Showing 9001 words to 12000 words out of 17897 words

Chapter 4 - AMEEN DA AMEENA HAUSA NOVELS BY FOULANI CERDIYA.txt

da ruwan, dan kar Mama tasan besh'aba domin bazata ji dad'i ba.

BAYAN SATI BIYU.

Lokacin da zaa tsaida magana yayi, gash'i suna so acikin dangin babanta wani yazo domin ayi maganar dash'i, kowanne akaje gidansa sai ya nuna ai kawai su hak'ura, wani in sunje masa da maganar yakance a week d'in zebar k'asar haka dai har sukaje gidan wani kawun baban Ameenah, to sh'i dayake bawani me kud'ine sosai ba, sai ya yadda, amma da wajewar bazai yimusu kayan d'aki ba.
Sukuma sun yadda saboda dai ayi abu cikin mutunci yafi.

BAYAN WATA D'AYA.

Antsaida bikin *Ameena da Ameen* nanda wata uku masu zuwa.

Awata ranar alhamis da yamma Mamy tazo gida itada Haleema, aka dunga sh'igo musu da buhuhhunan sh'inkafa da macaroni da taliya su maggi gish'iri, doya dadai sauran tarkace wanda Abba ne yasa akaho musu, anannema Mamy take sanar dasu karsu bawa kansu wahala akan kayan d'aki d'annesu yace subarsh'i, sh'i zai musu komi,
Godiya sosai sukayi, saboda sunji dad'i domin suna cikin zullumin kayan d'akin dama.

Kai kuyi hak'uri nagaji da typing wlh


Masoyana ina sonku aduk inda kuke kuma Foulani na amsar gausuwarku, Samee tawa Sameen Munay ina jin sak'on gaisuwarki sosai kuma ina amsawa, Allah yabar k'auna.


~Maman triplet~😘
[10/24, 7:08 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [19:06, 8/30/2016] "Yar Fara😘: *AMEENA DA AMEEN*

©Foulani Cerdiya

®NWA

67~68

BAYAN WATA BIYU.

Lokacin biki yagaba to, ankaho lefe nagani na fad'a, duk wanda yazo yaganin kayan saiya yaba domin kyawunsu kuma kana gani kasan Naira tash'a kuka.

Dan da Mamy da Haleema ne takanas sukaje dubai suka had'o mata kayan lefen sannan da furnitures dazaasa a d'akin.

Me gyaran jiki takanas Mama ta d'auko mata daga sakkoto, tazo tana mata gyara, ko giftawa zatayi tawaje sai kinji k'amsh'i, haka ko zama tayi na d'an lokaci a wajen in ta tash'i, sai ta bar maka tsarabar k'amsh'i.

A wata ranar alkhamis ana ya saura sati d'aya bikin Mamy ta sauko daga stairs, tayi d'akin Haleema dash'igarta tace"Haleema ko zakije gidansu Ameenah ki kai mata wannan, turarene me ky'au wanda na sayo mata a dubai.

"Aa Mamy kingafa Yah ameen betab'a zuwa gidan nasu ba tun bayan zuwan dayaje kaita, kawai yanzu kice yaje yakai mata,
"ok bari insa a kirash'i.

"Mamy gani"
Yah ameen ya fad'a yana tsugunnawa.
"dama canai kaje gidansu Ameenah kakai mata wannan".
Mamy ta fad'a tana mik'amasa ledar.

Wani fad'uwar gaba yaji, yarasa meyasa indai zaa ambaci sunan Ameenah sai yaji gabansa ya fad'i.....

"Ungo mana son"
"ok" ya fad'a yana karb'a.

Part d'insa yanufa yaje ya ajiye jakar a kan bed d'insh'i yash'iga d'aki, yayi wanka ya fito ya zauna a parlour yakunna Tv yana kallon tash'ar larabawa.
Wayarsh'i ce tafara ringing yana dubawa yaga k'aninsa Habeeb ne me biyemasa wanda yake karatu a egypt, d'agawa yayi ya kara a kunnensa
"Hello"
"Hello ang"...
Bek'arasa fad'ar abinda zaice ba ya katsesh'i
"Dallah karka cikan kunne malam" Ameen ya fad'a da y'ar tsawa.
"Kai Yah ameen wallahi kasauya hali, nifa inkayimin nayi hak'uri ita kuma fa?,"
" itawa?" Ameen ya tambayesh'i.
"Amarya mana," Habeeb ya bash'i amsa.
Nakusa dawowa fa Yah, i think on friday zandawo saboda I can't wait to see........Bye bye Yah .
Habeeb ya katse wayar.
Ai sai Yah ameen ya sh'iga tunanin maganar k'aninnasa Habeeb, " Yah mu in kayi mana mun hak'ura.....itafa wa?.....Amarya....
can't wai to see.........What??
"Mmtswww ya doka tsaki tare da jaho d'an fruit d'in gabansa yasomaci yana ta tunanin abubuwa da yawa.

Sai da dare yayi bayan anyi sallar maghriba sannan yafita yayo wanka ya sh'irya cikin wata sh'adda dakakkiya tayi masa ky'au, am mata d'inkin boda.
[19:07, 8/30/2016] "Yar Fara😘: Hula ya kafa abunsa, ya fesh'e jikinsa da turare me d'an karan k'amsh'i sannan ya fito.

Direct parking space ya nufa yad'auki motarsa har ya kunna ta ya tuna aiken da Mamy tayi masa "Mtsww yaja tsaki, sannan ya kash'e motar ya koma ya d'auko ledar, aransa yana mitar kamar sh'i wai zaa aikesh'i gurin k'anwarsa? yanzu inda zaice bazai jeba Mamy tayi fush'i, itakuma y'ar sa ido Haleema ta zuga"Mtsww ya k'ara jan tsakin, adai dainan ya hau motarsh'i yayi gidansu Ameenah.

Kodayaje layin bakowa kuma babu yaron da zai aika, kawai sai yayi zamansa cikin motar, giftawar yaro yagani kamar ya huce, da sauri ya fito yana magana "Hi boy"
"Hello" yaron ya amsa masa tare da mik'o masa hannu suyi musabiha, mamaki ne ya cika Ameen yaro k'arami kamar wannan yasan yayi musabuha da d'an uwansa musulmi lallai.
"Yadai Yaya naji kayi sh'iru?" D'an yaron ya tambayesh'i cikin siririyar muryarsa.
Murmush'i Ameen yayi najin dad'in ganin yaro k'arami me tarbiyya haka yakeson sh'ima ace yana da y'ay'a masu tarbiyya da hankali sh'iyasa yakeson yasamu y'ar mutunci da tarbiyya domin rayuwar y'ayansu ta inganta.
"Dama aikenka zanyi nan gidan," Ameen ya fad'a yana nuna masa gidan.
Dariya yaron yayi sannan yace"Ok gidanmu ne ai menene?, da mamaki Ameen yace
"Gidanku?"
"Lah eh mana"
yaron ya bash'i amsa. Hmmm
"Karb'i wannan ka kaima yayarka kace Mamy tace a kaho mata"

Ameen ya fad'a yana mik'o masa ledar .

Karb'a yayi sannan yace"Sunana Asleem"
kaifa?,
"Ameenullah" Ameen ya bash'i amsa fuska asake.
Sh'iga gidan Asleem yayi yabata tare da gayamata yadda sukayi, tash'i tayi da sauri tayo waje dai dai zai sh'iga mota ta k'araso.
Magana tafara cikin sark'ewar murya tace"Ka....cema..Mammyn. Nagode"
Kallonta kawai yake yadda tayi wani haske gash'i jikinta sai wani sh'ek'in kyau yake, ga wani sihirtaccen k'amsh'i daya bugi hancinsa, k'amsh'in me sanyi sanyi, me dad'i, yakasa tantance wannan wami irin k'amsh'ine.
Basarwa yayi yakalleta yawani yatsina hanci yace" Nid'an aikenki ne?,. "dan ita ta aiken kema cemiki akai kin isa ki aiken?............


Kuyi hak'urin rash'in typing wlh mun fara hidimar bikin sister ta.Shiyasa zaku dinga jina sh'iru.


~Maman triplet~😘
[10/24, 7:08 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [08:34, 9/1/2016] Foulani Cerdiya😘: *AMEENA DA AMEEN*
_BY_
FOULANI CERDIYA

®NWA

69~70

Ameen yacigaba da magana da cewar"Koma wane ya gayyatoki nan gurin,? oho.
Ya kad'a kansa ya sh'ige motarsa yabarta kamar statue.

Itadai tana ganin ikon Allah, yanzu ace a haka za'ayi rayuwa?
Mijin tanefa idan Allah yanufa, tunda baa d'aura auren ba.
Amma yake mata haka. Gash'ita kuma kasa cemasa uffan take, saboda sh'e like the way dayake accting, yana matuk'ar burgeta sosai sh'iyasa sai dai tasaki baki, tana kallonsa.
Murmush'i kawai tayi a lokacin dayaja motarsa yayi gaba.
Gida ta sh'iga, taga turarene guda uku aciki kamfaninsu d'aya sai dai different na k'amshi ammafa turaren nan yahad'u iya had'uwa.

"Kai Friendy nace miki babu komai wallahi ai i think Mamy tayiwa Mama bayani right,?, so kinga kar ki damu, wallahi its nothing, ai d'an lokacine pls kar kiyiwa Mamy maganar nan remain 5 days a auren nan fa. Ni inaganin better idan anyi auren amasa bayani tunda Iyayenmu sun san Good and kuma sun san Bad."

Ameenah ce duk take wannan maganar ita da Haleema, akan wai Haleema tace kar Mama ta fuskanci wani abu tunda Yah ameen baya zuwa, gash'i koda bikin ya k'arato sai dai in da aike Mamy ta aika Haleema takai mata.
Wai zatayiwa Mamy maganar kawai ya sani ya dunga zuwa fira. Amma ita Ameenah tace kar tasake tai maganar.

Ahaka suka bar zancen suka sh'iga yin abinda zai fish'sh'esu.

Biki ya k'ara k'aratowa. Komai anayinsa cikin mutunci da dattako, Event uku aka had'a d'aya namata zalla, d'aya ta iyaye ce, 'daya kuma ta ango da abokan ango d amarya da Family su.

Randa aka kaho mata invitation Card tayi mugun mamaki ita yanzu ranar dinner zataga yadda zaayi, Ameen zaizo kuwa? Tayaya tunda besan amaryansa bace.?

Anyi kamu inda aka kira Wata malama wato Aunty YBK tazo tayi lecture akan zamantakewar Aure, lecture d'in ta fad'akar sosai, matan aure wad'anda basa bin mazajensu jiki yayi sanyi. Aunty Ybk ta zuba bayani, sai dai muce Mamala Allah saka da alkhairi.
Anyi party inda k'awayen Ameena sukazo sosa tayi mmaki, ash'e duk Haleema tasanar musu kuma sunzo.

A yaune zaayi dinner da daddare, inda Aka sh'irya amarya cikin wani d'an ubansun kaya, fuskarnan tash'a gyara ga wani uban k'amsh'i datake zubawa, jikin nan ya d'au jan lalle da baki, gash'i tawani dad'a cika k'irjinta ya k'ara cikowa Mash'a Allah.


"Mamy hidimar me ake a gidan nan ne?
Ameen wanda yake zaune kusa da ita yana tambayarta.


®NWA
[08:35, 9/1/2016] Foulani Cerdiya😘: "Biki muke"Kawai ta bash'i amsa.
"Bikinwa"? ya k'ara tambaya.
"Ta d'ana mana aa Ameen kar kayi disturbing d'ina fa okay,"
Mamy tabash'i amsa cikin zafi zafi, sh'iru yayi yana nazari to wane d'anta kodai Habeeb ne tunda dama yaji yace masa zai dawo? but be k'are karatunsa ba how,? kaf maganar da sukayi da Habeeb ta k'ara fad'o masa arai, to s'hifa be gane komai ba, actually dayagaji sai yabar tunanin. Ya d'ago ya kalli Mamy yayi fuskar tausayi yace" Yanzu Mamy a gidanan nine babba amma bazaki iya gayan komai ba.
Kuma koma bikin wakike ai yakamata ace kin fad'amin mana,
Yak'aresa yin maganar kamar wani maraya.
"Ameen nasan halinka ne, sh'iyasa kaga ban fad'amaka ba, aiko lefe kamata yayi ace kai nabawa but dakaina naje saboda sanin halinka."
"Haleena Mamy?"
ya tambayeta da mamaki.
[08:36, 9/1/2016] Foulani Cerdiya😘: "Eh to tambayar ta isa haka dan kai ba d'an jarida bane ehhe".

Misalin bakwai dai-dai Haleema ta fito taci kwalliya tayi kyau cikin ashoben biki, d'akin Yah ameen ta nufa a bud'e yake tayi sallama ta sh'iga.
"Yah Mamy tace tana son ganinka yanzu yanzun nan".
"Ok" ya fad'a yana kash'e tv.

"Mamy gani".
"Yawwa Darling son kasan meye?"
girgiza mata kai yayi alamar aa.
"Dama yau ne Dinner d'in d'ana so kuma bazai samu damar zuwa ba saboda yayi tafiya, to shi ne nakeson cin arzik'in kaje dinner a matsayin kaine angon, kaga bedace ace anbar amarya ba ango ba ko?".
Sh'iru yayi yana tunanin wannan rainin hankalin da akeson yi masa, yazaai amarya bata saba kawai yawani je dinner yayi replacing ango?, "cab I can't wallahi" ya fad'a a zuciyarsa.
Mamy ta kallesh'i tare da cewar"kai nake saurare Darling son".
Numfash'i yayi kafin yake cewa" I'm sorry to say gaskiya Mamy bazan iya.....zu.......waba.


~Maman triplet~😘
[10/24, 7:08 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [08:27, 9/6/2016] Foulani Cerdiya😘: *AMEENA DA AMEEN*
_BY_
FOULANI CERDIYA
®NWA

71~72

"Son yanzu amatsayina na Mahaifiyarka insaka abu kuma kak'i yimin?
"Ni Mamy bawai nak'i yimiki bane, wallahi Mamy ni bazan iya zuwaba kawai nawani yi replacing ango,? da sh'i angon yasan da Dinner d'in amma yak'i dawowa koma inayaje oho masa.

Mamy ce ta k'ara magana da cewar" d'an uwanka nefa? yanzu bazaka iya sh'aremasa hawaye ba?
"wane d'an uwan nawa to?
Mamy tanason yaje dinner dan haka data tuna Habeeb zai dawo kawai sai catayi masa"Amaryar k'aninka Habeeb cefa?.
da sauri Ameen ya juyo yana zare ido yace"yanzu ni.........Ni....Zaku aurar da k'anina ban sani ba....?Amaryar k'anina kuma zanje in replacing haba Mamy ai ta rainanima wallahi, kuma ma ai bansan da bikinba dan Haka Allah sanya alkairi amma bazani ba.
Aransa kuwa tunanin rash'in kunyar Habeeb yake gani? watakan dan zaayi masa aure sh'ine ya kirash'i yana masa wannan fitsarar lallaima.
Mamy ce ta katseshi dan ta fuskanci idan tayi masa sh'iru wallahi tunda yace bazash'inba bazash'i ba dan tasan halin d'an nata
"Darling Son umarni nake baka kayi maza-Maza ka tash'i kaje d'akinka ka sh'irya zansa akaho maka kayan da zakasa." Tana gad'in haka ta wuce stairs tayi d'akinta ta barsh'i anan.

Babu yadda yaso dolensa ya tash'i jiki asabule yaje yayi wanka yafito, akan kujerar parloun sa yaga an ajiye masa sabbin kaya masu mugun ky'au.
Ya da'auka yayi d'aki dasu, mai kawai ya sh'afa ya gyara sumar kansa tayi luf-Luf, ya kafa hularsa zuciyarsa nata k'una.

Haka yaje gaban mudubi ya kalli kansa "Woww nayi ky'au kamar nine angon(Hmmm nidai Foulani ina ganin ikon God)".

Fitowa yayi yash'iga ciki yace mata ya fito, wata sabuwar motace fil aka fito da'ita,
Driver ne ya bud'emasa motar, Mamy danjin dad'i har parking space d'in tabiyosh'i tana fesa masa wani irin turare me sh'egen k'amsh'i.

Hannu take d'aga masa alamar Bye bye, but gogan naka sai yayi gefe da kansa a dole fush'i yake da takuramasan daakai.

Driver gidansu amarya ya nufa, sh'iko Ameen bece masa k'ala ba sai binsa da ido dayayi.
Ada-dai nan aka fito da amarya, ga motoci sai d'iban mutane takeyi wad'anda zasuje dinner, dama su Haleema tuni sunnyi gaba.
Dan haka Aka fito da ita drivern ne yafito ya bud'emata bayan motar, tash'iga ai bata ida zama ba taji dumm rass gabanta ya fad'i amma sai ta fuske tazauna driver yakoma mazauninsa yaja mota.
[12:34, 9/6/2016] Foulani Cerdiya😘: Kod'agowa Ameen beba inbanda danne-danne dayakeyi a phone d'insa,
K'amsh'intane yafara damunsa duk k'amsh'in yacakud'e danasa da nata, sai suka had'a suka bada wani sihirtaccen k'amshi ne me kwantar da hankalin wanda yajish'i.

Zuciyarsace ta bash'i daya kalli fuskar matar k'anin nasa, wacce ko gaisuwa bata iyaba, tasan ba angonta bane amma ta kasa koda gaidash'i,?.

Azuciyar Ameenah kuwa tunani take tayaya yazo dinner? dan a iya saninta besan bikinsa akeba, to kodai yasanima tunda gash'i zaiyi attending dinner d'in?
Tanaso ta koda gaidash'ine amma tana tsoron balainsa kar ya gwale ta sai taja bakinta tayi tsit bace kala ba.

Juyowa Ameen yayi da niyyar kallonta amma sai yafasa, turarentane yake addabarsa dan wani iri yakeji ajikinsa, ta maza yayi, yad'an saci kallonta, ita kuma kamar tasan abinda yake ta juya kanta gefe tana kallon titi, don haka bewani ganeta sosai ba" auxubillahi munashshaidanirrajim kawai yake fad'a aransa dan yaga sh'aid'an nason angazash'i kallon matar da batasa ba matar k'aninsa Habeeb.

To you all my fans ina baku hak'urin rash'in typing dabanayi, hakan yafaru dasanadin bikin damukayi, kuma bayan mun gama wallahi rash'in lafiya takamani but nafara jin sauk'in jikina yanzu zakudinga jina ko yayane Tnx u all😘


~Maman triplet~😘
[10/24, 7:08 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [15:47, 9/7/2016] Foulani Cerdiya😘: *AMEENA DA AMEEN*
_BY_
FOULANI CERDIYA
®NWA

73~74

Aransa yake tunanin ai duk laifin na Mamy ne tada tilasta masa zuwa dinner k'aninsh'i abinda bemasan anayiba, kenanma da Habeeb d'in zeyi attending dinner d'in bazai san ana bikinsa ba? kenan sai daima kawai yaga anayi kamar yadda yanzun yaga anayi, dan dai ansan yana da amfani sh'iyasa ma aka fad'a masa."Mtswww" yaja tsaki a fili.

Juyowa tayi dan ganin dalilinsa nayin tsakin, karaf tana juyowa suka had'a ido, ido cikin ido yake kallonta yad'an k'arawa idonsa girma da mamaki k'arara a fuskarsa,
itakam saroro tayi tana kallonsa, tunda anata tunanin yasan komai tunda gash'i zayaje dinner amma kuma ya'akai taga mamakin ganinta dayayi?.
Ameen ne yayi wani kw'akwkwaran numfash'i ya nunata da yatsa yace"da.....Ma..Kece Habeeb ze aura?"lallai ya girgiza kansa alamar mamaki.
Aransa tunani yake tayaya,"how"suka fara dating juna da brothern sa anyama kuwa Habeeb yasan meyake? dazai zab'i wannan mara kunyar yarinyar amatsayin mata? uwar y'ay'a? yarinyar da ba y'ar gidan *NAGARTA* ba (Littafin y'ar uwa).
Itad'inma tash'iga duniyar tunani sai dai bata zurfafa tunanin ba akazo gurin partyn.

Driver ne yayi masa maganar an iso.
Kasa fitowa yayi inda itad'inma tak'i fita tayi zamanta.
Ana hakane masu ashobe suka fiffito a'inda Haleema tayi wajen motar ta bud'e wani k'amsh'i taji ya daki hancinta ga wani irin ky'au da Amarya da angon sukayi,batasan sanda tace"Woww so cute".
Tajaho hannun Ameena tafito, sannan ta jaho hannun Ameen, bamusu yabiyota.

Masu ashob'en ne wasu a gabansu akasa su a tsakiya sannan wasu a bayansu.
Kamo hannunsa tayi ta kamo hannun Ameena ta had'asu guri d'aya"Wayyo Allah zo kuga yadda Ameen ya watsawa Haleema wata sh'egiyar harara, Sarai tagansh'i memakon tabar abinda take ina ai saima tayo saitin kunnensa tace"Pls Yah kasaki jikinka kar agane ba kaine angon ba".
Wak'a aka saki me taush'in dad'i.
Daga kan stage d'in dazasu zauna wajen da d'an duhu amma suna zuwa haske ya haska sai ga Welcome dara-dara daga bayan decoration haske ya haskaka koina tuni aka fara Dinner.
[15:47, 9/7/2016] Foulani Cerdiya😘: Haleema ce tafito tabada tarihin ango kuma tabada na amarya kuma tace Ameen da Ameena soyayyace me matuk'ar gaske a tsakaninsu kamar laila da Majnoon ko kuma ace romeo da juliet.
Inda ta k'ara da cewar basa tab'ayin nesa da junansu, saboda tsabagen soyayya da k'auna da kulawa.
A k'arsh'e tace Dan Allah kowa ya tafawa wad'annan couples d'in.
Aiko tuni aka d'au tafi Raf raf raf.
Cake aka nemi yankawa aikuwa zo kuga Ameen yadda yawani had'e rai ya yanka ta bud'e bakinta duk tsoro ya cikata yasa mata, itama ta yanko tazo sa masa memakon yaci iya Cake d'in sai ya had'a harda hannunta.
Camera tafara haskawa ta koina anata uban tafi masu d'aukar vedio nayi masu camera ta waya suna d'auka.
In banda harararta ba abinda yakeyi, itadai duk ta tsani kanta a gurin,
ankira ango da amarya wajen rawa hannunta yana cikin nash'i suka fito, y'ar rawa tafara a hankali, saboda kar tasaki jiki taji duka dan ze iya dukanta ma ayadda yake aikamata da sak'on harara.
Haleema ce ta hayo ta musu lik'i duk da ba rawa suke ba.
"Ke yau nefa kinsan sai kinyi rawa wallahi duk wannan rawar taki bazata tash'i a banza ba." Haleema ce tayi wannan maganar.
Inda tasanarwa dame kayan sauti akan ya sauya kid'a, atake kuwa yasa wakar nan me tsuma zuciya me taken Wayyo mijina k'aunarka na tsumani".
Wak'arnan ta narkar da zuciyar Ameen yadda take bin wak'ar tana d'an juyawa tana kallonsa dan yasan dash'i take.
Aiko camera sai tak'aru,
lik'i yayi mata da kansa saboda ta burgesh'i but tafa bash'i haush'i.
Yajaho hannunta duk da yasan ba Matarsa bace hasalima matar k'aninsa ce Habeeb.

Dawannan zanyi amfani in taya y'ar uwata k'awata Ummul Fadeela gama littafinta me suna NAGARTA.
Tabbas littafin nan yayi dad'i uwa uba ya fad'akar tawajen dogara da Allah da kama addua ako wani Hali mutum yake.
Baabinda zance sai dai ince Allah ya k'ara baseera Foulani na miki jinjina 👍🏻Foulani's Fans sun baki kyautar............. "toh nasan har su"oo da "oo sun zuba kunne dan suji bazan fad'a ba🤔.

~Maman triplet~😘
[10/24, 7:09 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [10:31, 9/8/2016] Foulani Cerdiya😘: *AMEENA DA AMEEN*
_BY_
FOULANI CERDIYA
®NWA

75~76

Hotuna aka sh'igayi Haleema tajaho sh'i akayi musu tare sannan suka sash'i a tsakiya aka d'auka.
Ransh'i ya b'aci amma bayadda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login