Showing 9001 words to 12000 words out of 14831 words
Chapter 4 - WANI SHARRIN Hausa Novels By Jajirtattu Writers Association.docx
zama na miji mai gaskiya da adalci." Ta faɗa tana fita daga ɗakin.
Baba ya yi shirin bacci ya kwanta ya bar ɗakin a buɗe domin ya san halin Inna komun dare sai ta dawo.
Inna sai da ta gama gayawa yaranta abin da ya faru, sannan ta dawo ɗakin Baba ta kwanta.
Washegari daman kowa tana yin abin karyawane ita da ƴaƴanta, idan ranar girkin tane zata yi da miji.
Yusra da Aysar sun dawo daga hadda suna shigowa, Zainab ta kama su ta zane Yusra Aysar na ganin haka ya zura da gudu har yana cin tuntuɓe, Mamy na toilet tana wanka, taji ihun Yusra ta ɗauko zani ta ɗaura ta fito a daidai Zainab ta kai mata duka a baya taji an riƙe hannun an murɗe, ta saka ihu tana kururuwa.
"Wallahi wallahi duk ranar da hannunki ya ƙara kai wa jikin ƴaƴana sai na yi miki mugun duka." Mamy ta ce tana yarfar da hannun, ta riƙo ƴarta suka nufi ɗaki.
"Wannan wani irin zalunci ne? Ko dan kinga basa ramawa idan kika dake su shi yasa kike yawan kai hannu jikin su." Mamy bata saurari zan cen da Inna take yi ba ta shige ɗaki wankan da bata ƙarasa ba kenan.
Kamar yanda Inna ta faɗa a rama mata kwana bakwai ɗin data ƙara, sai da aka rama mata sannan aka zauna lafiya, Mamy ta samu Baba da maganar tana son ta kira ma'aikata su fitar mata da toilet a cikin bedroom ɗin ta, ya yi shiru bai ce komai ba har ta gama magana ta fita.
Bayan kwana biyu da maganar Baba ya ɗauko ma'aikata, daman gidan akwai fili sosai aka shigo da filin bayan ɗakin Mamy aka fitar mata da toilet, sannan aka gina mata ɗan ƙaramin kitchen.
Bayan an gama itama Inna aka yi mata kamar yanda na Mamy yake, amman bai gina mata da kitchen ba ya ce ta ɗauki na tsakar gidan ta ringa amfani dashi, babu hayaniyya ko tashin hankali Inna ta amince domin kitchen ɗin tsakar gidan babbane.
Bayan wata biyu cikin Mamy ya shiga wata na shida, Inna ta shiga tashin hankali lokacin data yi ido biyu da cikin, kuma tun daga lokacin ta fara neman hanyar da zata illata Mamy.
Ajwa zaman dai Alhamdulillahi ammanfa maganar yawo bata daina ba, duk da cewar ba kullum take fita ba amman wani lokacin yana fita take ficewa, Mama tun tana magana ta kawo ido ta zuba mata, domin tana yin magana akan ɗanta komai yake ƙarewa.
Yau da sassafe Sa'idu ya fita Ajwa data ke jiran fitarshi itama ta fice, bai jima da fita ba ya dawo gida yana dafe kai, yana kallon ƙofar ɗakin yaga alamun ta fita cike da mamaki yake ƙara kallon ƙofar da kyau.
Da ya gaji da tsayuwa ya zauna a bakin ƙofa yana sauke numfashi a hankali, Mama data ji motsin shigowar shi ta nufo gurin tana tambayar shi ko lafiya.
Sa'idu ya ɗago jajayen idanunshi ya zuba wa Mama ido, da sauri ta riƙo hannun shi tana tambayar shi bai da lafiya ne Sa'idu ya kasa magana.
Ta taimaka mishi ya miƙe ta nufi part ɗin ta dashi, a saman doguwar kujera ta kwantar dashi ta ɗauko ƙaramin roba da ruwa a ciki, ta samu ɗan kwallin kayanta ta tsoma ta ringa matsa mishi a saman kai, a hankali ya ringa sauke ajiyar zuciya.
Sai da taga ya fara dawowa cikin hayyacin shi, sannan ta zubo mishi faten dankalin turawa ɗan kaɗan yasha ya kau da kai, maganin zazzaɓi ta ɗauko ta bashi yasha bai jima ba ya yi bacci.
Sa'idu sai azahar ya farka lokacin babu zazzaɓin sai dai rashin ƙarfi, a toilet ɗin parlourn ya yi alwala Mama ta shimfiɗa mishi darduma ya yi sallah.
Har bayan sallar magrib Sa'idu yana tare da Mama, kuma sai a lokacin Ajwa ta dawo shima dan tana tsoran Sa'idu ya riga ta dawowa ne.
Kuskus ta dafa daman tana da miya tayi wanka ta zauna tana jiran Sa'idu, har bayan sallar isha'i bai dawo ba cike da mamaki take duba lokaci domin ta san bai saba kaiwa dare a waje ba.
Data ga ƙarfe goma daidai ta miƙe ta nufi part ɗin Mama cike da tunanin yanda zata kasance tsakanin su.
Da takalmin Sa'idu ta fara cin karo a bakin ƙofa, Ajwa ta lallaɓa ta cire takalmi ta leƙa window ɗin parlourn Sa'idu yana kwance yana bacci a saman kujera Inna tana zaune a saman darduma tana lazumi.
Tayi ƙwafa tana fita daga part ɗin tana shiga ɗaki ta kulle tayi kwanciyar ta, Sa'idu bai farka ba sai sha biyu saura ya miƙe yana salati.
"Ya kake jin kan naka yanzu.?" Inna dake zaune saman darduma ta faɗa.
Sa'idu ya ce.
"Da sauƙi sosai."
"Ka tafi part ɗin ku idan Allah ya kaimu inada magana da kai." Mama ta ce tana mayar da hankalinta gurin Qur'anin dake gefenta.
"Allah ya tashe mu lafiya." Sa'idu ya faɗa yana fita daga ɗakin.
Sa'idu ya jima a bakin ƙofa yana ƙwanƙwasawa amman shiru, ya kira wayarta yaji a kashe kuma yana tsoran ya buga da ƙarfi kar Mama taji, ganin babu mafita yasa ya fara kiran sunan Ajwa, tana jinshi tayi banza dashi sai da ya kusa yin awa ɗaya a tsaye sannan yaji maganarta tana cewa.
"Dan Allah baku ji kunyar kanku ba, ace mutum da matarsa amman kin hana shi zuwa wajenta, saboda shegen sa ido da gulma."
Sa'idu ya ce.
"Ajwa na rantse da Allah idan baki bar wannan maganar ba na shigo sai ranki ya yi mugun ɓaci." Ya faɗa yana jin kamar ya kamata ya yi mata mugun duka.
"Ƙofa dai ba zan buɗe ba, wallahi sai dai ka koma ka kwanta a can." Ta faɗa tana komawa bedroom.
Sa'idu ya dafe kai cike da takaici, da sauri ya dafa aljihun shi makullayen shagon shi ya ciro daman akwai na ɗakin a ciki, kuma yaga alamun ta kulle da key ne ta ciki.
Yana gwadawa ƙofar ta buɗe ya faɗa ɗakin a fusace.
Free pages sun kusa ƙarewa.
Ta Batulu ce ✍️.................*WANI SHARRIN*
(Mutum ke nemowa kansa)
Channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*
*ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYADINA MUHAMMAD WASSALIM*
Written by ✍️
Sa'adatu Ta Batulu
(Jagabar Jajirtattu)
Bismillahir Rahamanir Raheem.
Chapter 9
Ajwa tana kwance taji Sa'idu ya faɗo ɗakin da sauri ta manne ƙarshen gado jikinta na rawa, ganin bai ganta a parlour ba yasa ya shiga bedroom ɗin a can ƙarshen gado ya hangota.
Ganin yanda jikinta yake rawa yasa shi runtse ido yana cije baki, Ajwa ta firgita da yanda ta ganshi duk da cewar idan ran shi ya ɓaci daman hakan yana faruwa.
Ganin idon sa a rufe yasa ta lallaɓa ta fice a ɗakin, Sa'idu yaji fitar ta kuma bai hanata ba domin idan ya ce zai yi magana wallahi zai iya karyata ba tare da ya sani ba.
Bai ƙara bi ta kanta ba sai da yayi wanka ya shirya kwanciyar bacci, ya kira wayarta bata ɗaga ba kuma ya san tana ganin kiran, ya miƙe ya nufi bedroom ɗin da yake da ya ƙinin tana ciki, yana turawa ya ƙofar ya buɗe domin ta san kota kulle sai ya buɗe.
Tana kwance tana chart taji motsin shi da sauri ta kifa wayar ta rufe ido, ya zauna kusa da ita yana kiran sunanta.
Ganin zata ɓata mishi lokaci yasa ya fara abin da ya kawo shi, Ajwa da sauri ta miƙe tana ture shi cike da masifa.
Dambe iya dambe suka ci da Sa'idu kafin yasa mata ƙarfi ya danneta, ya gama abin da zaiyi ya tashi ya fita Ajwa na kwance tana tsine mishi, haka zaman nasu ya cigaba da kasancewa kullum cikin yawo take idan yayi magana ta ce kasuwanci take yi.
Inna ta sanja salo duk lokacin da taga Mamy ta fito zata shiga toilet ko ɗakin Baba, sai tazo da sauri ta bangajeta ta wuce wani lokacin tana zaune a parlour zata ji an watso mata ruwa ko kuma a turo mata da shara, idan tayi magana masifa domin Baba yanzu sai abin da Inna ta ce yake yi.
Bayan sallar azahar dukkan su suna zaune suna fira a tsakar gida, Inna ta kalle su ta ce.
"Ina son kuje gidan Tani kuja mata kunne, idan kuma taƙi ji kuyi mata kashedi yanda zata fahimta." Zainab ta riga su miƙewa ta ɗauko musu hijjabai suka fita Inna tana faɗin.
"Wallahi ku tabbatar kun nuna mata cewar ku jinin Talatu ce." Mamy na zaune a bakin ƙofar ɗakin ta, ta miƙe tana cewa.
"Allah ya kyauta." Inna daman jiran ƙiriss take yi ta fara masifa tana zage zage, Mamy ta janyo net ɗin ta rufe ta ciki.
Inna tana cigaba da masifa bakinta har kumfa yake yi, Zainab ta shigo ta zauna Inna tana shirin tambayarta sauran suka shigo, bayan sun zauna suka bata labarin abin da ya faru Inna ta kwashe da dariya suka tafa da yaran cike da alfahari.
Abin da ya faru bayan sunje gidan Tani cike da rashin kunya Zainab ta fara magana.
"Ke baƙar munafuka algunguma tsohuwar ala wadai, wallahi idan kika ƙara shiga sabgar uwar mu sai mun naɗa miki dukan da sai kin kusa zuwa lahira, tsohuwar kawai wacce bata kama girmanta." Kowanne da cin mutuncin da yayi mata, Asabe jikan Tani dake bacci ta fito tana mayar musu da amsa, suka haɗu su kai mata duka sai da suka ga bata motsi sannan suka fita Zainab ta lakace wa Tani hanci A'isha ta dungureta.
Inna sai da tayi rawa saboda murna Mamy tana bedroom bata san waina da ake soyawa ba, daddare Baba ya dawo gida daman girkin Mamy ne ta gama komai ta nufi ɗakin shi Inna na zaune tana kallo Baba yana cin abinci, Mamy ranta ya ɓaci domin idan ita ce wallahi babu zaman lafiya, amman haka ta daure tayi sallama ta shiga toilet.
Bayan ta fito daga toilet ta cire hijjab ɗin jikinta ta nun ke Baba da ya kalleta da sauri ya haɗiye abincin yana tari, Inna haushi kamar ya kashe ta ganin ɗan iskan shigar dake jikin Mamy.
Kiran wayar Baba ya dawo dashi cikin hankalinsa yana ɗaga kiran ya yanke, ya ajiye wayar ya shiga toilet bai jima da shigaba suka ji sallamar ɗan yaro a tsakar gida yana cewa.
"Zainab Khadijah A'isha an ce su zo ana kiransu a waje." Yaron yana faɗa ya zura da gudu, Inna tayi shewa tana faɗin.
"Ƴaƴa mata masu farin jini." Ta hararari Mamy ta fita, babu tambayar wanda yake kiran ta basu umarnin su fita bayan sun shafa turare da powder.
Har ƙarfe goma babu labarin yaran Inna hankalinta ya fara tashi amman ta ce bari zuwa sha ɗaya da rabi idan basu dawo ba sai taje ta duba ko lafiya, tana zaune tana zan cen zuci har sha biyu saura.
Inna ta fita zuwa ɗakin Baba tana zuwa ta shiga dukan ƙofar kamar ba dare ba, tana zaune a saman darduma tana karatun Qur'ani tayi banza da ita cike da takaicin wannan masifar, Baba ya ringa jin bugun ƙofa tun ana bugawa a hankali har ta fara bugawa da ƙarfi, yayi tsaki ya sauko daga gadon ya ɗau jallabiya yasa yana faɗin.
"Dan Allah ki bar dukan ƙofar nan karki karya, sai ka ce ba dare ba."
Inna tayi ƙwafa tana cigaba da dukkan ƙofar Baba ya buɗe yana ɗaure fuska, cikin tashin hankali ta fara magana.
"Tun ɗazun yara sun fita zan ce har yanzu basu dawo ba, kuma na leƙa ƙofar gida amman banga kowa ba."
Baba ya ce.
"Bangane yara sun fita zan ce basu dawo ba.?"
"Dan Allah kazo kaje ka dubo su, wallahi wannan shirun bana lafiya bane." Inna ta faɗa tana fashewa da kuka, Baba ya ture Inna ya fita.
Ƙarfe ɗaya dai-dai ya dawo gida hankalin shi duk ya tashi, Inna tana jin shigowar shi ta fito tana tambayar ko ya gansu, ya kwantar mata da hankali akan ta bari zuwa gobe idan Allah ya kaimu, Inna ta fara masifa tana kuka ita wallahi Mamy ce tasa a sace mata yara.
Ranar babu wanda yayi bacci saboda masifar Inna, Mamy data ga abin babu sauƙi ta koma ɗakinta gurin yaranta ta kwanta, Baba a zaune ya kwana yana rarrashin Inna.
Washegari Baba tun da ya tafi sallar asuba bai dawo gida ba, ƙarfe goma akai sallama a ƙofar gida Inna ta miƙe ido duk ya kumbura ga rashin bacci ga kuka.
Matashi ne sanye da uniform ɗin ƴan sanda Inna ta dafe ƙirji tana salati, matashin ya gaisheta bai jira amsarta ba ya buƙaci su tafi, officer ana nemanta Inna ta ruɗe tana faɗin wallahi babu inda zata je.
Ganin babu sauki kuma tana ta zagin shi ya ɗaga ya bayar da umarnin shigowa, matane guda uku sanye da uniform ɗin ƴan sanda suka tasa ƙeyar Inna, Mamy tana fitowa motar na tafiya koda ta leƙa bata ga kowa a ƙofar gidan ba.
Sai da akai la'asar Baba ya dawo gida yayi zuru-zuru da ido kamar wanda ya tashi daga jinya, Mamy ya umarta data juye mishi ruwan flask yayi wanka.
Sai da yayi wanka ya zauna yana tambayarta Inna, domin tunda ya shigo bai ji motsinta ba Mamy ta ce bata san inda take ba.
Baba ya kasa cin komai saboda tashin hankali, ya bayar da kuɗin cefane sannan ya miƙe ya fita.
Yana fita ya samu wani mutum tsaye yana neman yaron da zai aika, ganin Baba ya fito suka gaisa mutumin ya ce.
"Dan Allah ina neman Alhaji Usman ne."
"Lafiya dai koh.?" Baba ya faɗa yana ƙare mishi kallo.
Two days zazzabi kuyi maneji da wannan.
Ta Batulu ce ✍️*WANI SHARRIN*
(Mutum ke nemowa kansa)
Channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*
*ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYADINA MUHAMMAD WASSALIM*
Free pages sun kusa ƙarewa.
Written by ✍️
Jagabar Jajirtattu
Chapter 10
Mutumin ya ce.
"Ana nemanka a officer ɗin mu dake can kan tudu."
Baba zai yi magana mutumin ya katse shi ta hanyar faɗin.
"Ba wani abin damuwa bane." Baba yayi shiru suka nufi bakin titi suka hau napep, suna shiga cikin police station ɗin Baba ya dafe ƙirjin shi yana faɗin.
"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un." Ya ringa mai mai tawa har sai da ya samu natsuwa sannan ya shiga officer ɗin da aka nuna mishi.
Wani babban mutum ne zaune a kujera yana sanye da uniform ɗin ƴan sanda Baba yayi sallama ya shigo, bayan sun gaisa cikin mutunci officer ya kalli mutumin da suka shigo da Baba ya ce.
"Shigo dasu."
10 minutes Zainab ta shigo Khadijah A'isha Inna suka shigo officer ɗin duk sunyi zuru zuru, Baba ya miƙe cike da mamakin abin da ya kawo su police station.
"Maine ne alaƙarka da wa in nan mutanen.?" Officer ya faɗa ba tare da ya ɗago ba.
"Iyalina ce da ƴaƴana." Baba ya faɗa muryan shi tana rawa.
"Sunje gidan mutane sunyi rigima har dambe." Officer ya faɗa yana tsare Baba da ido.
Kafin Baba yayi magana officer yaci gaba da cewa.
"Yanzu haka yarinyar da suka daka tana hospital akwance bata sanin wanda yake kanta."
An dinga ɗauki ba daɗi kafin Baba ya shawo kan officer ya bayar da belinsu, shima sai da aka kira saurayin Asabe domin shi ya shigar da ƙaran, bayan an bayar da belin officer yayi musu iyaka da gidan Tani, kuma dole Baba ya ɗau nauyin Asabe har zuwa lokacin da zata warke.
Suna fitowa daga police station ɗin yayi gaba abin shi duk yanda Inna take kiran shi bai tsaya ba napep ya tsayar zuwa gurin sana'ar shi.
Inna a ƙafa suka dawo gida suna tafe tana tsinewa Baba yaran suna taya ta, babu sallama suka faɗa gidan kowace tayi zuru zuru kamar masu ciwo.
Mamy tana zaune a ƙofar ɗakinta suna karatu da yara, bata ce musu komai ba suma basu kulata ba.
Inna ta kunna wuta ta ɗaura ruwan zafi domin tun a hanya Zainab ta bata labarin irin dukan da suka sha, kuma ko Zainab ɗin bata faɗa ba Inna taga tabon bulala ajikin yaran.
Kowacen su tayi wanka ta gasa jikinta bayan sun fito sun shirya Inna ta zubo musu taliya a babban plate, suka shimfida babban tabarma aka zauna suna cin abinci suna zagin Tani da Asabe.
Bayan sati ɗaya sun warware sun cigaba da harkokin su Inna ta ce su shirya ta aike su gidan ƙanwarta Ladi, bayan la'asar Mamy ta fito zata shiga toilet Inna tana zaune a tsakar gida ganin Mamy ta shiga toilet yasa ta miƙe ta ɗau buta ta tsaya a bakin ƙofa tana jiran ta fito.
Mamy na fitowa Inna ta bangajeta sai da ta kusa faɗuwa da sauri ta ce.
"A'uzubillahi minal shaiɗanin rajin." Inna dake cikin toilet ta fito da sauri tana cewa.
"Wanene shaiɗanin?."
Mamy ta raɓata zata huce Inna ta riƙota tana faɗin.
"Wallahi sai kin gayamun wanene shaiɗani."
"Sakin mun hannu bana son tashin hankali." Mamy ta faɗa fuska cike da ɓacin rai.
"Idan naƙi saki fa." Inna ta faɗa tana ƙara riƙe hannun da kyau
"Zan shayar dake mamakin da ba a taɓa shayar dake ba." Faɗin Mamy tana jin kamar ta rufe Inna da duka.
Kafin Mamy ta rufe baki Inna ta dunƙula hannu ta kai mata duka a ciki, da sauri Mamy ta tare tana ƙwace hannunta.
Inna ta ringa yunƙurin dukan cikin ganin abin bana hankali bane Mamy tasa dukka karfinta ta bangaji Inna ta huce ɗaki.
Tana shiga Inna na biyota dambe iya dambe, Mamy damuwarta karta illata mata cikin dake jikinta ganin dai ta kasa cin nasara akan Mamy yasa ta rarumo ludayi ta bugawa Mamy a kai gurin ya fashe jini ya fara fita, cikin ficewar hayyaci Mamy taji hannunta ya riƙo wani abu bata tsaya dubawa ta bugawa Inna a