaba mu kyaleshi ya sarara
zuwa jimawa muje" suna fita Dan naci ta fakaici idon lamunde ta koma tasashi agaba tanata
kallonsa tana murmushi.
Tunaninta daya yaza ay tayi rayuwa dashi dama haka yake idanuwansama kawai abun
kallone shine zetafi da ita inda yake ya aureta ko kuwa waye shima batasaniba tambayar
dataketaywa kanta kenan tabbas inasan shi zan rayu dashi bazan taba gajiya da kallonsaba.
Ja ene tsaye yake ta bala'I "kuka Bari ta kubce muku tafiku gudune ko Yaya wannan
yarinyar itace zata tonan asiri wajen tenkwai tabbas idan tasamu wannan labarin bazata
aurenba Ni Kuma itace rayuwata ita nakeso"
cike da bacin rai damusa yace "haba sarki me jiran gado duk tarin kyawawan matanka Amma
kace lallai sai wannan mummunar? "
A fusace yasa wuka ya tsarge wuyansa sai jini ya Fadi Tim kasa matacce "duk Wanda ze
aibaya tenkwai hukuncinsa kenan kodako kahone kyau bashine maceba diri shine mace Dan
haka ita nakeji tamun soyyarta har cikin bargona take" can yay wani tunani sannan yace
"tabbas dole aduke ta bakunci lahira a yau din nan da ita da rama bazan barsu surayuba
saboda idan suna raye tenkwai zata dinga tunawa da abunda ya faru Amma idan na kashesu
nasan zata kara tsoronna takara yarda dani ta Mika kanta gareni kawai Koda ba a daura
aurenba"
"bashari"ya Kira yaransa "yau tsakar dare tunda duhu ya fara zamuje mu kashe aduke suka
sannan muje har gida mu cinye rama Dan zatai maiko" (yafara tandar baki ya tsohon maye
Koda yake meye maraba yadama mayen ne) suka hau murna,ya wurgowa musu harara "kufara
shiri so nake akashe aduke abar gawarta amma ita nasanja shawara ba yauba saboda gobene
bikin cin jarirai Dan haka a barta sai ankwana biyu adai kashe aduke yau" Nan suka hau ihu
suna murna.
Mahaifiyar ja'e ko abun duniya ya isheta tabbas sunada bukatar sanjin rayuwa jikinta
nabata wannan bakon shize kawo musu sanji tayaya take wani tunani yazo mata ze zama daya
daga cikin bayin bangarenta su goma ne Amma akwai wani tabbas kamarsu guda da wanchan
sai dai shi be cika haskeba Amma ay akwai dabara akwai abunda suke sawa me rinar da fata
shizatasa masa ta sallami wanchan ya gudu Amma sai ya warke.
Take tasa aka kirawo mata darzan yana zuwa ya zube "angaisheda uwar tausayi uwa agun
yariman masarautar kuguru"
"magana nakeso miyi dakai kasaurareni sosai idan ka kuskure hukuncin kisane akanka inaso
nanda Dan wani lokaci zan umarceka dakabar garin nan zansaka a hanya kafita kabar garin
nan ka koma beguwa tunda su naji anacewa suna dai bautar gunki Amma basa cin mutum
Kuma suna karbar bako yafi kusa da garin Nan idan Kuma zaka iya ka karawa gabama to ka
kara" nan yace "ranki ya dade inada mata da d'a"
"kabarsu kaje idan komai ya nutsa kadawo garesu" cike da murna yay godiya Amma kasan
ransa yana jimanta yadda ze rabu da matar sa da d'ansa "karka kuskura ka nuna musu zaka
bar wannan gari nasan yadda zanyi dasu kawai".
Dare na tsalawa suka dauki hanya suka shiga gidansu aduke suka sadada dakin suna
shiga sukaga mutum a kwance kawai suka Burma mata wuka tasaki ihu suka kara mata suka
daddatsata cikin Daren Nan ga gari da duhu suka sa kai suka fito suna fitowa suka hau sowa da
murna saura daya burin ubangidansu ya cika ya mallaki abar sansa duka da anmasa alkawarin
aurenta amma yafiso ta amince masa yayi wannan alkawarin saita soshi baze taba sa mata
karfiba kamar yadda yakeyi soyake tabashi hadin Kai yaji Dadi ya morewa wannan jikin nata me
masifar laushi cike da farin ciki yashiga turakarsa ya kwanta.
Ahankali take takawa saboda ba isashshiyar lafiya tana shiga taji tana taka abu tana dubawa
taga jini mezatay tasaki wata kara anan tafadi tasume.
(tofa muje zuwa akara hakuri dai fans ??????????bana samun damar typing me yawa
abubuwan sunmun yawa kuyi hakurin biyoni kudai yanzu labarin yasoma)
*feedyn bash*
[9/11, 22:29] +234 810 679 5647: *?ARNAN DAJI?*
*NA*
*FAREEDA ABDULLAHI*
*_?KAINUWA WRITERS?? ASSOCIATION_*??
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
GAISUWA DA JINJINA AGAREKU MASOYANA INAJIN DADIN YADDA KUKE COMMENT
DINKU AKAN ARNAN DAJI NAGODE SOSAI
40-45
Cikin kuka tafara tambayarsa meyasa kuka shigo tare baban rama yace nazo zan shigo
naganshi a zaure yacemun yaje gida wajen aduke akasanar dashi cewar tana Nan shine Ni
Kuma naga ay shima Danane duk daya kuke shine nace mu shigo tare bansan wannan tashin
hankalin zamu tarar ba dabazan Bari yashigoba kodan karyaga wannan danyen aiki yanzu Bari
na hanzarta natafi daji nemawa aduke magani ku kula sosai da ita ku kula dakanku Kuma
maza kuyi mata wanka ku gasa mata jikinta ya fice da hanzari ya nufi daji gabansa nata faduwa
yadai dakene kawai kafin kace meye wannan rama ta Dora ruwa nan d Nan ta tafasa tenkwai ta
kinkimeta takaita bayi rama ta wanke ta tsaf Dan bawani kuzari a jikin ta suka kamata suka
wuce da ita gida dake kakarta ba wani gani take sosaiba batasan meya faruba suka ajiyeta
sukace ta kula d kanta kafin babansu ya dawo daga dajin itadai kawai kallonsu take ita tasan
metakeji Amma bataji zata rayu bazata samu rayuwa me inganciba saboda iska tana shigarta
har cikinta saboda su basu da sittira sai fatar nn dasuke Dan kare gabansu da ita da mamansu
ko manyan ganyaye suyi ado dasu baban rama natafe yana tunanin wannan zalinci a cikin daji
kawai yaga an xagayeshi suwa ze gani ja e ne da yaransa rai bace baban rama y chakumi
wuyansa la ananne badu ya tsinema mara mutunci gafallalle kacutar damu ka cutar da
zukatanmu meyasa baka nemi yardartaba kasa mata karfi bayan kasan dokace sawa matanmu
karfi saina dau fansa akanka macuci cike da bacin rai ya fara magana nizaka tonawa asiri ka
turon tenkwai taga abunda nake aikatawa nasan Kai zaka shigo kaganni kaje ka kiratako kasan
ba abunda nakeso irin ta a rayuwata ko kaho da uwata banasansu haka Dole zaka karbi
hukunci hukunci me tsanani daga gareni bazan barkaba kaima kasani duk Wanda yaga sirrina
saina kashe shi bazan kashe tenkwai ba Dan ita tawace amma zan kasheka zan kashe rama
zan kashe aduke dukansu sai kun bakunci lahira hhhhhhh suka kwashe da dariya cike da tsoro
yake kallonsu bani nakira tenkwai ba nashigo natarar suna gidan ita tasanar Dani Kai ka aikata
wannan aikin amma nama alkawari bazan gayawa kowaba zan rufe wannan maganar namaka
alkawari nabika nabi badu nayarda bazaka karasa rama a idonka ba bazan Bari ta fadi wannan
labarin ba nama alkawari banida kowa sai ita bata da kowa saini katemakemu ja e yasheke da
dariya kasan Koda wannan maganar tafita bawani abu bane saboda bame jadani a wannan
gari ninake milkin wannan gari nida kaho nasan cewa jama ar wannan gari basa so asawa
mace karfi Ni Kuma komai da karfi nake yinsa