Showing 9001 words to 12000 words out of 20000 words
Chapter 4 - MACE GUDA DAYA TILO HAUSA NOVELS BY SAKINAT.txt
mata dan haka
cikin sauri ta shige dakinta yana shigowa su
hasna na fitowa falo tambayarsu yayi ina
antynku? Tana daki suka bashi amsa cikin dakin
ya nufa tana zaune bakin gado ki fito ki bani
abinci yunwa nakeji.
MACE GUDA DAYA TILO...
4⃣2⃣
Na
UMMI A'ISHA
Yunwa nakeji office zan koma ko sai kin bata
min rai? Murna ce ta rufeta tafito ta nufi kitchen
shikuwa mamaki yakeyi wai wannan yarinyar ce
kiri kiri ta hanashi zama a office domin
tunaninta daya addabeshi. Gari na wayewa su
mummy suka dawo dama tayi musu shirye
shiryen karbarsu tayi girke girke da yan soye
soyen karbarsu. Da daddare daddy dakansa ya
shigo bangaren mummy ya kirawo lamin sudai
suna zaune suna sauraron abinda zai faru cikin
fada daddy yafara cewa lamin baka kyauta
mana ba yanzu ashe dama baka da mutunci?
An tabbatar min da cewa kana kawo mata gidan
nan da bama nan cikin sauri junada tace a'a
daddy karya ake yi masa abokan aikinsa ne aka
kawosu basu samu dakiba to shine ya kawo su
nan kafin su samu daki kuma saida ya fada
mana nida su husna cewa zasu zauna kafin a
sama musu masauki sannan kuma daina shiga
dakin yayi har sai da suka tafi cikin mamaki
yabita da kallo su hasna kuwa shiru sukayi
domin sun san wannan maganar ba gaskiya
bace kawai ta fadi hakane danta kareshi amma
ba wani abokan aiki girgiza kai daddy yayi yace
shikenan Allah ya rufa asiri suka amsa da amin
sannan dadyn yatashi ya koma sashensa shima
sashensu ya tashi ya tafi sai faman cika yana
batsewa yake.
MACE GUDA DAYA TILO...
4⃣3⃣
Na
UMMI A'ISHA
Suna nan zaune a falon mummy, mummy ta
fiddo musu da tsarabarsu ta basu kowa jaka
guda ta ciko masa da kaya, nan suka baje
kayan kowa yana ganin nasa sai murna sukeyi.
Shi kuwa lamin yana can dakinsa yanata
tunanin me junada ke nufi? Anya kuwa yarinyar
nan bata fara sonsa ba? Xumbur ya mike ya
nufi sashen mummy ya taradda su yanda ya
barsu mummy dan Allah baku dawo da maganin
ciwon kai ba? inajin akwai junada ya kalla ki
kawo min ina daki, mummy ce ta shiga dakin da
kanta ta debo mata maganin ta bata, mikewa
tayi ta nufi sashensu ta dauki ruwa a kofi marar
sanyi tana shiga dakin ta sameshi tsaye abinka
ga lecturer ansaba tsaiwa mika masa ruwan tayi
bai karba ba, yace kya iya zubarwa dan ba shine
a gabana ba, agidan uban wa kika zama matata
da zaki rinka korar min yanmata? Ai nafada miki
ni ban daukeki a matsayin mata ba, a yar aiki na
ajiyeki mamakine ya kamata lallai wani mutumin
ba ayi masa gwaninta yaci gaba da cewa banda
ke shasha ce kuma munafuka ina ruwanki da
sha'anina? Cikin bacin rai ta kalleshi gaka nan
babban munafuki mai sabawa Allah da
manxonsa dan nace ni matarka ce shine ina
nufin sonka nake? Allah ya sawwake me zanyi
da mazinaci, kazami mai bin yayan arna? Nayi
hakane dan na kareka daga masifar zina amma
ba don ina sonka ba ko kana nufin ban san illar
shaidar zir ba? Nasani amma nayi don na
tseratar da kai daga fushin iyayenka dan na lura
kana da karancin ilimin addini baka san hukuncin
mazinaci ba taja wani dogon tsaki ta juya tafice
dakinta taje ta kwanta tafara kuka sam bata so
haka ta faruba taso ace yanda ta sauke duk
wani girman kanta take binshi sau da kafa
shima yayi hakuri ya karbeta a matsayin
abokiyar rayuwa kuka takeyi sosai. Shi kuwa
yana nan tsaye inda ta barshi kamar dashen ice
ya kasa koda motsi maganganunta ne kawai ke
masa yawo a kwakwalwarsa abu 3 ne yafi bata
masa rai kalmar data kirashi da ita ta jahili da
kuma kiransa da mazinaci da tayi sannan cewa
me zatayi dashi yafi komai daga masa hankali
da bata masa rai, dakyar ya iya daga kafarsa ya
isa bakin gadonsa ya kwanta kansa sai zugi
yake masa kamar zai rabe gida 2.
[3/23, 11:25 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO...
4⃣4⃣
Na
UMMI A'ISHA
Kwana 2 yayi yana jinyar maganganunta
kuma tun daga ranar bai Kara yadda sun hadu
ba abinci ma idan ta ajiye masa baya ci yanda
ta ajiye kayanta haka zata dauka bai ko buda ba
abin duniya ya isheta, bayan ta gama ayyukanta
tazo ta tsaya ajikin window ta daga labule lamin
ta hango yana motsa jiki afilin wasa yasa farar
riga irin ta yan ball da wandonta yasa farin
takalmi combos yanata buga kwallo shi kadai
nan ta tsaya tana ta kallonshi har yagama ya
nufo cikin falon labulen ta saki ta nemi wuri ta
zauna a bakin gado su husna ne suka shigo
hasna tace ah anty junada wannan rigar fa?
Hararsu tayi tace ba ason sa ido da sauri husna
tace gaskiya rigar tayi kyau kamar shimi amma
har gwiwa take shigowar lamin ce ta katse
musu maganar yabi junada da kallo ita kuwa da
sauri ta jawo hijab ta saka su hasna ya kalla
yace yaran nan baku da kirki kwana biyu banida
lafiya amma ko ku dubani cikin sauri sukace wlh
yaya bamu sani ba eh amma wadda kuke tareda
ita ai tasani juyawa ga junada sukayi suna cewa
amma anty baki kyauta ba kallo tabishi dashi
yayi kyau sosai yana sanye cikin riga t. Shirt
brown da jeans blue yanata kamshin turaren
Phoenix kallonta yayi yace zakizo ki bani abincin
ko kuwa? Dasauri ta mike ta shiga kitchen ciki
yabita yana tsaye yana kallonta tana zuzzuba
masa abincin har tagama ta dauko zata fito
hanya yabata amma yana tsaye a bakin kofar
tsayawa tayi tace zan wuce to ki wuce mana ko
na hanaki ne? Ahaka ta wuce amma dole saida
ta dan bugeshi sannan ta iya wucewa bayanta
yabi har suka isa dining area din.
[3/23, 11:40 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TIILO..
4⃣5⃣
Na
UMMI A'ISHA
Kallo ya ringa binta dashi har ta gama
zuzzuba masa ta ajiye masa ta wuce dakinta
murmushi yayi yafara ci. Wasa wasa sai jinsa
yayi ya wayi gari da matsanancin son junada
kuma tun ranar data gaggaya masa
maganganun nan yaji zina ta fita daga ransa
baya sha'awar aikatata dan haka tuni yafara
neman gafarar ubangiji ba dare ba rana. Gaba
daya sonta yagama shigarsa ta ko ina bashi da
buri illa kasancewa da ita dan haka ya daura
aniyar nuna mata so afili tare da bin duk wata
hanya domin yasamu ta shaku dashi, yau sai 5
yadawo domin meeting sukayi kansa tsaye ya
wuce side dinsu amma ya tarar bata nan ya
tabbata tana wurin mummy dan haka ya nufi
can din yana shiga ya tarar da mummy a
babban falo tana waya ita kuma dama yaji
motsinta a kitchen dan haka kitchen din ya bita
ya taradda ita tana fere doya kamshin turarensa
kawai taji tasan yashigo tsayawa tayi cak daga
aikin da take bayanta ya karaso yazo ya tsaya
ahankali tamkar mai yin rada yace wai ni
meyasa duk abinda kikeyi daga kin ganni sai ki
daina sai kace wani dodo? Saboda ina sonka
tafada acikin zuciyarta amma a fili shiru tayi
bata amsa masa ba, da rana me kuka dafa?
Tuwon shinkafa ta bashi amsa yanzu kuma me
zaki dafa? Soyayyiyar doya da miyar koda
murmushi yayi to ni yanzu me zaki bani? Dan
yunwa nakeji babu abinci amma akwai snacks
to kawo min snacks din da juice tana jiyowa
sukaci karo sorry ya fada tareda ja baya ya
koma falo murmushi junada tayi tace Allah
yakara shirya min kai lamin yana zuwa ya zauna
kusa da mummy hayaniyar su husna ya ji a
dayan falon ya kalli mummy me yaran nan
sukeyi ne? Kallo mana mummy ta bashi amsa
murya ya daga hasna kuzo nan suna zuwa ya
fara masifa wato ku baku da aiki sai kallo ko?
Kun bar junada ita Kadai da aiki kuna jira ta
gama ta kawo muku kuci ko saboda ga baiwa?
To wlh baku isaba kune zaku rinka girki ba
matata ba ku tashi ku shiga kitchen ku karasa
aikin da takeyi tashi mummy tayi tana fadin
dakyau ka kyauta yara yan mata dasu amma ba
su iya girki ba idan akayi aurensu ya zasu yi ta
shigewarta dakinta su kuma su hasna suka
shiga kitchen juyowa yayi ga junada wadda tun
dazu take rike da kaya a hannu tana jiran ya
karba.
MACE GUDA DAYA TILO..
4⃣6⃣
Na
UMMI A'ISHA
Mika masa tayi ya karba yana cewa kar ki
kara yi musu girki a marerece tace ai basu iya
ba kallonta ya sakeyi yace karya suke sun iya ki
rabu dasu dolensu suyi falon taga yayi gaje gaje
kamar ba agyara ba dan haka tsayawa tayi
tafara gyara falon ahankali yafara binta da kallo
wannan yarinyar gaskiya kyakkyawa ce ta ajin
karshe sai wanda yake kusa da ita ne ma zaifi
tabbatar da hakan ta hadu ta ko ina da haka
yagama cin snacks din yatashi ya fice ya nufi
side dinsu ita kuwa dama duk a takure take
yana fita ta tashi ta shiga kitchen wurinsu
husna. Sai dare tabar side din mummy tare dasu
hasna domin har yanzu basu dawo sashen
mummy ba sanda suka shiga yana falo yana
kallo sannu yaya su hasna suka fada suka shige
kai kuzo nan ya fada jiyowa sukayi suka dawo
junada ya kalla wannan yaran har yanzu anan
suke kwana? Kai ta daga masa tace eh kallonsu
yayi to wlh kun kusa komawa inda kuka fito
dalla ku wuce ku bawa mutane waje da sauri
suka wuce ya kalli junada kawo min ruwan zafi
amma empty kar kisa milk to ta amsa masa ta
shiga cikin kitchen ta hado masa ta kawo masa
rissinawa tayi ta mika masa karba yayi yana
kallon yan yatsunta wanda suke tsananin
burgeshi tana bashi ta wuce dakinta. Washe gari
da wuri ta tashi ta gama abubuwan da za tayi
ta shirya domin ranar zasu fara exam tun 8:30
suka tafi lokacin ko tashi daga bacci baiyi ba
lokacin data shiga dakinsa kwance ta ganshi
daga shi sai gajeren wando ko riga babu
ajikinsa,ya kure A. C baccinsa yake hankali
kwance, kallonsa ta tsaya ta farayi fatarsa sai
sheki take kamar ta mace da gani zatayi laushi
ko ina najikinsa gashi ne ya kwanta luf luf wani
irin kyau taga yayi mata sleeping beauty ta fada
ahankali ta fice daga dakin. Shi kuwa lokacin da
ya tashi ya shirya ya fito sai yaji falon tsit da
alama sammako sukayi zuwa makaranta.
Ummi A'isha🏻
[3/23, 11:54 AM] Ummi A'isha🏻: [3/23, 11:45
AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO
....
4⃣7⃣
Na
UMMI A'ISHA
Falon ya fito yakarasa kan dining yaga flasks
a jere, yafara budewa soyayyen dankali da kwai
yaga sai kamshi yake, ya bude dayan farfesun
kaji ne shima kamshine kawai ke tashi duk
abinda tasan yana bukata ta hada masa nan ya
zauna ya cika tumbinsa sannan ya nufi cikin
dakinta yana shiga yaji kamshin room freshener
dana turaren wuta sun hadu sun doki hancinsa
dakin nata yafara kallo komai tsaf tsaf babu
datti ko daya gefen gadonta yaje ya kwanta
aransa yana tunanin cewa ya kamata ya ajiye
duk wani girman kansa ya rungumi matarsa ya
nuna mata soyayya dan tabbas yar halak ce duk
matsayinta da mukamin mahaifinta amma ta
kaskantar da kanta take yi masa bauta har
kayansa ta ke wankewa ga wulakancin datake
fuskanta daga wurinshi amma duk ta jure wani
irin juyi yayi akan gadon yace nayi alkawari sai
nayiwa junada abinda zata soni, zata kaunace ni
tashi yayi yakoma dakinsa domin duk ba yajin
dadin jikinsa sakamakon rashin ganin junada
dan haka yau bazashi aiki ba. Yana nan kwance
ya saka fari ya saka baki har ya kwashe awanni
bai ankara ba ya jiyo hayaniyarsu acikin dakin
junada, tashi yayi ya nufi dakin nata lokacin
hasna tana daya dakin tana wanka ita kuma
husna tana tsaye tana sanye da wata doguwar
shimi ta bawa kofar shigowa baya tana shirya
lecture note dinta ita kuma junada dogon wando
ne ajikinta da bra tana zaune akan gado tana
facing din kofa ta sunkuyar da kanta tana duba
questions paper din su husna gaba daya
hankalinta yana kan question paper din yana
shiga ya ganta yasalam ya fada sadaf sadaf ya
juya da niyyar ficewa amma sai aka samu akasi
kafarsa ta bugi kofa dago kanta tayi tana
dagowa suka hada ido wata kunya ce ta
lullubeta shi kuwa cewa yayi sorry you are
changing? Ya fice daga dakin hankalinsa a tashe
acikin ransa yana cewa lallai ashe yarinyar nan
lullube take da baiwa iri iri shiyasa take yanga?
Lallai da yaso tafka babban kuskure a
rayuwarsa, ita kuwa junada haka kawai ta kasa
jin zafinsa amma taji wata azababbiyar
kunyarsa ta kamata.
MACE GUDA DAYA TILO...
4⃣8⃣
Na
UMMI A'ISHA
Tun daga lokacin ta daina yarda su hadu,
wasan buya suka shiga tun bai gane ba har
yagano kunyarsa take ji murmushi kawai yayi
yace yaro yaro ne. Ahaka ahaka har suka kusa
gama exam dama shi kawai kyaleta yayi tagama
exam din lokacinne zai fito mata da manufarsa a
fili, da daddare yashigo a babban falo ya iskesu
suna cin abinci suna kallon wani Nigerian film
mai suna i promise kowa rike da filet dinta a
hannu gaba daya hankalinsu ya tattara akan
film din ahankali yazo kusa da junada ya zauna
batare da sunji motsin sa ba magana yayi yace
sannunku sarakan kallo gaba dayansu babu
wadda bata tsorata ba dan sam basuji shigowar
sa ba kallo junada ta fara binsa dashi yayi kyau
sosai rigar jikinsa maroon colour an zana
tsintsaye guda uku ajiki an rubuta Angry Birds
brown din jeans yasa kamshin turaren sa kamar
kullum ya baibaye wurin,husna ce tayi dariya
tace gaskiya yaya ka bamu tsoro wlh junada ya
kalla wadda har yanzu itama shi din take kallo
murmushi yayi yace ga babbar matsoraciya nan
wadda take neman cinye ni da ido dariya suka
sa ita kuwa murmushi tayi ta dauke kanta daga
kallonsa abincin nata ya dauka yace matso muci
nima yunwa nake ji kallonsa tayi tace ni na
koshi kaci sai in karo maka tsareta yayi da ido
tamkar mai yin rada yace wlh baki isa ba sai
munci abincin nan tare kafada ta make ahankali
ahankali yafara matsowa har yazo kusa da ita
sosai ya kamo hannunta daga shi har ita wani
bakon al'amari ne ya ziyarce su wani irin yarr
taji ajikinta, su husna kuwa tsayawa sukayi suna
ganin ikon Allah, ganin bazata ci ba yasashi
kwanto da ita jikinsa ya debo yana shirin bata
tamkar wata jaririya kunya ce ta kamata ganin
su hasna na kallonsu shi kuwa yama manta
dasu na wurin ganin taki ci yasa yajiyo asannan
ne ya gansu korarsu yayi yace kai ku bar nan da
sauri suka mike suka shige daki suna shigewa
ya jiyo gareta yasa tattausan hannunsa ya
kamo hannunta wanda ya dade yana burgeshi
ahankali yafara murza yan yatsunta acikin
hannunsa wani irin taushi da laushi yaji a
hannun nata tuni ya shagala yama manta da
batun abinci.
[3/23, 11:50 AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA
DAYA TILO...
4⃣9⃣
Na
UMMI A'ISHA
Ahankali ta zare hannun nata daga cikin
nasa ta kalleshi tace to kaci abincin kace yunwa
kakeji kallonta shima yayi idanuwan shi sun
canza launi yace ai nace miki tare zamuci tashi
tayi taje cikin kitchen ta zubo abincin ta dawo
wurin shi ta ajiye akan stool din gabansa
kallonta yayi yace to muci kinga cokalin guda
daya ne don haka sai muyi kama kama zama
tayi a kusa dashi abincin ya fara ci ya miko
mata cokalin karba tayi itama tafara diba tana
ci shi kuwa gaba daya hankalinsa yana wajenta
ahaka har suka gama cin abincin mikewa tayi
da nufin zuwa ta dauko musu ruwa da sauri ya
kamo hannunta yace barshi na dauko mana a'a
ka barshi zan dauko no barshi kawai mikewa
yayi yaje fridge ya dauko musu ruwan da kofi ya
dawo wajenta yace zakisha da kanki ko na baki
a baki? A'a zan sha da kaina tsiyayo mata yayi
ya mika mata ta karba tasha sannan ta mika
masa shima yasha, mikewa tayi tace zan shiga
daki binta yayi yace to muje tana gaba yana
biye da ita har cikin dakin a gefen gadonta ya
xauna ita ma zaman tayi domin a takure take
gashi tana son tayi wanka amma bazata iya
tashi tashiga a gabansa ba.
MACE GUDA DAYA TILO...
5⃣0⃣
Na
UMMI A'ISHA
Tashi yayi yace to sai anjima Allah ya jima
damu tafada a hankali fita yayi daga cikin dakin
ya nufi dakinsa ita kuma wanka ta tashi ta
shiga tana fitowa ta ganshi tsaye daga shi sai
gajeren wando da farar best kallonta yafara yi
sosai daga ita sai dan guntun towel, gashin
kanta har kugunta sai faman kamshin mai dadi
takeyi na sabulun da tayi wanka dashi yaya
lamin me kake so? Ta fada cikin rawar murya
kamar wanda yake koyon magana yace ruwan
wanka zaki zo ki hada min to ina zuwa ta bashi
amsa acikin zuciyarta kuwa cewa take aikin
nawa ya karu kenan tunda yanzu har dasu zuba
ruwan wanka, tsaye ya tsaya mata yaki fita
jiyowa tayi tace ina zuwa shiryawa zanyi
kallonta yayi sannan yace to shirya mana ko na
hanaki ne? Ganin bashida niyyar fita yasa ta
tattaro gashin kanta ta tufke tamkar gammo a
kunyace ta dauki dogon hijab ta sa tazo zata
wuce jawota yayi yace tsaya mana madam kisa
kayanki mana a'a sai na dawo zan sa to
shikenan muje wucewa tayi izuwa dakin nasa ta
shiga bathroom ta hada masa ruwan wanka
harda turaren wanka ta zuba masa ta fito
lokacin yana waya sunan Jen taji ya ambata
dan haka ba tayi wata wata ba ta fice daga
dakin cikin sauri zuciyarta sai faman tafarfasa
takeyi wato arnan nan ba zasu kyale mata lamin
ba ko? Allah yasa yarinya tayi gangancin zuwa
mata gida wlh sai ta raunata ta da wannan
tunanin ta shitya cikin rigar baccin ta ja mai
kyan gaske ta jawo hand out dinta ta soma
karantawa domin tana da exam gobe dama guda
2 ne suka rage mata. Washe gari ta tashi ta
hada breakfast ita dasu husna dankali da kwai
ta soya musu shi kuma lamin plantain da kwai
ta soya masa tayi masa farfesun kayan ciki ta
zuba masa ruwan zafi a cikin flask tazo ta jera
akan dining ta nufi dakin su husna taje ta taso
su agurguje suka shirya suka fito amma sai da
junada ta leka dakin lamin inda yake kwance
yanata shakar baccinsa da sauri taja masa
kofar ta fita cikin sauri suka shiga sashen
mummy suka gaidata sannan suka wuce
makaranta.
Ummi A'isha🏻
[3/24, 12:34 PM] Ummi A'isha🏻: [3/24, 10:11
AM] Ummi A'isha🏻: MACE GUDA DAYA TILO..
5⃣1⃣
Na
UMMI A'ISHA
Karfe 9 ya tashi yayi wanka yafito cikin
bakaken suit wanda sukayi masa kyau sosai,
kan dining yaje ya xauna yayi break yana
gamawa ya shiga dakin junada yauma kamar
kullum dakin a tsaftace yake sai kamshi ne yake
tashi fitowa yayi ya nufi side din mummy ya
gaisheta sannan yatafi office. Yau tun 1 suka
fito daga paper da wuri suka dawo gida su
hasna daki suka shige suna ramuwar bacci ita
kuwa junada kitchen ta fada tafara kacaniyar
hada abincin rana inji turawa sukace lunch, faten
doya da danyen kifi tayi tana gamawa tashiga
wanka yauma tana fitowa ta ganshi a tsaye
kamar jiya sannu da zuwa tace dashi yawwa
sannu ya amsa mata ganin kallon da yake mata
yasa tayi saurin sunkuyar da kanta kizo kibani
abinci amma bari nima naje nayi wanka kafin ki
gama shiryawa ya juya yafita, agurguje ta shirya
cikin wani bakin lace mai digon pink ajiki anyi
masa zanen fulawa ajiki dinkin riga fitet da skirt,
turaren urban woman shine turarenta ta feshe
jikinta ta nufi falo tana fitowa shima yana fitowa
yayi wanka ya canza shiga cikin wata riga
purple colour anyi zanen heart kanana an rubuta
cute style a tsakiya da wando brown, gayen nan
akwai iya daukar wanka tafada acikin zuciyarta
kujera yaja ya zauna ta zuba masa abincin ta
koma falon ta zauna tana hango shi yana cin
abincin shi kuwa mamaki yakeyi wai duk lokacin
da yarinyar nan take kusa dashi sai ya tsinci
kansa cikin farin ciki amma da zarar bata nan
sai ya samu kansa cikin tashin hankali tab!
Allah mai yadda yaso.
MACE GUDA DAYA TILO...
5⃣2⃣
Na
UMMI A'ISHA
Ahankali ahankali yake cin abincin har ya
gama, wayoyinsa ya tattara yataso daga dining
area din cike da ladabi tace yaya lamin dama
ina son yin magana dakai, kujerar dake kusa