Showing 15001 words to 17897 words out of 17897 words
Chapter 6 - AMEEN DA AMEENA HAUSA NOVELS BY FOULANI CERDIYA.txt
kwalla kallonsh'i take a hankali komai nasa burgeta yake"Inason wannan bawan Allah" Ameena ta fad'a a fili.
Komawa tayi ta zauna sakamakon sh'igowarsa.
ya sh'igo tsakiyar parloun tace"sannu da zuwa"
be kalleta ba in banda kallon Tv dayayi ya girgiza kai, tare da d'aukar remote ya sauya channel d'in ya sh'ige d'akinsa.
Yunwace ta damesh'i dan baison cin abincin waje, kuma Mamy bazata yadda yaci mata abinci ba cazatai ina matarsa,
kullum sai dai yash'a tea da biscuit, yau kuwa yunwa ta damesh'i ga kulolin abinci a ajiye dan koda Ameen baya nan kullum dash'i take girki, sai dai baa d'auka hasalima baya kwana a gidan.
Cikinsh'i ne ya fara ciwo, yarasa abinyi, idan yayi mata magana ajinsa ya zube matar da k'aninsa keso? budurwar k'aninsa zaiwa magana, ya gayamata matsalarsa, wallahi aa sai dai ciwon cikin ya kash'esh'i.
Sosai cikinsa kemasa ciwo, nish'i yake a hankali,.
Ameenah take k'ofar d'akin tanason yin knocking ta tambayesh'i ko akwai abunda yake so? amma tana tsoro gash' tazo tadda yana nish'i kamar mara lafiya.
"Yah ameen"Yah ameen" whats wrong?
sh'iru ba amsa ga nish'in sai dad'uwa yake.
"Whats wrong? are you ok?? noh??
pls open the door.
"Yah ameen"
hankalinta duk ya tash'i batason taga wani abu ya samesh'i.
Gawani uban nish'i dayake, tabbas jikinta ya bata baya da lafiya.
"Mezanyi inceci mijina?".
~Maman triplet~😘
[10/24, 7:09 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [06:00, 9/16/2016] Foulani Cerdiya😘: *AMEENA DA AMEEN*
By
FOULANI CERDIYA
®NWA
85~86
Buga mush'i k'ofar take 'karayi, "Ameen ka bud'emin "
Ameena ta fad'a da tausayi.
Nish'i yake sosai saboda cikinsa .
Zunbur tayi ta tash'i kamar wadda ta tuna wani abu,
d'akinta taje tajaho sabuwar wayarta, alokacin ta had'ata Allah yaso da charge, ta daddanna number Haleema.
Kira tash'iga yi amma baayi picking ba"kai Friendy bazata sauya tsarin nan nata ba in batasan number ba sh'ikenan bazatayi picking ba".
Ameenah ta fad'a tare da komawa bakin k'ofar Ameen, tana zuwa ta taddash'i ya bud'e k'ofar da sauri ta sh'iga ciki a bakin k'ofar ta tarar dash'i rik'e da ciki.
"Yah ameen"
"sorry ina maganinka yake in baka".
Sh'iru yayi mata, in banda nish'i dayake.
Aransa yanason ta taimaka masa amma miskilanci bazai barsh'iba.
Wayarsa yake nuna mata da hannu, tace"Mene?
tare da d'aukar wayar aranta tace ko doctor zaa kira?
bata tsaya sanya ba tashi'iga dubawa aikuwa taci karo da Family doctor kamar yadda akayi saving,
kira tayi bugu biyu ana uku aka d'aga, "hello" aka fad'a daga d'ayan b'angaren,
"Hello doctor pls kazo gida Yah ameen bayada lafiya,
"Haleema ce" ya tambaya.
"aa pls unguwar lamid'o crescent zaka zo, tafad'a masa sunan layin,
baafi mintunoni ba taji bell d'in gidan tana k'ara bud'emasa tayi ta kaish'i har d'akin.
Bayan ya dubash'i ya tabbatar mata da yunwace a dinga kula da abincinsa, to kawai ta iyaamsa masa dan tasan abincin kullum sai an ajiyemasa baya da niyyar cine kawai.
Bayan doctor ya tafi tash'iga kitchen ta had'omasa tea me xafi dan ya warware masa cikinsa.
dawo wa tay taga yana had'a gumi, tea d'inta ajiye sannan tazo kusa dash'i tace"ka cire rigar sai inbaka tea kash'a kaga gumi kake had'awa,"
sh'iru yayi mata ganin haka yasa ta fara b'alle maballin rigar tasa "Alhamdulillah ta fad'a a ranta, tana mejin kunyar abinda tayi.
Tea d'in ta d'auko tasamu hankerchf ta goge masa gumin fuskarsa sannan ta tallafosh'i tafara bash'i, da farko gefe yayi da fuskarsa yawani had'e rai, sai data k'ara tallafosh'i ta d'uramasa sannan ya sh'a.
'kin kallonsa take saboda tas kofin zai iya zubewa dan jikinta har rawa yake.
Bata kyalesh'iba sai da yajish'i dam sannan ta k'ara goge masa gumin, ta ballo masa maganin ta bash'i yash'a.
Sh'ikam yasaki baki kawai yana kallonta, mamaki ta bash'i sosai.
gy'aramasa kwanciya tayi ganin yafara gyangyad'i, tazuba masa ido tana k'arewa halirtarsa kallo wanda idan ido biyune bata isa tayi ba(dama kika samu kalleshi son ranki)
sh'idai wannan a kama da sh'iru sh'irunsa inda kasan wani jarumin india Abishshek, babu inda suka banbanta sai ta abunda baa rasa ba, amma suna tsananin kama.
Dawannan tunanin bacci ya d'auketa itama, a gefensa.
Inda garin dad'in bacci yasa hannayensu suka manne da juna batare da sanin suba.
[08:11, 9/16/2016] Foulani Cerdiya😘: Sai kusan 12:30 Ameen yafara tash'i, yaji dad'in jikinsa sosai kuma cikin ya lafa masa daga ciwon dayake.
Gefensa ya kalla yaganta kwance tana bacci, sosai yayi mamaki, me yakahota bacci har d'akinsa,? kallonta yayi kyakykyawa ba kyan hali,.
"Mtsw Ke dalla tash' ki fita d'akinki, ko an gayamiki nan d'akin baccinki ne?
Mik'a Ameenah tafara tare dayin salati,
gefe Ameen yayi da kansa abun haush'i wai matar k'aninsa?.
Murza ido take tana kok'arin tash'i amma Ameen ya k'ara daka mata tsawa "bazaki tash'i ba?"
Watstsakewa tayi sosai ta kallesh'i da mamaki, mara lafiyan ne ya warke, yake mata tsawa?
"badake nake ba? tash'i ki fita ko in ball dake".
Murgud'a baki tayi tana kallonsa ta gefe, ni kike murgud'awa baki?,
jahota yayi yasa hannu ya matse bakin sannan yasa hannunsa yadinga d'illan bakin da hannunsa d'ayan.
"zaki k'ara murgud'an baki"?
"uhm uhm"Ameenah ta fad'a tana girgixa kai alamar aa.
"Tash'i ki fita yasaki bakin tare da hankad'ata.
"uhm uhm Ameenah tafara alamar kuka tare da turo baki gaba.
"Allah Allah ya.....i.s....
bata k'arasa ba ya biyota da gudu aiko itama tuni tazubawa k'afarta mai ta kwasa a million..........
Kuyi hakuri wayatace ta samu matsala.
Love you all my Fans💋
~Maman triplet~😘
[10/24, 7:10 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [08:27, 9/17/2016] Foulani Cerdiya😘: *AMEENA DA AMEEN*
_By_
FOULANI CERDIYA
®NWA
87~88
D'akinta ta nufa sh'ima kuwa ya mara mata baya, tana zuwa ta danna kof'a ta sh'ige ta rufe ruf,
Bugawa yake amma tayiwa k'ofa lock ta ciki, haka ya hak'ura ya wuce ya koma d'akinsa.
Toilet ta sh'iga tayi wanka tare da d'auro alwala, sallah tayi sannan tad'anyi makeup tasa wasu pakistan kalarsu blue black, ta gyara gash'inta tazuba dash'i dadai kafad'arta Masha Allah gaskiya Ameena tayi kyau.
Fitowa tayi ta lek'a parlour, bayanan ta salallab'o a hankali tazauna akan kujeran d'aki.
Kallo ta kunna tash'ar Zee aflam suna film d'in _Rajkumar_ "Wow"tayi tsalle tare da fad'in "My Best actor kenan".
kallonta take cikin kwanciyar hankali film d'in yanayi mata dad'i sosai. Dan har d'ankwalin data d'an yafa ya sab'ule
Sh'igowa yayi yana ganinta yayi kwafa, ya kalli tv ya kalleta yadda take tawani jin dad'i, kawai sai yaji haush'i ya d'auko remote d'in ya sauya channel d'in zuwa Mbc action.
Juyowa tayi dan ita batasanma ya sh'igo ba, mamakine ya sauka a fuskarta tayaya film d'inta yad'au dad'i sannnan kuma ya sauya mata?.
Har zatayi sh'iru sai kuma meta tuna oho mata ta kallaesh'i tawani buntsuro baki ta sauko daga kan kujerar ta zauna kan centre carpet, tace cikin yanayin sh'agwaba"Haba haba itafa rayuwa ba haka take ba kawai anzo an sauyaea mutane tash'a mu me zamu kalla da wannan k'azaman horayan".
Sakin baki yayi yana kallon ikon Allah, sh'ida gidansa dan yasauya abinda yaga dama har zaayi masa complain?,
Bece mata uffanba illa kallo daya bita dash'i.
Tayi ky'au amma fa baky'an hali tunda ba ilimin addini balle asamu kunya.
Ameen ke wannan tunanin a zuciyarsa.
Mik'ewa Ameenah tayi tash'iga kitchen tad'anyi preparing simple abunci dai-dai cikinta bata wani dad'e ba ta fito, samunsh'i tayi ya sauya channel d'in ya koma zee aflam d'in.
Dad'i taji sosai harda fad'in"Lah me takwaran sunana komawa kayi kaga basu gama ba ma."
Tafad'a tare da zaunawa plate d'in abincinta ta ajiye dan yad'anyi sanyi.
Ganin tana murmush'i yasash'i saurin sauya channel d'in alhalin kuma sh'ima yanason ganin film d'in, kawai saboda itane bazai kalla ba.
Ga girkinta k'amsh'insa ya bud'ad'e masa hanci, jiyake kamar ya d'auka yaci dan yanajin yunwa sosai,
wayo yayi mata yace"ke jeki kitchen ki had'amin tea".
Had'e rai tayi, tsabar ya rainamin hankali na kunna kallo ya kash'e sannan yanzu yazo yawani sani aiki,
"ko bazaki tash'iba".
[08:50, 9/17/2016] Foulani Cerdiya😘: Tash'i tayi tana bubbuga k'afa tana gunguni.
Tana sh'iga kitchen d'in ya d'auki plate d'in abincin yaje fridge ya d'auko ruwa ya sh'ige d'akinsa.
Abincin ya kalla ya had'iyi yahu kawai yayi bismillah yafara ci, "woww delicious".
ci yake yana tand'ar baki har ya gamaci ya kora ruwansa sannan ya d'an huta yanason fita parloun yana jin kunyar abinda zaice mata.
Ameenah kuwa ta had'o tea tafito bata gansh'iba kawai sai ta ajiyemasa.
Plate d'in abincinta tash'iga nemowa amma bata gansh'i ba.
Yunwa sai cinta take, ta k'ara lek'awa k'ark'ashin kujerar amma still bataga plate d'inba,
sai tayi tunanin ko kitchen ta barsh'i? bata fito dashi ba dama.
Dan haka ta koma kitchen d'in ta duba amma wayam babu plate d'in abincin ta.
Ameen ne ya lek'o ya tarar bata nan dan haka kawai ya sh'ige kitchen d'in anan ya sameta, turus tayi data ga plate d'in a hannunsa,
"Takwaran sunana ina abincin?
Ameenah ta tambayesh'i.
"Uhm ke dallah kinga bawai wani abun nayi dash'i ba, kinsan doctor yace adaina barina da yunwa so nad'auka naci, sai kije kish'a tean" Ya fad'a cikin masifa tare da ficewa a kitchen d'in.
Tsorata Ameenah tayi sosai, dan catake zaneta zaiyi.
Ameen yana komawa d'aki yafara tunane-tunane, "a gaskiya dole nabar k'asar nan, matar da k'anina keso, an auramin, matar da ba itace zab'ina ba"Afili yake wannan zancen.
can ya tuna inda yayi karatu suna nemansa tun bayau ba, dan haka atake anan yabud'e laptop tash'i yafara sh'irye sh'irye,
visa ne ta rage masa, dan haka dazarar komai yayi settle tafiya zeyi ko in sungaji sa sallameta su dasuka aurota, amma sh'i tafiya zaiyi ugenda.
Toh fa kunji kuma wata sabuwa.
Zanyi amfani da wannan dama in mik'a sak'on ta'aziyyata gareku Futhatulkhair inai miki gaisuwa Allah jik'an kaka.
Aunty sis kema ina miki gaisuwa Allah ya jik'anta yayi mata rahma.
~Maman triplet~😘
[10/24, 7:10 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [14:40, 9/21/2016] 08106619411😜: *AMEENA DA AMEEN*
_BY_
FOULANI CERDIYA
®NWA
91~92
Ita yanzu a haka rayuwarta zata cigaba babu so da tattalin miji.
Haleema ce ta tash'i tash'ige d'aki domin ajiye jakarta, sannan ta d'an watsa ruwa.
Tunani tash'igayi, tunanin ko yaush'e zai dawo itama bata sani ba, gash'i bata da numbern sa, to ko tana da ita ma ai bata k'asar bace"Ohh My God!! Need Your Assistance Ya rabb" .
Ameenah ta fad'a a fili, tare da zaro envelop d'in da yabata ta bud'e ta fara karantawa.
Bawani abu bane a ciki illah kud'i masu yawa in zata buk'aci wani abun.
Abinda yafi bak'anta mata rai sh'ine inda yace"In tagaji da zaman zata iya sanarwa da wad'anda suka ajiyeta."
Bak'in cikine sosai ya ziyarceta, watakan bama zamansa take ba lallai, hawaye ne suka sh'iga zubomata ainda Wani zazzafan zazzab'ie ya rufeta, atake a gurin ,
Haleemah ce tafito ta taddata tana rawar sanyi, tsoro taji ta zaro ido tace"sannu Friendy zazzab'i?.
"Eh"
Ameenah ta fad'a tana b'oye takardar a k'asan kayanta.
'Dagota Haleema tayi, kud'i taga ya zubo, ta tsugunna ta harhad'a mata tazura cikin envelop d'in sanan ta k'ara rik'ota suka sh'ige bedroom.
Kw'antar da ita tayi tare da kash'e mata Ac sannan taja mata blanket, tayi mata sannu sannan ta fita daga d'akin.
Kitchen taje ta had'a abinci tafito.
Wash'egari Ameenah tad'anji dad'in jikinta, dan har Asleem da Tasleem sunzo sunyi kwana uku, da suka ga ta wartsake yasa suka tafi.
Mama da Mamy duk sun d'auka ciki ne da ita, amma ita tasan ba haka bane.
"Friendy wai yaush'e cikin nan zai fara d'agawa ne".
Haleema ce ta fad'a a lokacin da suke zaune a palour suna kallon Film d'in Salaam Namaste...
"Hmm Friendy kenan kina ban dariya waike waya fad'a miki cikine dani?,"
Ameenah ta fad'a tana harararta.
"Aa bakiga bane kinyi wani haske, gash'i kin d'an rame laulayin da ya saki a gaba".
"Hahhh kyayi ki gama dai"kanki akeji".
*Ugenda*
Toh tun bayan saukar Ameen ya sauka a hotel, bayan ya huta ya watstsake, sannan yatash'i ya sh'iga cikin gari, wani dad'ine yake sh'igarsa jiyake kamar ya yarda kwallon mangora ya huta, amma a d'aya b'angaren zuciyarsa jiyake kamar yayi Missing wani abu.
Bayan zuwansa da kamar sati d'aya yafara aiki a gash'i alhamdulillah yanata aikinsa yadda ya kamata.
Wata ranar Monday da yamma Ameen ya fito daga aiki kenan rik'e da briefcase ya gaji ga yunwa, saurin dayake yasa yabugi wata matash'iyar yarinya wacce bazata fi sh'ekara ash'irin da uku ba,
Jakar dake hannunta ce ta fad'i a k'asa....
"Am sorry" Ameen ya fad'a yana d'auko mata jakar ya mik'a mata,
kallonsa tayi sosai ta rasa aina tasan fuskarsa, sh'ima kallon sani yake mata a makarantar da yayi karatu,
"Bakomi" Budurwar ta kats'e masa tunaninsa.
"Nagode" Ameen yafad'a yana k'are mata kallo.
[14:42, 9/21/2016] 08106619411😜: "Don't Mind" matash'iyar ta fad'a tare da hucewa.
Sh'ima tafiya yayi domin yayi matuk'ar gajiya, yana buk'atar ya huta.
~Maman triplet~
[10/24, 7:10 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN*
_By_
FOULANI CERDIYA
®NWA
89-90
Tundaga wannan rana Ameenah bata k'ara sakash'i a idonta ba sai da akayi kusab sati biyu sannan ne ta gansh'i.
Data gaidash'ima k'in amsawa yayi, dan ko kallonta ma baya sonyi, domin a ransa yanajin wani irin ba dad'i da zararar ya d'aga ido ya kalleta.
Yau dai Ameen ya gama had'a komai nash'i, tafiya ce kawai ta rage masa.
Kodayaje gidansu da zancen Mamy tak'i, Amma sai cayayi dasu An kirash'i wani taro ne a school d'insu, dan haka ba yadda suka so Abba ya bawa Mamy hak'uri tare da fad'in tayi hak'uri yaje ya dawo badai wata biyu yace ba.
Bayan sati d'aya.
Ameenah zaune kan kujerar dake parlourn, kallo take tajuyo daddad'an k'amsh'insa na tash'i, lumsh'e ido tayi sannan ta bud'e a lokacin da yake k'araso saitin ta, d'agowa tayi ta kallesh'i yayi ky'au cikin k'ananun kaya, sumar kansa tayi luf luf fuskar nan bayabo ba fallasa sh'i wani irin mutum ne befiya dariya ba, sai dai murmush'i,
murmush'inma sedai kiga hak'orinsa biyu yad'an fito, itadai Ameenah ji take kamar taje tayi hugging d'insa tight ta hanash'i fita duk inda zaije, amma ina bata isaba.
"Ke yadai naga kin wani k'ureni da ido haka".
Kunya taji ta dabai bayeta ya kamata tana kallonsa,
"Ahm gani nayi kunyi kama..."
"kama dawa" Ameen ya tambaya.
Tunanin wa zatace masa takeyi saboda tayi hakanne dan ta kare kanta.
"Da sh'i".
Kawai ta bash'i amsa.
Tsawa ya daka mata"Dawa nake kma".
"Habeeb".
Kawai taiya fad'a tunda d'an uwansa ne.
Numfash'i yayi sannan yace"ohh dan ina kama da saurayinki sh'ine zaki tsireni da ido kina kallo?."
zaro ido Ameenah tayi a ranta tana fad'in innalillahi wai sh'i wannan wani irine? nifa Habeeb ba saurayina bane nafad'i hakane dan na tsira ash'e bab tsira ba,
katsemata zancen zucin yayi dacewar"K'arb'i,"
hannu tasa kawai ta karb'a batare data k'ara kallonsa ba .
Jaka taga yaja yafita daga Parloun yayi wajen motoci,
lek'awa tayi ta tagar d'akin tana hangosh'i har ficewarsa,
Ko ina zash'i haka harda su jaka?,.
Komawa tayi ta d'auko wayarta, tafara game taji takun mutum,
tsalle ta daka tare da fad'in" oyoyo oyoyo Friendy nahi fush'i.
"Ke Amaryar yaya kinga yadda kikayi ky'au gaskiya abubuwan sun amsh'eki,"
Haleemah tafad'a da zolaya.
"Wasu abubuwan fa"
Ameenah ta tambaya da son jin amsar.
"Dalla kina nufin baki gane ba, kinga jakata haka kawai Mamy wai inzo in tayaki zama kar kad'aici ya dameki".
"Kad'aicinme?"
"Ba Yah ameen yatafi ugenda ba,"
Mamaki k'arara a fuskarta tace"Ugenda? yaush'e?.
"Ohhh yanzu ai yatafi ma"
Ameenah ta fuske ta fad'i haka saboda kar Haleema tasan abunda ke tsakaninsu,tunda ita be gaya mata zaiyi tafiyaba dan bata ma isaba.
~Maman triplet~😘
[10/24, 7:10 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [13:06, 9/25/2016] Foulani Cerdia😘: *AMEENA DA AMEEN*
_BY_
FOULANI CERDIYA
®NWA
95~96
Kira ya k'arayi, "Mtsw"Ameena tad'anja tsaki kafin take kallon wayar tace a fili"Kai koma waye wanan zai dameni". Zumb'uro baki tayi kamar yana kallonta "Hello" ta fad'a tana kara wayar a kunnenta,
"Pls kozan iya sanin dawa nake magana?,"Ameen ya fad'a.
"wai ba nace maka mutum bace,?"
Ta fad'a da tsiwar da da batasan da itaba.
"Uhm"Ameen yasaki numfas'hinda har cikin kunnen Ameenah,..
"kiyi hak'uri kifad'amin mana, sunanki pls".
Tunani tayi nad'an muntuna sannan tace"After na fad'a maka sunana kaima zaka gayan," "?
"ok"
d'an jim kad'an tayi sannan tace
"Sunana Fanteka,".
Dariyace ta sub'uce masa, yad'an dara sannan yace.
"Toh fa sorry to say, amma sai nake ganin kamar fanteka wani abun amfani ne ko?,"
Ameen ya tambaya.
"Eh haka na taso ana fad'amin agida,
kaima sai kagayamin sunanka yanzu".
"Ok......Suna......A.."
Ameen be k'arasa fad'aba wayarta ta mutu sakamakon rash'in charge,.
"Hello.hello"Ameenah ke fad'a sai data duba wayar taga ta mutu ba charge,.
"Mtsww"Ameenah taja tsaki tare da ajiye wayar,
ta janyo pillown dake kan kujerun ta sa kanta,tare da rufe idonta, tana tunanin waye wannan medad'in muryar haka?,
gaskiya ba Ameen bane,dan muryarsh'i batakai wannan zak'i ba, amma dagaji guy d'in nan ya had'u.
Idonta ta bud'e dai-dai yasauka akan pic d'in Ameen dake manne jikin gefen bangon 'dakin yayi d'an murmush'i a jiki,
tunanin datake ta tsayar dash'i da fad'in"Auzubillah minashshaidanirrajim" inada aure ina tunanin wani"astagfirullah".
Toh ab'angaren Ameen d'inma haka abin yake, dan gaba d'aya yatafi duniyar tunanin wannan muryar da kuma memuryar,
ji yake ajikinsa kamar muryar watace wacce yakejin yayi missing, kai bama ita bace, any way in na koma 9ja zanga wannan fantekar.
[13:32, 9/25/2016] Foulani Cerdia😘: Abba da Mamy na zaune, Mamy takecewa Abba" Abban yara kaga fa yaron nan har wata na Biyar ya sh'igo gash'i be dawo ba kuma ma ko ya kiramu yayi mana bayani inwani abunne ya tsaresh'i."
Numfasawa Abba yayi tare da kurb'ar juice d'in dake hannunsa yace"Nafu tunanin wani abunne ya rik'esh'i amma karki damu, duk randa yaga dama ya kira".
"Allah ya sh'irya ya kuma kare mana sh'i" Mamy ta fad'a.
~Maman triplet~😘