Showing 18001 words to 21000 words out of 26984 words

Chapter 7 - IG AJEEMAL BOOK 3 BY Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt

ba kwari Nisha ta mike zaune saman bed tana ajiye wani dogon hamma gamida mika tana salati kafin ta lumshe idanu jin daddad'an kamshe tureren Ajmal da tun jiya ya hana hancinta hutawa gurin shakar k'amshinsa.

Jin kamshensa ne ya kara mai da ta tunanin ta ta mance yau da oganta suka kasan ce guri guda but koda ta juya ban garan da ya kwanta wayam yake baya nan alamar ya fice sai kamshin turaren jikinsa da ya kasa gushewa kai kace haryanzu yana kwance gurin ,.

Jiki a sanyaye Nisha ta tazamo daga saman bed din ta mike ta nufi bathroom, kasan cewar Nisha ta ga lamar daukewar period d'in nata gaba daya yasa bawani jinkiri ta yi niyya ta shiga tsarkake jikinta daga bisani tayi wanka ta tsaftace jikinta kafin ta fito ta kimtsa jikinta daga nan ta matsa wardrobe ta shiga janyo wata white t shirt mai gajeren hanu da wata straight skirt coffee brown mai taushi da sulbi ta sanya jikinta daga nan ta kuma janyo hijab ta shinfida sallaya ta tada sallah.

Koda ta idar ta da d'ai bisa saman sallayan tana addu'oi gamida lazumi kafin ta mike ta ninke sallayen ta kuma cire hijab din tanemi hula ta sanya bisa saman kanta ta nufi parlour, zuwanta parlourn shiru yake ba kowa sai TV da aka kunna yanataa faman aiki cikin parlourn.

Guri Nisha ta nema ta zauna daga gefe tana mai cigaba da kallon TV but sam hankalin ya baya ga kallon yana can wani wajan tana karanta wasikar jaki tsawon lokaci tana zaune gurin but shiru ka keji ba Ajmal ba alamar shi, ganin haka yasa Nisha mikewa cikin sanyin jiki tanufi bedroom d'in domin dabawa taga ko lapiyar rashin fitowarsa because ta dad'ai zaune parlour but bataji motsin fitowar shi ba .

Koda ta shigo cikin bedroom din nasa still dai baya ciki sai ma shaidar da yabata nacewa baya nan ya fice saka makon jallabiyar sa da ta hango saman bed wanda ya cire, dan haka sai juyawa tayi ta koma parlour ta zauna tare da tunanin ina Ajmal ya je bai tasheta ballai ya sanar da ita ba gashi tsawon lokaci babu shi babu alamar shi, jikin knocking daga bakin door yasa ta dan mike a hankali ta isa ga door din ta murd'a handle din door din ta wangale door din Tana zazzare idanu.

Wasu kyawawan matasan yan mata ne kallo daya zaka musu kasan ma aikatan cikin hotel din ne suna sanye cikin uniform din kowacce hannayenta dauke da kyawawan bedsheet da alamun sunzo gyara musu muhallinsu ne dan haka ba shiri Nisha ta basu hanya suka shigo sai faman jijina mata kai suke alamar ban girma Nisha kuwa sai daga musu hannu tayi tana because daga ita harsu bamai jin yaren kowa daga nan Nisha sai maida door din tayi ta rufe ta koma inda take ta zauna.

_______Nisha tana daga zauna ma aikatan yan matan nan suka g'yara komai suka wanke suka goge suka kuma share komai yafito kyal kyal duk da dama can ba abunda ya baci koyayi dotti but komai ka kidane ko bai baciba za akuma gyarawa ko ajanza masa tsari, saida suka kimtsa komai kafin suka sa kai suka fice, ba jimawa da fitarsu Nisha na daga zaune ta sake jin karan knocking cikin ga jiyawa ta kuma mikewa ta isa ga door din ta bude .

Har'ila yaude wani ma aikacin nasune tafe da kyakykyawan tray d'in breakfast bisa hanunsa cikin girmamawa shima cikin dukar dakai irin na girmamawa ya mika mata tray din abincin Nisha tasa hanu ta karba kafin ya juya ya koma inda ya fito itama Nisha tarufo door ta dawo ta dare tray din bisa table, Nisha zuciyar ta duk ta da gule gaba ta takura tarasa mai sa Ajmal ya daukota ya kawo ta nan ya fita yabarta ita daya bayan shiyace ba zai dinga barinta ita kadai tana kasan cewa ba gaba daya sai takejin badadi a ranta.

A taikaice dai wunin yau ita kadai tayi shi Ajmal ko lekota baiyiba still koma bai kirata ba ta ban garan Nisha abun duk ya daga mata akwatin hankali da tunanin ina Ajmal ya je haka tunsafe gashi harana tana shirin fad'uwa tsoro duk ya da bai bayeta wannan shine kulawar da yace zai bata ya rabota da kasarta ya kawota kasar mutane ya ajiyeta yayi tafiyar sa Nisha abun duk ya dameta ko abin takasa zama taci yanda aka kawo mata breakfast fadi'n haka a ka dawo aka dauka ko tabawa batayi ba hatta lunch din ma ba ta taba ballai taci karshema bedroom ta shiga ta takura kanta ciki ta shiga aikin kuka da baya bata wahala..

Guraren karfe 8:30 na dare

Ajmal ne ya turo door kansa tsaye ya shigo parlourn yana sanye cikin wani black suit yayi matukar kyau dashi but daga yanayin yanda yashigo zaka fahimci amatukar gajiye yake sosai direct bedroom d'insa ya nufa ya cire suit din jikinsa ya fad'a bathroom wanka yayi sosai daga bisani ya fito ya kimtsa jikinsa daga nan ya kuma shirya kansa cikin wasu kyawawan kananun kaya blue shirt mai gajeren hanu mai laushi da taushi sai white jeans gajere zuwa gwiwansa daga nan ya fito ya nufi bedroom din Nisha.

Ko da Ajmal ya tura door ya kutsa kai ya shiga daga bakin door din bathroom ya hangi Nisha ta fito tana daure da towel bisa k'irjinta da alamar daga wanka ta fito, Nisha kallo daya tayiwa Ajmal dake can bakin door yana aika mata da kallo ta dauke idanu ta maida kanta kasa yayinda ta shiga takowa ta karisa bakin bed ta dauki kayanta dake shirin sawa ta juya tana shirin komawa cikin bathroom.

Ta ku d'aya zuwa biyu Ajmal ya sha gaban Nisha ya tsaya yana aika mata da wani kallo but sai ya ga Nisha tayi gefe da nufin kauce masa kanta kasa , Ajmal kuma tare ta yayi ya kuma tsayawa gabanta ya wani had'e rai ya bata face still gefe Nisha ta karayi ta kauce masa ranta a had'e sai faman bata fiska take tana tura baki hakan yasa Ajmal ya janyo hanunta ya fisgota jikinsa still dai Nisha bata dago sun had'a ido da Ajmal ba .

Hanu Ajmal ya kai ya dago habar Nisha time din wasu sirarun hawaye datake ta faman boyesu tun time din shigowar sa suka hada ido sai yanzu suka shiga gangarowa ta gefen idanunta kamar ana turosu daya nabin d'aya shaa kasancewar Nisha mai dilar k'wallah cid'aka Ajmal yad'ago Nisha suka karisa bakin bed suka zauna Nisha sai faman ajiyar zuciyar take , Ajmal lallausan farin hand d'insa ya sanya ya shiga goge hawayen dake malale bisa kuncin Nisha yana fad'in.

"Bana ce karna sake ganin wa dannan hawayen ba? mai ya kawosu yanzun?"

Wannan tambayar da Ajmal yayiwa Nisha sai tsokano ta yayi ta fashe masa da kuka harda yar shashsheka, Ajmal har cikin heart d'insa yake jin kukan Nisha baisan kukan mai take ba but tun shigowar sa ya fahimci halin da take ciki yasan daga cikin bai wuce makone da kad'aicin barinta zama ita kad'ai ba , Ajmal jinginta yayi jikinsa yana shafo suman kwanta wanda ke kwance luf.

" Banason wannan kukan stop it "

Nisha sai narkewa tayi jikinsa tana jan hanci gamida ajiyar zuciya tana goge hawayen face d'inta sam ba taso kuka ya kwace mata ba to amma kukan yaci karfinta ne ba k'aramin ta kaicin Ajmal take kulace dashi yau but ta kasa yi masa uzuri duk da ba ta san uzurin nasan ba , Ajmal riga da skirt din da ke hanun Nisha ya amsa ya nufi wardrobe ya maida shi ciki daga bisani Nisha ta ga Ajmal ya dauko mata wani sleeping dress wata yar shilan shalan din riga mai hanun vest tsayin rigar bai wuce cibiya ba tare da wani gajeren wando shima dai bai wuce iyaka cinya ba mai santsi sai duguwar rigar da za adaura sama mai bud'edd'en gaba tare da madaurin da mutum zai daure saman waist d'insa .

Sleeping dress din yayi kyau sosai white color mai d'igo d'igon baki jikin kayan, Ajmal ya dawo ya ajiye mata saman cinyarta yana fad'in

"Ki sanya wa d'annan"

Nisha sleeping dress din ta bi da kallo kafin ta kuma maida kallonta ga Ajmal wanda tuni ya juya baya ya nufi hanyar fita, to ita yanzu mai zatayi da wannan sleeping dress din da Ajmal ya ajiye mata yake nema da ta sanya ita sam bazata iya sanya suba koda a ce ita kad'ai ce ballai da tasan tare da Ajmal zata kasance anyama kuwa Ajmal qalau yake rana d'aya ya dauko wa dannan yan iskan kayan ya ce ta sanya .

Ba da d'aiwa Ajmal ya dawo cikin bedroom d'in hanusa dauke da tray d'in abinci ko da ya dawo yanda ya barta haka ya dawo ya taddata zaune bisa bakin bed tana ta faman juya kayan da ya ajiye mata yace ta sanya, wani sassanyar iska Ajmal ya furzar cikin bakin sa yana mai ta kaicin rashin jin magana irin na yariyar is too young but ta cika taurin kai da yawa simple
Instructions but sai ka ta surutu kana na na tawa .

Saman table Ajmal ya dire tray d'in kafin ya nufo inda Nisha take zaune ya tsaya bisa kanta yayinda hand d'insa ke zube cikin aljuhunsa yana kallonta kafin yace

"Ko kina da bukatan taimako ne gurin sa kayan ?"

, Nisha da kanta ke kasa sai dan d'ago kai tayi suka had'a ido da Ajmal wanda ya tsare ta da ido yana tambayar ta , sauke idanunta kasa tayi tana girgiza kai kafin tace

" Ni ba zan iya sa wa d'annan ba "

Nisha ta fad'i tana ya motsa face kaman mai shirin kuka sai faman turo baki take

"Nikuma su nake da bukatan kisa"

Ajmal ya bata amsa a takaice yana wani bata fiska

Nisha mis mis tayi da idanu ranta babu dad'i tamike ita dai taga ta kanta kayan sawa ma sai anyiwa mutum dole zame jiki Nisha tayi da niyar barin gurin ba tare da ta dauki kayan ba ganin haka yasa Ajmal ya janyo hanunta ya fisgota da karfi wanda sai da yan hanjin cikinta suka kada tsabar tsoro ,

"Where are you going for".

Cikin sarkewar murya Nisha tace

"Kayi hakuri dan Allah wannan kayan sunyi min kadan na sasu bazan iya...."


Kafin ta kaiga karishe maganar ta sai gani tayi Ajmal ya daura hanusa bisa kirjinta d'aid'ai madaurin towel d'inta because ya fahimci komai sai tayi masa musu kafin tayi ita kuwa Nisha jin Ajmal na kokarin zame mata towel yasa ta fiddo idanu waje tana zazzare idanu gamida sanya hanu ta dafe nashi da kokarin hanashi abunda yake but sai gani tayi ya sanya hanu biyu yana kokarin bude towel din gaba d'aya da iyaka k'arfinsa jikinta harya suma baiyyana ganin haka yasa Nisha d'urk'ushewa da iyaka karfinta ta kife gurin tana fidda wani walallain numfashi cikin tsoro da takaici ganin karfin hali irin na Ajmal gurin tilastata ga abunda bata da ra'ayi.

Shima biyota kasan Ajmal yayi ya d'urk'uso yana hararo ta wanda ta kifa kai kasa a kunyace a tana fidda wahalallen numfashi

"Zaki sa d'in ko na sanya miki da kaina?"

Da sauri Nisha ta kuma mikewa tana girgiza kai kafin ta kuma tattaro towel d'inta da yakusa barin jikinta ta mike gamida janyo sleeping dress d'in tanufi bathroom da gudu ta mai da door ta rufe

"Better "

Ajmal ya furta a hankali time d'in da ya mike shima ya nufi sofa ya zauna da tunanin yanda zai sanya turin kan Nisha izuwa laushi da kuma wannan kunyar karyan duk saiya yakice ma ta su

Ajmal
Stor y and writing
By
Oum amreesh

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Book 3

TAKUN KARSHE

Page 104

______ Ajmal na daga zaune ya rank'wafo gamida dafe goshinsa da hand d'insa sai faman lumshe idanu yake yana budewa because nauyi da yaji kan nayi masa hanu ya kai ya dauki zazzafan coffee d'in dake saman kyakykyawan tray din ya kai bakinsa ya suma shaa.


Jim kad'an Motsin fitowar Nisha daga bathroom sanye cikin Shirin kyakykyawan sleeping dress dinta face d'inta a hargitse kamar ta fashe da ihu saboda ta kaici kayan da Ajmal ya sanya ta sa wanda ta ke ganin tamkar ma ba kayan bisa jikinta yanda tufafin ya kasance sam bai suturta mata jikiba because santsi da showing da yake da.

Ajmal lips d'insa na jikin cup d'in coffee but idanunsa kuwa yana ga Nisha yana kare mata kallo daga sama har kasa yana karawa, ita kuwa Nisha kanta gefe sai ya mutsa take tana tura tsukekken bakinta tare da tattaro rigar tana cakumarsa gamida kankamoshi da ya ke ta faman budewa kasan yayinda take tafiyar Santala santala cinyoyinta na baiyana.

Gefe saman bed ta zauna tana ta kauda kai kefe ko kallon inda Ajmal yake zaune batayi ba sai rinanniyar voice d'insa da ya suma dashewa ya doki dodon kunnuwanta da yake umartarta da ta kariso, sannan ne Nisha ta juyo da kanta suka had'a ido da Ajmal wanda ya had'e gira yana worgo mata harara.

Ba musu Nisha ta mike a hankali ta nufi inda Ajmal ke zaune taimasa tsaya idanunta bisa kasa ba tare da tazauna ba Ajmal hanu ya kai ya fisgo hand din Nisha ta fad'o saman sofan wanda yasa Nisha g'yara zama gamida wuro wuro da idanu tana kallonsa, ba tare da ya bita kanta ba ya ajiye cup d'in coffee d'in dake hanunsa kafin ya shiga turawa Nisha tray d'in abinci gabanta alamar ta cii .

Tura baki Nisha ta kuma yi gamida d'an kauda kai gefe tana fadi'n

"Na koshi"

Duk da tasan yanda cikin ta keta faman k'ogi saboda yunwan kasancewar haramtawa kanta sanyawa cikinta wani abin wunin yau, Ajmal sam baya son yawan surutu but ita kuma ya fahimci komai ya fad'a sai ya kuma na natawa kafin tayi ko yanuna macin ransa but bayason haka yayi mata abu karfi karfi ko kuma dole kasan cewar bayaso ya bata mata yana da bukatar ya bita saisa saisa some times haka kawai yakan ji tausayin yarinyar ya kan darsu cikin zuciyarsa wanda yakasa sanin dalilin hakan but ita kuma ta kasa fahimta.

Ajmal hanu ya kai ya bude plate d'in ya daura saman cinyarsa kafin ya kai hanu hab'arta ya juyo da ita suna fiskantan juna da tafin hanunsa Ajmal ya kai hanu cikin plate d'in roasted chicken ankewaye shi da kayan lambu gwanin sha'awa sai fidda wani daddad'an kamshi yake Nisha sai ganin Ajmal tayi ya yago cinyar kazar ya miko Santa bakinta wanda yasa Nisha sake kawar dakai tana ya mutsa face tana fadi'n

"Please na koshi"

Azahirn gaskiya ransa yana matukar sosuwa da takaicin abunda yarinyar ke masa duk lallabata dayake but sai ta dinga basar da shi kasan cewar yana da labarin wunin yau ba ta wani sa komai cikinta ba duk wani motsin ta tamkar akan idanusa takeyi yau ta hora kanta da zama da yunwa wanda baisan dalilin ba tunda bawai yunwar ne bata ji ba but bai sani ba ko rashin ganinsa ne yasa ta kasa cin komai ko rashin sabo da nan danno launin abincin su bai fahimta ba but shi dai burinsa ayanzu ta sanya wani abin cikinta dan haka Ajmal ba tare da gajiyawa ba ya kuma kai mata saman lisp d'inta yana fadi'n.

" Please "

Nisha jikinta ne yayi wani irin sanyi ya mutu ganin da giyar Ajmal harda marairai ce face yana lallabarta akan yunwar cikinta , d'an gimtse face Nisha tayi kafin tasa hanu ta karbi cinyar kazar gamida d'an tura baki tana fad'in

" Zanci dakaina"

Ba musu Ajmal ya kyaleta wanda daga nan ya yago tissue ya goge hand d'insa kafin ya mike tsaye yasa kai ya fice daga bedroom d'in da rakiyar idanu Nisha ta bi bayan Ajmal dashi ganin yanayin da ya fita tamkar wani majinyaci sai faman sake jiki yake kamar wanda aka zarewa lakkan jiki, wani goron numfashi Nisha ta ja ita dai mamaki take tunda suka zo Ajmal ya sauya mata ba kamar da da suke gida ba yanzu komai cikin natsuwa ba fad'a .

Nisha jiki take cikinta kamar ana gobara tsabar yunwan dake tattare da ita kamar jira take Ajmal ya gama fita ta kai cinyar kaza bakin ta suma ci daga nan ta shiga bude sauran plates d'in bubun tab'awa gasu sai wanda ta yi ra'ayi zab'a ta ci ,Nisha saida ta d'an taba kazar ba laifi sannan ta kara da wani hadadden fruit salad wanda take sha takejin dadinshi har tsakar kanta.

Bayan da ta kammala ta shiga tattare gurin daga bisani ta dauki tray d'in ta dangana dashi parlour inda ta ajiye saman table because ta san koda yaushe za aiya shigowa dauka , dan haka ta juyo ta dawo cikin bedroom d'in direct ta nufi bathroom ta wanko bakinta kafin ta dawo ta haye saman lallausan bed d'inta ta kwanta gamida k'udundunewa cikin blanket tana sauke sassanyar ajiyar zuciya.

Nisha yauma juyin ta dingayi tajuya nan ta juya can bacci yaki zuwa ba dan komai ba sai dan tsoron

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login