Showing 12001 words to 15000 words out of 20000 words
Chapter 5 - MACE GUDA DAYA TILO HAUSA NOVELS BY SAKINAT.txt
da
ita yazo ya zauna yace ina sauraronki dama dan
Allah idan nagama exam ina so kabarni naje
bauchi kallonta yayi yace me akeyi? Babu
abinda akeyi ta fada tana wasa da yan yatsun
hannunta wani hamshakin murmushi yayi
sannan yace to idan kin tafi ni kuma ki barni
dawa? Kiyi hakuri zakije bauchi amma ba yanzu
ba kinji? Kai ta daga tace to shikenan a falon
tabarshi ta shiga dakinta, yana nan zaune har
su hasna suka fito harara yafara aika musu da
ita sannan yace wato baku ji abinda nace muku
ba ko? Allah yabaku sa'a tashi yayi ya nufi side
din mummy. Washe gari suka gama exam sun
samu hutu harna 3 weeks dan haka yanzu sai
zaman gida babu inda suke fita shima lamin
hutun sukeyi dan haka kullum yana gida, gaba
daya ya canza ya daina shan kunu da babbata
rai yana bin duk wata hanya da zasu shaku da
junada kuma yana kokarin kyautata mata a
kowanne lokaci,yauma tana kitchen tana girka
abincin dare yashigo su husna kadai yaga a falo
suna aikin kallon wani American film mai suna
prison break ko magana baiyi musu ba ya wuce
kitchen din lokacin daya shiga tana tuka tuwon
semo vita ahankali ya lallaba ya rufe mata ido
tana jin hannunsa tasan shine domin komai
nasa kamshi yake na turarensa, murmushi tayi
tace yaya lamin murmushi shima yayi yadawo
kusa da ita yace sannu da kokari yawwa sannu
da zuwa tafada tana kwashe tuwon kawo na
kwashe miki yafada yana kallon fuskarta a'a ai
baka iya ba tafada waya gaya miki? Ki tambayi
mummy kiji idan ban iya ba a'a ni basai na
tambayi mummy ba su hasna zan tambaya to ai
lokacin da nakeyi su husna basu da wayo a'a to
duk yadda akayi baka iya ba na iya mana ko
lokacin da nake Malaysia nine nake girki na ba
girki kakeyi ba take away kake ci ai nasani a'afa
kar kisa nayi fushi gobe kina tashi kiga nagama
shirya breakfast hmmm da kuwa kaga nafi yarda
da abinda ka fada uhm kinga zaki sa yau naki
yin marking din papers din dalibai na tunda kince
ban iya tuwo ba a'a wasa nake ka iya tuwo
harda miya daidai lokacin tagama kwashe tuwon
taje ta sauke miyar danyar kubewar data yi ta
kalleshi to idan bakayi wa dalibanka marking ba
yaya zakayi dasu? Kowa yasamu carry over
yafada yana ficewa daga cikin kitchen din.
[3/24, 10:21 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO..
Na
UMMI A'ISHA
5⃣3⃣
Bayanshi tabi da kallo tana murmushi saida
tagama shirya komai acikin flask sannan ta
debo ta kawo kan dining ta jajjera ta karasa
wajen su husna wanda suke zaune sun kurawa
tv ido suna kallo, gefensu taje ta zauna itama ta
fara kallon, lamin ne ya fito shima yazo gefenta
ya zauna daga shi sai short nicker da farar riga
body hug laptop dinsa ya ajiye akan Stoll din
dake gabansa ya miko mata wata takarda ungo
rinka fado min mark din ko wanne dalibi karba
tayi tafara karanto masa kallonsa tayi yanzu fa
muma da dalibanka ne tsaf zaka bamu carry
over ko? Kwarai kuwa shi yafi komai sauki ma
musamman ma wadannan yaran masu masifar
kallon tsiya murmushi tayi ta kalleshi ya
sunkuya ya dukufa yana daddana laptop din
fuskarsa dauke da murmushi fado min mark din
Khadija Aminu 25 a'a ban yarda dakeba sai dai
35 don yarinyar tanada kokari kusanma tafi duk
matan ajin kokari ras taji gabanta yafadi to ko
itama budurwarsa ce? Tafada acikin ranta kin
san ku mata baku fiya karatu ba shiru tayi masa
bata bashi amsa ba shi kuwa bai ma san Kalmar
daya fada ya bata mata rai ba da haka suka
gama fuskarta babu walwala shima saiya samu
kansa cikin damuwa, kiran sallar magribar da
suka jiyo ana kwallawa a masallacin gidan ne
yasasu tashi gaba dayansu,nan yabar kayan
aikin nasa yashiga dakin junada a bathroom
dinta yayi alwala sannan yafito ya tafi
masallaci, abinda yake Kara burge junada kenan
domin sam lamin baya wasa da sallah, yana
fitowa daga masallaci sashen daddy yawuce
anan ya taradda mummy murmushi yayi yace
mummy kema nan kika taho? Dariya tayi tace to
ai babana kune kuka kwashe min abokan hirar
tawa sai asannan daddy yayi magana yace to
shi basai yana zuwa yana tayaki hirar ba zama
yayi akusa da daddy yace to ai sai nazo indai
mummy tace nazo din, ko cewa tayi nadawo
gaba daya ma sai nadawo dariya sukayi gaba
dayansu daddy yace ina matar taka take?
Kwana 2 ban ganta ba amma ina ganin girkinta
kullum murmushi mummy tayi tace ai gaskiya
yayi dacen mata yarinyar nan karfi da yaji ta
hanani yin girki kullum sai dai ta dafa ta kawo
min ta dauke ni tamkar mahaifiyarta Allah yayi
mata albarka shidai lamin shiru yayi amma har
cikin ransa yaji dadyn yabon junada dasu daddy
sukayi dama yasan dole su mummy su sota
domin ko acikin yayansu sunfi sonshi,son da
suke yi masa nema ya shafi matarshi.
MACE GUDA DAYA TILO..
Na
UMMI A'ISHA
5⃣4⃣
Anan ya zauna har saida aka kira sallar isha
sannan suka tafi masallaci shida daddy, yana
fitowa daga masallaci ya wuce side dinsu nan
ya taradda su sun baje suna cin tuwo gaban
junada ya je yasa hannu acikin kwanonta yafara
cin tuwon sudai su husna mamakin yayan nasu
sukeyi kwana biyu domin duk ya canza sai
tattalin matarsa yake gamida tarairayarta
murmushi yayi mata yace gaskiya miyar nan
tayi dadi itama murmushin tayi tace ko? Eh
mana ai tayi dadin da bazai misaltu ba gobe ma
kiyi mana ita kin san ita kubewa tanada
mutukar amfani ajikin dan adam likitoci sun
tabbatar da haka dariya tayi tace to kai kuma
yaushe kabar lecturing ka koma doctor? Ranar
da kika bar daliba kika koma noman kubewa
dariya tayi masa sosai sannan tace gaskiya ya
kamata nasa maka waigi dan naga alama santi
kake murmushi yayi ai tuwon naki ya kai
matsayin da za ayi masa santin yanzu daddy
ma nasan yana can yana santin wannan miyar
kubewar hmmm kai dai tunda kayi shikenan
yana koshi ya mike idan kin gama ki shigo min
da laptop dina da sauran kayan cikin daki to ta
amsa masa dakinsa ya wuce yaje ya kunna
labarai a BBC yana kallo sai wurin 9 sannan
tashiga dakin nasa da laptop din a hannunta ya
baje akan gado yana kallo daga shi sai gajeren
wando idonta ta sauke kasa batare data kalleshi
ba tace ga kayan naka ajiye anan kishiga
bathroom ki hada min ruwan wanka, wanka
zanyi ajiyewa tayi ta shiga cikin bathroom din
sai data dan wakeshi tafesa air freshener mai
kamshi sannan ta hada masa ruwan wankan ta
fito na zuba maka to ki jirani na fito sai mu
karasa wannan aikin ko? Tom ta nemi wuri ta
zauna agefen gadon bai dade sosai ba yafito ya
sameta zaune inda ya barta.
MACE GUDA DAYA TILO...
Na
UMMI A'ISHA
5⃣5⃣
Bakin gadon shima yaje ya zauna ya kamo
hannunta ya rike cikin nasa junada ita dai shiru
tayi tana ganin ikon Allah murmushi yayi ya dan
kalleta yace junada kalleni kin kallonsa tayi
magana ya sakeyi ki kalleni junada ni mijinki ne
abokin rayuwarki, komai da kikaga yana da
sanadi kuma akwai yadda yake zuwa yanzu ki
tashi kishiga toilet ki dauro alwala kizo mu
gabatar da sallar ma'aurata tunda kin korar
mun yan mata kinga sai ke ki dauki dawainiya
ta dam! Taji gabanta ya fadi me lamin yake nufi
ta tambayi kanta dubansa tayi cike da mamaki
ta fizge hannunta daya rike cikin nasa tace
ma'aurata? A ina na zama matarka? Ta ina
muka zama ma'aurata? Kamanta abubuwan
daka fada a baya? Kai da bakinka kace ba ka
daukeni a matsayin mata ba a yar aiki ka
ajiyeni, dan haka ina son kabarni a matsayin yar
aikin kamar yadda zuciyar ka ta kudurta tun
farko kar ka canza min matsayi daga yar aiki
kuma yanzu duk abinda zaka fada bazai yi tasiri
agareni ba saboda nasan ba gaskiya bane
kafada ne kawai saboda ka cimma wata manufa
taka tana kaiwa nan ta tashi fuuuuu! Tafice ta
bar dakin shi kuwa lamin yakasa koda motsi
dama yasan dole sai haka ta faru tsakaninsu
duba da yadda haduwarsu ta kasance tun
farko,wani guntun tsaki yaja to ita wannan
yarinyar me takeso tace? Nufinta ba sonta yake
yiba kawai sha'awarta yake? Mts dama haka ita
zatayi tunani gani zatayi kamar sha'awarta nake
dan haka da zarar na cika burina zan daina
kulata alhalin kuma ba haka bane alokacinne ma
zanfi kulawa da ita zanfi nuna mata tsantsar
soyayyar da nake yimata, zan nuna mata kauna
wacce bata samu ba afarkon aurenmu yafada
acikin zuciyarsa.
UmmiA'ishah
[3/24, 12:34 PM] Ummi A'isha🏻: [3/24, 10:28
AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO...
Na
UMMI A'ISHA
5⃣6⃣
Ji yayi zuciyarsa ta fara tafarfasa kamar ana
hada mata wuta lallai ma yarinyar nan to itada
ahaka zasuyita zama? Wannan ma ai shirme ne
kuma ba mai yuyuwa bane tunda shi yanada
bukata ita kuma ta tsare ta kasa ta hanashi
kula ko wacce mace sai ita kadai MACE GUDA
DAYA TILO tashi yayi yafara zagaye dakin nasa
yayinda bacci kuma yayiwa idanuwansa kaura.
Ita kuwa junada tana zuwa daki tafara godewa
Allah domin ta san yafara amsar add'arta tunda
gashi har lamin yafara nuna son kasancewa da
ita ina sonka lamin tafada acikin zuciyarta wani
murmushi tayi sannan tace zan mallaka maka
kaina amma ba yanzu ba sai lokacin dana
tabbatar da ka gama kamuwa da ciwon sona
kagama yarda da cewa nikadai ce MACE GUDA
DAYA TILO acikin zuciyarka da wannan tunanin
ta tashi tayi shirin bacci tayi kwanciyarta ba
tare da damuwar komai ba shi kuwa lamin yana
can yana ta faman sintiri atsakar dakinsa kamar
wani soja awannan daren dai sai bacci barawo
shine yayi nasarar sace shi daf da asuba. Da
misalin 8 ta fito ta shiga kitchen kamar kullum
ta shirya lafiyayyen breakfast ta kawo kan dining
ta jera tana gamawa ta shiga dakinta tayi
wanka ta fito tashirya cikin wata body hug baka
mai dan siririn hannu da wata bakar skirt ta
matseta sosai ta gyara gashin kanta ya sauko
har gadon bayanta ta feshe jikinta da turaren
urban woman tasa wata bakar hula mai gashi ta
nufi falo tana fitowa ta hangoshi akan dining a
zaune ya zubawa abincin ido fuskar nan tasa
tayi mutukar kyau yana sanye da orange colour
din t. Shirt mai gajeren hannu da blue din jeans
hannunsa daure da agogo golden colour gaba
daya falon ya gauraye da kamshin turarensa
manyan idanuwansa ya dago yafara kallonta
fuskarta tasha make-up kayan da tasa sunyi
bala'in matseta kuma sunyi mata kyau abunka
da farar mace nan da nan yaji ya rude ya nemi
nutsuwarsa ya rasa tuni hankalinsa ya soma
neman tashi kallo kawai yake binta dashi dakyar
ya iya furta pls zo ki hada min tea din,
ayangance kamar mai tausayin kasa ta tako
zuwa kan dining din ta dan russuna yaya ina
kwana acan kasan makoshinsa yace lfy beauty
MACE GUDA DAYA TILO
Na
UMMI A'ISHA
5⃣7⃣
Tea din ta fara hada masa sai wani shan
kamshi take shi kuwa lamin yasaki baki sai
binta da kallo yake sai kace wani soko tana
gama hadawa ta kawo gabansa ta dire masa ta
juya zata tafi hannunta taji ya ruko cikin nashi
jawota yayi ya zaunar da ita akan cinyarshi
yafara murza yan yatsunta cikin nashi ahankali
kamar kullum yarr! Taji nan da nan ta tuno da
yan matansa acikin zuciyarta tace yanzu suma
haka yake yi musu ko? Wata zuciyar tace mata
fin haka ma yayi kamar wadda aka tsikara tayi
zumbur ta mike ta fincike hannunta kallon
mamaki yabita dashi wai junada meye yake
damunki ne?. Bata kalleshi ba ta wuce daga
dining area din falo taje ta zauna ta kunna kallo
tana nan zaune har ya gama yin break din ya
taso ya dawo falon ya zauna yana zama ta
tashi ta shige dakinta tayi zamanta abin duniya
ya taru yayi masa yawa shima mikewar yayi ya
nufi side din daddy anan ya iske mummy zama
yayi suka fara hira babu laifi ya dan jin saukin
damuwar da yake ciki. Anan ya kusan wuni sai
da yamma yakoma side dinsu yana shiga ya
tarar dasu husna suna zaune a falo ita kuma
junada yajiyo motsinta a kitchen dakinsa
yashiga yayi wanka yafito cikin ash colour din
riga da bakin wando kansa tsaye ya shiga
kitchen hangota yayi tana kaiwa da kawowa
acikin kitchen din daga ita sai wata yar
mitsitsiyar shimi ja da dogon wando masha
Allah yafada acikin zuciyarsa ahankali ya karasa
daf da ita ya tsaya tana jinsa taki jiyowa ta
shareshi gyaran murya yayi sannan yace sannu
da aiki beauty sunan taji har cikin ranta ita dai
tana son muryarsa shiyasa take son taji yana
mata magana koda kuwa fada ne jikinta ya
matso ya ziro hannuwansa ta bayanta yace
kawo in yanka miki salak din a'a kabarshi
nagode ta fada cikin wata iriyar murya domin
gaba daya ya gama rikitata lokaci daya saboda
duk yabi ya dabaibaye ta ya hanata sakat kafa
sakar min nauyinka nauyi kuma? Ni wanne nauyi
gareni? Au kai bakasan kanada nauyi ba? Ni
banida wani nauyi babu mamaki ma idan akace
kin fini nauyi uhm anya kuwa zan fika nauyi? To
ko za agwada ne? A'a ba sai mun gwada ba
tafada tana girgiza kai hmmm yayi murmushi ke
kin fiya raki dayawa.
MACE GUDA DAYA TILO
Na
UMMI A'ISHA
5⃣8⃣
Kin fiya raki da yawa tun yanzu kin fara
cewa inada nauyi anya kuwa zaki iya naukar
nauyina? A'a bazan iyaba tayi masa gatse acikin
zuciyarta kuwa cewa take wadan nan tsiga tsiga
matan ma suka iya daukar ka balle ni?
Hannuwan shi ya janye daga jikinta yace natafi
masallaci ya juya yafita ita kuwa wata ajiyar
zuciya ta sauke. Tunda ya fita salla bai dawo ba
sai bayan sallar isha yau falon babu kowa
mamaki ne ya kamashi to ina suka shiga?
Dakinta ya nufa ya murda yajishi a kulle yadawo
nasu hasna shi kuma a bude yake amma basa
ciki duk yadda akayi suna side din mummy
yafada acikin zuciyarsa can din ya nufa
yasamesu sunata hira da mummy amma babu
junada ganin haka yasa ko zama baiyi ba yafice
sai yanzu ya gano wato daki ta shiga ta rufe
kenan dan kar ya bukaci wani abu agurinta tsaki
yaja yace ni kuwa zan baki mamaki junada in
dai nacika lamin baxan sake nuna miki bukatata
akanki ba kan dining yaje ya samu ta shirya
komai faten dankali da hanta sai salad data
hada masa domin tasan shi yana son salad
zama yayi yaci ya koshi sannan ya shiga
dakinsa wanka yayi abin mamaki hatta ruwan
wankan ta hada masa murmushin mugunta yayi
yace yarinya ina tausaya miki cike da damuwa
yayi baccin wannan rana.
[3/24, 10:32 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO
Na
UMMI A'ISHA
5⃣9⃣
Washe gari da safe ya tashi yayi wanka ya
shirya ya fito yauma kamar jiya taci ado tamkar
baturiya cikin wata doguwar Riga dark brown
shara shara mai hannun shimi ta tufke gashin
kanta wanda yake lodi guda ta kame akan kujera
har cikin zuciyarsa yaji sonta ya ratsashi babu
karya ta tafi da imaninsa ahankali ya jefeta da
wani irin kallo wanda shi kadai yasan
ma'anarsa falon yashiga ya zauna ina kwana
yaya lamin tace dashi cike da murmushin da
yake karawa fuskarsa kyau yace lfy lau kawo
min tea kawai yau babu abinda nake sha'awar
ci kallonsa tayi nayi maka farfesu fa a'a ki ajiye
min anjima zanci yanzu fita zanyi tashi tayi taje
ta hado masa ruwan zafin ta kawo masa kadan
yasha sama sama yatashi ya kwashi wayoyinsa
da key din motarsa ya fita lekensa ta farayi ta
window ga mamakinta sai taga ko side din
mummy bai kalla ba ya shiga motarsa yafita
daga gidan to ina ya tafi?? Ta tambayi kanta
karfa yakoma yawon bin matan da yasaba
gabanta taji ya fadi ya Allah ka kare wannan
bawa naka,ka kawar da idonsa daga kan matan
banza Allah ka dawo min dashi lfy wani irin
kishine taji yana taso mata agaskiya tana kishin
lamin sosai domin tasan mijinta ya hadu ta
kowanne bangare tamkar tauraro yake acikin
taurari kana ganinsa kaga cikakken bafulatani
yanayin da taganshi lokacin da yana bacci ne ya
fado mata hmmm dole yan mata suna rububinsa
domin kyansa ya isa.
MACE GUDA DAYA TILO
Na
UMMI A'ISHA
6⃣0⃣
Haka ta zauna sukuku ko tea dinma ita
takasa sha domin duk a tunaninta yawon neman
mata ya tafi musamman ma yau da taga ko
sha'awar taba hannunta bai yi ba, nan ta nemi
wuri ta zauna tanata sakar zuci ta na nan zaune
har su husna suka tashi daga barci suka fito
sukazo suka isketa a falon suka fara kokarin yin
break ita kuwa hirar da suke yimata sama sama
take ji domin bata cikin nutsuwa hankalinta
naga abin sonta lamin ni dai ummi A'isha yar
kallo ce, tana nan zaune motsi kadan ta kalli
agogo har 12 tayi ganin bai shigo ba yasa ta
tashi tashiga kitchen tabar su husna suna kallon
wani Indian film atashar zee aflam mai suna
muhabbatien,aiki take amma sam babu walwala
da sukuni a tattare da ita ahaka ta gama hada
hadaddiyar fried rice dinta wadda tasha hanta
da carrots ga cabbage yaji sai kamshi take tayi
wara wara da ita gwanin sha'awa dan ko ni
ummi A'isha saida naji yawuna ya tsinke, tana
gama hada fried rice din ta soya naman zabbi
tayi masa kykkyawar suya ta tattara komai ta
zuzzuba a cikin food flask ta kawo kan dining
tafara jajjerawa su husna dake falo suka fara
tandar baki hasna ta taso tace Anty me kika
girka mana ne? Hararta tayi tace mijina nayiwa
girki ku jira idan yaci ya rage sai ku karashe
sauran dariya hasna tayi ta koma falon tana
fadin to bari mu zauna zaman jiransa husna
dake zaune tana sauraronsu tace ai kema hasna
nasha fada miki mu tattara mu koma sashen
mummy amma kika ki gashi nan ai muna ganin
wariyar launin fata awajensu dariya sukayi
hasna tace ai Anty tana shagwaba yaya tafi
sonsa ma akanmu murmushi junada tayi tace ai
dole dama nafi sonsa tunda matsayinsa yafi
naku dariya suka yi ita kuwa daki ta shiga tayi
wanka ta shirya cikin atamfa super kalar ruwan
kwai ta yiwa fuskarta kwalliya sosai ta kafa
dauri kamar goggoro ta feshe jikinta da
turarruka masu dadi tasa sarka fashion golden
colour ta fito falo lokacin karfe 4 har tayi wuri ta
nema ta zauna tana jiran gawon shanu, ni dai
ummi A'isha ina daga gefe ni ma ina sauraron
zuwan oga lamin.
Ummi A'isha
[3/24, 12:34 PM] Ummi A'isha🏻: [3/24, 10:37
AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO..
Na
UMMI A'ISHA
6⃣1⃣
Tana nan zaune har 5 tayi tuni su hasna sun
tafi sashen mummy ita kuwa junada ta cika tayi
dam kiris ya rage ta fashe, sai 5:30 ya shigo
gidan tana zaune a falo ya bude ya shigo
hankalinsa kwance fuskarsa wasai ganin haka
yasa junada taji ta dada tsarguwa da shi kallo
bishi da shi babu alamun damuwa ko kadan a
fuskarsa sallamarsa ce ta katse ta, ta amsa
fuska babu annuri can nesa da ita yaje ya zauna
tuni ta gasgata zarginta fuskarsa dauke da
murmushin keta yace ina su hasna? Kamar ba
zatayi magana ba tace suna side din mummy
kallonta yayi kwalliyar tata tayi masifar yi masa
kyau gamida jan hankalinsa amma bai nuna
mata hakan ba shi kansa ya san junada first
class ce asahun kyawawan mata kamar yadda
yake first class a sahun kyawawan maza
dagowa yayi yaga ta kafe shi da ido ko kiftawa
batayi wai lfy kuwa? Ya tambayeta lafiyar ce ta
kawo haka tafada tana mai ci gaba da kallonsa
har sai da ta tabbatar da zarginta domin lips
dinsa taga alamun jan baki ajiki a fusace ta
mike yabita da kallo ya ce gobe ki shirya za
muje bauchi banza tayi masa ta shige dakinta
shi kuwa tashi yayi ya hau kan dining yafara
kwasar girkin da ta tanadar masa. Ita kuwa
junada tamkar zata mutu dan kunar rai,
hankalinta duk yabi ya gama tashi ita kam ya
zata yiwa lamin ya daina neman matan nan?
Wata zuciyar tace duk laifinki ne meyasa
alokacin da yazo miki da bukatarsa baki bashi
hadin kai ba? Ai da kin amince dashi kin bashi
kulawa to da babu macen da zata sha gabanki
awurinsa saboda duk matan da zai yi mu'amula
dasu awaje babu wacce zata nuna miki