Showing 3001 words to 6000 words out of 14831 words
Chapter 2 - WANI SHARRIN Hausa Novels By Jajirtattu Writers Association.docx
sai ta koma duk in da za suje zata rakasu, har toilet idan zasu shiga Mamy ke rakasu Mamy tana kawar da kai amman tana cutuwa, kuma Baba har kullum ganin laifinta yake yi akan bata ƙaunar ƴaƴanshi.
Mamy na zaune a parlour tana yan kewa Yusra ƙumba taji an yi sallama, A'isha dake zaune a tsakar gidan tana wanki ta amsa sallamar suka gaisa, sannan baƙuwar ta ce.
"Dan Allah umman Yusra tana nan.?"
"A'a bata nan." Khadijah dake fitowa daga ɗaki ta faɗa.
"Dan Allah ko tayi nisa ne.?" Baƙuwar ta faɗa tana shirin fita.
"Mu ma bamu san inda taje ba." A'ishah ta faɗa tana hararan ta.
Baƙuwar ta juya zata fita taji muryan Mamy a bayan ta tana faɗin.
"Maman Abdul." Cak baƙuwar ta tsaya ta juyo cike da mamaki, Mamy tayi murmushi ta riƙo hannun ta suka shige ɗaki.
Mamy da baƙuwar suka zauna a two seater Yusra ta ɗibo ruwa a jug ta ajiye mata, ta duƙa har ƙasa ta gaisheta sannan ta shige bedroom.
"Amman gaskiya yaran can basu da mutunci wallahi." Maman Abdul ta faɗa tana shan ruwan da Yusra ta ajiye.
"Uhm Allah ya kyauta." Mamy ta faɗa tana kawar da maganar.
Maman Abdul ƙanwar Mamy ne uwa ɗaya uba ɗaya.
Sai dare Maman Abdul ta tafi gida bayan anyi sallahr isha'i, Baba ya dawo gida kamar yanda ya saba Mamy ta tafi room ɗin Baba.
Yana zaune yana kaɗa ƙafa cike da rashin mutunci, tayi sallama ta shiga tayi mishi barka da zuwa, Baba ko kallon gurin da take bai yi ba, domin ƙiris yake jira daman.
Mamy ta shiga toilet tayi alwala tazo ta kwanta, Baba abin yaji ya ƙara ɓata mishi rai.
"Wai dan Allah mai ke damunki ne.?" Baba ya faɗa yana hararanta.
"Abban Yusra dan Allah maine ne lafina a gidan nan.?" Mamy ta faɗa hawaye na zubowa daga cikin idanunta.
"Saboda bakya sona, domin duk wanda baya son naka ai kai ne baya so a fakaice." Baba ya faɗa still yana hararanta.
"Yanzu kuma laifin mai na yi.?" Mamy ta faɗa tana jin zuciyarta na zafi.
"Ɗazun keda ƴar uwarki kun haɗu kun zage mun yara kunci musu mutunci, wannan abin kunya ne wallahi kema fa kina da yaran, sannan har kina hana su abinci bayan kuma ubansu ya nemo abincin." Baba ya faɗa a hassale.
"Zan jure duk wani cin mutunci da cin fuska daga gareka, amman wallahi ba zan lamunci hakan daga yaranka ba, abubuwa da yawa kayi mun wanda ya dace inyi zuciya in rabu dakai, amman ban yi hakan ba a cikin ƴan uwana babu wanda ya san halin da nake ciki, ka ƙwace girkina ka bata yaranka su zageni mahaifiyarsu tayi mun kaima kazo ka ɗaura daga inda suka tsaya, to wallahi ba zan ɗauka ba yanzu shirun da nayi ba tsoro nake ji ba." Mamy ta faɗa tana shirin barin ɗakin, daman da hijjab a jikin ta.
Baba ya riƙo ta yana faɗin.
"Haka kika ce koh.?"
Mamy cike da ɓacin rai ta ce.
"Eh haka na faɗa."
"Aiko zaki tafi gidan ubanki, domin wallahi ba a haifi matar da zata hora mun yara ba." Baba ya faɗa yana shigewa toilet.
Cike da furgicin furucin daya furta Mamy tabi shi da ido har ya shige.
Mamy ta share hawayen fuskan ta sannan ta ce.
"Aiko zan bar maka gidanka kamar yanda ka faɗa."
"Idan kin tashi tafiya karki tafi mun da yarana, domin ba a kawo ki dasu ba." Baba ya faɗa daga cikin toilet.
"Daman babu inda zanje maka da yara, dole su zauna a gidan ubansu." Daga hakan ta fita, ɗakinta ta koma ta ƙwanƙwasa Yusra ta buɗe mata ƙofa ta shiga, kai tsaye bedroom ta nufa ta sauko da akwati ta shirya kayanta, sannan ta zaunar da Yusra Aysar yana ta bacci abin shi.
"Duk rintsi duk wuya ki kula da ɗan uwanki, ki zame mishi innuwa a duk inda yake." Mamy ta faɗa hawaye masu zafi na zubowa daga idonta.
"Mamy ina za kije da daddaren nan.?" Yusra ta faɗa tana hawaye.
"Yusra zama na da mahaifinki ya ƙare, zan tafi namu gidan." Mamy ta faɗa tana tusayin rayuwar da zata bar ƴaƴanta.
"Mamy dan Allah ki tafi damu." Yusra ta ce tana fashewa da kuka.
Mamy ta rarrashi Yusra har sai dai ta yi bacci, sannan ta kwantar da ita ta kwashe akwatin ta fita, ta tsaya a bakin ƙofa ta kalli yaran.
"Allah ka tsare mun yarana a duk inda suke."
Mamy ta furta tana barin ɗakin, Khadijah da A'ishah na tsaye a window suna leƙen tsakar gidan, suna hango Mamy suka ce.
"Allah ya kiyaye hanya."
Mamy tayi murmushi ta ja akwatin tana faɗin.
"Ƴaƴa mata kuke masu rayuwa a ƙarƙashin wani."
Daga haka Mamy ta fita napep ta samu ta faɗa mishi inda zai kai ta.
Sun yi tafiya mai tsawo kafin ya tsaya a bakin wani babban gida, get ɗin gidan coffee ne.
Mamy ta fito mai napep ya ciro mata akwatin, ya ajiye mata kuɗi ta ɗauko masu yawa ta miƙa mishi, mai napep yana ta zabga godiya Mamy hankalinta baya jikinta, gaba ɗaya tunaninta na gurin yaranta.
Mai gadi ya buɗe kofar ta shiga ciki ya biyota da akwatin kayanta, babban gida ne part biyu ɗaya babba ɗaya ƙarami, sai rumfar ajiye motoci.*WANI SHARRIN*
(Mutum ke nemowa kansa)
Channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
*(J.W.A)*
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA✊*
Written by ✍️
Jagabar Jajirtattu
Allahumma salli ala sayyadina Muhammad wassalim.
Chapter 4
Akwai motoci guda uku ajiye a rumfar, Mamy ƙaramin part ɗin ta nufa ta ƙwanƙwasa, ta jima tana ƙwanƙwasa ƙofar sannan taji alamun tafiya.
Kyakkyawar dattijiya ce ta buɗe ƙofar tana tambayar waye, tana buɗe ƙofar taci karo da Mamy tsaye da akwati.
Mamy ta rungume mahaifiyarta tana share hawayen daya zubo mata.
Dattijiyar ta riƙo hannun ta suka shiga ciki Mamy na janye da akwatin kaya, a parlour suka zauna.
Mamy ta ɗaura kanta a jikin mahaifiyarta tana cewa.
"Hajiya dan Allah karki tambayeni komai."
Ruwa ta ɗauko mai sanyi ta miƙa wa Mamy ta ce.
"Sha ruwa kije bedroom ki kwanta."
Mamy ta shanye ruwan ta nufi ɗaya daga cikin bedrooms ɗin dake parlourn.
Bayan kwana biyu da tafiyar Mamy Yusra da Aysar, sun zama marayun ƙarfi da yaji duk wani aikin gidan yaran ke yi, gashi sun hana su zuwa makaranta, Baba kuma baya zama a gidan sai dare yake dawowa, kuskure kaɗan duka.
Gidan Ajwa Sa'idu ya dawo daga kasuwa ya samu bata nan, ya shiga part ɗin mahaifiyarshi ya ajiye ledoji guda biyu ya ce ta ɗau ɗaya ta ajiye wa Ajwa ɗaya, har zai fita mahaifiyarshi ta kira shi.
"Kaci abinci.?" Mahaifiyar shi da suke kira da Mama ta faɗa tana tsare shi da ido.
Sa'idu ya yi shiru bai ce komai ba daman magana bata dame shi ba, ganin ya yi mata shiru bai bata amsa ba yasa ta sanja tambayar ta hanyar cewa.
"Ina matar taka take."
"Daman daman." Mama ta ɗaga mishi hannu ta ce.
"Zauna in zuba maka abinci kaci."
Sa'idu ya zauna daman yunwa yake ji, Mama ta zuba mishi abinci yana ci suna fira.
Sa'idu bai tashi ba sai da aka kira sallar magrib ya yi alwala ya tafi masallaci, kuma har lokacin Ajwa bata shigo gida ba, sai da akai sallar isha'i ya shigo gidan kai tsaye ya wuce part ɗin Mama, tana zaune tana lazumi Sa'idu ya yi mata sallama ya ɗau ledar daya shigo dashi guda ɗaya ya fita.
Ajwa na zaune tana lissafin kaya Sa'idu ya yi sallama ya shigo, tayi mishi barka da zuwa tana ɗauko ruwa ta ajiye a kusa dashi.
" In zuba maka abinci.?" Ta faɗa hankalinta na gurin kayan ta.
" A'a na ƙoshi." Sa'idu ya faɗa yana ajiye mata ledar da ya shigo dashi.
"Bangane ka ƙoshi ba." Ajwa ta faɗa cike da tuhuma.
"Saboda naci abinci a gurin Mama kuma na ƙoshi, sai dai ki dafa mun Lipton domin na san babu a plask." Sa'idu ya faɗa yana kwanciyya a saman kujera.
"Kaje Mama ta dafa maka, tunda har ta iya baka abinci to Lipton ɗin ma sai dai ta dafa maka." Ajwa ta faɗa cike da masifa.
Sa'idu ya ɗauko waya yana dannawa Ajwa haushi kamar ya kashe ta, Sa'idu yana lura da ita amman ya shareta.
Sai da suka zo kwanciyya bacci Sa'idu ya riƙo hannun Ajwa yana cewa.
"Ɗazun na dawo gida bakya nan, kuma baki gaya mun zaki fita ba."
Cike da rashin kunya ta ɗago zata fara masifa, suka haɗa ido da Sa'idu ta kau da kai tana faɗin.
"Kasuwa naje sarin kayan siyarwa, domin na gaji da zaman banza babu sana'a."
"Shi ne bani da arziki da zaki gaya mun zaki je kasuwa, sai dai ki tafi ba tare dana sani ba."
Sa'idu ya faɗa yana matse hannunta dake cikin nashi.
"Uhm nifa bana son ƙorafi wallahi." Ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwace hannunta daga cikin nashi, ammman yaƙi bata damar hakan.
"Sau biyu kina fita ba tare da izinina ba, kuma kin san hakan babban kuskurene mace ta fita ba tare da izinin mijinta ba." Sa'idu ya faɗa yana sakin hannunta.
"Shike nan ba zan fita ba idan ya kama, sai ka dawo ka fara ƙorafi, kafi son in zauna a gida sai ka ce wata akuya." Ajwa ta faɗa tana hararan shi.
"Ajwa Ajwa Akwai sau nawa na kira sunanki.?" Sa'idu ya faɗa a hassale.
"Sau uku." Ta faɗa tana tura baki.
"Wallahi idan kika ƙara fita gidan nan bada izinina ba sai na ɓata miki rai, domin ba zan lamunci wannan gantalin ba." Yana gama faɗa ya shige bedroom ya barta zaune tana ƙananun maganganu.
Haka suka kwanta kowa ya juya wa ɗan uwanshi baya.
Washegari Sa'idu ya bayar da kuɗin cefane ya fita, Mama tayi sallama ta shigo daman jiran Sa'idu ya fita take yi.
Ajwa ta amsa sallamar ciki ciki tana hararan ta, Mama tayi kamar bata ganta ba ta samu guri ta zauna ta fara magana kamar haka.
"A matsayina na uwa wacce ta haifa ta san zafin haihuwa, zan baki shawaran da zata amfaneki." Ajwa tayi shiru tana kallon ta, Mama taci gaba da magana.
"Dan Allah ki daina fita ba tare da izinin mijinki ba, domin Sa'idu mutum ne mai tsananin kishi akan abin da yake so."
"Ƙarata kenan ya kawo gurinki!." Ajwa ta faɗa cike da mamaki.
"Ni ban san abin da ya faru tsakanin ku ba, kawai ina lura da abubuwa da suke faruwa ne, kuma bana jin daɗin hakan shi yasa na ce zan sameki idan ya fita muyi magana dake." Mama ta faɗa tana kallon Ajwa data buɗe baki tana kallon ta.
"Uhm Allah ya raba mu da munafurci." Ajwa ta faɗa tana shigewa ɗaki.
"Lallai yarinyar nan baki da kunya daga faɗa miki gaskiya shi ne zaki kirani da munafuka, to a gurin Talatu na koyi munafurcin mara mutunci wanda bata san arziki ba, wallahi sai na sa Sa'idu ya yi mun maganinki." Mama ta faɗa tana miƙe wa.
"Dan Allah idan ya dawo kisa shi ya rubuta mun takardar saki, ƙarshen dai abin da zaki sashi kenan." Ajwa ta faɗa daga cikin ɗakinta.
Mama tayi ƙwafa tana fita daga part ɗin cike da haushin abin da Ajwa tayi mata.
Da rana Sa'idu ya dawo cin abinci daman kullum a gida yake cin abincin rana, Ajwa na zaune a tsakar gida tana wanke wanke.
Sa'idu ya yi sallama ya shigo Ajwa ta amsa ta cigaba da wanke wanken da take yi, ɗaki ya shiga ya zauna yana jiranta amman shiru babu Ajwa babu labarinta, da ya gaji da zaman sai ya fita tsakar gidan harta gama wanke wanken tana zaune tana danna waya.
"Inata jiranki kizo ki bani abinci amman baki shigo ba." Sa'idu ya faɗa yana ƙare mata kallo
"Baka da labarin yanzu na daina dafa maka abinci a cikin gidan nan.?" Ajwa ta faɗa cike da rainin wayyau.
"Banganeba.?" Sa'idu ya faɗa fuska ɗauke da mamaki.
"Abin da kunnenka ya jiyo maka shi na faɗa." Ajwa ta faɗa tana shiga ɗaki.
Sa'idu zai bita Mama data ke sauraron duk abin da ya faru ta ce.
"Zo muje in zuba maka abincin kaci."
Cike da ɓacin rai Sa'idu yabi bayan Mama kamar yanda ta faɗa, shinkafa da miya ta zuba mishi.
Sa'idu ya kasa cin abincin sai juya spoon kawai yake, domin shi lamarin Ajwa abin tsoro yake bashi.
Mama data fahimci damuwa na son yin tasiri a cikin ranshi ta ringa kawo mishi labarin mahaifin shi, da kuma sauran ƴan uwanshi, a hankali Sa'idu ya cinye abincin duka ba tare da ya lura ba, kawai shafa plate ya yi yaji babu abinci Mama tana ta dariya.
"Tun da an raba girki, saura kuma a raba kwana." Ajwa da tun ɗazun ta shigo ta faɗa.
"Bangane a raba kwana ba mai kike nufi.?" Sa'idu ya faɗa yana jin kanshi na sarawa.
"Jiya ta fanshe ni ta girka maka abinci yauma ta ƙara girka maka abincin, mai ya yi saura da ya wuce a raba kwanan girki a tsakanin mu." Ajwa na gama faɗar hakan Sa'idu ya wanke ta da mari guda uku, yana shirin ƙarawa Mama ta riƙo shi tana yi mishi tsawa.
Ajwa ta fashe da kuka ta fita tana cewa.
"Wallahi tun da ka mareni to ka mari aurenka, domin wallahi na gama zaman aure dakai."
Ajwa ta janyo babban akwati ta haɗa kaya ta nufo gidansu, lokacin Yusra da Aysar na wanke wanke a tsakar gidan.
Ta Batulu ce ✍️..............*WANI SHARRIN*
(Mutum ke nemowa kansa)
Channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g
Group 👇
https://chat.whatsapp.com/LSKW0PJdQ6Z2S2wltDG6oT
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*
*S REZA DATA JOY 30DAYS VALIDITY*
*MTM📶*
1GB-600
2GB_1,200
3GB-1,800
5GB-2,300
*AITEL 📶*
1GB-850
2GB-1,600
3GB-2,440
*GLO📶*
1GB-455
2GB-900
3GB-1,350
Chat 08100785178
Written by ✍️
Sa'adatu Ta Batulu
(Jagabar Jajirtattu)
Allahumma salli ala sayyadina Muhammad wassalim.
Chapter 5
Ajwa tana shigowa a daidai Aysar ya miƙe zai ɗibo ruwa, ta ture shi ya faɗi a kai rashin saa ya faɗi akan hannunshi, hannun sai da ya yi ƙara.
Da sauri Yusra ta miƙe tana kuka ta zura da gudu zuwa room ɗin Baba.
Ajwa tayi tsaki ta shiga room ɗin Inna ko sallama, Baba ya fito Yusra na bin bayan shi.
Aysar na kwance yana kuka Baba ya ɗaga shi, ƙarshe dai sai da aka kai Aysar gurin mai ɗaurin karaya.
Aysar sai da ya suma saboda azaba Yusra sai kuka take yi, bayan an gama ɗaurin hannun Baba ya dawo dashi gida.
Baba ya tambayi Yusra garin yaya hakan ta faru.
"Aunty AJ ne ta ture shi ya faɗi." Yusra ta faɗa a tsorace.
Baba ya tashi rai a ɓace ya nufi ɗakin Inna, yana sallama ya fara faɗa kamar zai haɗa su ya dake su.
"Wannan zaluncin har ina, daga zuwanki gida kin kama yaro kin karya shi saboda mugunta." Baba ya faɗa cike da takaici.
Dukanninsu babu wanda ya motsa ballantana ya yi magana.
"Kuma kizo ki gaya mun abin da ya kawo ki gida, bayan ko wata ɗaya ba kiyi a gidan miji ba." Cewar Baba yana fita daga ɗakin.
Ajwa durƙushe a gaban Baba tana kuka.
"Wallahi idan baki gaya mun abin da ya haɗaki da mijinki ba, sai na ɓata miki rai a gidan nan, mutum ya girma amman har yanzu babu hankali, daga zuwanki gidan ma sai da ya san kin dawo saboda masifarki." Baba ya faɗa yana jin kamar ya rufe ta da duka.
Ajwa ta buɗe baki zata yi magana Baba ya ɗaga mata hannu yana faɗin.
"Ki tabbata duk abin da zaki faɗa babu ƙarya a ciki, domin kin sanni kamar yunwar cikin."
Ajwa ta faɗa mishi yanda suka yi da Sa'idu sannan ta ce.
"Mahaifiyarsa take zuga shi duk abin da yake yi, kuma bata son a faɗi laifinsa."
"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un." Abin da Baba yake ta maimaita wa kenan, domin yama rasa abin da zai ce mata.
Baba ya yi mata nuni da ƙofar fita yana shiga toilet, shi wallahi masifar Ajwa ta fara isar shi, yarinya kamar rainon sheɗan.
Washegari Baba yaje ya samu ƴan uwanshi da maganar Ajwa, domin suje gidansu Sa'idu biko, sun ajiye magana zasu je bayan sallar la'asar Baba daga nan gidansu Mamy ya wuce.
Mai gadi ya shigar dashi parlourn gidan bisa umarnin Hajiya, Baba yana zaune kamar munafuki ya nata raba ido.
Mamy tayi sallama ta shigo Baba ya zuba mata ido cike da kewarta, Mamy ta gaishe shi bayan ta zauna ta ɗaure fuska.
"Dan Allah ki manta da abin da ya faru ki dawo ɗakin ki, ko domin yaranki." Baba ya faɗa yana yin fuskar tausayi.
"Daman da yara kowa yake fakewa domin ya cutar da kai, to wallahi ni har cikin zuciyata na haƙura da zaman aure dakai, yara kuma Allah zai raya su a gidan ubansu." Mamy ta faɗa tana shirin barin parlourn.
Baba ya yi saurin cewa.
" Wallahi idan babu ke yaran nan ba za su iya rayuwa ba, dan Allah kar ki yanke musu jin daɗi."
"Wallahi sai dai su mutu ko kuma ni in mutu, akan dai in koma gidanka in cigaba da rayuwa, dan Allah ka tashi ka tafi kawai domin babu sasanci a tsakanin mu, zaman aure ya haɗa mu da kai kuma yanzu babu wannan auren, to ka bari muyi rabuwar mutunci." Mamy ta faɗa tana barin parlourn.
" Yanzu haka Aysar ya karye a hannu, Yusra kuma ba zata iya jinyar karaya ba." Baba ya faɗa cike da yaƙinin Mamy zata sauko, amman sai yaji tana faɗin.
"Ka kawo mun shi, in yi jinyarsa a nan idan ya warke sai ya koma gida." Mamy ta shige bedroom tana fashewa da kuka, tayi kewar yaranta kuma tana muradin ganinsu, amman bata buƙatar cigaba da zaman aure da ubansu.
"Ki zauna kiyi tunani akan goben ƴaƴanki." Hajiya ta faɗa tana miƙa mata ruwa mai