Showing 6001 words to 9000 words out of 14831 words

Chapter 3 - WANI SHARRIN Hausa Novels By Jajirtattu Writers Association.docx

sanyi.

"Tsawon lokacin nan ban taɓa zuwa na gaya muku, halin da nake ciki ba Hajiya dan Allah karku ce dole sai na koma gidan shi." Mamy ta faɗa tana dafe kai.

"Wallahi ba zan taɓa yi miki dole ba, amman ina son ki zauna da kanki kiyi tunanin makomar rayuwar ƴaƴanki, kafin ki yanke hukunci kiyi tunanin yanda goben yaran zata kasance." Hajiya ta faɗa tana fita daga room ɗin.

Baba ya koma cike da damuwa domin bai taɓa tunanin Mamy zata ƙi amincewa ba, amman ya yi alƙawarin wallahi duk inda zasu je sai dai suje amman ba zai taɓa sakin taba.

Yana shiga gidan ya ƙara cin karo da wani sabon tashin hankalin, Ajwa ne take ta dukan Yusra ƴan uwanta na ƙara zuga ta.

Ganin basu lura da tsayuwar shi ba kuma tana cigaba da dukanta, ya yi gyaran murya.

    Da sauri ta yar da bulalar tana sosa kai Baba ya miƙar da Yusra yana share mata jikinta, Baba ya kalli bakin Yusra da ya fashe yana jini, ruwa ya ɗauka ya wanke mata bakin suka nufi ɗakin Mamy.

Aysar na ganin Yusra ya fashe da kuka yana faɗin.

"Ni dai ki kaini gurin Mamy na."

Baba ya zauna a tsakiyar su yana rarrashin su, shima lamarin gidan nan wallahi ya fara isar shi, mafita kawai yake nema domin ya gaji.

Sai da ya tabbatar da sunyi shiru sannan ya tambaye su ko sunci abinci, Yusra ta faɗa mishi basu ci komai ba tun safe.

   Baba yaji damuwar shi ta ƙara zama sabuwa, domin shi bai da labarin duk abin da yake faruwa.

Cike da dubara ya ringa tambayar yaran duk abin da ke faruwa a gidan, Aysar ya faɗa mishi komai, Baba jin irin abubuwan da yaran ke fuskanta yasa shi jin ƙwarin gwiwar mayar da Mamy ɗakin ta, ko ba dan komai yaran suna buƙatar kulawarta.

Baba ya fita ɗakin ya tsaya a tsakar gida yana kiran yaran gaba ɗaya.

Ta Batulu ce✍️............................ 08138098887 WhatsApp only*WANI SHARRIN*

(Mutum ke nemowa kansa)

Channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*

*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*

Written by ✍️

Sa'adatu Ta Batulu

(Jagabar Jajirtattu)

*ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYADINA MUHAMMAD WASSALIM*

Chapter 6

Ɗaya bayan ɗaya suka fito suna duƙar da kai, Baba ya kalli Ajwa ya ce.

"Ki shirya anjima zaki koma ɗakin ki."

Ta turo baki tana ɓata fuska ya yi kamar bai ganta ba, domin yanda yake ji wallahi zai iya zane ta saboda haushinta yake ji.

"Duk cikin ku babu wanda aka taɓa yiwa horan yunwa a gidan nan, amman shi ne zaku ringa hora ƙananun yara da yunwa koh.? Saboda kun zama mugaye marasu tausayi, to daga yau ba zan ƙara ɗaukar wannan iskancin ba, idan kuma kun ƙi ji wallahi zan ɗauki mummunar mataki akan ku." Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba.

Daga ƙarshe ya jefa musu dubu ɗaya yana umartar su.

"A dafa mun macaroni da kifi yanzu." Yana gama faɗa ya bar gidan gaba ɗaya.

Ajwa ta riƙe baki tana cewa.

"Yaushe Baba ya zama hakan.?"

"Tun bayan tafiyar Inna." A'isha ta faɗa tana ɗaukar dubu ɗayan.

Suka dafa macaronin gaba ɗaya gida, saboda ba zasu iya tambayar shi kuɗin cefane ba.

A ɗan ƙaramin roba suka zubawa Yusra da ƙaninta.

Yusra ta fito tana raɓe raɓe Ajwa ta janyo ta.

"Shegiyya mai baƙin hali irin na uwarta." ta faɗa tana hararan ta, ita fa a rayuwar ta wallahi ta tsani wannan yarinyar.

Sai da ta gama zaginta sannan ta miƙa nuna mata robobin abincin su tana faɗin.

"Dangin mayu ɗauka kar ku cinye mu ɗanye."

"Sai dai ko ubanki shi ne dangin mayun." Baba ya faɗa yana shigowa gidan.

Yusra ta ɗau abincin ya kirata ya kalli ɗan abincin dake roban, ƙwafa ya yi yana shiga ɗakin shi.

Yusra data kusa shiga ɗakinsu Ajwa ta dakatar da ita tana faɗin.

"Dan ubanki zoki ɗauki abincin nan ki kai mishi." Ta ta dawo ta ɗau flask ɗin ta shiga ɗakin haɗe da sallama.

Baba ya ƙirƙiro murmushi yana tambayarta jikin Aysar, tayi murmushi tana cewa.

"Da sauƙi." ta ajiye ta flask ta fita.

Abincin su ta ɗauka ta shiga ɗaki Aysar yana kallon ɗan abincin ya fashe da kuka, ta ƙara mishi da nata sannan ya yi shiru, ta zuba mishi ido tana tuna maganar da Mamy ta gaya mata ranar da zata bar gidan, taji an dafa ta.

"Haba yarinyar kirki tunanin mai kike yi inata sallama ko motsi baki yi ba Aysar nata miki surutu kin yi banza dashi."

"Baba dan Allah ka kaimu gurin Mamy, ko kuma ka ce mata ta dawo." Yusra ta faɗa tana fashewa da kuka.

"Ko ɗazun naje gidan Mamyn kuma ta ce tana nan dawo in sha Allah." Bayan ya faɗi maganar ya kau da kai.

Sai da ya tabbatar sunyi shiru sannan ya ajiye musu flask ɗin abincin shi, Yusra ta ɗauko babban plate ta zuba musu abincin rabi, suka zauna suna ci Baba yana bawa Aysar a baki.

Hannu baka hannu ƙwarya haka ta ringa cin abincin, daga ƙarshe Baba ya cire hannunshi ya zubawa Yusra ido.

Kaɗan suka rage abincin Baba ya rufe ya ajiye ta gyara gurin Yusra.

"Kuje kuyi alwala kuyi sallah zan tafi masallaci, sannan ku rufe ƙofa idan na dawo zanyi magana sai ku buɗe." Baba ya ce yana fita daga ɗakin.

Bayan an idar da sallah ƴan uwan Baba suka kira shi a waya suka sanar dashi suna jiranshi a gida.

A zaure Baba ya gansu suna tsaye.

"Ya baku shiga gidan ba kuka tsaya a waje?."

Baba ya faɗa cike da mamaki.

"Daman akwai mutane a gidan.?"

Isiya ya faɗa cike da mamaki, Baba jin hakan bai ƙara cewa komai ba ya shiga gidan suka bishi a baya.

Bayan sun zazzauna suka faɗa mishi abin da ya faru, bayan sunje gidan iyayen Sa'idu.

"Yanzu babu yanda za a ɓullowa lamarin.?" Baba ya faɗa yana jin tashin hankalin sa na ƙaru, domin wallahi zaman Ajwa a gidan shi babu alkhairi.

"Duk yanda zamu shawo lamarin abin yaƙi domin mahaifiyar Sa'idu ta ɗauki zafi sosai, maganar gaskiya dole ne su ɗau zafi da lamarin, yarinya sai ka ce ana kaɗata da ruwan hanji." Isiya ya faɗa cike da takaici,

Baba dai ya yi shiru yana sauraron su.

Haka dai suka tafi babu wata magana mai daɗi, domin dai mahaifiyar Sa'idu ta ce lallai sai sun ko yawa ƴarsu hankali sannan zata cigaba da zaman aure da Sa'idu.

Ajwa duniya sabuwa ta buɗe da zaran Baba ya fita kasuwa zata fice maƙota, sai lokacin data san yana gab da shigowa gida take dawowa.

Hajiya ta turo ƴaƴanta su duba Aysar da jiki, lokacin da za su tafi yaran suka fashe da kuka suna roƙonsu dan Allah su tafi dasu, Baba yana kasuwa Hajiya ta kira shi ta faɗa mishi yanda ake ciki, sannan ta roƙi alfarmar ya barsu su zo suga mahaifiyarsu ƙila idan ta gansu hankalinta ya dawo jikinta.

Baba ya yi na'am da maganar surukar shi, suka haɗawa yaran kaya suka kulle ƙofar suka tafi dasu.

Lokacin da Mamy taga yanda yaran suka koma, kuka ta ringa yi domin gaba ɗaya sun fita hayyacinsu, lokacin l'''da suka zo cin abinci taga yanda suke ci kamar mayunwata, bata iya zama a gurin ba ɗaki ta koma.

Hajiya ta ɗibo abinci ta biyota dashi, sai da ta tabbatar taci abincin ta ƙoshi sannan ta ce.

"Kinga makomar rayuwar ƴaƴanki, kinga abin da nake ta gaya miki koh,? Bana matsa miki bane amman ina son ki gane gaskiya, duk lalacewar zubar ɗaki wallahi yafi waje."  

Hajiya harta kai bakin ƙofa sannan ta tsaya.

"Idan kin zaɓi ki zubar da rayuwar yaranki, to shi kuma wanda bai zo duniyar ba yaya makomar tashi rayuwar." Hajiya ta faɗa tana janyo mata ƙofar .

Mamy a zabure ta miƙa tana maimaita zancen ƙarshe da taji Hajiya ta faɗa.

Tashin hankali wanda ba a saka mishi rana, shin mai Hajiya take nufi da wannan zancen, shine abin da Mamy take mai maitawa.

"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ba dai ciki bane a jikina." Mamy ta faɗa tana tuna last period ɗinta.

Ta Batulu ce ✍️...............*WANI SHARRIN*

(Mutum ke nemowa kansa)

Channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g

Channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029Vb6euGfDTkK50GtWht0G

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*

*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*

*ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYADINA MUHAMMAD WASSALIM*

Written by ✍️

Sa'adatu Ta Batulu

(Jagabar Jajirtattu)

Chapter 7

Mamy ta dafe ciki tana jin zuciyarta kamar zata fashe, Hajiya ba zata fahimci irin rayuwar da take fuskanta a gidan aurenta ba, kuma ba zata iya faɗa musu halin da take ciki ba, koba komai shiɗin uban ƴaƴanta ne.

Ganin tunanin babu mafita ta fita ta aiki yarinyar dake musu wanke wanke, ta siyo mata PT.

Ba a jima ba ta dawo da aiken da akai mata Mamy ta karɓa ta shiga toilet, tabbas ya nuna mata jan layi, amman bata yarda ba.

Haka ta yini cike da fargaba da tashin hankali, bayan kwana biyu ta shirya ta tafi hospital gwajin farko ciki ya bayyana a jikinta watan shi huɗu, hankali tashe ta dawo gida domin ta san komawarta gidan Abban Yusra ya zama dole.

Tana shiga parlour ta fashe da kuka tana ɗaura kanta a jikin Hajiya, Isma'il babban yayansu ya karɓi takardar hannunta, ita dai Hajiya tana zaune tana murmushi domin ta fahimci dalilin kukan.

Yusra ta shigo parlourn bakinta ɗauke da sallama Mamy tayi saurin share hawayen fuskarta  tana murmushin da yafi kuka ciwo, Hajiya ta umarce ta su shiga daga ciki za suyi magana da Isma'il.

Bayan kwana uku da ƙyar Mamy ta koma ɗakinta, Hajiya ta siya mata fridge da keken ɗinki Isma'il ya yi alƙawarin sanja mata kayan ɗaki, a ranar data koma Baba ya tasa Ajwa a gaba ya rakata gidan mijinta, domin ya san in dai ya barta a gidan to wallahi za a samu matsala domin Mamy bata ɗaukar iskanci, akwai lokacin data zagi Mamy ta kamata ta zane ta aka ringa rikici da ƙyar ya shawo kan matsalan.

Daƙyar mahaifiyar Sa'idu ta haƙura shima wallahi saboda ganin idon Baba ne, ko mutuwa na kunyar ɗa da mahaifi, Ajwa ta duƙa ta nemi gafararta kamar yanda ya umarce ta.

Bayan ta bata haƙuri ya tasata har ɗakinta yana rarrashinta, domin Ajwa sai rarrashi bata jin faɗa hasalima idan kayi mata faɗa akan abu gobe sai tayi wanda ya fishi, tayi mishi alƙawarin zaman lafiya da mijinta yaji daɗi sosai yana ta saka mata albarka.

Koda ya bar gidan Ajwa gurin ƴan uwanshi ya nufa ya faɗa musu abin da ya faru har tafiyar Mamy gida, suka ringa mishi faɗa suna nuna mishi kuskuren shi, sun jima suna fira sai da akai sallar magrib da isha'i sannan ya nufo gida.

Ya leƙa bedroom ɗin Inna suna zaune suna cin abinci, ya fita ya leƙa Mamy tana zaune tana karatun Qur'ani Yusra na rubutu Aysar na game, ya shigo ya zauna kusa da yaran  suna  fira Mamy ta yi addu'o'i ta shafa.

Ba a jima ba yaran su kai bacci ta ɗau Aysar ta shiga dashi Baba ya ɗau Yusra ya bita, bayan sun kwantar dasu Mamy ta zauna tana shafa cream daman wanka ta fito, yana tsaye yana musu addu'a yaji ƙamshi mai daɗi yana ratsa zuciyarsa, ko kafin ya juyo Mamy ta hau gadon ta kwanta a gefen su.

"Banganeba." Ya faɗa cike da mamaki.

  Tayi kamar bata ji abin da ya faɗa ba ta janyo blanket ta rufe musu jiki tana addu'ar bacci.

"Dan Allah kar muyi haka dake haba matar kirki, matar aljanna." Sai dai kuma har ya gama magana bata motsa ba, ganin hakan ya nufo hanyar fita daga room ɗin yana cewa.

"Ki dafa mun Lipton yanzu ki kawo mun." Ya faɗa yana fita da sauri,  Mamy ta dafe kai cike da takaici ta gyara kwanciya tana ƙara rufe jikinta.

Kamar ba zata tashi ba ta miƙe tana tsaki tana cewa.

" Ni wallahi bana son damu, baccin ma baza a bari mutum ya yi cikin kwanciyar hankali ba."

Ta haɗa Lipton kamar yanda ta san yana buƙata, ta ɗauko hijjab ta ɗaura a saman sleeping dress ɗin jikinta, kofar ta kulle ta nufi room ɗin Baba.

Yana ganin shigowar ta ya karɓi cup ɗin hannunta yana jin ƙaunarta na ƙara ratsa sassan jikin shi, ganin tana shirin juyawa ya riƙo hannunta ya zaunar da ita, ya fara magana cike da rarrashi da kulawa.

"Ni dai ban san ta inda zan fara ba, domin na san ni mai laifine a gurinki, dan Allah dan Annabi kiyi haƙuri karki ce komai, kuma in sha Allah daga wannan lokacin hakan ba zai ƙara faruwa ba."

Gaba ɗaya ya riga ya ɗaureta da jijiyoyin jikinta, ba dan ta amince da hakan ba ta nuna mishi komai ya riga ya wuce, Mamy a ɗakin ta kwana.

Bayan sati ɗaya da dawowar Mamy suna zaune lafiya da mijinta, daidai gwargwado tana kawar da kai a lamarin yaran shi kuma hakan ya yi mishi daɗi sosai, sai dai kuma a ranar Inna ta dawo satin ta uku a can.

Yaran sun yi murna sosai ganin mahaifiayarsu, bayan ta huta taci abinci suka fara bata labarin abin da ya faru, tunda suka fara magana take murmushi har suka gama, Mamy tayi sallama ta tsaya daga bakin kofa suka gaisa da Inna tayi mata ya gajiyar hanya, daga haka ta koma ɗakinta Inna ta bita da kallo cike da tuhuma.

Da daddare Baba ya dawo gida cike da farin ciki, amman ganin Inna a tsakar gida yasa yaji gabansa ya faɗi, Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un haka yake ta mai mai tawa har ya samu natsuwa.

Ina tayi dariya tana yi mishi barka da zuwa ta amshi ledar hannunshi ta nufi room ɗin shi, Baba ya saki baki da hanci yana kallon ikon Allah.

Ɗagowar da zai yi suka haɗa ido da Mamy dake fitowa daga toilet, daman akwai hutar nepa, tayi murmushi tana wucewa ta gabanshi, ƙamshin turaren ta ya yi mishi sallama ya lumshe ido cike da muradin matarsa, sai dai kuma ya san hakan ba abu ne wanda zai yiwu ba.

Ganin tsayuwar ba zata fishe shi ba ya nufi room ɗin shi yana waigen Mamy data jima da shiga ɗaki.

Inna tana zaune tana kallo a TV ya yi sallama ya shigo, yana shigowa tayi mishi barka da zuwa sannan ta ce.

"Na haɗa maka zoɓo irin wanda kafi so." Tana gama faɗa ta fita.

Baba ya juye ruwan flask ɗinshi ya yi wanka, har ya gama ya fito Inna bata shigo ba ya samu kaya marasu nauyi yasa ya zauna yana ƙure gudun fanka, lokacin zafi ne kuma baya son zafi ko kaɗan.

Inna tayi sallama ta shigo hannunta ɗauke da plate, ta ajiye cups ne guda biyu a saman plate ɗin Baba yana ganin zoɓob yaji yana sha'awar yasha, Inna ta miƙa mishi guda ɗaya tana shirin zama ya tambayeta abinci.

Ta ɓata rai tana cewa.

"Abinci kuma, koka manta yau na dawo garin.?"

"Tunda baki dafa abincin ba kije ki kiramun wanda take da girki ta bani abinci." Ya faɗa yana ajiye cup ɗin.

Cike da takaici da baƙin ciki Inna ta fara magana.

"Wannan ai cin fuska ne da tozarci, ta yaya zaka ce inje in karɓo maka abinci bayan kuma na karɓi girki."

"Ikon Allah." Baba ya faɗa cike da mamaki.

"Wallahi babu abincin da zanje in karɓo maka, kuma dole a rama mun kwana bakwai ɗin dana ƙara."

"Wai dan Allah Talatu kina da hankali.?"

"A'a ban dashi sai dai ka bani naka." Baba ya fita daga ɗakin Inna tayi ƙwafa tana cewa.

"Wallahi duk inda zaka je zaka dawo ka same ni."

Room ɗin Mamy ya nufa ya ƙwanƙwasa yana faɗin.

"Raliya." Mamy jin muryanshi ta buɗe ƙofar daman tana zaune ne tana karatun Qur'ani.

"Akwai abinci ki bani.?" Baba ya faɗa yana zama a kujera.

"Eh akwai." Ta faɗa tana janyo flask ɗin abincin shi, daman tayi girkin gaba ɗaya na gidane sai bayan ta gama girkin ta fahimci nufin Inna shi ya sa ma bata kai mishi abincin ba.

Ta zuba mishi shinkafa da miya ta buɗe fridge ta ciro jug mai ɗauke da zoɓo, Baba ya yi bismillah yana cika bakin shi da abinci, ya kusa cinyewa suka ji an daki ƙofar da ƙarfi kamar za a karya.

Ta Batulu ce...................... ✍️*WANI SHARRIN*

(Mutum yake nemowa kansa)

Channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g

*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*

*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*

Wannan page ɗin sadaukarwa ne ga duk mahaifiyar dake son farin cikin ƴaƴanta.

*ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYADINA MUHAMMAD WASSALIM*

Written by ✍️

Sa'adatu Ta Batulu

(Jagabar Jajirtattu)

Chapter 8

Inna tana shigowa ta cakumi hijjab ɗin jikin Mamy tana cewa.

"Wannan wani irin cin amana ne, ranar girkina kin tasa miji a gaba kina bashi abinci, ko gidan ku ba a kaiki islamiyya bane."

"Ai kowa ya kalleni ya kalleki ya san wacece ba taje islamiyya ba a cikin mu, ko kin manta ilimi baya ɓuya a duk inda yake." Mamy ta faɗa tana ƙwace jikinta.

Baba yana zaune yana cin abincin shi.

"Mai dattin hula bai yi karatu ba ballantana mai dattin ɗan kwalli." Inna ta faɗa kamar zata kai mata duka.

"Shi ya sa mai dattin hulan ya ƙare a karen ɗan siyasa." Faɗin Mamy tana shirin barin gurin, Inna jin cin mutuncin data faɗa yasa ta kai mata mari, kafin ta sauke hannu Mamy ta mayar mata da mari biyu.

Baba da ya gama cin abinci da sauri ya miƙe, ya kamo Inna ya fita da ita Mamy tayi tsaki tana rufe ƙofar ɗakin ta.

Inna cike da mamaki take bin shi da kallo har suka shiga ɗakin shi.

"Haba dan Allah Talatu nazo ki bani abinci kin hana, naje an bani abincin kin zo kin fara ɓarnar hali kamar yanda kika saba, wai dan Allah sai yaushe zaki yi hankali.?"

"Sai ranar daka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login