Showing 6001 words to 9000 words out of 17897 words
Chapter 3 - AMEEN DA AMEENA HAUSA NOVELS BY FOULANI CERDIYA.txt
musu peck, suma sukayi mata ta sh'ige d'aki.
Mama tana alfahari da y'arta saboda kasancewar bata tab'a jahomata magana ba, gash'i tana taimakawa k'annenta wajen karatunsu,
sai dai tace"Masha Allah.
~Maman triplet~😘
[10/24, 7:07 PM] +234 701 117 6189: [8:52AM, 8/19/2016] Foulani Cerdiya😘: *AMEENA DA AMEEN*
©FOULANI CERDIYA
®NWA
54~55
BAYAN WATA D'AYA.
Yanzu in kaga Ameenah gaba d'aya ta sauya, ko hira ake sedai tayi sh'iru saboda tunanine yake addabarta, kai ko a hanya ta taho zata iya bigeka ma bata sani ba.
Agida kuwa su Asleem da Tasleem suyi ta damunta da"Ya sayyada wai meyake damunki?
yanzu baki mana tatsuniya, kindena zama kiyi hira da Mama, meyasa? takance tasu
"bakomai Twins d'in Mama.
Mamar matayi tambayar har tagaji, takaita asibiti a duba ko bata da lafiya ne? amma lafiyarta k'alau dan haka da tagaji sai kawai ta kyaleta.
Acan gidansu Ameen kuwa, kullum Mamy zatayi masa zancen yarinyar nan, seyayi kamar zemata kuka ita kuma tasan had'in dazatayi masa bana sh'arri bane dan ta yadda da tarbiyyar yarinyar da zata bash'in,
Haleema y'ar sa ido, sedai kiji ta lallab'o tace"Mamy wai wacece wannan d'in ne?
kigayamin inji mana.
Haleema tanayin hakan ne dan kar k'awarta ta rasa zab'in ranta, tanaso taji wacece dan tasan hanyar dazata bullowa da abun, but Mamy tak'i gaya mata.
Yau Alkhamis da misalin k'arfe takw'as na dare, Ameena ce zaune ita da Twins d'in Mama, tana k'aramusu karatun Alqur'ani sakamokan an basu hadda a islamiyya.
Yaro ne ya sh'igo da sallama yace"wai ana sallama da Ameenah,
"What??, Me?, Ameena ta fad'a tana nuna kanta da hannunta,
da sauri tace
"kace batanan."
"kace tana zuwa"
Mama fad'aa tana kallonta, kitash'i ki fita, jik'aki zamuyi mush'a koyaya?
sai ayita zuwa gurinki fira amma sai kik'i fita, to yau sai kinfita.
Tash'i tayi taja hijab d'inta Fuuuuu ta fita.
Tana zuwa ta taddash'i tsaye jikin motarsa ash, cikin sh'adda milk, ya kafa hularsa _Zanna bukar_
sai tash'in k'amsh'in turare yake.
Tsayawa tayi k'ik'am bata masa sallama ba.
"Barkanki da fitowa yake gimbiyar mata"
"barkanka" abinda ta iya cemasa kenan ta d'inke bakinta tayi masa sh'iru
"To dafari nidai sunana Haruna ina zaune a garin abuja inda anan nake aikina,
nazo biki nan kano naganki, kuma naji kin burgeni har nayi
sh'aawar mu had'a halak'a ta soyayya fatan zaki karb'a?."
tunani ta tafiyi a gidan biki wajen rawa anan yaganta kuma yace yana sonta? Anya??
katse mata tunanin yayi da cewar"Haba yadai naji kinyi sh’iru ne,? kobanyi miki ba?
"Aa bakomi
hira yadinga yimata sedai ta bish'i da uhm eh aa.
daga k'arsh'e dayaga ba wata hira kawai yayi mata sallama tare da mik'o mata kud'i tak'i karb'a,
se cayayi ba abinda zakiyi min wanda zesa im nakoma gida in dunga tunaninki?
"mezan maka?
Ameenah ta tambaya,
"Haba baby Meenah ko d'an irin hugging da kissing ai nasamu ko,?
ya fad'a yana k'ok'arin kami hannunta, sauri tayi ta janye tace"ya haka Malam??
"mekake tunani?
ni y'ar iskace? ko kuka me? mtswww to kasanja tsar...."ke dalla saurara kina y'ar rawar D'j dan nazo namace inasonki sh'ine zakimin shauting?
"Kaicona!!! ta fad'a da gudu tayi cikin gida.
[5:11PM, 8/19/2016] Foulani Cerdiya😘: Kafin ta k'arasa cikin d'akin tasaita kanta dan kar su Mama sugane wani abu.
Koda ta sh'iga bata musu magana ba ta sh'ige d'akinta tayi kw'anci tana tunanin halin
Wash'egari
Mama tana zaune tana yanka salad taji tsayuwar mota a k'ofar gida.
Sallama tayi tayi ta sh'igo "Lah Mamyn Haleema? sannu da zuwa
Mama ta fad'a da mamakin ganinta dan ta dad'e batazo gidan ba.
Ameenah
Dafara'arta tafito tana "oyoyo Mamynmu
Mama ta dafata suka sh'ige d'aki bayan an gaggaisa Mama take cewa"kin d'auke k'afarki daga gidanmu ko Daughter?
"aa wallahi Mama ba haka bane"
"To aini gani nabiyoki "
Ameenah ta sunkuyar da kanta alamar kunya.
ta tash'i ta aiki Asleem ta sayo mata lemo me sanyi ya kahomata, taji yaron ya burgeta sosai.
Bayan tash'ane suka fara hira da Mama ganin haka yasa Ameena ta fita tabar musu d'akin domin bedace tasasu a gaba tana kallo ba.
Bayan tafita ne Mamy ta kalli Mama tace
"dama nazo miki da wata magana ne, kuma inafatan zakiyimin alfarma,
Gaban Mama ya fad'i dajin wannan abu amma sai tace "menene Mamyn Haleema?
Mama tafara da cewa dama............
Ayya wayata ba charge 😫sorry Fans
~Maman triplet~👨👨👧😘
[10/24, 7:07 PM] +234 701 117 6189: [8:05AM, 8/21/2016] Foulani Cerdiya😘: *AMEENA DA AMEEN*
©FOULANI CERDIYA
®NWA
56~57
"Dan Allah Maman Ameenah kimin alfarma, "
"wace abune wannan Mamyn Haleema? kifad'amin mana, kinfi k'arfin komi a gurina".
"Dama so nake kibani y'arki, so nake ki yadda in had'a *AMEENA DA AMEEN* aure,
ammafa sai in kin amince kin yadda tunda kece mahaifiyarta."
Gumine yake ketowa Maman, dan maganar tazo mata a bazata, coz batayi expecting hakan ba but why?,
tayaya zata had'a y'arta da yaron da taji Haleeman da Ameenan suna cewa yafiye fad'a da miskilanci,
Mamy ce ta katseta daga tunanin datake tace"Maman Ameena yanaji kinyi sh'iru ne?
ko kin bayar da ita ne?
"Sh'in Ameen yana son Ameenah?
sh'i yace miki ki nemo masa aurenta?
inke kika zab'a masa ya amince?"Mama ta tambayi duka dantaji amsar da Mamyn zata bata.
To itama Mamyn ta tafi tunanin amsar bawa Mama,
"ki kwantar da hankalinki na isa da Ameen , bash'i yace in nemo masa ba, ni na duba dacewar hakan, ina ganin Aurensu zai kaho sauyi a rayuwarsa, ki yadda in had'auren *Ameena da Ameen* pls Maman Ameenah,
Tayaya? babbar mace kamar wannan tazo ta nemi abu agunta ta hanata? matar da take taimakonsu a rayuwa, sai dai abinda ta nema d'inne kamar da wuyar bayarwa, Y'afa?....
"Maman Ameenah in kinga bazaki iyaba sh'ikenan
Mamy ta fad'a cikin fuskar tausayi,
"yaron nan matar dana bash'i a farko bata masa adalci ba, bata juri duk abinda yake mata ba, bata rufa masa asiri akomai ba,
Hankali da nutsuwar Ameenah da tarbiyyarta su suka jani suka saminsh'aawar had'a *Ameena da Ameen* itace dai-dai sh'i". Amma idan kinga bazaki bayar da itaba s'hikenan.
Maganar ta sh'igi Mama sosai kuma taji tausayinsa tunda beyi dacen mata ba.
"sh'ikenan Mamyn Haleema Allah yasa hakane yafi alkhairi.
[8:40AM, 8/21/2016] Foulani Cerdiya😘: Da sauri Mamy tajuyo cikin farin ciki tace"da gaske? da gaske kin yadda Maman Ameenah?
"eh na yadda mu had'asu, "
"Insha Allah zamuga alkhairi tunda da niyyar hakan mukayi Allah sa albarka acikin auren *Ameena da Ameen*"
"Ameen ya rabb" suka fad'a a tare.
Kowanne da tsantsar farin ciki a zuciyarsa.
Bayan Mamy tafuto zata tafi ne, take cewa Ameenah" yaush'e zaki zo? kink'i gidanmu yanzu,
"aa Mamy ba haka bane zanzo soon"
"Allah yasa.
Daganan sukayi sallama da cewar sai Abbansu Ameen d'in yadawo zasu tsaida magana dan baya gari.
[10/24, 7:07 PM] +234 701 117 6189: [13:56, 8/23/2016] Foulani Cerdiya😘: *AMEENA DA AMEEN*
©FOULANI CERDIYA
®NWA
58~59
Bayan fitar Mamy ne Mama tayi kiran Ameenah, take cemata"Ameenah Mamyn Haleema tazomin dawata Magana.Daganan ta kw'ash'e duk yadda sukayi da Mamyn amma bata gayamata cewar da Ameen zaa had'asu ba.
Tunani sosai ta sh'igayi saboda zancen yazo mata a bazata, ita dawani d'an nata Mamy zata had'asu?,
ya zatayi,
ita datake son Ameen yanzu idan bash'i bane fa? idan k'aninsa ne shi'kenan an mata yankan k'auna da abin son zuciyarta, sai dai data tuna hirar Mamyn da Ameen, sai take tunanin to kodai shi'ne? Allah yasa haka to.
D'aki tash'iga jiki asalub'e, ta haye gadonta tafara tunanin yadda za'ai a had'ata aure dawani wanda baya sonta cab jink'iri mak'ari.
"Yah Ameen "Yah Ameen ka tash'i Daddy yadawo yana ta kiranka kazonan sai sh'ar bar bacci kake".
Haleema ketash'insa, amma saboda jiya ya d'auko Abbansu daga airport kuma cikin dare ne dan Haleeman ma tayi bacci a lokacin, shi'yasa batasan ya dawo ba sai da safe data ganshi' sh'i ne har take tuna masa yataa'shi.
Bargonsa ta janye, ta jaho d'an yatsan k'afarsa "ka tash'i.Tafa'da da k'arfi, tafice da gudu, dan dole ya tash'i ya sh'iga toilet yayi brush,wanka da alwala saboda besamu sallah asuba ba.
Bayan yagama yayi addua sosai sannan ya tash'i, yayi cikin gida.
kodash'igarsa cikin gidan a dining ya taddasu sunfarayin breakfast, sallama yayi sannan ya nemi guri yazauna.
Gaida iyayen nasa yayi,suka amsa ckin sakin fuska, daga nan ya jaho flat d'in abinci yayi serving kansh'i.
Bayan sungama cine Abbansu yayi gy'aran murya, sannan yafara magana kamar haka
"My son! kaga dai be kamata mubarka haka ba, duk ka tsufa sh'ekara tafiya take, kwara ka amfani kurciyarka,
kai yanzu ba yaro bane, kana da y'an uwa k'anne kuma suna koyi da abunda kakeyi ne, inso samune inaso kayi aure, kuma nasa Mahaifiyarka tayi maka zab'i na hak'ik'a, ba irin wancen ba."Inafatan zaka amince da duk wacce aka kaho maka amatsayin mata".
Shi'ru falon yayi, kasancewar kowa yayi tsit yana saurar Abban.
Duk kansu inka kalli fuskokinsu da farinciki, banda Yah Ameen wanda yake ta faman had'a uban gumi dukko da sanyin Ac dake ratsasu. Tunani yake sh'idai yanason matar daxai aura ta kasance dawasu qualities wanda yake burin samun mace dasu, yanzu idan ba haka take ba yaya zaiyi, wallahi aure ze k'ara.Haka yaketa tunani kafin Abban ya katseshi da cewa"nasan kana da biyayya da hak'uri, kayi hak'uri ka tallafi kowacece insha Allah zakaga Alkhairi."
"toh Abba insha Allah zanmaka biyayya domin farantawa MAHAIFINA zan auri koma wacece"
"Allah yayi maka albarka"Mamy ta fad'a tana faraa.
"Allah yabaku zaman lafiya" Abba ya fad'a. A'inda ba abar Haleema y'ar sa eyes ba sai da tace"Allah yasa ku haifo y'an uku masu kama dani da Abba da Mamy ko?.
Duka aka tuntsire dariya amma banda Yah ameen wanda ya kad'a bujensa yafita.
Abba ne ya kalli Mamy yace"
"Aise akahomin Y'artawa in ganta ko? duk da dai naaganta a photo inason naganta; dan intabbatar da banyiwa d'ana zab'in banza ba,
duk da nasan Haleema bazatayi k'awar da bata kirki ba."
"Abba k'awata kuma?
Haleema ce tayi tambayar tara da k'arawa eyes d'inta girma.
[14:13, 8/23/2016] Foulani Cerdiya😘: Mamy ce ta tare ta da fad'in "eh k'awarki Ameenah saura ki bari yaji yasan kowace ranki zai ba'....."Wayyo Allah sweet kill me woooo,"Mamy
Haleema tayi gunta da murna ta rungume ta ta k'ara kallon Mamyn tace"Mamy are you serious?
kafin ma Mamy ta bata amsa tayi gun Abba sh'ima ta rik'e masa hannu tace"Abbana da gaske *Ameen da Ameena* kuka had'a?
sh'ima be bata amsa ba sai murmush'i kawai dayayi ganin y'ar autar Mata na farinciki ,ta mik'e tana tsallen murna" Dole inyi murna da celebration, kunsan daga jin sunan ma Abba couples d'im sun had'u? aiko? kuma sun dace da juna? ko? *Ameenah da Ameen* woww perfect match wayy.... Bata k'arasa Mamy wacce Haleema ta cika mata kunne da ihu tace
"Ke dallla kincika mana kunne dawannan sh'ash'ancin naki, sh'iyasa tunda wuri nak'i gayamata dan nasan sh'irme zatayi mana.
"Aaa Mamyn yara banson fad'a yazakice bazatayi murna ba? barta tayi, yayanta take tayawa murna.
"Autar mata(sunan da Abba yafi kiranta dashi) tash'i kije ki sh'irya kije gidansu y'artawa ki tahomin da ita".
"Yee ok Abbana.Da gudu tafita daga parlon tayi d'akinta, tana mejin dad'in wannan abu burin k'awarta Aminiyarta, Sister ta zai cika.
By; ~Maman triplet~😘
[10/24, 7:07 PM] +234 701 117 6189: *AMEENA DA AMEEN*
BY;FOULANI CERDIYA
®NWA
62~64
Ameen ne ya juyo yana hararar Haleema yace"
"Mamy ga driver nan a zaune, aikin meyake?".
Haleema ce tayi saurin cafe zancen ta k'irkiro k'arya tace.
"Uhmm, ai sh'i driver aikensa za'ayi," Mamy koma kin aikesh'insa?
"Aa dai yanzu nake sh'irin kiransa,".
Ameen ne ya kalli inda Haleema ke zaune yace
"Hmmmmmm!! zan kama yarinya ne duk randa Abba ya tafi,
yasa kai ya fice,"
Sai kina hak'uri fa y'ata, d'annawa akwai kirki"
"uhm" murmush'i kawai tayi, itadai so take sud'an bar parloun sukoma d'akin Haleema dan takasa sakewa, duk kuwa da yanda su duk suka sake da ita, musamman Abba dayake jin kamar 'yar daya haiface.
Yarinyar ta burges'hi saboda nutsuwarta da kunyarta.
Kiran sallar maghriba aka fara, sh'ine dalilin dayasa suka tash'i Abba yayi masallaci, Ameenah da Haleema ma sukayi d'akin Haleeman,
suka d'auro alwala suka fito sukayi sallah kowacce ta roki' ubangiji buk'atunta.
Tv dake parloun suka kunna suka fara kallon Mbc bollywood, suna wani film ne wanda Ameenah ke mugun so, wato *vivah*
murmush'i ne d'auke a fuskarta, dan intana kallon, sai taga Ameen yayi yanayi da jarumin film d'in _Shaheed kapoor_
sai dai ya nuna masa hasken fata, amma gani take ma yafi _Shaheed kapoor_ d'in ky'au.
Masoyan sun burgeta, dan tana kallonne ma, Haleema taga tension d'in Ameena baya kanta dan haka ta kalleta da tsokana tace"Ah su juliet tunanin romeo akene?
"hmmmmm" Ameenah ta harareta batace mata uffan ba.
Mamy ce ta kira Haleema tace ta kira Yah ameen, ai tana zuwa d'akinsa ta sh'iga a bud'e amma bayanan,
ta sh'iga bedroom, bata gansh'iba,. Bata kuma ji motsin ruwa ba bale ta lek'a toilet d'insa.
Dan haka kawai ta fita.
Ashe sh'ikuma yana ciki, Haleemah na fita, ya d'auko Key d'in motarsa zai fita.
Haleemah na sh'iga ta sh'aidawa Mamy bayanan,
ganin dare na k'arayi tace"jeki kira driver yazo ya maidata,
"Daughter bari nazo ko? Mamy ta fad'a tana d'an dafe da kafad'ar Ameenah,
stair d'inta ta hau,
Haleemah ta dawo tace ma Ameenah tazo ga driver nan zai kaita.
Mamy ce ta sauko dawata bag me ky'au,
daga gani kayan kw'alliya ne a ciki dasu turare dan naji k'amsh'i sosai.
Haleema ce ta ruk'omata ledar da Abba ya bata ta tsaraba, da bag d'in da Mamy ta bata.
Tayiwa Mamy godiya, tayi mata sallama
inda Mamy tace"kicewa Mamanki sai nazo ina gai'sheta"
"to"
sannan suka fito.
Karaf idon Ameenah cikin na Ameen ya fito sai uban k'amshi yake, ya sauya kaya zuwa dark blue sh'adda taji aiki,.
K'amsh'i kawai yake bugawa,
Ameenah ce ta tab'o Haleema "ke ina zash'i?
da daddaren nan,! yawani ci wanka?,
"oho masa, koma ina zash'i ki barni dash'i, kar kice masa uffan ki tsaya kiyi kallo.
"Toh" kawai tace da ita.
"Yah ameen so kake Mamy tai fush'i dakai ne?
cataifa ka kai Friendy gida sh'ine zaka fita,
Hararta yayi tukun kafin yace"Baga driver can ba nifa unguwa zani,
"Driver Mmy aikensa zatayi gidansu Aunty khadeeja,(Tsohuwar matarsa idan baku manta ba).
Sai dai in drivern yakaita gida kai kuma kaje aiken da drivern, gidansu Aunty khadej. ................"Shut up,
muje, abinda kawai ya isa cewa kenan, dan bayason ya tuna da khadeeja taci amanarsa sai dai Allah ya isa .
Hannu ta d'aga Jinjina Ameenah tayi mata, kin iya suburbud'o k'arya. Sukayi dariya
tabud'e mata mazaunin me zaman banza, ta zauna,
kallo kawai yabisu dash'i, danya fuskanci yaran halinsu yafi k'arfinsh'i.
S'higa ya kunna mota, zai juya yafita, Haleema tace"Au Yah Ameen, Mamy tace ka sh'igar mata da wannan", ta mik'o masa Ledar nan da bag,
"wai daganan sai ku gaisa da Mamanta.
Karb'a kawai yayi yako d'orasu asaman cinyar Ameenah,
yaja motar yabar gida,.
Har ya fita titi, besan inane gidansu ba, besan wacce unguwa take ba,
yanason ya tambayeta amma baison yimata magana,.
Dan haka kawai ya zaro phone nash'i ya kira Haleema, yana tambayarta inda zai kaita,.
"Ah yah Ameen ka tambayeta mana".
Abinda tace kenan ta katse wayar.
"Mtsww"
Parking yayi kawai yaci gaba da danna wayarsa, tanason yimasa magana amma tanajin tsoro, gash'i har anfara kiran ish'ai.
~Maman triplet~😘
[10/24, 7:07 PM] +234 701 117 6189: [06:17, 8/28/2016] Foulani Cerdiya😘: *AMEENA DA AMEEN*
BY; FOULANI CERDIYA
®NWA
65~66
Zaman sh'irunne ya ish'eta, tanason tayi magana amma tana gudun kar yamata wulak'anci yayi banza, itakuma babu abinda ta tsana sama da wulakanci, sh'iyasa ma ta gudurce aranta bazatayi masa magana ba har sai lokacin da yaga dama yayi mata maganar.
Wak'arsa kawai yakeji ko a jikinsa, amma fa so yake yayi yakaita ya dawo saboda akwai abinda zaijeyi yanzun,
so yake tagaya masa inda zai kaita bawai alallai sai yabud'i baki yayi mata magana ba.
Lokaci d'aya yaja tsaki"Mtswwww"
yayi sh'iru bece uffan ba, ita kuwa Ameenah sai ta juya fuskarta gefe tana ta zumb'urar baki ganin har nine 9 ta kusa, ita batason Mama tayi mata fad'a ne sh'iyasa.
Ameen ne ya k'ara jan tsaki ana biyu, tare da cewar"Ke dallah tash'i ki fitarmin daga mota tunda bakisan inda zaa kaiki ba" Kinwani yi sh'iru sai kace mutuniyar kirki, nanko a shaid'ananci inajin sh'aid'anma ya fiki iyawa".
Daurewa tayi, tayi magana kamar zata fash'e da kuka tace cikin inda- inda.
"Ni........ai baka.....tam..bayen inda...zaka kaini ba, kawai jinayi kayi parking basai in tunanin wani abun zakayi gunba".
"to tash'i ki fita kinemi keke napep _D'an sahu_ kihau inyaso sai sh'ima kimasa sh'irun karki fad'a masa inda zai kaiki kigani in be je yasayar da kanki ba".
"G/k'aya ne"
"G/k'ayan ma nan da nan kusa kusa mtsww iyayin banza kawai". ya fad'a yana wani harare - harare.
Motar ya figa, dasuka sh'igo tadinga nuna masa hanya har suka.
bud'e motar tayi ta fita, tabar masa kayan daya d'ora mata a cinya akan kujerar data tash'i,
bayadda zaiyi ya d'auko ledar da bag d'in aransa kawai dan dai Mamy ce tace ayi amma wallahi da bata isa ya kahota ba, ballantana har yawani sh'iga gidansu"mtsww" ya k'ara jan tsaki a karo na uku.
Bayan ta fita ta sh'iga gida tasanarwa da Mama zaa zo gaish'eta tace to.
"Bismillah ka sh'igo mana"
lums'he idonsa yay sannan ya d'ora k'afarsa cikin gidan,
wayarsa tafara ruri, ya d'auko ya duba ganin My only Mum yasa sh'i saurin d'agawa"Hello Assalamu alaikum"
Mamy"
daga ciki wayar kuwa Mamy ce tace"ka kaita gidan?,
"Aaa yanzu zamu sh'iga dai."
Tace"ok ka d'an bawa Mamanta wanii abun mana,"toh Mamy"
yace tana kash'e wayar.
Domin a rayuwarsa yana girmama duk wani abu dazata sash'i, bata tab'a sash'i abu yak'iyi koda ace kuwa bayaso, yasan bazata sash'i abinda ba dai-dai ba.
Ciki suka sh'iga a parlour ya tadda inda Mama take, kai a k'asa yagaish'eta kamar kuwa yasan surikarsa ce.
Bayan sun gaisa yayi mata sallama tare da ajiye mata y'an d'ari -d'ari bandir uku,
da ky'ar Mama ta karb'a, tayi masa godiya sosai sannan ya fita.
Dayafito a ransa yake cewa"A haka kamar masu tarbiyya hmmm amma y'arsu agun rawa kamar jiki ya karye. Yawani yatsina fuska tare da sh'iga motarsa.
[08:37, 8/28/2016] Foulani Cerdiya😘: Har zaija motar kuma sai yaji kamar tsayuuwar mutum a gefensa dan haka ya fito ya duba, turus yayi ganin ta tafito d'auke da jug na ruwa.
kallonta yayi da mamaki yace"yadai??
kw'arjini yayi mata sh'iyasa batason ganin tayi masa kallo cikin ido.
"Aa dama Mama tace bakash'a ruwa ba zaka tafi sh'ine na biyoka dash'i.
"Ok nagode ya fad'a yana ciro jarkar ruwa daga cikin motarsa, "ina dash'i in zansh'a basai kin kahomin ba ? right?,
ya fad'ayana wani d'age gira dan haka sai anjima"
yaja motarsa yabar gurin,
wani malolon bak'in ciki ne ya cikata ganin yamai da'ita like statue, tafi minti uku agurin kafin daga baya taja matattun k'afafunta wanda da kyar suka iya d'aukarta tayi cikin gida, amma kafin tash'iga tasamu tad'an zubar