Showing 1 words to 3000 words out of 20000 words

Chapter 1 - MACE GUDA DAYA TILO HAUSA NOVELS BY SAKINAT.txt

anuary 2017
aisha ummi at 04:23
MACE GUDA DAYA TILO
[3/11, 4:49 PM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO... 1⃣
Na
UMMI A'ISHA
Matashin saurayine sanye da kayan yan
bautar kasa (N. Y. S. C) kayan sunyi mutukar
yimasa kyau, tsaye yake agaban allo yana yiwa
dalibai yan department of sociology lecture din
biology, a jami'ar tarayya dake jihar bauchi,
kowanne dalibi ya nutsu yana sauraron lecture
din domin babu karya malamin akwai iya darasi
kuma akwai zakin murya radau,wannan shine
shigarsa hall din na 3 ,yauma kamar kullum ya
kwashe fiyeda awa 1 yana yimusu lecture akan
introduction to biology, kwas kwas sukaji tafiyar
takalmi alamun ana shigowa cikin hall din,
hankalin kowa yakoma kanta, jiyowa shima yayi
yabita da kallo daga sama har kasa, farace
sosai dan har yellow take dan tsabar fari, bata
da tsayi sosai amma tana da dan jiki,
idanuwanta manya ne farare tas,tanada dogon
hanci da dan mitsitsin baki, tana sanye da wani
pink din leshi da mayafinsa takalmin kafarta
kuwa mai dan karen tsinine shima pink
hannunta rike da jaka pink colour, kanta tsaye
ta nufi inda zata zauna, he! Taji malamin ya
fada ko jiyowa batayi ba taci gaba da tafiyarta.
[3/11, 6:16 PM] Ummi A'isha: MACE GUDA
DAYA TILO...2⃣
Na
UMMI A'ISHA
Cike da haushi yabi bayanta yasha gabanta
tare da nuna mata hanyar fita get out from my
class taji yafada, idanuwanta ta bude sosai
tafara kallonsa farine tas dogo mai tsananin
kyau yana da idanuwa sosai hancinsa tamkar
biro kuma yana da yar kiba daidai misali ita
kanta tasan yanada kyau kuma ya hadu kallon
banza ta wurga masa tare da Jan wani dogon
tsaki, mamaki ne ya kamashi dan babu macen
da ta taba yi masa tsaki sai wannan yarinyar
yar rainin hankali, tsawa ya daka mata yace
who are you dazaki shigo min class yanzu? Me
kike takama dashi? Ke yar gidan uban waye?
Gaba daya ajin yayi tsit kowa ya zuba ido yana
kallonsu domin idan da sabo to sun gama
sabawa da halin wannan dalibar wani mugun
kallo ya bita dashi sannam yace oya carry your
legs and get out from my class tun kafin na
wulakanta ki, ni banma taba ganin wannan
fuskar taki acikin class dina ba, ita kuwa gaba
daya bakin cikin duniya yagama rufeta batare da
tace masa ko kala ba tajuya tafice daga cikin
hall din zuciyarta cike da bacin rai, lalle gayen
nan yau xan nuna masa ko ni wacece zaisan
dani da sauran matan da yasaba yiwa wulakanci
akwai banbanci ayau sai naga waye ubansa a
kasar nan.
[3/11, 6:18 PM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO
3⃣
Na
UMMI A'ISHA
Dawowa yayi yahau kan step din yaci gaba
da lecture din daya keyi, Director din makarantar
ne yashigo cikin hall din shida mukarrabansa
nan da nan idon kowa ya koma kansu wanda
ciki harda shi kansa malamin, dasauri director
din yazo gabansa yana cewa me yahadaka da
wannan yarinyar junaida mukhtar? Kasan ko
wacece ita? Bude baki copper din yayi tareda
niyyar yin magana amma cikin tsawa director
din ya katse shi tare da cewa look Lamin kaifa
ba staff dinmu bane service kawai kazo yi dan
haka mun dakatar dakai daga wannan
aikin,yanzu ka biyoni office inada magana dakai
yana kaiwa nan ya juya yafita shida wadanda
suka rakoshi, ajin kuwa tsit kakeji kamar ruwa
yacisu shi kuwa malamin wanda aka kira da
lamin kayansa yashiga tattarawa ya rufe laptop
dinsa ya saka acikin jakarta ya yiwa daliban
sallama wadanda akalla zasu kai kimanin dari
biyu kasancewar combined lecture ne
[3/11, 6:22 PM] Ummi A'isha: MACE GUDA
DAYA TILO
4⃣
Na
UMMI A'ISHA
Gaba daya yan ajin jikinsu yayi sanyi domin
wannan bashine karo na farko da dalibar tayi
sanadiyyar korar malaman makarantar ba,
ahankali ya gama hada kayansa cikin jakar ya
dauka ya rataya akafadarsa ya sauko ya futa
daga cikin hall din, yana fita hall din ya cika da
surutun daliban dake ciki, wasu tausaya masa
suke wasu kuma bakin cikin tafiyarsa suke
yayinda wasu kuma suke Allah wadai da halin
wannan dalibar mai suna junaida mukhtar.
Kansa tsaye ya nufi admin block,office din
director ya shiga suna zaune shida students
affairs da registerer da hed of department can
gefe kuma wannan kyakkyawar yarinyar ce
zaune tana kallonsa, da sallama yashiga suka
amsa tareda nuna masa kujerar da zai zauna,
yana zama director yafara balbale shi da fada
tareda cewa yazama dole kabata hakuri kuma
ka nemi afuwarta akan abinda yafaru dazu baki
ya bude cike da mamaki wai shine zai bawa
wannan yarinyar hakuri instead ace itace zata
nemi afuwarshi kallo yabisu dashi daya bayan
daya sannan yace impossible yaza ayi ace nine
zan bata hakuri bayan itace tayi min laifi? Head
of department ne ya katse shi ta hanyar cewa
kasan yar gidan waye kuwa? Ko yar gidan waye
wlhi bazan bata hakuri ba kallonsa suka farayi
cike da mamaki director yace to ai kuwa tunda
bazaka bata hakuri ba yazama dole kabar
makarantar nan ayau.
[3/11, 6:23 PM] Ummi A'isha: MACE GUDA
DAYA TILO
5⃣
Na
UMMI A'ISHA
Mamakine karara ya bayyana akan fuskarsa
domin kuwa babu dalilin da zaisa akoreshi akan
kawai ya hukunta dalibarsa wacce ta karya
dokarsa, wata xungureriyar takarda director ya
miko masa yace gashi ka zaba acikin biyu
nafarko ko kabawa junaida hakuri ko kuma ayau
dinnan ka bar mana makarantar nan domin
bazamu zuba maka ido ka yimana sanadin
aikinmu ba, wannan yarinyar babanta shine
permanent secretary na education kuma shine
Head of service na wannan state din dan haka
kazabi daya, shiru lamin yayi yana tunani wato
dan babanta ne head of service shikenan sai ta
raina mutane? Shi ai ya zata duk wannan
kafafar da take babanta ne governor dama head
of service ne kawai? Wani guntun tsaki yaja
aransa yace lallai nima dan bakusan waye ni ba
shiyasa kuke neman wulakanta ni,ni ai ubana
yafi nata matsayi tunda secretary to the state
government ne kaf state dinmu ubana shine na
3 daga governor sai deputy sai ubana amma
ban taba nunawa ba registerer ne ya katse masa
tunani ta hanyar cewa lamin kaifa muke jira kayi
magana kallonsu yayi sannan ya juya ya kalli
yarinyar yace wlhi bata isa nabata hakuri ba
nazabi barin makarantar, takardar ya karba ya
tashi yafita daga cikin office din ya nufi motarsa
wadda ke ajiye awurin da aka tanada domin
ajiye motoci.
[3/22, 7:56 PM] Ummi A'isha🏻: [3/15, 7:05 AM]
Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO
6⃣
Na
UMMI A'ISHA
Motarsa kirar Toyota corolla yabude ya shiga
ya fita daga cikin makarantar ,gudu yake
shararawa sosai kamar wadda zai tashi sama
yafita daga garin bauchi ya nufi birnin yola.
Karfe 3 dai dai yashiga cikin yola Chief olusegun
obasanjo housing estate ya nufa, ahankali yake
tukin har ya iso tangamemen gidan nasu wanda
yake cikin jerin gwanon gidajen, hon yayi mai
gadi ya bude masa gate din yashiga cikin gidan
securities sai daga masa hannu suke yi ajiye
motar yayi a muhallinsa sannan ya tasamma
cikin gidan, babban falon gidan ya shiga daya
daga cikin kannenshi ya hango kwance cikin
luntsumemiyar kujera tana kallon Indian film
sallama yayi dasauri ta dago tana cewa oyoyo
yaya lamin karasowa ciki yayi yana cewa
wacece? Hasna ce ko husna? Murmushi itama
tayi tace yaya kenan wai kai meyasa baka
ganemu? Dariya yayi mata sannan yace to
mummy da daddy ma basa ganeku balle ni da
bani na haifeku ba dariyar itama tayi sannan
tace to husna ce hasna na kitchen tana yimana
fried indomie murmushi yayi yace sarakan
kwadayi kenan ina mummy? Mummy tana side
din dad tabashi amsa mikewa yayi ya nufi side
dinshi.
[3/15, 7:08 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO
7⃣
Na UMMI A'ISHA
Dakinsa yashiga ya zauna ya zubawa carpet
din dake malale acikin dakin ido, tunanin
matakin da zai dauka akan wannan yarinyar shin
me take takama dashi? Yanzu kenan duk burin
da ya dauka ya rushe? Babban burinsa shine
yayi lecturing lokacin service dinsa domin yana
kaunar koyarwa a jami'a amma yau gashi wata
MACE GUDA DAYA TILo tayi masa sanadi ta
rusa masa duk budget dinsa ai kuwa yazama
tilas ya rama wannan wulakancin da tayi masa
da wannan shawara ya tashi ya shiga hadadden
toilet dinsa yayi wanka ya fito yashirya cikin
wata green din t shirt mai hoton heart ajiki sai
blue din jeans ya taje sumar kansa ya fesa
turaren smart collection ya fito, falon
mummynsa ya wuce yana shiga ya tarar da ita
zaune cikin kawatacciyar shiga tana waya
gefenta yan biyunta ne zqune suna cin
indomie,kusa dasu yaje yazauna yana fadin
hasna kin gama girkin dasauri kanwar tasa ta
kalleshi tana fadin lah yaya lamin yaushe ka
dawo? Ban jima da dawowa ba ya bata amsa
dai dai lokacin mummyn tasu ta gama wayar ta
kalleshi tana cewa babana saukar yaushe? Wlh
dazu nadawo mummy daddy yana gari kuwa?
Kallonsa tayi tace bakuyi waya bane? Dazun nan
yadawo daga Holland kaje ka sameshi yana falo
mikewa yayi ya nufi falon mahaifin nasa.
[3/15, 7:12 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO
8⃣
Na UMMI A'ISHA
Ahankali yake ratsa falikan har ya isa na
mahaifin nasa ya sameshi zaune yana hutawa
sallama yayi masa sannan ya nemi wuri ya
zauna yafara gaida shi cikin murmushi mahaifin
nasa ya amsa sannan yace lamin har kadawo
daga bauchin? Jikinsa asanyaye yace dady sun
sallameni sunce sai dai naje wani wurin nayi
service din kallonsa mahaifin nasa yayi sannan
yace laifin me kayi musu? Kansa ya sunkuyar
kasa sannan yace babu laifin komai daddy to
yanzu ya zakayi? Ya tambayeshi dama daddy
cewa nayi yanzu zan koma can N. Y. S. C
Secretariat din na sanar musu inyaso sai ayi
posting dina Bayero university kano ina ganin
hakan zaifi, to shikenan Allah yasa hakan shi
yafi alkhairi mahaifin nasa yace dashi amin ya
amsa sannan yatashi ya fita daga cikin falon.
Ita kuwa junaida tana tashi daga office din
director tashiga sabuwar motarta kia 1 door ta
nufi gidansu dake unguwar area 7 tana isa ta
wuce dakinta ta jefar da jakarta, mayafinta,
takalminta, wayarta ta haye gadonta ta kwanta
rufe idonta keda wuya tafara ganin wannan
saurayin matashin yana yimata gizo gaskiya
babu karya ya hadu zuciyarta taji tafara dukan
uku uku kamar zata tsage, idanuwanta ta bude
sannan ta mayar ta rufe still shi din dai take
gani lokacin da yake yayyafa mata masifa acikin
hall din.
[3/15, 7:13 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO
9⃣
Na UMMI A'ISHA
Zaune ta tashi cikin sauri, Fara zagaya cikin
dakin nata tayi sannan ta saki wani kayataccen
murmushi toilet ta shiga ta silla wanka sannan
ta fito ta sanya wata doguwar riga ta shan iska
ta nufi falo acan ta hango mahaifiyarta zaune
tana kallo karasawa tayi cike da shagwaba ta
fada kan cinyarta tana cewa umma nifa yunwa
nake ji dasauri takalleta tace haba autana me
yasa kike son zama da yunwa kira tafara
kwallawa daya daga cikin yan aikin gidan
dagudu ta runtumo tazo ta durkusa agabansu
kallon junada ta yi tace auta me zaki ci?? A
yangance tace ta dafa min indomie with egg da
sauri mai aikin ta tashi ta nufi kitchen domin
aiwatar da abinda aka sata ita kuma taci gaba
da zubawa uwar shagwaba.
[3/15, 7:15 AM] Ummi A'isha: MACE GUDA
DAYA TILO..
1⃣0⃣
Na UMMI A'ISHA
Tun da sassafe lamin ya baro garin Adamawa
ya nufi bauchi gudu yake babu kakkautawa ya
kure A. C din motar ya kunna wakar no one be
like you yana saurare amma acan kasan ransa
kuwa abinda zai aiwatar kawai yake tunani.
Karfe takwas ya shiga cikin bauchi dan haka
wani guest house ya zarce inda zai huta. Sai 10
ya fito yashiga cikin garin kofar jami'ar yaje ya
yi packing yana ganin shige da ficen daliban
yana nan xaune acikin motarsa ya rurrufe glass
din wanda ya kasance mai mutukar duhu ne na
waje baya ganin na ciki sai na cikine ke hango
na waje, wata mota pink colour ya hango tana
tahowa kirar new discussion R888 sai datazo
saitinsa sannan yaga ashe wannan yarinyarce
junada aciki tasha ado tamkar wata sarauniya
komai blue nan da nan ta kutsa kan motar tata
cikin makarantar shi kuwa murmushin mugunta
yayi tareda fadin yarinya kin tabo gidan rina dan
haka zaki yi bayani.
[3/22, 7:56 PM] Ummi A'isha🏻: [3/17, 9:52 AM]
Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO..
1⃣1⃣
Na
UMMI A'ISHA
Yana nan zaune har ya hango adam dama
shi yake jira, Adam daya daga cikin dalibansa ne
wanda yafara koya musu kuma course mate din
junada mukhtar ne shigowa motar adam din
yayi sannan yafara gaida lamin ta hanyar cewa
morning sir, morning lamin din ya amsa yace
dama zuwa nayi kabani duk labarin da kasani
akan wannan yarinyar junada mukhtar murmushi
Adam yayi sannan yafara bashi labarin. Alhaji
mukhtar Magashi shine mahaifinta kuma
asalinsu yan garin bauchi ne cikin karamar
hukumar Giyade babanta ya rike madafan iko da
yawa daga karshe aka bashi mikamin head of
service na wannan jahar matarsa 1 da yaransu
uku junada ce yar auta sai yayunta maza guda 2
Khalid da Amir, yar gatace ta karshe kasancewar
ita kadai ce mace kuma gata yar auta komai
daka sani na rayuwa yimata ake bata da wata
matsala sai kwaya daya.
[3/17, 9:54 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO...
1⃣2⃣
Na
UMMI A'ISHA
Matsalarta shine bata son karatu ko kadan
gata shagwababbiya ce ta karshe amma duk da
haka mahaifinta yana hukuntata idan ta aikata
ba dai dai ba sai dai ita mahaifiyarta tafi batata
don bata tsawatar mata idan tayi ba dai ba,
tunda muka shigo makarantar nan bata zuwa
lecture sai time din data gadama, bata
respecting din malamai balle yan uwanta dalibai
bata da lokacin tsayawa tayi karatu amma kuma
babu malamin da ya isa yabata carry over
saboda director yana daure mata gindi, yana iya
korar mutum akanta saboda kawai yana jin
tsoron kar ta fadawa mahaifinta abashi query
bayan kuma shi mahaifinta ba irin wadannan
mutanen bane masu zarmewa akan yayansu, ka
ganta nan har muka shiga level 300 bata taba
samun carry over ba alhalin kuma ba karatun
takeyi ba. Wani matashin murmushi lamin yayi
tabbas yanzu ya samu hanyar da zai rama
abunda tayi masa ta hanya mai sauki juyawa
yayi ga Adam yayi masa godiya sannan ya yi
masa sallama yatashi motarsa ya bar wurin,
garin kano ya nufa yana tafe yana nishadi ya
kunna wakar you are my African queen ahaka
har ya isa B. U. K.
[3/17, 9:56 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO..
1⃣3⃣
Na
UMMI A'ISHA
Yana isa ya kai takardunsa cikin sa'a sukayi
accepting dinsa musamman ma da suka ga
cewar ba a Nigeria yayi karatunsa ba a Malaysia
yake yi, psychology department suka turashi
suka bashi yan level 100 inda zai daukesu
Biology, sati 1 suka bashi tareda bashi inda zai
zauna amma bai karbi masaukin ba kasancewar
yanada inda zai zauna. Karfe 4 yagama abinda
zaiyi yabar cikin makarantar ya nufi yola. Bai
isa garin yola ba sai kimanin karfe 7 nadare
yana zuwa mahaifinsa ma na karasowa dan
haka cikin gidan ya shiga yajira karasowar
mahaifin nashi wanda bodyguard dinsa suka
ysnyameshi kamar wanda za adauke,da
fara'arsa ya tari dan nasa yana fadin tafiya tayi
sauri my son dafatan andace? Murmushi yayi
sannan yace yes dad sunyi accepting dina dafa
kafadarsa uban yayi tareda jan hannunsa suka
jera suna tafiya tamkar wasu abokai har suka
karasa cikin falon uban sannan shi lamin din ya
juya ya wuce side din mummy yana shiga ya
tarar da babban yayansa yana zaune yana cin
abinci akan dinning wajensa yakarasa yabashi
hannu suka gaisa sannan shima ya nemi wuri ya
zauna yace broz nabar bauchi university fa na
koma kano murmushi yayan nasa yayi wanda
suke mutukar kama amma shi bakine sabanin
lamin wanda yake fari sol, dubansa yayi yace to
nidai ina baka shawara wlhi babu kai babu yan
matan jami'a, dan nasan halinka da shegen
neman mata.
[3/17, 9:59 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO...
1⃣4⃣
Na
UMMI A'ISHA
Kai ko tsoron Allah bakaji balle tsoron
wadannan cutukan na zamani, rai lamin yabata
sannan yace kaifa kanada takurawa wlh
shigowar mahaifiyarsu ne yasashi yin shiru
domin baya son taji zancen da yakeyi
kasancewar yanada yakinin duk gidan babu
wanda yasan yana neman mata in banda yayan
nasa cikeda murna tace sannu babana shima
cikin sigar shagwaba yace yawwa mummy dama
nazo miki da wani albishir murmushi tayi tace to
Allah yasa alkhairi ne ai kuwa mummy alkhairi
ne kuma nasan zakiyi farin ciki sosai kallonsa
suka tsaya yi itada yayan nasa tace to fadi inji
cikin farin ciki yace na samo matar aure a
bauchi dan haka kisanar da dad aje a tambayo
min domin aure nake so, wani farin cikine ya
lullube uwar tace to Allah yasa albarka kuma
naji dadi bayan kagama karatu za ayi bikin?
Dasauri yace no nanda 3 months nake so ayi
cikin mamaki tace to zai yiwu ahada da na
abdulrahman yayankane? Yes mum haka nake
so ayi cikin fara'a tace to Allah ya yarda tatashi
ta fita daga cikin falon. Yayansa ne ya kalleshi
yace ai gara kayi auren yafi maka amma kana
yaronka dakai sai jarabar mata just 26 years?
Koni da nake 29 bana bin mata sai kai? Cikin
kunkuni lamin ya mike yabar cikin falon ya nufi
side dinshi aransa kuwa fadi yake wannan
dinma da zanyi ai na ramuwar gayya zanyi bana
Allah bane.
[3/17, 10:00 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO...
1⃣5⃣
Na UMMI A'ISHA
Yana shiga hadaden dakinsa wanda ya
kawatu mutuka da kayan alatun more rayuwa ya
fada saman gado ya jawo wayarsa BlackBerry
B210 Vicky yakira daya daga cikin yanmatansa
ringing 2 ta dauka cikin harshen turanci tafara
gaida shi murmushi yayi yace nayi missing dinki
daga can kamar zatayi kuka tace nafika damuwa
da rashinka kusa dani yanzu yaushe zakazo?
Silin din dakin ya kurawa ido yace gaskiya Vicky
zaki dade baki ganni ba amma next week zan
shigo kano to idan nazo i will call you murmushi
tayi tace ok sai najika i luv you, luv you too ya
amsa mata ya ajiye wayar ko minti 2 ba ayiba
wayar tasa tasoma ruri hannu ya mika ya dauko
yana dubawa yaga Jenifer ce cikin murmushi
yaje hello madam j how are you? Daga can ta
amsa da fine my Prince.
[3/22, 7:56 PM] Ummi A'isha🏻: [3/22, 4:21 PM]
Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO..
1⃣6⃣
Na
UMMI A'ISHA
Kamar zata saka kuka tace yaushe zamu
hadu? Wani malalacin murmushi yayi sannan
yace very soon but yanzu ina yola ne kin san
babu halin kizo amma idan nasamu time zanzo
dakaina cike da jin dadi tace to ina jiranka i love
you me too yabata amsa ya kife wayar. Daya
wayar tashi ce ta soma kara ya dauka ya duba
sunan Mary yaga ajikin screen din cikin sauri ya
daga yace hello my Mary yakike? Daga can tace
abnormal murmushi ya aika mata dashi yace
what's wrong? Cikin shesshekar kuka tace
kamanta dani kwana biyu baka nemana
rarrashinta yafara yi domin duk cikin yanmatan
sa itace star yafi ji da ita domin Mary akwai
kyau ga diri shiyasa ma yafi sonta fiyeda sauran
dakyar ya samu ya lallasheta tadaina kukan
sannan yayi mata alqawarin zai tura mata kudi
ta account dinta sai ta yanki ticket din jirgi daga
Lagos tazo kano ta sameshi saida yayi da gaske
sannan ta hakura sukayi sallama yana ajiye
wayar yaga yayansa daga bakin kofa yana tsaye
yana kallonsa fuskarsa babu walwala yace lamin
abinda kakeyi baka kyautawa wai kai me yayan
arnan nan suke baka ne ka manne musu? Wlh
kaji tsoron Allah dan babu mamaki yanzu yana
fushi dakai kuma inajin ma har giya kana sha
sai asannan lamin yayi magana yace ni babu
abinda nake sha nasan dai ina neman mata
amma bana shan ko sigari balle giya.
[3/22, 4:22 PM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO...
1⃣7⃣
Na
UMMI A'ISHA
Harara ya wurga masa sannan yace kalli lips
dinka yadda sukayi ja ahaka xakace min baka
shan giya na yarda? Kallonsa yayi yace yaya sai
dai idan sharri zaka yimin amma wlh bana shan
giya hararsa ya kuma yi yace kaji dashi dai ya
juya yayi ficewarsa shi kuwa lamin tashi yayi ya
shiga toilet domin watsa ruwa. Abangaren
junada kuwa tun ranar data sa aka kori lamin
duniya tayi mata zafi domin ta tsinci kanta
dumu dumu cikin kaunarsa gashi bata san a
inda yake ba bare tasa anemo mata shi, yauma
ranta abace ta shirya cikin wani brown din
material ta nufi sch amma sam zuciyarta babu
dadi gaba daya ranta abace yake kuma ko yaya
ta rufe idanuwanta shi take gani abinda yafi
tsaya mata arai shine yadda kullum sai tayi
mafarkin kyakkyawar fuskarshi, ranta ajagule ta
fito daga dakinta ko ummarta bata yiwa sallama
ba ta fita sabuwar motarta Prado baka ta dauka
ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login