Showing 1 words to 3000 words out of 14779 words
🕊️🕊️ *Hammad zairah*🕊️🕊️
*Boss lady*
🦅Mikiya writer's asso.....
🔞Ki watsar da na banza ki dau na kirki.
Please idan zuciyar ki ba mai ƙarfi bace kada ki fara sister
*Labari ne mai bangare uku*
*Meeyrah*
*Hammad*
*Jannat*
*Littafi dai Free ne*😜
*Dedicated to nimcylove*
1️⃣✅3️⃣
Katsina 2pm
18 nov 2024
Yanayin garin ya yi dai dai da irin lokacin nan na sanyi saboda yadda yanayin garin ya yi hazo hazon na sanyi kowa ka gani lokacin da rigar sanyi jikin shi wasu ma harda first mas sun rufe fuska saboda yanayin garin' wanda a wannan lokacin kuma duƙe ta tana aikin da ta saba Kuka take mai cin rai sosai kamar zata shiɗe ta kalli ƙannen nata a karo na ba adadi ta furta innalilahi wa'innailahir raji'un Allah kai mana ɗauki ƴar ƙaramar yarinyar ta matso kusa da ita ta ce "Anty Mereeh please am sorry in sha Allah komi zai zo mana da sauƙi mu rinƙa addu'a Allah zai kawo mana ɗauki kada ki damu da abin da baba sabo yai mana in sha Allah asiri zai tonu mu bar ma Allah kawai"
Aliyu kanin Mereeh ya miƙe ya ce "Aunty bari na tafi zuwa anjima zan dawo ki kula da su yai gaba abin shi"
Mereeh ta tashi wani ɗanɗumamen tuwo ne kulli uku, ta sa ɗan gawayin ta ɗumama su'ta malla ma kowa nashi ta samu wata tsohuwar kula ta sama kanin nata a kula ta maida ta aje gefe, wajen karfe uku na rana sai gashi da farin ciki a fuskar shi kamar wanda aka biya ma maka ta fito tare da mai sannu da zuwa ya miƙa mata wata leda ta amsa tare da faɗin mai muka samu friend ba dai ka gajiya da hidima da auntyn ka ko??
Murmushi ya yi tare da sosa ƙeya yace"Aunty uhmm dako nayi a can tasha shine sai na siyo mana kofin shinkafa sai ɗan barkonon da na siyo a dafa maci mai da yaji wallahi bana san muna zama da yunwa ba ma Kamar taslim ita da take ƙarama"
murmushin dake ƙara ma fuskarta ƙyau tai mashi tare da faɗin Allah ya dafa mana, ta aje mai towon da ta aje mai tunda rana duk da haka sai da ya tasa su ita da taslim suka ƙara ci.
Innalillahi Allah mun tuba ka yafe muna ya Allah' ta kuma jawo taslim jikinta Wadda take kwance shame_shame kamar gawa ta ce "Aliyu Please ka bari idan naje gidan baba sabo ɗin abinda muka samu sai a kaita asibitin"
"Kinsan dai baba Sabo bai da mutum ci ko kaɗan am nasan ko da munje neman taimako nasan ba bamu zai ba, amma tunda kin dage sai ki tafi ya rungumo taslim ɗin ita kuma ta ɗauki hijabin ta baƙi wanda cikin hijabin nata shine mai ɗan dama tana fita ta samu napep ta hau bai sauke ta ko ina ba sai ƙofar gidan baba sabo, daidai lokacin kuma ya fito sai mita yake an bata mashi rai"
.........
"Don Allah sameer kada ka aikata min haka kai kasan kaine aure na na biyu idan kai mun haka ka cuce ni ka cuci rayuwata am idan wani abu na maka don Allah ka yafe mun in sha Allah ba zan kuma ba ka taimaka min!"
Ƙafarshi da ta riƙe ya fisge ya falla mata mari ya ce" idan hauka kike to ki dawo haiyacin ki banza mara hankali kuma ki tafi gidan ku nasa ke ki saki ɗaya" wani irin takaici ne ya kamata ta Marasa mai zata ce mashi yanzu illa bin shi da ido dake, wayar shi ya ɗauka tare da kiran beb din shi daman ita tace ala dole sai ya saki matar shi ko zata aure shi kuma ya cika mata aikin da tace tana so cikin farin ciki da murna yake sheda mata ya ai watar da abin da take so, sulalewa tai ƙasa tama rasa mai zata yi zaune suke ƙalau amma yau rana ɗaya ita ce sameer zai ma haka ta ma rasa wane irin tunani zata ai watar kanta ya ƙara ɗaukar zafi kwanciya tai bakin gado Cikin zuciyarta ta na faɗa mata kada ta tafi ta tsaya ƙila ya maida ita ɗakin ta, wanka ta tashi tai tare da ɗaura indomi domin ta sama ma cikin ta abincin don yunwa take ji ba kaɗan ba"
........sameer ban ɗauka cewa da gaske zaka iya rabuwa da matar ka ba yanzu!
ƙara damke hannun ta ya yi cikin nashi ya mata murmushin gefen baki tare da faɗin uhmm ke kinsan ina san ki har cikin jinin jikina ina jin san ki, so ba abinda zaki ce na maki na kasa i love You so much nimrah.
Wani daɗi ne ya ƙara kama mata zuciyarta Saboda abinda ya faɗi mata ko ba gaske bane tabbas taji daɗin abin da ya faɗa' suka cigaba da firar masoya abin su bai koma gida sai after 10pm dai-dai lokacin kuma jannat tana zaune kan darling table tana jirar dawowar sa ƙarar buɗe get ne yasa ta mike da sauri ta fito don tarar shi ita ta ma manta da abin da ya faru ɗazu!
________________________
Baffa ina ƙwana? Cewar matashiyar yarinyar da ke duƙe gaban ɗan madaidaicin mutum.
Dafa kanta ya yi ya ce" alhamdulilahi fatsuma idan Allah ya kaimu anjima ina san na tafi jeji ɗebo magungunan in sha Allah"
Baffa ina so na bika nima.
a'a fatsume kada kice haka kinga Yanzu ma kina da aikin ki da zaki ki hakuri idan na ɗebo dai kin daka min su.
Wacece fatsume
Malam habu bafulatanin asali ne fari ne dogo yana da hanci yana da mata maryam mace kamula mai san jama'a suna da yarinya ɗaya fatsume suna nuna mata so da kauna' fatsume tana da shekaru goma sha uku Allah ya ɗauki ran maryam sun sha kuka ita da baban ta har kuma yau bai ƙara aure ba Saboda yana gudun Kada ya auri matar da zata cuci mai ƴar marainiyar ƴar sa, yana kiwon shanu kaji awaki kuma yana bada magani..... fatsume tana da tarbiyya sosai ga San mutane kamar uwar ta, tana da ɗan ilimin zamani na mahammadiya ma akwai dai-dai misali.
Wannan shine takaitaccen tarihin fatsuma..... baffa ya ɗauki ƴar jakar shi da yake zuwa jeji ɗibar magani ya tafi ita kuma ta fara aikin gida!!
.....Lafiya na ganki anan??cewar baba sabo.
Durkushewa tai ƙasa tana kuka tare da faɗin don girman Allah baba sabo ka taimaka mana ba don mu ba "taslim ce ciwon ta ya tashi gashi bamu da kuɗin zuwa asibiti"
A tsawace baba sabo ya ce" ikon Allah wai don Allah mai kuke san maidani ne haba nace ki fidda miji ki aure amma kin ki saboda kina samun abinda kike so shi ne dalilin da kika ki aure"
A'a baba wallahi ba haka bane mudai yanzu muna neman taimakon kuɗin da zamu kai ta asibiti don Allah a taimaka mana da ko nawa ne..
Wani irin mungun tsaki yaja tare da miƙa mata dubu biyu' tai mai godiya tare da mikewa ta nufi titi don tarar abin hawa..
Buge ta ya yi da hannun shi na hagu tai sauri ta duƙa tana mai dafe bakin ta da hanci jini tagani a hannun ta da sauri ta shiga ɗakin ta bayi ta faɗa tana mai kuka tana wanke bakin nata....
Ammi ammi ammi tana ɗan jijjigata tana ƙwalla ta ce ammi komi ya yi farko zai yi karshe ina ji a jikina ɗan uwana na raye bai mutu ba!
Ƙwallar ta ta share karo na uku kenan da take share shi ta riƙe hannun ƴar ta ta, jidda nikai na ina jin haka amma kuma bazan tabbatar da hakan ba har sai nagan shi a gabana.
Mai martaba ne ya shiga cikin ɗakin nata jidda ta gaida shi tare da barin wajen don su gana da ita ya ce" Allah subhanahu wata'ala ya halicce mu ne ba don komi ba sai don mu bauta ta masa Akwai ƙaddara mai ƙyau da akasin haka idan muka karba hannu biyu sai Allah ya dube mu da idon rahama kullum ina ƙara faɗa maki halima kidaina wannan kukan ki ta addu'a har Allah ya bayyana na mana shi....
ta ƙwanta kan kafaɗar shi ta ce wallahi ko naji a Cikin rai na na dangana sai kuma naji zuciya ta tai rauni narasa mai ke damuna.
Baki ya ƙara bata tare da ƙwantar mata da hankali..
........Ta mutu ta mutu aunty mereeh tun da kika tafi ba daɗe wa ba Allah ya mata rasuwa haka yake sheda mata yana kuka!
Duƙawa tai ta rufe mata ido tana mai mata addu'a Allah ya jikanta' shikenen yanzu su biyu suka rage daga ita sai kanin ta Aliyu baba da mama sun yi hatsari a motar kuma ba abinda aka fitar komi ya kone a motar yanzu kuma gashi taslim ta rasu ta barsu, kuɗin da baba sabo ya bata akai mata hidima dashi don kaita gidan gaskiya sun sami makota suka taya su zaman makoki, baba sabo yazo masu ta'aziya ranar da akai addu'ar uku yazo masu da rabin tiyar dawa wai suyi towon dawa, zai tafi ne Aliyu ya bi bayan sa don su yi magana!!
Tom lafiya kuma "Ali ka biyo ni nan?"
Uhmm daman baba ina san kuɗin gadon mu a ɗan bamu wani abu cikin gadon mu idan ba damuwa.
Kai dalla can banza kuɗin gadon ku daman kuna dashi ne? Bana san sha shan ci.
Ɗaga murya Aliyu ya yi ya ce" haba baba sabo kuɗin mu hakkin mu ai suna gunka mun nema ka bamu hakkin mu amma kana Magana maganar banza idan ka cinye ne ai sai ka faɗa musan mai muke ciki........ mutanen da ke gun ne suka taso suna ma Aliyu magana kan ya yi hakuri amma ina zuciya tazo wuya ya ce wannan macuci ne ya hana mu hakkin mu yana ganin muna wahalar rayuwa amma ko in kula damu ya ki bamu hakkin mu..
Limamin Masallacin ne wanda dashi ake zaman ya ce" baba sabo tabbas cin dukiyar maraya ma bai da amfani idan har da gaske yaron nan yake ka taimaka ka basu hakin su tun kafin Allah ya tambaye ka, nan dai ya fara mai wa'azi, amma ina wanda ya yi nisa bai jin kira"
Gado na ce na cinye daidai lokacin kuma wani daga cikin abokan Aliyu ya ce ya faɗa mata tafito ta ce" haba Aliyu ba nace kada ka kara mai wannan Maganar ba idan har kana jin magana ta don Allah ka kyale zancen nan bana so' shi da yaji yaje can zamu haɗe Inda bashi taja hannun Aliyu suka shiga cikin gidan"
Tafe yake a hankali yana dibar maganin shi sannu a hankali duk ya dibi ganyen da yake so, wani mutum ya gani kamar mai lafiya amma irin kayan da ya gani jikin yasa ya tabbatar mai da ba Lafiya ba ya isa gare shi ya ce bawan Allah, amma ina shi dai sai bin shi da ido yake....
Littafin nan free page ne idan naga ruwan comments zan cigaba daga inda aka tsaya
Boos lady taku ce
Mai san magana dani sai ya min magana a 08160647868
🕊️ *hanmad zairah* 🕊️
*Boss lady*
Dedicated to nimcyluv
🦅mikiya writer's asso....
4️⃣🔸5️⃣
A ƙwana atashi ba wuya a gun Allah yau har taslim tai ƙwana bakwai da rasuwa jin gidan suke ba daɗi daman wani lokacin ita ce mai sasu dole sai sunyi magana yanzu ko bata, Aliyu ya miƙe tare da faɗin Aunty na bari na ɗan fita...
Kai ta gyaɗa mai shi kuma ya fita wajen ƙarfe 12 na rana wata ƙawarta tai mata sallama da murna a fuskar ta ta tare ta suka gaisa tai mata gaisuwa lokacin da akai rasuwar basu nan sun fita ita da su mummyn ta hutu, saboda ita ta cigaba da school mereeh ce dai ba halin ci-gaba ruwa ta ɗebo ma a kofi cikin tausan ta ta furta ƙawata kuma wai kawun naku bai baku rabon na ku ba??
Murmushi tai mata saboda ita har mantawa take ma da wani baba sabo, uhmm hanan wannan kuma ai sai dai kawai mu bar shi da Allah saboda ko lokacin nan sai da muka mashi magana ya ce ya cinye mun bar ma Allah!!
Oh my god hanan ta furta tare da faɗin am sorry mereeh komi zai dawo dai-dai.
kuka tasa ta ce" ina maganar dai-dai hanan mun rasa mama mun rasa ba ga taslim ita ma ta tafi ta barmu, wannan duniyar bana jin daɗin ta ji nake kamar na kashe kaina na huta😭😭"
Dafa mata kai tai tare da bata hakuri sai da ta tabbatar da ta hakura sannan ta ce bani account ɗin ki ko ba yawa nasa maki.
Saboda buƙatar kuɗin yasa ta bata nan take ta tura mata dubu ɗari biyar ta ce ba yawa tai mata sallama ta tafi gida.
Ko da Aliyu ya dawo gida ya tadda abin farin cikin nan yaji daɗi sosai nan ta ce ya koma makaranta saboda sun yi jarabawar shiga aji na na huɗu a sakandire ya ji daɗin haka kuwa, kasuwa ta tafi wata tsohuwar firiza ta siya don ta riƙa sai da ruwa sobo da kunun aya suga ko za'a dace...... Wajen ƙarfe 8pm suka ji Kwankwasor ƙofar gidan nasu Aliyu ya fita don ganin su waye, mota ce cike take da kayan abinci wanda ya buga ya ce "sako ne daga hanan ta ce akawo nan gidan!"
Da sauri Aliyu ya basu hanya suka dinga shiga da abincin cikin gidan alhamdulilahi kawai mereeh take maimaitawa buhun shinkafa uku' wake buhu ɗaya taliya katan biyar sai jarkar mai da manja ya miƙa mata wani leda ta amsa tare da mai godiya suka tura gidan hamdala kawai suke ita ɗan uwan nata suna shiga cikin ɗakin ta buɗe kuɗi ne naira dubu 50 ta wata ƙaramar takarda an rubuta..
"Ƙawata kiyi hakuri da wannan su mummy ne suka baki saboda na faɗa mata halin da kuke ciki ga kuɗi nan sai ku cefane"
Ƙwallar farin ciki ce ta mamaye ta ta furta"Aliyu kagani ko Allah mai rahama mai jin ƙaine Allah mun gode maka"
Rungume Aunty mereeh ɗin ya yi suka sa kukan farin ciki..
Jalingo ƙauyen malam idi
_______
Yaro baka magana ne?
Shi dai sai bin shi yake da ido don bai san mai zace ba, ya kama hannun shi suka fito cikin jeji gida suka nufa inda ya iske fatsume har ta gama masu komi na aikin gida sallama ya yi.
Da sauri ta fito don tarar baffan nata sai kuma tai turus ganin shi da kaɗo suna tare ta ce" baffa sannu da zuwa"
Murmushi ya mata ganin irin kallon da take bin kaɗo dashi ya ce" fatsuma shimfiɗa mana tabarma" shimfiɗa wa tai tare da basu ruwa a kwanon sulba ta ɗauko fura ta aje nan ma ta koma gefen su ta zauna"..
Jannat kiran ƙawarta tai tare da laburta mata abinda ya faru tsakanin ta da sameer salatı tai ta nuna mata ırin damuwar da ta shiga ciki da suka gama wayar ne ta taɓe baki ta ce Allah ya kara sauran saki ma da idasa mata ta tashi ta shirya don taje gidan jannat din...
Sameer ne ya fito ya zo inda take ya ce wai baki da gidan uba ne da ba zaki tafi ba ne komi??
Don Allah ka.. Mai dani ɗaki na ba don ni ba ka taimaka min.
Wani banzan kallo ya watsa mata ya ƙyalƙyale da dariya ya ce saboda gidan tsoho babu dadi kike tsoran tafiya kumi? Na naki daga nan zuwa jibi ki bar min gida duk wani abu naki ki tattara ki bar min gida ya fita cikin gidan rai ba ce..
Cikin ƙankanin lokaci ta Isa gidan jannat yadda ta sameta Abin ya mata, tai taba baki kan ta hai hakuri komi zai dawo dai-dai amma cikin ƙasan zuciyarta ba haka ba da ta duƙa a kan cinyar ta tana kuka ita kuma dariya take mata harda gwalo suna cikin wannan yanayi ne sameer ya dawo gidan gaisawa sukai da ƙawarta ta kamar ba abin da ya faru tsabar munafunci irin na maza harda matsawa kusa da jannat tare da faɗin beb baki mana abinci bane??
Da kallon mamaki ta bishi don ya daure mata kai abin' cikin zuciyar ta kuwa tunani take kila ya maida ita ne har wani tsallen daɗi take ji ta furta mai yanzu nake san wai na ɗaura mana kaina ke ciwo!!
Ai tunda ga ƙawarki sai ta girka mana kin huta.
Ƙawarta sai ta shiga ruɗu to ko daman karya jannat keyi mata saboda Yadda taga abin ya koma mata wasan kwaikwayo..
Mai martaba ne zaune kusa da matan nashi sun sashi tsakiya ya ce" fulani a ƙalla yau wajen kwanan wata da bacewar yaron nan amma banji kin furta min komi ba". Wacce aka kira da Fulani kanta a ƙasa ta ce Allah ya gafarce ka ranka ya dade ai min hakuri wallahi abubuwan ne sai a hankali duk lokacin da nazo maka zancen sai na ƙasa Saboda ina jin san yaron nan tamkar nice na haifeshi har cikin ran mai martaba yaji dadin abinda tace don fulani karshe ce wajen iya tsara zance..
Hakuri taba abokiyar zaman nata ita ma bata nuna mata komi ba, daga