Showing 1 words to 3000 words out of 26984 words

Chapter 1 - IG AJEEMAL BOOK 3 BY Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt

Ajmal
Story and writing
By
Oum AmReesh❤️
....
..............
.......... call me on this number 08105565436

or WhatsApp DM
.................09031917169

Thanks you

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Book 3

Takun karshe

Page 95

_______ Daya daga cikin bedroom din dake parlourn kasa inda kayiwa Nisha jeren kayan dakinta bedroom biyu bisa kasa duk kayanta ne ciki, nan aka shiga da Nisha ita kuwa tana biye da su duk inda akayi da ita nan takeyi haka salma itama na biye da su.

Saman lallausan bed d'inta suka zaunar da ita jikin Nisha duk a sanyaye kanta kasa sai wasi wasi cikin zuciya, ruwan hawayen na tama neman su tayi tarasa duk sun kafe,.

Ammi da Goggo rabi sai da suka taushe ta gamida na siha sosai kafin suka tafi suka barta tare da Salma Nisha najin fitarsu sai yaye mayafin face d'inta tayi gamida fadawa cinyar Salma ta fashe da kuka kasa kasa tana shashsheka sai yanzu kukan yazo mata.

Lallashinta Salma tashiga yi kafin ta dago Nisha zaune tana kallon ta.

" Please kidaina asaran hawayenki a banza because yaufa ranar ki ce kuma daren mafi daraja cikin rayuwar ki wanda ba zaki taba mancewa da shi ba"

"Salma idan na ce Ina farin ciki da wannan ranar nayi karya Salma ji nake zuciyata kamar zata faso k'irjina ta fito" Nisha ta fad'i cikin kunar zuci

"Please banaso kina fadin haka ki nitsu ki kwantar da hankali ki ki fiskanci rayuwar auranki, ki sauke duk wani nauyi da hakkin da Allah ya daura bisa kanki kibi mijin ki ki so abunda yakeso ko dake ba kyaso" .

Salma ta fad'i tana dad'a tausan kafin Nisha ta kauntar da kai bisa shoulder d'in Salma tana sauke ajiyar zuciya gamida karewa kyalekyalen dakin yanda aka kawata komai cikin aminci sun dau tsawon lokaci suna zaune haka Salma na kwantar wa da Nisha hankali.

Sallaman da suka jiyo can parlourn ne yada daga Nisha har sallama suka shiga zare idanu kafin Salma ta yi saurin jan mayafin Nisha ta rufe mata face tana fadi'n

"G'yara ki kimtsa bari naje na duba".

daga haka Salma ta g'yara mayafinta itama ta fice ta nufi parlourn , kamal ta gani cikin manyan kaya ya sha kyau kaikace angone da kanshi tare da Muhaiseen wanda ya sha ado shima suna tsaye tsakiyar parlour hannayensu dauke da manya manyan ledar suka ajiye bisa saman table din parlourn.

"Aww ashe angwayene da kansu".

Salma ta fad'i tana washe baki dariya su Kamal su kayi kafin Kamal ya ce

"Sorry karmu dameku da yawa sako muka kawo but zamu rage wa amarya jin dadi mutumin fa yana jiranki a waje ya kira phone din bakiyi picking ba ".

"Okay Amma banaso na tafi na bar Nisha ita kadai gaskiya gashi dare yayi sosai ni da farima shigowar ku nayi zatun tare kuke da shi angon nata".

"Oh karki damu baiyi nisa ba yanzu saizo ke dai kiyi sauri karki bata masa lokaci" Kamal ya fad'i

"To shikenan bari nayi mata sallama saina fito"

daga haka Salma ta juya ta koma bedroom din cikin hanzari daga bisani suma su Kamal suka sa kai suka fice .

Koda ta koma yanda ta bar Nisha haka tadawo ta taddata handbag d'inta Salma ta dauka ta rataya bisa shoulder d'inta Tana fadi'n


"To ni zan wuce MB na jirana sai mun yi waya". Salma ta fad'i tana kallon Nisha

"Wayene ya shigo". Nisha ta tambaya cikin sanyin murya.

"Oh Kamal ne suka shigo da sakko da alamun angonki yana hanya shima kinga ni kuma ya kamata na tafi kar na hana ruwa gudu " . Salma ta fad'i cikin tsokana

ga mamakinta caraf Nisha ta rike hannayenta gamida mikewa tsaye tana bude mayafinta tayi raurau da idanu tana shirin kuka

"Please ni tsoro nake ji karki tafi ki barni",. Nisha ta fad'i tana karewa kata faran d'akin kallo, murmushi Salma tayi jin abinda Nisha ke cewa tana zare idanu

"Karki bani kunya mana tsoron meye kuma shima angon naki yanzu zai kariso na tabbatar duk yanda yake yanzu yana kan hanya karki sawa kanki wani damuwa".

Salma na fadi'n haka ta maida ta ta zaunar da ita tana kuma fadi'n

"Sai da safe sai munyi waya".

Nisha ba ta iya ce da ita k'ala ba haka tabita da rakiyar ido harta fice daga bedroom din daga nan Nisha ta kwanta bakin bed din gamida ta kure kamar mai jin sanyin........

Ta ban garan Heelah duniya gaba ki daya yayi mata zafin ta kaici goma da ashirin idanunta duk sun fito waje tayi bala'in rama da fari sam zuciyarta taki gamsuwa da abunda yake faruwa auran Ajmal da Nisha ji tayi kamar a mafarki gashi yanzu anyi mai kankat Nisha ta tare d'akin Ajmal ma tsayin kishiyarta because tun fara shagulgulan bikin tamkar akan idanunta ake kasance war ba abunda ba ta gani ba ko bata ji labari ba yanda shagulgulan bikin suka kasan ce saboda bikin nasu ba inda bai tasa ba duniya ta dauka ta ko Ina.

Wani kuka Heelah ta saki mai sauti cikin ta kaici tunanin ta Nisha na can tare da mijinta ,Aheel na daga gefe kwance yana bacci , mom ne ta turo door ta shigo cikin bedroom din ta taddata ita cikin wannan halin wanda yasa mom saurin karisowa saman bed din kusa da ita ta zauna cikin damuwa da halinda ta ganta ciki

" Haba Heelah mai kikeyi Haka ni na zatama baccin naki yayi nisa amma sai na zo na taddata kin tusa yaro a gaba kina kuka salon ki katse masa bacci komai?".

"Mom bazan iya bacci ba wallahi wacce yarinyar tana can suna cin amanata wallahi ba zan bar yarinyar nan ba tunda kin kasa daukan mata kanta ni da Kaina zan dau mataki wallahi zamanta bazai daure gidanan ba ".

"Da Allah rufe min baki ce miki nayi na kasa daukan mataki kanta komai ai yanzu labarin ya suma yanzun ta shiga gonarki yanda hukuntata ya zama wajibi".

" hmm ke dai ki sha kurumin ki , ki daina d'aga akwatin hankalinki karkije ki sawa kanki wani ciyon tun da nace kibar komai hanuna sai ki zubamin ido kawai ta shigo hanu ai .,"

"Kwanta ki hutawa ranki, ki kwantar da hankali kamar kinyi pillow da gawa da duk kinbi ki daga hankali kin fita hankali da tunanin ki akan wata can yar guda d'aya wacce bata wuce attishawar tsaki ba ".

Mom ta fad'i cikin lallashi da laluma tana g'yara Mata kwanciya kamar wata yarinyar ta rufe ta kirif daga nan ta mike zata fice, cikin raunin murya Heelah tace

"Mom gobe zan koma d'akina bazan cigaba da zama anan ba ".

"Uhm da dai kin d'an kara murmurewa ki karajin karfin jikin ki bakiga yanda kika fita kamanninki bane?"

"Nidai k'alau nake na samu sauki gobe zantafi ". Heelah ta fad'i cikin kosawa , ganin yanda Heelah ta kafe yasa mom ta amsa mata da cewa

"To shikenan Allah ya kaimu goben". Daga haka Mom ta fice gamaida rufo mata kofa damuwa da takai ci gurin ta itama ba a magana.....

Guraren 11 Ajmal ya turo door din parlourn ya shigo yana sanye cikin kyakykyawar shiri mai kyau da jan hankali manyan kayane jikin sa ruwan zuma hade da babban gare wanda ya sha ingantaccen aiki ya fito tas cikin shirin mayan mutane yayi kyau matuka kamar ka sa ce shi ka gudu .

Face d'insa ba yabo ba fallasa ya karisa shigowa tsakiyar parlourn sai faman wulwulga idanu yake gamida kai kallonsa door din Nisha sai kuma ya kau da kai direct ya nufi bedroom d'insa .

Yana shiga ya sanya hanu ya cire hular saman kansa ya cilla gefe daga bisani ya zare babban rigar sai da ya raba jikinsa da manyan kayan jikinsa ya rage da gashi sai short kafin ya zauna saman sofa yana mai da ajiyar zuciya gaba ki daya yau yayi ba la'in gajia gurin partyn da suka gabatar yau da daren tsakanin angwaye da friends d'insu hayaniyar mutane duk ya sanyashi ciyon kai .

Wani dugun ajiyar zuciya ya saki gamida mikewa tsaye yanufi bathroom ya wanke jikinsa gamida tsaftace jikinsa kafin ya fito shirya cikin kayan baccin sa riga da wando mai matukar laushi da taushi daga nan ya ya haye saman bed d'insa ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya.

Yau ko takan coffee bai bi ba kasan cewar cikinsa tam yake sunyi ciye ciye gurin wani abun ma da da son ransa ya shiga cikinsa ba duk doctor fu'ad ne ke tura masa kafin yayi wani yun kurin ya tusa masa bakinsa.............

Nisha jiki ba kwari ta mike daga kwanciyar da tayi dan har wani gajeren bacci tayi na wahala da tsoro idanunta duk sun shige ciki kanta kuwa kamar wanda aka daura mata wani abu bisa kai saboda yanda ya mata nauyi mikewa tayi ta sakko daga saman bed din ta nufi bathroom ta wanko face d'inta ta dawo bakin bed din tayi shiru tana karewa bedroom din kallo da tunanin shirun da taji Ajmal ba shigo ba duk ta takura a matukar tsorace take.

Phone din ta ta janyo 11 ma ta wuce idanunta ne ya ciko da k'wallah tab sai faman kallon door take tana jiran tsammanin shigowar shi but shiru kamar anshuka dusa hakan yasa ta g'yara mayafin saman kanta tamike asukwane ta fice daga bedroom din ta nufi parlourn.

Ko da tazo tsakiyar parlourn ba kowa shiru parlourn sai manyan ledar da ta gani an ajiye bisa saman table din hakan ya sa tayi tunanin Ajmal ya shigo da su

Upstairs din ta bi da kallo da tunanin ta Ajmal ya dawo but bai yi tunin ya dubata ko ya waiwaye ta ba sofa ta nema ta dan d'ofana ta k'urawa guri guda ido tana tunani ..

Allah yasa bawani babin wula kacin zai bude mata ba kasan cewar dawowar ta tsaginsa saboda a tunaninta ganin cewar ya tatare dakinsa but ba iya biyowa ta kanta ya duba ta ballai yasan mai take ciki, zare mayafin saman kanta tayi ta janyo ledar take kallah ta shiga dubawa , abubuwan da ake kawo duk wata amarya ce a ciki abubuwan ciye ciye barkate gasunan hanu ta sa ta ja goran yughourt ta bude ta kafa bakinta ba tare da wani ta raddadiba ta suma shaa because yunwa take ji sosai rabonta da abincin zata iya cewa tun safe shima cin sama sama ne.

Sai da ta sha ya kusa rabi kafin ta sauke tana ajiyar zuciya gamida komawa tayi lamo jikin sofa ta k'udundune jiki tana wulga yan idanu Nisha yanda taga rana haka ta ga dare sam ta kasa tsugul ta kasa nitsuwa ga tsoro da take ji ita kadai parlourn shiru ga kuma ta kaicin rashin k'arama wannan dare da Ajmal baiye ba yayi mata banza ko in kula kamar baisan da zaman taba ya kasa fitowa ya dubata halinda take ciki.

Haka Nisha ta dinga g'yang'yad'awa gurin tana farkawa a haka har bacci barawo ya sace ta gurin kwance, da suba k'iraye k'iraye sallah a kan kunne Ajmal ya sauka wanda ya sanya shi bude idanu gamida salatin annabi yana mika yana sauke duguwar hamma.

A kasalance Ajmal ya yaye blanket din da yake lullube ciki ya zaro santala santala kyakykyawan fararen k'afafuwansa ya zamo daga saman bed din ya nufi bathroom ya wanko bakinsa gamida yin alwala ya fito ya sanya fara jallabiyar sa yanufi hanyar fita .

Koda ya nufo downstairs ya iso tsakiyar parlourn sai Nisha ya kalla kwance saman sofa bacci yayi nisa tana sanye cikin adonta na amare ga mayafinta gefe yana lilo dan kallabin kantama ya bar saman kanta.

lumshe idanu Ajmal yayi jin wani abi da ya tsikare zuciyarsa gaba daya sai yaji ba dad'i ganinta haka shi kansa yasan bai mata adalci ba but ba yanda zayi because jiya ya tsinci kansa cikin gajiyar sosai da bai taba jin irin ta ba ta wannan ban garen .

Karisawa yayi har sofan da Nisha ke kwance yasa hanu ya sunkuce ta daga ita har mayafin nata wannan karon baccin Nisha yayi nisa don ko jin Ajmal ya daga ta ba tayi ba.

Cikin bedroom d'inta Ajmal ya mai Nisha ya nufi bed da ita ya suma k'okarin kwantar da ita but sai ji yayi tsam Nisha ta rike hanunsa bisa k'irjinta ta run gume

"Uhm please karka tafi kabarni, bana son kasake nisa dani na yi kewarka sosai". Nisha ta fad'i cikin muryan bacci tana sake shigewa jikinsa, Ajmal mamaki ya ishe sa yaushe daren ma yayi ba lallai gari yawaye ko mai take fad'i haka nan Ajmal ya sake janye jiki gamida jan hanunsa dan karfi yayi baya yana kallonta.

Ita kuwa jin yanda ya janye yasa ta dan bude idanu ta ware su bisa face d'in Ajmal wanda ke tsaye yana binta da wani kallo cikin mamaki duk da yasan ba cikin hankalinta take wannan sun batun ba sake waru idanu tayi ganin Ajmal tsaye bisa kanta yasa ta mike daga kwanciyar tana zare idanu gamida kallon d'akin da tunanin yanda tasamu kanta ciki tunda tasan dai ba anan ta kwanta ba but ganin Ajmal cikin bedroom din shi ya bata amsan tambayar ta.

Dan tura baki Nisha tayi gamida juya baya ba tare da sake kallon Ajmal wanda yake tsaye ba because haushinsa ne tab cikin zuciyarta saboda halin rashin ko in kula da ya nuna mata jiya time din da aka kawota ko lekata bai yi ba , yanzu harda dauko ta ya maido ta bedroom ko waya akesa oho Nisha sai tura baki take tana sumbatu.

Shi kuwa Ajmal ko takan yanayin da take bai bi ba sai sake kallon Nisha yayi wacce ta juya masa baya yana fadi'n

Asuba tayi ki kije kiyi alwala ki daura niyar yin sallah kafin Ajmal ya kai ga karisa maganar sai tsintar muryar Nisha yayi da cewa

"Bana yi " . yanda ta bashi amsa a fisgene ba tare da kuma ta jiyo ta kalleshi ba yasa Ajmal suma lalub'o face d'inta dan ya tabbatar da itace mai ba da amsar ko dai yar yanzu cikin yanayin baccin take .

"Mai kike nufi?". Ajmal ya tambaya yana hade gira ganin cewa cikin hankalinta take infact ma idanuta a bude suke , jin wata tambaya da ya kumayi yasa Nisha ta jiyu rigigine face d'inta na kallon celling tana fadi'n

"Eh fashi nake ina period". ta bashi amsa ba tare da takalli sun hada ido ba, Ajmal bai iya ce da ita komai ba jin yanda take bashi amsa tana wani ya mutsa gamida tura baki yasa yayi tunanin ba sense d'inta take ba shiyasa take bashi amsa gaba gid'i .

Ajmal yasa kai yayi yafi ce daga nan ya fito ya fice yanufi masallaci cikin hanzari because har yana shirin makara anshiga, ta ban garan Nisha ita kanta mamakin kanta ta karfin gwiwa wajan tsintan kanta dayi masa rashin kunya wanjan bashi amsa but Allah haushinsa ne fal cikin zuciyarta duk da tasan kad'anne daga halayensa bai kamata ta daurawa kanta damuwar hakan ba especially da tasan kallon jeka nayi ka yake wa auran.

Ajmal

Story and writing
By
Oum AmReesh

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Book 3

Page 96

______Rintsa idanu Nisha tayi gamida mirginawa ta sakko daga saman bed d'in jiki ba kwari ta suma cire nan nauyan laces din dake jikinta wanda take jin yayi matukar ta kurawa jikinta sai da ta zame tufafin jikin nata da duk wani kyale kyalen da ke jikinta sai da ta cire because tun ba yanzu ba suka ta kurata sai yanzu ta samu daman ciresu.

Daga nan ta nemi towel ta daura bisa jikinta tare da shigewa bathroom dan tsaftace jikinta daga nan ta fito da towel bisa k'irjinta bedroom din ta bi da kallo mai fadi'n gaskiya shi kanshi bed din dake bedroom din gari guda ne ko a mafarki ba taba hasashen kasan cewa cikin wannan daular ba komai dake ciki sabone sai ta samu kanta ba kuwace ciki bedroom din tama rasa inda zata dosa daya, dugun wardrobe din tabi da kallo inda aka jira mata kyawawan trolleys d'inta maroon colour da kasa gefe kuma shima wani jerin trolleys ne dark blue reras gwanin sha'awa .

Nan tanufi jerin trolleys d'in ta janyo guda ta Suma kallon tarin kayan da ke ciki duk tarin kayan dake ciki rasa na sawa tayi domin duk yawanci manyane kuma masu nauyi kuma duk din kakune sai wanda ta zab'a but ayanzu bata da bukatan kayan da zai takura jikinta.

Gefe ta janyo wani katuwar trolley d'inta wanda ta sanya kayanta da take bukatan kasan cewa dasu ta zuge zip idanunta ya sauka kan wata duguwar rigar material mara nauyi tare da mayafinta ta janyo shi gamida mai da zip din trolley d'in ta rufe ta dauki kayan ta suma sawa ta fito d'as da ita.

Parlour ta koma ta nufi saman table din inda ta bar ledar haka ta tadda shi dan haka tashiga tattare ledar ta nufi kitchen duk wani abin ya lalace cikin ledar sai cirewa tayi daga nan ta sanya sauran abubuwan cikin fridge ta ajiye daga nan ta fito ta koma bedroom d'inta.

Saman bed din ta ta koma ta kwanta abunta domin kuwa bacci ne sosai idanunta kankace mai tuni bacci ya dauke ta, duk da baccin nata bawani tsaye yayi ba guraren 9 da wasu mintuna ta bude idanu gamida tashi ta mike daga saman bed din ta koma bathroom ta wanko face d'inta kafin ta ja jiki a hankali ta tunufi hanyar fita ta nufo parlour.

Ko da ta fito sai cin karo da Baraka tayi wacce tashigo ta ajiye musu breakfast bisa dining table wanda jin motsin fitowar Nisha ne yasa Baraka sakin murmushi gamida karisowa inda Nisha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login