Showing 12001 words to 14831 words out of 14831 words
Chapter 5 - WANI SHARRIN Hausa Novels By Jajirtattu Writers Association.docx
kai daga nan bata ƙara sanin abin da ya faru ba.
Bayan sallar isha'i Mamy ta buɗe idonta da taji yayi mata nauyi, Hajiya ta gani zaune a kusa da ita.
A hankali ta cigaba da buɗe ido Yusra Aysar suna ganin ta farka suka matsa gaban gadon suna mata sannu, a hankali abubuwan da suka faru suka cigaba da dawo mata daki daki, lokaci ɗaya ta ware ido tana ƙarema ɗakin kallo hospital ne take kwance a kai, ta shiga tambayar kanta waya kawo ta hospital.
Hajiya ta gama karantar tunaninta sannan ta dafa kafaɗarta tana yi mata sannu, Mamy ta shafa cikin jikinta taji yana nan tayi ajiyar zuciya, goshinta taji yana zafi kamar ana zuba garwashi ta rintse ido tana shafa gurin bandeji taji ta taɓa.
Hajiya ta taimaka mata ta rama sallolin dake kanta, sannan ta zauna a saman darduman tana jan charbi.
Mamy sai da ta kwana uku a hospital kafin a sallamota, lokacin da zasu shiga mota tayi tunanin gida Hajiya zata wuce da ita amman dai taga saɓanin haka, shiru tayi ta zubawa sarautar Allah ido har suka ƙarasa gidan, Mamy taji hawaye ya zubo mata ta kalli mahaifiyarta zata yi magana Hajiya ta rufe mata baki tana girgiza kai.
Suna shiga suka samu an shimfida babban tabarma da mutane a zaune Isma'il ya miƙe yana riƙo Mamy suka zauna sannan aka gaggaisa, iyayen Baba ne da iyayen Mamy Inna tana zaune rabin fuska manne da bandeji ita kaɗai sai uwar mijinta a gefenta.
Aka tattauna game da abin da ya faru kowa laifin Inna ya gani, amman Hajiya sai ta rufe Mamy da faɗa Isma'il yana bata haƙuri.
Mamy ta rarrafa gaban uwar mijinta ta riƙo hannayenta hawaye yana zuba a cikin idonta ta ce.
"Dan Allah Mama kisa Usman ya sakeni." Mutanen gurin kowa yayi tsit, an rasa wanda zai yi magana Isma'il ya buɗe baki zai magana Hajiya ta ɗaga mishi hannu.
Baba ya matsa gaban Mama yana faɗin.
" Wallahi Mama ba zan iya sakinta ba." Yana faɗan haka ya bar gurin, domin ko sama da ƙasa zata haɗu ba zai iya sakin Mamy ba.
Inna baƙin ciki kamar ya kasheta, domin taso Mama ta matsa mishi dole sai ya sake ta.
Da ƙyar Mama ta rarrashi Mamy tayi shiru sannan ta kama hannunta suka nufi bedroom ɗinta, bayan sun shiga ta zaunar da ita saman kujera ta bata ruwa tasha.
Sai da taga ta fara sauke ajiyar zuciya sannan ta zauna kusa da ita ta fara magana.
"Zaman aure ibada ne ba zaman jin daɗi ba zaman aure bauta ne ba zaman holewa ba."
"Tun da kika ji ance bauta kin san abin sai ka gamu da jarabawa iri iri, idan kasa haƙuri da tawakkali sai komai yazo maka da sauƙi, kuma ina son kisan abu guda ɗaya ubangiji yana jarabtar bayinsa wanda yake sone, dan Allah ki ƙara haƙuri akan wanda kike yi domin nasan zaman gidan Usman sai mace mai haƙuri da juriya."
Hajiya tana tsaye tana sauraron su ganin ma duk abin da zata faɗawa Mamy uwar mijinta ta gaya mata yasa ta koma, ta umarci Isma'il ya mayar da ita gida.
Mama ta daɗe a ɗakin Mamy tana kwantar mata da hankali kafin ta fito, koda ta fito babu kowa a tsakar gidan sai Yusra da Aysar suna wasa ɗakin Inna ta shiga bayan tayi sallama.
Itama ta jima a ɗakin tana yi mata nasiha kafin ta tambaye ta yara, Inna ta faɗa mata cewar ta aike su Mama tayi sallama ta tafi Inna tabi ta da harara tana jin hutar tsanar Mamy a ranta, domin idonta ne ya fashe lokacin da Mamy ta buga mata taɓarya a fuska ya sameta a ido, amman doctor ya ce babu wani matsala in sha Allah.
Lokacin da yaran suka dawo suka samu mahaifiyarsu a haka ɗakin Mamy suka nufa wai zasu zaneta, Inna ta hanasu tana ce musu ba yanzu bane lokacin da ya dace su rama mata ba su jira lokaci yana zuwa.
Gidan Ajwa.
Ta Batulu ce ✍️*WANI SHARRIN*
(Mutum ke nemowa kansa)
Channel 👇
https://whatsapp.com/channel/0029Vb6Kd5SFnSz8T3XpQ22g
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*
*TEAM JAJIRTATTUN MARUBUTA*
Marubuciyar
*RAYUWAR MU*
*MA'EESHAT*
*WANI SHARRIN*
*ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYADINA MUHAMMAD WASSALIM*
Written by ✍️
Jagabar Jajirtattu
Chapter 11
Da safe Sa'idu da ciwon kai ya tashi ƙarshema a gida yayi sallah, Ajwa na kaiwa da kawowa idan suka haɗa ido ta harare shi, lokacin data gama breakfast ta ajiye a gabanshi tana magana cike da rashin kunya.
Sa'idu da yake jin kanshi kamar ya fashe ya rintse ido yana mamakin halinta, domin ko lokacin da yake neman aurenta bai taɓa ganin wani mugun hali a tare da ita ba, hasalima kunyar shi take ji har aka ɗaura musu aure.
Yau ba taje ko ina ba shima Sa'idu haka yana kwance zazzaɓi ya rufe shi ko abinci ya kasa ci, bayan sallar magrib ya ya kalli Ajwa ya ce.
"Dan Allah ɗan taimaka mun inje gurin Mama, mu gaisa kinga yau kwatakwata bata sakani a ido ba kuma na san hankalinta na kaina." Yanda ya fara magana haka ya gama ba tare data ɗaga ido ta kalleshi ba.
Ganin taƙi cewa komai yasa ya miƙe yana bin bango ya fita har zuwa part ɗin Mama, tana zaune tana lazumi taga shigowar ɗanta mafi soyuwa a gare ta.
Sa'idu ya kwanta ya ɗaura kansa a ƙafafun Mama yana jin wani irin sanyi a cikin zuciyar shi, yana ɗaura kanshi ajikin ta taji jikinsa da zafi alamun babu lafiya a tare dashi.
Bayan tayi addu'o'i ta miƙe pillow ta ɗauko ta mayar da kanshi a kai, sannan ta haɗa shayi mai kauri ta ɗakko mishi magani.
Da ƙyar ta ringa lallaɓa shi har yasha shayin rabi yana gama sha ya fara amai, sai da ya amayar dashi gaba ɗaya sannan ya fara lumshe ido.
A daren sai da aka ƙara mishi ruwa ana gama ɗaura mishi drip ɗin ya fara bacci.
Ƙarfe goma daidai Ajwa ta shigo ɗakin bayan tayi sallama, Mama tana zaune kusa da Sa'idu ta amsa tana zabga mata harara, ganin halin da yake ciki sai da ta tausaya mishi.
Ta zauna a ƙasa ta gaishe da Mama tana tambayar mai jiki, ta bata amsa da cewar.
"Mai jiki gayi nan kina ganinshi." Daga haka tayi banza da ita, a tunanin Ajwa Mama zata tashi Sa'idu ta ce ya koma gurin matar shi ya kwana a can amman sai taga saɓanin haka, Mama tana lura da ita kuma ta gane nufinta amman tayi kamar bata gane ba, domin a tayi alƙawari a wannan lokacin wallahi sai Ajwa ta gane kurenta.
"Ni kam ɗazun dana zo neman Sa'idu ba cemun kika yi yana kasuwa ba.?" Mama ta faɗa cike da tuhuma.
Ajwa ta buɗe baki cike da ƙwarin gwiwa ta ce.
"Eh ya tafi kasuwa ne ya dawo a haka."
Mama tayi banza da ita har zuwa sha biyu sannan ta gyara mishi kwanciyya, ta ɗauko pillow da carpet ta shimfida tayi kwanciyar ta.
Tashin hankali wai matar nan mai take nufi ne?? Tana nufin a nan zamu kwana saboda masifa, miji da matarsa a hanashi zuwa inda take wallahi akwai sake, domin ba zai yiwu ba hakan Ajwa ke zancen zuci tana kallon Mama data juya mata baya.
Ƙarfe ɗaya ta bar ɗakin cike da ɓacin rai da takaici, Mama tana jin ta fita itama ta miƙe tayi alwala ta hau darduma.
Washegari jikin yayi sauƙi har masallaci sai da yaje bayan ya dawo ya shigo ɗakin, Ajwa na kwance tana bacci ya tashe ta akan taje tai sallah.
Bayan ta idar tamiƙe ta nufo gurin shi yana kwance bacci ya fara kama shi yaji motsi ya buɗe ido yana tambayar ko lafiya.
"Magana zamuyi da kai." Ajwa ta faɗa tana hararan shi.
"Dan Allah ki barni yanzu domin bacci nakeji."
"Baccinka yafi maganar da zanyi ne.?"
"Ƙwarai kuwa babu ƙarya baccina yafi mun ke dau dubu, ba wai iya magana ba." Ya faɗa yana juya mata baya.
"Ni kuma wallahi sai ka tashi munyi maganar yanzu." Ajwa ta faɗa tana komawa saitin fuskanshi.
"Wai dan mai yasa bakya da hankali da tunani? Mijin kine fa baida lafiya ya kwana ba a gurinki ba, kuma ya shigo babu kulawa babu tausasawa ballantana ki tambaye shi ya jiki, amman kin tare shi da masifar da kika saba."
"Nice masifaffiyar.?"
"Eh ko nayi ƙaryane? Ba masifaffiyar bace irin masifa da jaraba, ni wallahi sai yanzu nake nadamar auren jahila mara ilimi, mai ƙwaƙwal war kifi daƙiƙiya."
"Sa'idu nice irin jarabar.?" Ajwa ta faɗa cike da mamakin furucin shi.
"Na rantse da Allah idan baki bar gurin nan ba sai nayi miki mugun duka."
"Wallahi sai dai ka kasheni amman saika amsa mun tambayata."
"Ai ba irin jaraba kaɗai bace irin tsiya wanda bata san mutunci ba, jahilar banza da wofi."
Ya miƙe zai bar ɗakin yaji tana faɗin.
"Ga jahila can mai raba kwana da matar ɗanta, jahila ita ce mai shiga tsakanin mata da." Marin data ji shi ya hanata ƙarasa abin da tayi niyyar faɗa.
Sa'idu ya ciro belt ya zaneta sai da ya tabbatar ta daku sannan ya ce.
"Ki tafi gidanku na sakeki." Da sauri ya fita ɗakin yana zuwa part ɗin Mama ya yanke jiki ya faɗi, Mama tana zaune a parlour taji kamar ƙaran faɗuwar mutum, tana dubawa taga Sa'idu ne kwance baya numfashi.
Ta fashe da kuka ta nufi maƙotansu ko hijjab bata ɗauka ba, ƙarshe hospital suka kai shi domin duk yanda suka yi bai farfaɗo ba.
Ajwa da ƙyar ta janyo jiki ta ɗau wayarta number Inna ta kira, tana jin an ɗaga ta fashe da kuka tana cewa.
"Zai kasheni." Daga haka numfashin ta ya ɗauke.
Inna hankali tashe ta kwashi yaranta suka nufi gidan Ajwa, sun tsayar da mai napep suka ce ya jirasu yanzu zasu fito.
Basu jima da shiga ba Zainab ta fito hankali tashe ta cewa mai napep.
"Dan Allah ka taimaka mana." Mai napep ya taimaka suka fito da Ajwa zuwa hospital.
Emergency aka nufa da ita domin jini ne ya ɓalle mata, Zainab ta kira wayar Baba lokacin yana toilet yana wanka Mamy tana gyara ɗakin taji ringin, har wayar ta katse bata ɗaga ba wani kiran ya ƙara shigowa shima tayi banza dashi, an kira wayar yafi biyar Baba yayi gyaran murya Mamy ta ɗau wayar ba tare data tsaya duba mai kiran ba ta ɗaga, babu sallama Zainab ta fara jero mishi abin da ya faru Mamy tayi mutuwar zaune jin abin da yake faruwa.
Zainab tana gama magana ta yanke wayar ba tare data jira amsar da za a bayar ba, Mamy gaba ɗaya jikinta yayi sanyi a haka Baba ya fito ya sameta, ya karɓi wayarshi dake hannunta ya duba wanda ya kirata ya ajiye wayar.
Sai da ya gama shiryawa sannan ya kira wayar Inna Zainab ta ɗaga tana kuka, Baba ya tambayeta sunan hospital ɗin ta faɗa mishi, bayan ya gama wayar ya kalli Mamy ya ce.
"Haɗamun abincin in tafi dashi hospital."
Mamy bata ce komai ta miƙe ta haɗa mishi kamar yanda ya buƙata, tana mamakin mijin nasu domin abubuwa da yawa bata sani a gidan sai dai taji a gari ko kuma azo a gaya mata, ɓatan su Zainab har yanzu bai ce mata komai ba duk da cewar ta tambaye shi amman yaƙi faɗa mata abin da ya faru, tana zaune a gida aka kirata aka gaya mata lokacin da aka faɗa mata Baba yana can yana neman yaran, amman ta nuna mishi bata san abin da yake faruwa ba.
Bayan ta haɗa abincin har da ruwan zafi ta zuba a basket ya karɓa ya tafi.
Yana zuwa cikin hospital ɗin ya kira wayar Inna ya gaya mata yana ƙofar shigowa, Zainab da wayar yake hannunta ta fito ta shigo dashi.
Kwanan Ajwa biyar aka sallamota Inna gida suka wuce da ita kamar yanda Inna ta faɗa, abin da ya ɗaurewa Baba kai tsawon lokacin nan babu wanda yazo daga familyn Sa'idu, ko da ya tambayi Inna banza tayi dashi.
Bayan sun koma gida Mamy tayi sallama bayan sun gaisa ta tambayi mai jikin, babu wanda ya amsa Baba yana zaune yana tambayar Ajwa abin da ya faru yana ganin shigowar Mamy yayi shiru yana mazurai, Mamy ta miƙe mishi takarda ta ce.
"Yaro ya kawo ya ce a baka."
Baba ya karɓa ya buɗe.
"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un." Cewar Baba yana kallon Ajwa.
"Dan ubanki yaushe ki kai auren da zai sakeki." Baba ya faɗa yana zabga mata mari, ya manta da Mamy dake ɗakin.
"To munafuka zaman uban mai kike yi." Inna ta faɗa tana hararan Mamy, sai a lokacin Baba ya kalli gurin ya dafe kai Mamy ta miƙe ta fita.
Juyin duniya Ajwa taƙi faɗar abin da ya faru, ta dai gaya musu shi ya dake ta amman sauran taƙi faɗa, Inna ta rantse sai an shigar da ƙara domin duk wanda yaga irin tabon dake jikin Ajwa ya san dukkan rashin hankali akai mata, kuma ga ciki tana dashi.
Baba ya rarrasheta sannan ya ce zai tura ƴan uwanshi su tambayi abin da ya faru, Inna ta hana ta ce wallahi sai dai su zo biko wannan lokacin tunda wancan shi yaje bikon, saboda rashin sanin darajar kai irin nashi.
Ajwa ta fara zaman gida kwana biyu kamar tayi sanyi kafin ta dawo da iskancinta, bayan sallar magrib an gama girki Yusra ta kwaso abincin su ta shigo ɗaki Mamy dake zaune a tsakiyar parlour ta kalli Yusra tana cewa.
"Naji warin kalanzir."
Yusra tayi dariya ta ce.
"Gaskiya sai dai hancinki amman ni banji warin komai ba."
Mamy tayi shiru cike da mamaki domin ita warin kalanzir takeji, Yusra ta ajiye abincin a parlour Aysar ya miƙe ya ce.
"Daman yunwa nake ji kamar zan mutu."
Yusra tayi dariya tana tsokanar shi, Aysar ya ɗibo abincin a spoon har ya kai baki Mamy ta dakatar dashi ta ce.
"Ɗauko flas ɗin ruwan zafi in haɗa maka shayi."
Aysar ya fashe da kuka Yusra ta ɗauko abincin ta kai gurin hancinta, da sauri ta kawar da kai Mamy ta karɓi abincin ita ma ta kai hancinta, ta rintse ido ta cewa Yusra.
"Ɗauko mun spoon."
Yusra ta miƙa mata wanda Aysar ya ɗauko Mamy ta buɗe tsakiyar abincin, ƙasane aka cakuɗa da kalanzir aka zuba a ƙasan abincin sannan aka zuba shinkafa a saman shi, kallon kallon aka fara tsakanin Mamy da Yusra Aysar ya karɓi abincin ya juye a ƙasa.
"Allah ya kyauta."
Mamy ta faɗa tana kwashe abincin ta fita dashi.
Yusra ta gyara gurin Mamy ɗakin Baba ta shiga bayan tayi sallama, yana zaune yana cin abinci ta ajiye mishi abincin a gabanshi ta faɗa mishi abin da yake cikin abincin, Baba ya kira Inna ta shigo tana hura hanci.
Jin abin da Baba yake faɗa yasa Inna ta fara masifa da tujara, ta rantse ba ita ce ta zuba ƙasa da kalanzir acin abincin ba, Mamy ta ɗau abincin ta fita tana cewa.
"Akwai Allah."
Baba ya ɗau flask ɗin abincin shi ya bita dashi Inna tayi ƙwafa.
Tun daga lokacin Inna ta sanja salo idan tayi girki ko shinkafa mai miya ko tuwo, idan ta zubawa Mamy to ba zata zuba mata miya ba, ko kuma idan ta zuba mata tuwo sai ta kaɗa lalli a matsayin miya ta zuba mata, Mamy ta fita sabgarta ta rungumi sana'ar ta da kuma ƴaƴanta, har zuwa lokacin da cikin ta ya isa haihuwa Ajwa cikinta ya fara fitowa, Baba ya sai filin dake bayan gidan shi ya shigo dashi ya sanja ginin gidan gaba ɗaya yanzu kowacen su two bedrooms take dashi, da toilet kitchen kuma a bakin ƙofa sannan kuma ya ƙara gina ɗaki ya kamar sauran ya rufe gidan yasha siminti, tun lokacin da Inna taga yayi wannan ginin ɗakin ya rufe hankalinta ya tashi domin ta san aure yake shirin ƙarawa.
Ƙanwar Inna ta zo daga garinsu da yaranta guda biyu, itama iskanci take zubawa kamar gidan ubanta, Mamy babu ruwanta da shiga sabgarta.
Yusra ta dawo daga makaranta Aysar ya shigo gida da gudu yana mata dariya, itama ta biyo bayan shi tana cewa.
"Wallahi idan na kama ka sai na zaneka."
Tana shigowa gidan taji tayi karo da mutum, ko kafin ta ɗago taji ruwan mari a fuskarta, tako ina ta faɗi tana kiran sunan Mamy.
Yaya makomar cikin Ajwa? da gaske ne aure Baba zai ƙara? Idan ma auren zai ƙara Inna zata barshi? Yaya zaman ƙanwar Inna a gidan? Mai yasa Baba ya kasa ɗaukar mataki a kan Inna? Maine ne makomar Khadijah A'isha Zainab?
Yanzu za a fara chakwakiyya iya chakwakiyya, labari mai cike da tarin darasin rayuwa makirci kishi hassada mugunta barkwanci, kar in cika ku da surutu duk mai buƙatar cigaba zai biya 500 only in saka shi a paid group, idan na gama typing 700
Account number 👇
Sa'adatu Ibrahim opay
8138098887
Shaidar biya
08138098887
Ta Batulu ce......... ✍️