Showing 1 words to 3000 words out of 14831 words

Chapter 1 - WANI SHARRIN Hausa Novels By Jajirtattu Writers Association.docx

*WANI SHARRIN*

(Mutum ke nemowa kansa)

Channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*

*(J.W.A)*







*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*

Bismillahir Rahamanir Raheem.

Ya Ubangiji yanda na fara lafiya kasa in gama cikin ƙoshin lafiya.

Allah kayi daɗin tsira ga shugaban mu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama.

Ina ƙara miƙa saƙon ta'azziyya na babban rashin da ƙasa tayi na Sheikh Muhammadu Ɗahiru Usman Bauchi, ubangiji ya gafarta mishi Allah yasa dashi da masoyin shi.

Ban rubuta wannan labarin domin cin zarafin wata ko wani ba, duk wanda labarin ya yi daidai da rayuwarshi ya yi haƙuri.

Written by ✍️

Jagabar Jajirtattu

Chapter 1

Dubanin jama'a ne suka shaida ɗaurin auren Ajwa Usman da angonta Sa'idu Hashim.

Wani yaro ya shigo gidan yana shailar an ɗaura auren yanzu.

Inna Talatu da yara ke kiranta da Inna ta fito tsakar gida tana rangaɗa buɗa tana faɗin.

"Aure ya ɗauru ƴan baƙin ciki sai dai su mutu." Inna sai habaice habaice take yi amarya Ajwa tana yiwa mahaifiyarta kirari cike da alfahari.

Ganin abin ba mai ƙarewa bane dangin mahaifin Ajwa suka janye amarya domin hakan abin kunya ne a garesu.

Bayan sallar isha'i aka zo da motocin ɗaukar amarya, mahaifin Ajwa ya yi mata nasiha mai ratsa jiki sannan a ƙarshe ya ce.

"Dan Allah dan Annabi ki rufa mun asiri ki zauna lafiya a gidan mijinki, babu ruwanki da abin da bai shafeki ba kar inji kar in gani." Daga haka suka wuce da ita gurin motar da aka ware saboda ɗaukar amarya.

Gidan amarya part biyu ne ɗaya na mahaifiyar Sa'idu ne ɗaya kuma na Ajwa two bedroom ɗaya da toile ɗaya babu toilet, parlourn yasha kujeru saiti masu ruwan ƙasa da ratsin fari labulayen ɗakin ma irin kujerun ne.

Kitchen yana tsakar gida da toilet sai ɗan ƙaramin tsakar gida, yasha siminti gidan daidai zaman talaka ma sha Allah gidan ya yi kyau.

Ƴan kai amarya sun koma gida suna ta santin gidan Ajwa, Inna sai jin daɗi take yi tana yiwa amaryan ta habaici.

Washe garin biki kowa ya watse ƴan uwan mahaifin Ajwa na nesa basu koma ba, amaryar Inna mai suna Raliya amman yara suna kiranta da Mamy, tayi sallama ɗakin Inna suka gaisa da raguwan mutanen da basu koma gidajensu ba, daga nan ta zauna suka ɗan taɓa fira tayi sallama ta koma ɗakinta.

Bayan sati ɗaya da bikin Ajwa amarya tana zaune lafiya da mijinta da uwar mijinta, Sa'idu ya fahimci amaryansa bata san addini ba gaba ɗaya, tun a nan suka fara samun matsala da mijin.

Sa'idu ya fahimci Ajwa tana da taurin kai sai ya rabu da ita, bayan sallar magrib yake biya mata ƙawa'idi da ahalari.

Ajwa tana da kirki sosai sannan kuma tana son dangin mijinta, amman idan ka taɓa ta fitinanniya ce lamba ɗaya, sannan bata son zama guri ɗaya mace ne mai son yawo, bata da matsala da uwar mijinta domin tana ƙoƙarin kyautata mata, amman fa itama uwar mijin ba kanwar lasa bace idan ka ta ɓata.

Yau girkin Mamy ne Alhaji Usman wanda yara suke kira da Baba, ya yi sallama ya shigo room ɗin Mamy tana zaune tana chart a saman kujera.

Room ɗin yasha turaren wuta yana ta ƙamshi, parlourn na ɗauke da saitin kujeru black and white labulayen ɗakin ma haka.

"Talatu zata yi tafiya kuma tana san girki ya dawo hannunta, har zuwa lokacin tafiyar nata." Baba ya faɗa yana zama a ɗaya daga cikin kujerun parlour.

A zabure Mamy ta miƙa tana kallon Baba cike da mamakin furucin bakin shi.

"Bangane abin da kake nufi ba." Mamy ta faɗa murya na rawa.

"Talatu zata yi tafiya kuma tana son a rama mata kwanakin girkinta, idan ta tafi girkin sai ya dawo hannunki gaba ɗaya har zuwa lokacin da zata dawo." Baba ya faɗa yana danne danne a wayarshi.

"Amman dan Allah a ina a ka taɓa jin irin wannan, sai ka ce muna garin arna." Mamy ta faɗa tana jin jina rainin hankalin Talatu.

"Kina nufin nine arnen ko Talatu.?" Baba ya faɗa a fusace.

Mamy ta fashe da kuka tana cewa.

"Wallahi ban yarda ba sai dai ta fasa tafiyar."

"Shawara ya rage naki, domin na gama magana." Baba ya faɗa yana fita daga room ɗin.

"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wannan wace irin masifa ce." Mamy ta faɗa hawaye masu zafi na zuba daga cikin idanunta.

Mamy tayi alwala ta ɗau Qur'ani yaranta Yusra da Aysar suka kewaye ta, Mamy tana karatu tana hawaye, sai da taji zuciyarta ya yi sanyi sannan ta ajiye Qur'anin tayi nafila, sai da ta tabbatar zuciyarta ya yi sanyi sannan ta miƙe ta shige bedroom, Yusra ƴar shekara goma tabi bayanta Aysar ɗan shekara bakwai ya fita zuwa gurin Baba.

Aysar yana fita suka haɗu da Zainab a tsakar gida.

"Zo nan dan uwarka."

Aysar ya zura da gudu ya koma ɗaki, Zainab tayi ƙwafa tana cewa.

"Zaka san na kiraka ka gudu."

Bayan sallar azahar Inna ta aiko Zainab amsar kwanon abinci, a bakin ƙofa ta tsaya tana tsaki, Aysar ya fito zai yi alwala Zainab ta riƙo shi ta zabga mishi mari guda biyu sannan ta ranƙwashe shi tana cewa.

"Shege mai baƙin hali irin na uwarsa."

Mamy na zaune a parlour tana kallon abin da ke faruwa, amman tayi kamar bata gani ba, domin idan ta ce zata yi magana ƙarshe abin ya koma kanta.

Aysar ya fashe da kuka Yusra zata fita Mamy ta hana.

"Kwanon abinci." Zainab ta faɗa tana hararan ƙofar ɗakin.

Yusra ta ɗau flas ɗin Mamy da kwanoni guda biyu ta fita, Aysar na duƙe yana kuka ta riƙo hannun shi tana share mishi hawaye, Zainab ta bigeta ta wuce da sauri Yusra ta dafe bango, Mamy ta share hawayen fuskarta sannan ta fito, hannun Aysar ta riƙo tana share mishi hawaye.

Mamy ta shiga da Aysar ɗaki Yusar kuma taje kai kayan abincin, Inna Zainab Khadijah A'isha dukkan su yaran Inna ne Ajwa ita ce babba a gidan.

Yusra jiki na rawa ta ajiye kayan hannunta zata koma, taji an daka mata tsawa an ce.

"Uban waye sa'an wasanki a gurin nan." Khadijah ce take wannan maganar.

Yusra ta dawo ta zauna fuskanta cike da hawaye.

"Shegiyya mai baƙin hali." A'isha ta faɗa tana ranƙwashinta a kai, Yusra ta dafe kai tana hawaye.

"Wallahi idan baki shanye wannan hawayen ba, yanzu zan saki mai dalili." Zainab ta faɗa tana hararan ta.

Mamy duk tana sauraron abin da ke faruwa, kuma ta fahimci zasu iya haɗuwa su zane mata yarinya kamar yanda suka saba, Mamy ta fita zuwa tsakar gidan ta kira Yusra.

Duk wannan abin dake faruwa Inna tana zaune tana raba abinci, kuma bata hana su ballantana ta tsawatar musu.

20 minutes da shigarsu ɗaki Zainab ta kira Yusra a kan tazo ta kwashi abincin su.

Kwanon Aysar ba a zuba komai ba Mama ta kalli Yusra, dake kallon kwanon abincin ƙaninta ta ce.

"Sai da nagama rabo na tuna dashi, dan haka kuyi maneji."

Yusra bata ce komai ba ta shiga ɗaki, ta ajiye abincin a gaban Mamy sannan ta faɗa mata yanda suka yi da Inna.

Mamy ta haɗa musu abincin duka harda nata, suka zauna suka ci amman basu ƙoshi ba, kasancewar abincin ba wani na kirki bane.

Mamy ta ɗauko ƙaramin murhu ta kunna gawayi bayan ya tashi ta ajiye a bakin ƙofa, taliya ta dafa da mai da yaji ta zuba wa yaran sannan ta zuba nata.

Bayan sun gama ci Yusra ta fita da kwanonin da suka ɓata, ta haɗa wanke wanken gaba ɗaya ta wanke Aysar na ɗaurayewa, ta kwashe kawonin zata shiga ɗaki Zainab data zo wucewa ta tureta, kwanonin da suka suka zube ta faɗa a kan su har da wuƙa.

Yusra jin zafi har cikin ƙwaƙwalwar kan ta yasa ta ƙwalla ihu, da sauri Zainab ta shige ɗaki.

Mamy ta fito da sauri ganin Yusra kwance a saman kayan wanke wanke tana kuka, yasa tayi saurin ƙarasawa gurin.

"Garin yaya kika faɗi, kamar bakya gani." Mamy ta faɗa tana riƙota.

Da sauri Yusra ta duƙa tana dafe gefen cikinta, Aysar dake ƙoƙarin kwashe kayan da ya zube ya kalli Mamy a furgice yana cewa.

"Lah Mamy jini a cikin Aunty."

Hankali tashe Mamy ta kai idununta gurin da Aysar yake nuna wa, tabbas jini ne yake ɗiga kaɗan kaɗan ajikin Yusra.

Daman da hijjab a jikin Mamy da sauri ta ɗauko Yusra tayi hanyar waje da ita Aysar ya bita da gudu.

Mamy chemis ta nufa hankali tashe tana tafe tana haɗa hanya, domin ko ganin gabanta bata yi saboda tashin hankali.

Ta Batulu ce..........✍️*WANI SHARRIN*

Mutum ke nemowa kansa

Channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*

*(J.W.A)*







*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*

Written by ✍️

Jagabar Jajirtattu

  

Allahumma salli ala sayyadina Muhammad wassalim.

Chapter 2

Ko sallama bata yiba ta faɗa chemis tana faɗin.

"Dan Allah ka taimaka mun."

Mai chemis ɗin ya amshi Yusra ya kwantar da ita a saman wani ƙaramin gado, almakashi ya ɗauka ya yage daidai gurin da jinin ya ɓata, wani abune ya yanke ta a gurin kuma yankar ya shiga sosai.

Dressing ɗin gurin ya yi Yusra ta fashe da kuka tana ƙan ƙame Mamy, sannan ya yi mata alluran pain relief ya bata magani, Mamy sai a lokacin hankalinta ya fara dawowa jikinta, ta tambaye shi kuɗin ya faɗa mata.

"Dan Allah idan ba damuwa wannan yaron ya biyo ni, ya karɓi kuɗin." Mamy ta faɗa tana nuna wani matashi da suke zama tare da mai chemis ɗin.

"Ok badamuwa, Hassan kuje ka amso kuɗin dan Allah." Mai chemis ɗin ya faɗa yana kallon shi.

Mamy ta riko hannun Yusra suna tafiya Aysar na bin su a baya, Baba yana zaune a ƙofar gida ya hango Mamy.

Cike da tuhuma yake bin ta da kallo Mamy tayi kamar bata ganshi ba ta shige gida, bata jima da shigaba ta fito ta miƙa wa Hassan dubu biyar sannan ta koma.

Kayan wanke wanken yana gurin a zube Mamy ta je zata kwashe kayan, ta ga jini a jikin ƙaramin wuƙar data yanka albasa.

Cike da tunani ta wanke wuƙar ta kwashe kayan wanke wanken ta shiga ɗaki, Yusra na kwance tana kuka Aysar yana rarrashinta.

"Daga ina kike.?" Baba ya faɗa shigowa ɗakin.

Mamy ta buɗe baki zata yi magana Baba ya ɗaga mata hannu, ya nufi gurin da Yusra ke kwance a two seater tana kuka.

"Garin yaya hakan ta faru.?" Baba ya faɗa yana duba gurin da aka yaga a kai dressing.

"Aunty Z ta tureta shi ne ta faɗi a saman wuƙa taji ciwo." Aysar ya faɗa yana turo baki.

"Subhanallahi ƙila ko bata lura bane." Baba ya faɗa yana shafa kan Yusra.

"Ɗazun ma ta mareni, kuma ta hanani abinci wai ya ƙare." Aysar ya faɗa yana kallon Baba.

"Biyoni parlourna." Baba ya faɗa yana fita a fusace.

Mamy ta harari Aysar ta fita zuwa parlourn Baba, fyalle ɗaya ne sai toilet amman parlourn yana da faɗi sosai, akwai gado drower saitin kujeru masu ruwan zuma da baƙi.

Baba ya yi sallama ya shigo Inna Zainab Khadijah A'isha suna bin shi a baya, Baba ya zauna kusa da Mamy dake zaune a kujera mai zaman mutum uku, Inna ta zauna a kusa dashi suka saka shi a tsakiyyar su.

"Mai ya faru kika hana Aysar abinci.?" Baba ya faɗa yana tsare Inna da ido.

Saboda abincin bai kai ba shi ya sa ban zuba mishi ba, Inna ta faɗa tana tsare shi da ido, Baba ya yi ƙasa da kai yana jin kanshi na sarawa.

"Gaskiya ba zan yarda da horan yunwa a cikin gidan nan ba, daidai gwargwado Allah ya hore mun abin da zan ciyar da iyalai na, dan haka bana son in ƙara jin an hana wani abinci a cikin gidan nan." Baba ya faɗa yana kau da kai. Inna tayi ƙwafa hararan shi.

"Ke kuma na dawo kanki, mai ya haɗaki da Yusra.?" Baba ya faɗa yana tsare Zainab da ido.

"Zagina tayi shi ne na dake ta." Zainab ta faɗa tana turo baki.

"Bayan kin dake ta kuma kika jefar da ita, ta faɗa saman wuƙa koh.?" Baba ya faɗa cike da ɓacin rai.

Zainab ta harari Mamy tana cewa.

"Ni ban ture ta ba, kawai na dake ta ne saboda ta zage ni."

A fusace Baba ya miƙe ya kai mata mari Inna ta tare.

"Wallahi ba zan ɗauki wannan iskancin ba,  idan mutum zai gyara to, idan kuma ba zai gyara ba zan ɗauki mummunar mataki." Baba ya faɗa yana fita a parlourn.

Ɗaya bayan ɗaya suka fice yaran Inna ta kalli Mamy tayi murmushi ta ce.

"Duk wanda ya ci tuwo dani, wallahi miya yasha." Daga haka Inna ta fita.

Kamar yanda Baba ya faɗa haka ya faru, Inna sai da tayi sati biyu tana girki sannan ta tafi garinsu, da Zainab ta tafi A'isha Khadijah ta bar su a gida domin su ɗauko mata rahotanni abin da yake faruwa.

Bayan kwana biyu da tafiyar Inna Mamy na zaune a kitchen ɗin su tana girki, Khadijah ta shigo zata ɗauki cup ta taka ƙafar Mamy da zata fita ma ta ƙara taka ƙafar.

Mamy ta riƙo hannun Khadijah ta juyo cike da rashin kunya zata yi magana Mamy, ta zabga mata mari sannan ta yi magana cike da gargaɗi da kashedi.

"Wallahi duk ranar da kika ƙara gigin aikata, makamancin wannan abin sai na zane ki a gidan nan, babu wanda zai ƙwaceki, idan kun yiwa yara wannan bai dame ni ba domin na san akwai ko lokacin da baza ku iya taɓa su ba, amman taɓa ni shi ne babban kuskuren da zaki yi a cikin rayuwarki." Daga haka Mamy ta koma gurin da take zaune, ta bar Khadijah buɗe da baki.

Baba ya yi sallama ya shigo Khadijah ta fashe da kuka tana cewa.

"Wallahi ban lura bane, amman dan Allah ki yi haƙuri."

"Mai ya faru." Baba ya faɗa yana ƙarasawa gurin.

"Na taka tane ban lura ba, shi ne ta mareni duk da na bata haƙuri." Khadijah ta faɗa hawaye na zubowa.

"Dan Allah ki ringa haƙuri da yara, tun da ta baki haƙuri to ba sai ki haƙura ba." Baba ya faɗa yana jin haushin Mamy.

"Wannan ne kake cewa yarinya.?" Mamy ta faɗa cike da jin haushin mijin nasu.

"To ba yarinyar bane.?" Baba ya faɗa yana zabura kamar zai kai duka.

"Yarinyar da ko yau akai mata aure zata zauna, ita kake kira da yarinya.?" Mamy ta faɗa tana sauke girkin data ji ya fara kamawa.

"Daman an jima ana gaya mun kin tsani yara na ban yarda ba ashe da gaske ne, wallahi ba zan lamunci wannan zaluncin ba." Ya faɗa yana shiga parlourn shi.

Khadijah tayi murmushi tana cewa.

"Allah ya ƙarawa Baba lafiya da nisan kwana."

Daga haka tayi gaba tana juya jiki, Mamy dariya abin ya bata, domin lamarin mijin nasu da ƴaƴanshi ba yau ta saba gani ba, amman kullum sabon abu take gani a cikin gidan.

Mamy ta aiki Aysar ya ya karɓo kwanon abinci, Aysar ya dawo yana kuka fuska duk shedar mari.

Mamy bata ce komai ba ta zaunar dashi, ta rarrashe shi.

Ta ɗau plas mai ɗan girma a kwandon Inna ta raba abincin kamar yanda aka saba, ta ɗau plas ɗinta dana Baba ta shiga ɗaki, bayan ta ajiye kayan abincin ta fito ta tsaya a bakin ƙofar ɗakin Inna ta ce.

"Khadijah kizo ki ɗau abincin ku." Mamy taji shiru kuma gashi tana jin firan su, sau biyu tana magana jin basu amsa ba ta tafi abin ta, domin bata jure rainin wayyau.

Bayan sallar azahar Baba ya dawo gida, A'isha da Khadijah suna zaune a tsakar gida.

"Kunci abinci.?" Baba ya faɗa yana shiga ɗaki.

Khadijah tabi bayan shi.

Ta Batulu ce.........✍️*WANI SHARRIN*

Mutum ke nemowa kansa

Channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*

*(J.W.A)*







*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*

Written by

Jagabar Jajirtattu

Allahumma salli ala sayyadina Muhammad wassalim.

Chapter 3

Baba ya zauna a kujera Khadijah ta zauna a ƙasa.

Mamy tayi sallama ta shigo hannunta ɗauke da babban plate mai ɗauke da plas ɗin abinci da jug ɗin ruwa ta aje.

"Khadijah ta lafiya.?" Baba ya faɗa yana tsare ta da ido.

"Yau ba a bamu abinci ba." Khadijah ta faɗa tana share hawaye.

Baba ya tsare Mamy dake zuba mishi abinci a plate, ya ce.

"Mai ya faru, kika hana su abinci.?"

"Nayi ta magana su zo su ɗau abinci, amman su kai banza dani." Mamy ta faɗa tana zama a kusa dashi.

"Ba muji kiran da tai mana ba." Khadijah ta faɗa tana share hawaye.

"Mai yasa da kika ji shiru baki ɗauki abincin kin kai musu ba.?" Baba ya faɗa yana ɗaure fuska.

"Saboda zaman su nake yi, dole in bisu da abinci ɗaki." Mamy ta faɗa cike da jin haushi.

"Wai dan Allah mai yasa bakya ƙaunar zaman lafiya ne.?" Baba ya faɗa yana tsareta da idanu Mamy tayi shiru, Baba ya kalli Khadijah dake zaune kamar munafuka.

"Jeki ɗauki abincin naku." Baba ya faɗa yana ɗaukar plate ɗin da aka zuba abinci, Khadijah ta fita tana tura baki.

Baba sai da ya gama cin abinci yasha ruwa sannan ya kalli Mamy.

"Wai dan Allah mai yasa bakya ƙaunar yaran nan.?" Baba ya faɗa cike da tausasawa.

"Yanzu kana nufin bana ƙaunar yaranka.?" Mamy ta faɗa cike da mamaki.

"Ƙwarai kuwa domin da kina ƙaunarsu baza ki barsu da yunwa ba." Baba ya faɗa yana fita a ɗakin.

"Allah ya kyauta." Mamy ta faɗa tana gyara gurin da Baba yaci abinci.

Haka zaman ya ka san ce tsakanin Mamy da su Khadijah, kullum da salon iskancin da zasu fito dashi, Mamy ko kallo basu isheta ba, idan Yusra ta fito su kama ta su daka Aysar tun da yaga hakan ya daina fitowa shi kaɗai, idan Baba ya yi magana su ce rashin kunya suke yi musu, Mamy data fahimci abin zalunci ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login